Advertisements
Chapter 7 Reading KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA

Author :  NANA HALEEMA Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 28

18K to 21K   out of 83.2K words

nema?."
"Omar ta ya zan sani? A gaban ka fa ya kira ni."

Omar ya ce, "wanne lokaci zaki ba shi?."
"Bana ce ba." Ya kalli Didi cikin bada umarni ya ce, "ki faɗa masa yazo jibi, jibi
juma'a kenan, ina gida nan zan so na zauna a tatauna dani. In da tsiya ya zo gidan
ya tarar, in arzuƙi ne ya kawo shi ana yi masa maraba." Tayi murmushi ta ce, "to
babban Yaya." Jin abinda tace sai yayi murmushi amma bai ce komai ba.

"Kai yaushe zaka yi auren ne?." Ya ɗan juya idanunsa ya ce, "kwana biyu meyasa ki
ke yi min zancen aure ne?." Tana murmushi ta ce, "ai ka kai ka yi ɗin ne Omar,
santalelen saurayi kamar ka ga kyau ga kwarjini ai dole ayi maka zancen aure."
"Ni wallahi bana kawo zancen aure a raina ko kaɗan."
"Ko me yasa?."
"Sai na fara aurar da ke" ya faɗa yana miƙewa tsaye.

Ƴar dariya tayi ta ce, "Ko kuma ni na fara aurar da kai ba." Bai yi magana ba ta
miƙe tsaye tana kallon sa duk da ya kere mata a tsayi sosai ta ce, "burina naga
kayi aure ka haifa mana mai sunan Mama Omar, duk macen da ta same ka zata yi sa'a,
a haka ne ake kallon ka a baibai amma ni da na san ka, na san sa a tana tare da
wacce zaka aura, musamman in ka ɗauki nasihar da nake yi maka a kullum."

Fuska sake yake kallon ta ya ce, "Yanzu in aka aure ni ba a yi sa a ba kenan?."
"Eh to, kusan hakan zan ce." Yayi murmushi mai sauti ya kalle ta ya ce, "ina zuwa."
Fita yayi daga gidan gabaɗaya. Kasancewar unguwar akwai duhu da ya fito ƙofar gidan
daga wajan gidan su ne kawai mai haske sauran wajan babu haske.

A hankali yake takawa yana jiyo magana na tashi ana daga inda yake nufa,
muryar maza ya ji suna cewa, "hmm to Omar da Aisha meye basa aikatawa, kai a banza
ta kai yanzu bata yi aure ba?. Wannan ingarmar namijin da take kwana dashi waje
ɗaya ta tashi ba dole mugun abu ya faru ba."

Ɗaya daga cikin su ya ce, "wai don Allah da gaske ku ke?." Na ukun ya ce, "to kai
gani ka ke wasa ne? Baka ganin yaron ko kula mutane baya yi saboda ya san iskancin
da yake yi?. In da ma ace iya dabancin ya tsaya da sauƙi, to har da lalata da ƴar
uwarsa. Ai ba a banza ta kai wannan shekaru babu aure ba, tana samun duk abinda ƴa
mace take samu a gidan mijinta a wajansa. Kai baka ganin da an zo neman aurenta sai
a gudu ba? Wannan mugun abun da suka binne ake tonowa."

"Kuma fa ashe gado ya yi, ubansu tantirin ɗan iska ne tsohon ɗan giya. Ai barewa
baza tayi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba, nan gaba zaman unguwar nan sai Omar ya hana
mu."

Omar yana jinsu ya runtse idanu cikin ɓacin rai da ƙunar zuciya, ya koma da baya ya
hangi yaransa a gefe yayi musu alamun da su yi shiru kar su yi magana su zo inda
yake. Nuni ya yi musu da kowa ya kama mutum ɗaya a cikin ƴan majalisar da suke
gulmarsu. Cikin sanɗa suka ƙarasa inda suke sai caraf ko wanne ya riƙe mutum ɗaya.

Omar ya tako ya bayyana a gabansu ransa a ɓace sosai duk suka kalle shi
cikin firgici da tsoro. Alama yayi musu da su sake su, dukkan su suka sake su ya
bisu da kallo dan dukkan su manya ne a haife zasu haife shi. Babu wanda yayi
ƙoƙarin miƙewa a cikin su saboda duk sun tsorata matuƙa suna kallon Omar. Abin ka
da wanda yake gulmar wani kuma ya kama shi, wanin ma kuma irin Omar."

Tsakiyar su ya shiga ya zauna tare da ɗauko ƙaramar wuƙa a ƙasan takalmin yana
shafa ta a hankali ba tare da ya kalle su ba. Duk sun ruɗe, jikinsu ya fara ƙyarma
cikin tsoro. Zaman da ya yi a cikin su yafi komai tsorata su, ga wuƙa kuma a
hannunsa. Ajiyar zuciya Omar ya yi, ya daidaita kansa kana ya ce, "Ku maimaita
hirar da naji kuma yi yanzu." Tsit suka yi kowa ya kasa cewa komai, Omar ya kalli
ɗaya daga cikin su sai kawai ya zube a ƙasa saboda tsoro jikinsa na rawa sosai.

"Ku maimaita na ce" ya sake faɗa a kausashe yana kallon su. Nan ma suka yi shiru
ya girgiza kai ya ce, "kenan kun san ba daidai ku ke faɗa ba ko? Shikenan, tunda
baza ku yi magana ba bara na saka a saka ku magana."

Kallon na gefen sa ya yi nan take suka taho da wuƙa suka ƙaraso wajan. Omar ya sake
kallon mutanen yaga duk sun tsorata gasu kuma manya dan suna cikin manyan unguwar.

Ɗaga musu hannu yayi alamun kar ya ƙarasa inda mutanen suke ya ce, "Maganar da ku
ka faɗa a kaina da Didi naji kuma zan ɗauki mataki akan hakan, abinda ya saka bazan
iya yi muku komai ba kun girma iyayen wasu ne ku. Ba dan ina jin tsoro ko kunya ba,
sai dan haka na yi niya."

Bash ya ce, "Damisa ai in babba bai ji tsoron hawa jaki ba, jaki bazai ji kunyar
kayar dashi ba."
"Allah ya baka haƙuri" ɗaya a cikin su ya faɗa yana kallon Omar. Omar zai yi magana
wani matashin saurayi ya ƙaraso wajan ya ce, "Baba lafiya?."

Omar ya kalle shi ya kalli wanda ya kira da Baba bai ce komai ba yana jira ya ji ne
zai ce. Murya na rawa Baba ya ce, "lafiya lau." Yaron ya ce, "lafiya naga wannan a
tsakiyar ku da wuƙa a hannunsa?." Omar Bash ya kalla yayi masa alamun da a kawo
yaron, ai kuwa suka damƙe shi aka ɗukar dashi a kusa da Omar.

Cikin takaicin da ya ke ji a zuciyarsa ya fara tsinke fuskarsa da mari cikin
tsananin fusata. Ya jawo rigarsa ya kalle shi ya ce, "ku hana iyayen ku yin magana
a kaina da rayuwata, in ba haka ba wallahi duk abinda nayi musu ku yi kuka da kan
ku." Ya sauke numfashi cikin baƙin cikin da yake ji a zuciyar sa ya ce, "ina yiwa
mutum alfarma sau ɗaya tak a rayuwarsa, to na yiwa iyayenka, na ga girman su duk da
basu duba girman su ba suke faɗar ko wacce magana a kaina, ina gargaɗin ka da su
kansu akan abin yazo ƙarshe daga yanzu, In hakan ya sake faruwa bazan ɗagawa kowa
ƙafa ba" ya faɗa yana sakin yaron tare miƙewa zai bar wajan.

"Me ka ke taƙama dashi?." Yaron ya faɗa yana kallon sa." Juyowa kawai yayi bai ce
komai ba ya juya ya bar wajan, inda zai je ɗin ma ya fasa dan in ya tsaya wallahi
zai iya yiwa yaron kaca-kaca da fuska kawai ya bar wajan yafi alkhairi.

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️*Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t

*Book 1*
*P 06.*
Duk abinda ya faru a kan idanun Nayla da Salma da suka ta dawo daga unguwa
aka ajjiye su a farkon layin suka shigo a ƙasa. Sai da suka tabbatar ya shiga gida
sannan suka shiga wajan Hajja Salma tana faɗin, "Shi wai wannan bawan Allah babu
abinda ya iya sai mugunta?." Hajja ta kalli Salma ta ce, "wa kenan?." Nayla ta
ƙaraso ta zauna ta ce, "Waye in ba wannan basamuden na gidan Didi ba, Hajja kin ga
yadda ya kama fuskar wani yaro yana mara kamar Allah ya aiko shi?."

Hajja ta ɗan yi tsaki ta ce, "wai a cikin ku Hauwa'u da Salma wacece take son
Ummaru ne?." Salma da take shan ruwa sai da ta ƙware jin abinda Hajja ta ce ruwan
ya dawo mata ta fara tari. Nayla ta kalle ta ta ce, "Sannu Sis, dole ki ƙware fa,
wannan kalami na Hajja sai ya saka zuciyarka ta daina aiki na wucin gadi. Wai so,
Allah na tuba meye abin so a wannan mutumin? Sai dai hasken fata."

Salma da ta dawo daidai ta kalli Hajja ta ce, "So fa Hajja?." Hajja ta kalle su ta
ce, "bai kai a so shi ɗin bane ba?." Nayla ta taɓe baki ta ce, "ya kai, amma a
wajan ƴan jagaliya kamarsa. Da ilimin mu da komai Hajja ki faɗi wannan maganar a
kan mu? Wannan ai kamar babban saɓo ne wallahi."

Hajja ta ce, "to tun ɗazu ku ke maganarsa har yanzu kun kasa dainawa, wanda ake so
shi ake yawaita magana a kansa ai." Nayla ta kalli Salma suka ƙyalƙyale da dariya
Nayla ta ce, "Shi tantirancin sa ne ya saka mu ke magana a kansa, kuma abin
alfaharin sa ne ma mata masu class kamar mu suna maganarsa. Batun so kuma Allah ya
tsari gatari da saran shuka, Allah na tuba ya wuce na zaunar dashi na koya masa
karatu?. Wai a taƙaice ma yayi makaranta kuwa? Dan irin su wallahi basu cika karatu
ba, addini ma gararar su yake yi."

Hajja ta murmusa kawai bata ce komai ba Salma ta ce, "to ina ya ga
lokacin yin wani karatu kullum ana yawo da wuƙa? Kuma wallahi laifin ƴan unguwar
nan ne da ba a samu wani shegen da yafi shi hauka ya koya masa hankali bane shiyasa
yake abinda ya ga dama. Haka kawai ya kama mutum yana zabga masa mari ga iyayensa a
zaune." Hajja ya ce, "na faɗa muku Omar bashi da matsala, kuma tunda ki ga haka
ɗayan biyu ne, in ma an zagi mahaifiyarsa ko kuma an yi magana mara daɗi akan
Aisha."

Hajja ta kuma cewa, "kun san mutanen hausawa da wani banzan tunani, tunda Aisha
bata taɓa aure ba kuma suna zaune gida ɗaya da ƙaninta shikenan ake musu kallon ƴan
iska. Majalisar maza ake zama ana dasa gulmar su wai neman junan su suke yi." Nayla
ta buɗe idanu ta ce, "a'uzubillahii! Kaji wani jahilci don Allah."

Hajja ta ce, "Wannan maganar ba baƙuwa ba ce ba a unguwar nan, sau da yawa za a zo
neman aurenta amma da wanda yazo neman auren ya
tafi shikenan bazai dawo ba an je an zuga shi an ce ai tana bin ƙaninta suna
lalacewa a gida. Jinkirin aure bashi da daɗi, dan babu yadda zaka canja ƙaddararka
ne amma wanda yake cikin irin yanayin shi kaɗai ya san halin da yake ciki. Aisha
kam tana ganin jarabawa, wanann ya zo sai an fara abu kamar na kirki sai a watsar,
gobe ma wani yazo shima ya gudu."

Salma cikin tausayi ta ce, "Allah sarki Didi! Amma duk masu faɗar wannan kalami mai
munin tsiya ba su yi mata adalci ba, kuma sai Allah ya yi musu hisabi."

Hajja ta ce, "tunda ku ga yana wannan hukuncin daƙyar ba maganar yaji suna yi ba,
dan shi zaki iya zagin shi ya wuce ki amma kar ki taɓa Aisha, sonta yake kamar ya
bata ran da yake dashi ta haɗa da nata, saboda Aisha itace kamar uwarsa da ubansa."

Nayla ta ce, "gaskiya indai haka ne yayi daidai wallahi, in ma ƙara ya kai su gaban
hukuma ai daidai ne. Wannan wanne irin ƙazafi ne mai baƙin muni haka?." Salma ta
dawo kusa da Hajja ta zauna ta ce, "Hajja to ina ƴan uwan su ne?." Hajja ta kalli
Salma ta ce, "ke bacci nake ji, in Allah ya kaimu gobe na baku labarin asalin su
Aisha da Ummaru." Nayla ta ce, "kai Hajja ki faɗa mana yanzu mana." Hajja ta harare
ta ta ce, "yanzu da nace wata tana sonsa cikin ku sai kuka ce a'a, in ba so ba meye
na son jin labarinsa?."

Nayla ta gimtse fuska ta ce, "Hajja ki daina kawo batun nan ko da wasa don Allah,
kawai muna so mu sani ne ba dan wai wani abun ba. So ki ke Daddy yaji labari ya
zane mu?" Ta faɗa tana kallon Salma suka ƙyalƙyale da dariya. Hajja tunda taji sun
ce Daddy ta san mahaifin Salma suke nufi babban ɗanta kenan. Hajja ta ce, "ko shi
daddyn in ɗaya tana son Umar ɗin ina ruwansa?."

Salma ta wara idanu ta ce, "Maza ki yi istigifari Hajja, dan wannan babban saɓo
ne." Hajja tayi dariya ta girgiza kai ta ce, "Ni ko labarin gidan Daddyn ma baku
bani ba, kun shigo kuna yi min hirar saurayin Hauwa'u" ta faɗa tana kallon Nayla da
tsokana.

Nayla ta ce, "Hajja ki daina cewa saurayina, saurayina yana Kaduna ba a Kano yake
ba. Sannan ba sunana Hauwa'u ba Hawwa nake, ki dinga cire u ɗin nan don Allah."
"Bazan cire ba, Hauwa'u zance, Kuma na faɗa Umar saurayinki ne." Nayla rai ta ya
ɓaci amma ganin Hajja tsokanarta take yi sai tayi dariya suna hira da Salma dan
Hajja ya shiga ɗaki.

*Kaduna.*


Abiy da Mama a zaune a falo, Abiy yana cin abinci Mama na gefensa ganin ya kammala
cin abincin sai ta kalle shi ta ce, "ɗazu Nayla ta kira ni, na ce mutanen Kano ya
Hajja." Abiy ya murmusa ya ce, "nima daga dawowa ta gidan nan zuwa yanzu sau biyar
ta kira ni, Ai naga alama tana son zama wajan Hajja sosai."

Mama ta yi murmushi ta ce, "itama Hajjan tana matuƙar jin daɗin zama da Nayla ai,
kasan Nayla ba dai hankali da iya magana ba." Abiy ya murmusa kawai bai ce komai ba
kafin ta ce, "Kwana nawa ka bar ta yi ne?."
"Sati ɗaya."
"Haba Abiy, ina laifin ka barta tayi sati uku tunda dai ta kammala service ɗinta
kuma baka samar mata aiki ba. Tahzif ɗin da ta shiga ma ta kammala tana gida a
zaune. Hajja na son zaman ta a can, ita take ɗauke mata kewar mahaifiyar ta da ta
rasa take kallon Nayla tamkar Bilkisu."

Abiy ya kalle ta ya ce, "Bana son zaman ta a Kano ne gabaɗaya, kar ki manta abinda
ya so faruwa da ita a shekarun baya, ba dan Allah ya kiyaye ba da an cutar da ita.
Tun daga nan zaman ta a Kano ya gama fita daga raina, da ina da iko ma ko kwana
ɗaya baza tayi a can ba, to ban isa na rabata da dangin mahaifiyarta da suke can
ba. Kuma suna tsananin son Nayla da ƙaunar ganinta, dole ne na barta ta je gare
su."

"Na sani Abiy, Amma ai komai ya wuce kuma yanzu Nayla ai tana da hankali da wayon
da abinda ya faru a baya bazai faru yanzu ba sai dai ƙaddara. Hajja tana sonta, tun
farko ta nuna maka ka bar mata Nayla kawai dai ka ƙi ne. Kuma suma sun yi mana kara
a kanta sosai."

Abiy ya ce, "har abada bazan iya barwa kowa Nayla ba, ke bama Nayla ba kaf ƴaƴana
biyar har Nayla shida bana tunanin zan iya barin su su je wani wajan su zauna
gaskiya. Sai dai aje ayi ziyara a dawo, ni ne na haife su haƙƙin riƙe su a hannuna
yake."
"To ka ƙara mata lokaci kafin ta fara zuwa aiki ta zauna a Kano wajan Hajja."

Abiy ya sauke numfashi ya ce, "zan yi tunani a kan hakan na gani, amma a yanzu dai
sati ɗaya na bari tayi, in naga zan ƙara mata sai na ƙara mata, In naga bazan iya
ba ta dawo gidan mahaifinta." Mama tayi murmushi ta ce, "Hakan yayi, Allah ya
kaimu." Ya amsa da amin kafin ya tashi ya shiga ɗaki ya bar Mama a zaune a wajan.

"Nayla hmmm! Ai wallahi sai na raba ku, yadda ta bar gidan nan a bana
tunanin zata sake dawowa cikin sa, in ma ta dawo na ɗan lokaci ne kawai amma sai
nayi amfani da wayo da dabarar da na nisanta ka da Nayla. Sai na san yadda na yi
Nayla ta je gidan mijin da zai ci ubanta, ya hanata walwala ya kuma hanata jin
daɗi. Burina Nayla ta rayu a gidan auren da zata sha wahala kamar ydda uwarta ta
wahalar dani, Zan fashe wahalar da na sha akanta!." Girgiza kai Mama take yi tana
hasaso lokacin da wannan buri na ta zai cika. Bata nufin Nayla da ko wanne irin
sharri ko makirci, ta raini Nayla daidai da yadda ta raini ƴaƴanta, ta bata
tarbiyya da rayuwa mai kyau. Ita babban burin ta Nayla ta yi aure a inda zata sha
wahala kuma sai tabbatar da ta cika wannan buri na ta hankalin ta zai kwanta, ta yi
ƙwafa ta miƙe zuwa daƙi.


Washe gari
Kano.

Washe gari Alhamis Nayla da azumi ta tashi kasancewar ta mai ibadar azumin litinin
da alhamis, ranta a jagule gabaɗaya bata da walwala saboda rashin chajin waya,
daman gidan Daddy da suka je da daddare ne ya saka ta cikar wayarta kuma ta ƙarar
gashi yanzu kuma babu wuta kuma ba a gyara solar Hajja ba.

Hajja na kula da ita tana zaune a falo tayi shiru masu yiwa Hajja aiki suna ta
aikace-aikacen su kafin kammala su bar wajan. Hajja ta kalle ta tace, "Hauwa'u baki
da lafiya ne? Ko ki karya azumin." Ta kalli Hajja ta ce, "Rashin chaji bala'i ne
Hajja, duk shi ya saka ni a wannan yanayin."

Hajja ta ce, "ki kaiwa Aisha ta saka miki mana." Nayla ta dafe ƙirji ta ce, "har
kin saka gabana ya faɗi, ni in sake shiga wannan gidan...? Ai har abada." Hajja ta
ce, "To a ina zaki saka chajin?."
"Bara Salma ta tashi mu ji ya za a yi." Salma ce ta fito da kayan bacci ta kalli
Nayla ta ce, "meye naji kina maganata?."
"Salma chaji nake so wallahi, Ke kin san bana son zama babu chaji."
"Ga power bank ɗina can ki saka, amma ba zai yi miki da yawa ba dan shima babu
chajin."

Jin haka sai taji daɗi ta saka chajin amma duk da haka bai mata ba dan da gani
chajinsa ya kusa ƙarewa. Sallama aka yi aka shigo falon duk suka kalli wanda ya
shigo.

Ganin Daddy ya saka Nayla ta miƙe tana cewa, "Lah Daddy sannu da zuwa." Kallon ta
yayi yana murmushi ganin fuskar ƙanwarsa Bilkisu a kan fuskar Nayla ya ce, "yauwa
Hawwer, yanzu ma ki ka tashi kenan?" ya faɗa yana kallon Salma da ta fito daga
kitchen da kofin shayi.

Hajja ta ce, "Yanzu kam suka tashi dan ko wanka ba su yi ba." Gaisawa suka yi da
Hajja kafin suma su gaishe shi ya kalli Nayla ya ce, "Jiya kun je bamu haɗu ba, ya
services ɗin naki?."
"Daddy ai na gama, yanzu aiki nake jira."
"Ma sha Allah, Allah ya taimaka ya kawo miji na gari." Hajja ta amsa da amin kafin
ta ce, "Duk sun girma sai aure, su huɗu ne gasu nan kan su ɗaya. Hauwa'u, Salma,
Ummimi da Zainab." Daddy ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya ne

7 / 28