Author : NANA HALEEMA Category : Complete Novels
ce hakan ya saka ta haska jikinta sosai, ta ɗauki hula
ta saka sannan ta ɗauko ƙaramin mayafi ta ɗora akan hular. Kallon kanta take yi,
dan ta kanta san tayi kyau itama sosai, ta fesa turare masu daɗin gaske sannan ta
sauka falon ƙasa a lokacin takwas daidai.
A daidai wannan lokacin Omar ya shigo cikin gidan ya kalli Yahya suka gaisa yana
cewa, "yanzu Hajiya yake tambayarka." Omar ya ce, "gani ai, tana ina?."
"Tana ciki bata fito ba." Omar ya kalli agogon wayar sa ya ce, "ƙarfe takwas aka ce
min, yanzu kuma takwas da mintina biyu, In takwas da sha biyar tayi wallahi babu
inda zan je."
Shi dai Yahya kallon sa yake yi da mamaki, ganin sun haɗa ido sai Yahya ya ce, "ban
san ko sunanka ba amma ƙarfin halin ka yana bani mamaki." Omar ya kalle shi ya ce,
"Omar sunana."
"Koda na ji, yanayinka da maganarka da ta masu suna Omar ka yi kama, Daman da
wahala ka ga masu suna Omar ba irinka ba, ko kaɗan ba sa lamuntar raini." Ɗan
murmushi Omar ya yi kawai amma bai ce komai ba.
Narma ce ta fito tana duba waya tana cewa, "wai ina driver nan yake ne? Bana son
wulaƙanci da iskanci fa, dan ya raina ni ni ce zan zauna ina jiran sa?."
Inda yake ta kalla ta ga ya kalle ta ya ɗauke kai kafin ya ƙarasa wajan motar ya
buɗe mazaunin driver ya shiga ya zauna ita kuma ta ja ta tsaya. Ƙwanƙwasa glass ɗin
gaban motar tayi ya sauke glass ɗin ƙasa. Wani irin kallo take masa na raini da
ƙasƙanci ta ce, "Malam ka sakko ka buɗe min, ko kana so kace ni zan buɗe?."
"Baki da hannu?" Ya faɗa ba tare da ya sake kallon ta ba.
"Ina dashi, kai nake so ka buɗe min."
"Ashe baza ki je" ya sake kallon agogo ya ce, "kina da mintina bakwai in lokaci ya
cika babu inda zan je."
Kallon sa take yi shi kuma ya kalli glass ɗin gaban motar kamar motar sa, fuskarsa
ɗaure matuƙa ga wani kwarjini da fuskar take fitarwa. Duk da tana jin tsoronsa
musamman yadda ya ɗaure fuska amma hakan ya saka ta kuma cewa, "ni kuma indai baka
buɗe min ba bazan je" ta faɗa tana komawa gefe ta ja ta tsaya tana so ta ƙure shi
iskancinsa.
Shi kuwa kallon ta yayi zuciyarsa a sama matuƙa, abu ɗaya kawai ya sani ko zata
mutu ta dawo wallahi bazai buɗe mata mota ba sai dai kar ta je. Zama ya cigaba da
yi a cikin motar sai kace motar ta Didi ce. Agogo yake kallo yana jira lokacin da
ya bata ya cika ya fita ya bar gidan. Su dai ma'aikatan gidan kallon ikon Allah
suke yi, mamakin Omar su ke yi ɓangare ɗaya suna jin daɗi an samu daidai da Narma,
suna tsaye suna so su ga waye zai ci wasan.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️*Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 11.*
Kowa a wajan kallon ta yake yi ana kuma jira a ga Omar zai fito ya buɗe mata motar
ko bazai fito ba. Ga mamakin su Omar bai fito ba yana zaune a cikin motar kamar
motarsa, ita kuma tana tsaye har lokacin tana jira ya fito ya buɗe mata. Mamakin sa
take yi ganin bai sauko ya buɗe mata ba kenan bazai yi ba? In haka ya faru wacce
irin kunya zata ji a gaban ma'aikatan gidan?. Wayarta ce tayi ƙara ta ga ƙawayenta
da suke jiran ta zasu fita ne, ta buga uban tsaki ta kashe wayar tana sake kallon
sa babu alamun ma zai fito dan ko kallon inda take ma baya yi.
Shi kuwa Omar ƙoƙarin daidaita ɓacin ransa yake yi dan in ya fita a yadda yake jin
zuciyarsa tsaf zai sharara mata maruka masu zafi, shi kuma ba haka yake so ba, yana
so su rabu lafiya ko dan alƙawarin da ya yiwa Didi, sannan yana so su rabu lafiya
ko dan kuɗin mahaifinta da ya karɓa. Shiru na kusan mintina biyar hakan ya yi
daidai da saursa minti biyu ya kama gaban sa.
Yahya ne ya ƙaraso wajan motar a sanyaye ya ƙwanƙwasawa glass ɗin gefen Omar, Omar
glass ya sauke yana kallon sa ya ce, "Omar don Allah kazo ka buɗe mata ka huta."
Omar ya kalle shi ya ɗauke kai dan babu amfanin ma yi masa magana.
Yahya ya juya ga Narma ya ce, "Hajiya bismillah" ya faɗa yana buɗe mata amma sai ta
bishi da banzan kallo na wulaƙanci ta ce, "Wallahi shi zai buɗe min, in kuma bai
buɗe min ba daga yau ya bar aiki a gidan nan, sai naga waye ubansa a Kano da yake
min wannan wulaƙanci. Shashasha dashi ƙazami."
Buɗe kofar taga an yi sai tayi murmushi ta ɗauka zai buɗe mata ne, ga mamakin ta
kai tsaye inda take ya nufa fuskarsa a ɗaure, yana zuwa ya kalle ta ya ce, "in kika
sake furta abinda kika furta ɗazu sai kin yi dana sanin haɗa ido dani a rayuwarki,
in kuma kina ganin wasa nake yi ki maimaita abinda ki ka ce yanzu" ya faɗa ciki
tsawa yana tsare ta da idanunsa masu ban tsoro da kwarjini.
Ɗiff Narma tayi tana kallon idanun sakamar yadda ita yake kallo, da sauri ta ɗauke
kai daga kansa, ganin ta yi shiru ya cize baki yana karkatar da baki irin yadda ƴan
daba suke yi ya nuna ta da taysa ya ce, "ki san irin maganar da zaki dinga faɗa min
in kina so kan ki da zaman lafiya, In kuma kina so na huda cikin ki sai ki cigaba."
Yahya ya kalla ya cilla masa key ɗin motar shi kuma ya chafe, Omar bai ce komai ba
ya juya ya fita daga gidan.
Wata uwar ƙara Narma tayi ta shiga cikin gidan a guje ta faɗa kan kujera ta fashe
da kuka mai ƙunar rai. Wai ita Narma wani banzan ɗan daba, ɗan shaye-shaye ya yiwa
wannan wulaƙacin a gaban ma'aikata, kawai saboda Dad ya bashi damar haɗa ido da ita
shine yake zaƙewa. Ita Narma mai capacity wani ɗan tasha ya wulaƙanta a gaban masu
aiki a ƙarƙashin ta.
Hannu na rawa take kiran Dad, yana ɗauka kawai ta fashe masa da kuka. Dad ya ruɗe
sosai ya ce, "Oh Narma, what wrong? Why are you crying like this?." Kuka take yi
sosai cikin baƙin cikin da take ji a zuciyarta. Sai da tayi kukan ta gaji murya na
rawa ta ce, "Dad i was really disrespected by that guy in front of the maids, Dad
ƙawayena suna can suna jira na amma yayi tafiyarsa. Dad gaskiya ni bana son aiki
dashi, ka barni da wanda muke tare dasu a nan."
Dad ya ce, "stop crying and talk to me, what happened?." Narma ta bashi labarin
abinda ya yi mata sannan ta ce, "Dad wai waye shi da yake min haka ne?."
Dad ya ce, "ba kowa bane fa ce ɗan daba kuma ɗan tasha, ba kowa bane fa ce ƴan
bangar siyasa wanda mu ke amfani dasu wajan cikar burin mu. Bana son yin wasa da
Tiger shiyasa kika ga ina biye masa duk abinda ya ce, zaɓen gaba nake ji ke kin san
kujerar da nake nema, irin su Tiger makami ne sosai a tafiyar mu shiyasa ki ka ina
biye masa. In ba dan haka ba shi waye? Ko inda motarki take bai isa yazo ba,
lafiyarsa nake so ya bani wajan kare ta ki shiyasa nake jure duk abinda yake miki.
Sorry my daughter kar ki damu da wannan, abu ne ƙarami da mun ci zaɓe shikenan
bazai sake ganin koda fuskarki ba. So wipe your tears my dear, i know what i'm
going to do."
Narma ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "But Dad if he doesn't stop bothring me and
upset me, i will have him arrested wallahi." Dad ya ce, "kar ki damu, ni zan san
abinda zan yi. Yanzu kin zuwa dinner ɗin?."
"Na fasa."
"Gobe ƙarfe nawa zaki je arewa 24 ɗin?."
"Zuwa 11am."
"Okay ki kwantar da hankalinki ki huta kin ji? Babu abinda zai sake faruwa." Amsa
tayi kawai ta kashe wayar zuciyarta na aiyana mata irin abubuwan da ya kamata ta yi
masa wanda zata huce.
Shi kuwa Omar yana fita ya tarar da Bash a machine ya ɗauke shi suka bar
wajan zuciyarsa na faɗa masa gwara ya bi shawarar Didi ya ajjiye aikin nan in ba
haka ba wallahi zai yiwa ƴar mutane illa. A haka suka je unguwar yana sauka akan
machine wayarsa tana yin ƙara, ko bai duba ba ya san Senator ne hakan ya saka kawai
ya danna ya kara a kunne.
Kafin Sen ya yi magana ya ce, "batun aikin nan na ajjiye shi bazan yi ba, matuƙar
zata dinga ɗaga min murya tana faɗa min magana mara daɗi bazan jure ba, gwara na
ajjiye shi a huta kawai. In ban ajjiye ba zaka tarar da abinda bazai maka daɗi ba,
ba a ɗaga min murya na ƙyale, ba a yi min ihu a kai, ba a yi min maganar banza. Dan
tana ƴarka baza ta yi min abinda bana so na ƙyale ba."
Sen wani takaici ya tokare masa maƙogwaro amma bai nuna ba ya ce, "Tiger ya kamata
ka san ƴata ce yarinyar da ku ke tare."
"To dan tana ƴarka sai me? Dan tana ƴarka sai na bari tayi min abinda yake so? Ta
tambayi waye ni a garin nan, babu wanda yake ɗaga min murya balle rashin kunya ko
zagi. Sanin ƴarka ce ya saka nake faɗa maka, ka ja mata kunne. Senator ba haka
Tiger yake ba, Tiger baya jure koda ɗaga murya ne balle maganar baki."
Sen ya danne ɓacin ransa ya ce, "na ɗauka yadda ka ke girmama ni zaka girmama
ƴata." Omar ya ce, "in da ta so zamu girmama juna, bata girmama ni ba nima bazan
girmamata ba. Shiyasa na ce a bar aikin nan kawai." Numfashi Sen ya sauke ya ce,
"na zaɓeka ne saboda na san zaka iya kular min da ita sosai, na zaɓeka akan jami'an
tsaro masu bindiga amma na ga kamar hakan bai maka ba."
"Kawai bana tolerating nonsense ne" ya bashi amsa kai tsaye ba tare da wani tunani
ba.
Tolerating nonsense, Senator ya maimaita a zuciyarsa cike da mamaki, wai daman har
yana da karatun da ya san ne kalmar take nufi, kuma dan bashi da hankali shi yake
faɗawa haka akan ƴarsa?. Lallai ya zama dole ya san abin yi, da an kammala zaɓe zai
saka a yi masa abinda zai manta ma ya taɓa sanin Sen a duniya.
Sen ya ce, "Amma Tiger meye buɗe mota? Da ka buɗe mata kun tafi da shikenan." Wani
murmushi ya yi na rainin hankali kana ya ce, "a kaf duniya Yayata kaɗai zan iya
yiwa haka, bayan ita babu wani ko wata a duniya da zan buɗewa mota. Ka faɗa mata
indai sai na dinga buɗe mata mota zata shiga ta je inda take so to baza ta je ko
ina ba." Duk da ba a zafafe yake maganar ba amma kalamansa ciwo suke yiwa Sen sosai
kawai bashi da zaɓi ne.
"Is okay, ka koma ka kai ta yanzu."
"Bazan iya ba, na riga na dawo gıda sai dai wani lokacin."
"Well, gobe zata je interview ƙarfe sha daya na safe."
"Allah ya kaimu" ya amsa a daƙile dan wallahi gabaɗaya ma aikin ya fita daga ransa,
dan ya san cigaba da aiki da ita babbar damuwa zai haifar, tabbas zai iya zama
silar komawar sa prison dan wallahi bazan sasssuta mata ba.
Bayan ya kashe wayar gida ya shiga wajan Didi, ganin ta a zaune kamar ba ita ba ya
saka shi ya ƙarasa ciki fuskar nan a tamke sosai ya ce, "Didi lafiya?." Ta kalle
shi ta ce, "kaina ne yake min ciwo Omar, har zazzaɓi nake ji."
"Mu je a dubaki" ya faɗa yana kallon ta. Girgiza kai ta yi ta ce, "kar ka damu na
sha magani zan warke."
"Ki zo mu je a baki magani" ya sake maimaitawa yana kallon ta. Kallonsa itama tayi
dan tasan baya ƙaunar ya ji tana ciwo kwata-kwata, yafi so da ta ce babu lafiya ayi
maganinsa. Maganin da ta sha ta nuna masa ta ce, "na sha magani."
"Waye ya baki?."
"Jikar Hajja Salma, ka san karatun lafiya tayi." Shiru yayi kawai jin ance jikar
Hajja kawai sai fuskar Nayla ta zo idanunsa ba tare da ya san dalili ba, ya kulle
ido ya buɗe akan fuskar Didi ya ce, "yanzu da sauƙi?."
"Sosai ma."
"Allah ya ƙara lafiya" ya furta a sanyaye. Ta amsa da amin tana kallon sa tana
mamakin abinda ya ɓata masa rai.
"Ki je ki kwanta" ya katse mata tunani yana kashe tv ɗin. "Bana jin bacci Omar,
Zaman kaɗaicin nan damuna yake yi sosai, in ka fita sai ni kaɗai, na danna wayar na
gaji, nayi kallon na gaji."
Bai ce mata komai ba ya zauna daga nesa da ita yana kallon ta. Gabaɗaya jikinsa
yayi sanyi baya so yaji tana yin ciwon kai balle harda zazzaɓi, baya so yaga Didi
na rashin lafiya, gabaɗaya sai ya damu kansa kamar shi ya ɗora mata. Didi ta kalle
shi ganin yana kallon ta tace, "kar ka damu fa, da nayi bacci na tashi zan ji
daɗi." Kai ya ɗaga mata kawai bai ce komai kuma bai daina kallon ta ba.
Ganin ya damu sai ta miƙe ta ce, "ka kashe hasken falon zan je na kwanta." Kai ya
ɗaga mata kawai ta shiga ciki dan kawai ta kwantar masa da hankali.
Shiru yayi yana tunani, bai san dalili ba kawai fuskar Narma ta kawo masa ziyara a
idanunsa, yadda take kallon sa tana tsaye da mamaki a idanunta na kalaman da take
faɗa masa shi yake gani. Tsaki ya yi ya kawar da tunanin daga zuciyar sa yana zaune
bai tashi ba.
Bai kashe hasken ba kuma bai tashi ba dan bazai iya tafiya ya bar Didi ita kaɗai
ba, in ya tafi sai yaga kamar ciwon zai same ta sosai. A kan kujera yayi bacci ba
tare da ya san hakan ba sai dan bazai iya tafiya ya bar ta ba.
Ƙarfe huɗu na dare ta farka kamar kullum, tayi mamakin ganin haske a falo
a kunne, ta leƙo ta ganshi a kwance yana bacci hankalinsa kwance. Murmushi tayi ta
ƙaraso ta kashe hasken falon ta koma ɗaki ta yi alwala ta tayar da sallah.
Sai da aka kira asuba sannan ta ƙaraso inda yake ta kalli gefen sa taga ya ajjiye
ƙaramar wuƙa da wani ƙarfe da alama a jikinsa suke, ta girgiza kai ta tashe shi ya
buɗe ido ta sanar dashi lokacin sallah ya yi sannan ta koma ciki shi kuma ya tashi
ya fita.
Bayan an idar da sallah ya dawo har ɗakin ta ya shiga kamar yadda yayi tunani tana
kan sallaya ya ce, "Didi ina kwana." Murmushi ta yi ta ce, "ka tashi lafiya mai
bacci a falo?." Murmushi shima ya yi sannan ya ce, "ya jiki?."
"Na ji sauƙi sosai. Yau baka tashi sallar dare ba, ko baccin ne?."
"Kawai ban tashi ɗin bane, Allah ya ƙara lafiya" abinda ya ce kenan ya wuce ya fita
daga falon nata.
Kamar yadda Sen ya ce masa ƙarfe sha ɗaya bai jira sha ɗayan tayi ba ya tafi dan
shi mutum ne mai girmama lokaci, baya son african time kwata-kwata, shiyasa in kace
masa ƙarfe goma to tabbas goman zaka ganshi, in ka san ƙarya ka ke ma gwara kar ka
faɗa masa. Tare da Tk suka je har cikin gidan ya nemi waje ya zauna bayan suka
gaisa sama-sama da masu aikin gidan.
Su kam mamaki suke yi ganin da alama ba a kore shi ba akan abinda ya yi jiya, suna
jinjina ƙarfin hali da kuma sa'ar da yake da ita, in ba haka ba waye zai yiwa Narma
haka ya kwana lafiya. Yahya ne ya zo zai zauna kusa dashi Tk ya ce, "kai yanee?."
Yahya ganin Tk da yanayin sa ya saka shi yin sak ya miƙawa Omar hannu ya ce, "Omar
barka da safiya." Kallon sa ya yi suka gaisa Tk ya ce, "to kama gabanka."
Kallon sa Omar kawai ya yi sai Tk ya yi shiru shi kuma ya kalli Yahya ya ce, "ka
zauna." Ba musu ya zauna ya ce, "ban ɗauka ma zan ganka kazo yau ba duba da abinda
ya faru jiya, na ɗauka shikenan kwantiragin aikinka ya ƙare." Omar bai amsa masa ba
sai agogo da ya kalla sha ɗaya saura mintina goma sha biyar. Numfashi ya sauke ya
ce, "tana da sauran mintina sha biyar."
Yahya ya ce, "don Allah Omar na tambayeka." Kallon sa kawai yayi alamun ina ji shi
kuma ya ce, "don Allah ne ka ke taƙama dashi ka ke yiwa ƴar sanata haka?." Omar ya
ɗauke kai daga kallon sa ya ce, "ka tambayi sanatan."
Zai sake magana kawai suka ga an taho a guje an zube a gaban Omar yana cewa,
"Madugu uban tafiya, madugu uban matsiyata, a hauka a zame ka hau mutum ka zauna
daidai. Gadon ƙaya ka ke wallahi duk wanda ya hauka babu shi babu bacci, wando
ƙarfe ka ke saka ka sai wanda ya shirya. Ba ayi maka wargi ka ƙyale, jan wuya jinin
Didi, Allah ya ja da ran yayar mu."
Kallon wanda ya zube a gaban na sa ya ke yi ya kalli Tk sai Tk ya ce, "Damisa ai
kunama ne ɗan yankin su Jijiya." Kai ya girgiza kawai ya kalli yaron da ya miƙe ya
ƙaraso wajan Tk yana cewa, "kai ashe babbar giwa ce da kanta a wajan nan, ina na
sani ina can ina shirme."
Yahya ya maimaita sunan Damisa yana kallon Omar Tk ya ce, "eh Damisa, shine dai
wanda ka ke jin labari a radios shine a zaune a gaban ka! Kayi hattara domin taken
Damisa ƙi sabo." Yahya ya girgiza kai yana mamakin to me ya haɗa shi da Sanata
kuma? Lallai dole ya yi jiji da kai, wannan kirari dake kwarara masa, kuma ga sunan
sa da yayi tambari kusan kowa ya san shi, ko baka san shi ba kasan sunan sa.
Yahya ya sake kallon sa ganin maza buyu suna gefensa a tsaye shi kam sai aikin
danna waya yake yi yana kuma kaɗa ƙafa, in ka shigo gidan sai ka ɗauka mai gidan ne
a zaune saboda yadda ya kame kai baza ka ce ma shi bane.
Mamaki Yahya yake yi sam bai yi kama da ƴan daba ba sai ma kama yake yi da jaruman
gaske, kallo ɗaya zaka yi masa kayi tunanin babban hamshaƙin mai kuɗi ne ko ɗan mai
ƙudi saboda yanayin fatarsa da kyaun da Allah ya bashi, in ka sake kallon sa sai ka
ɗauka soja ne, saboda kwarjini da ƙirarsa. In ka kalli fuskarsa kaga yalwar gashi
sai ka ɗauka wani babban