Advertisements
Chapter 8 Reading KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA

Author :  NANA HALEEMA Category :  Complete Novels

Chapter   8 / 28

21K to 24K   out of 83.2K words

wannan, Allah ya kawo
namiji na gari."

Hajja ya ce, "Amin. Amma ga mazaje nan a gidajen ku meye amfanin su?. Zaratan
samari nawa muke dasu?." Salma da Nayla suka kalli juna Daddy ma dariya ya yi ya
ce, "basu da amfani kan Hajja, muna jira wani ya furta yana son ƴar uwarsa ne sai
ayi."
"Har sai an jira? Lallai kace zan rarraba su ga duk wanda naso. Duk wanda na ce na
bawa ɗaya a cikin su ai babu wanda zai musa ko?."
"Babu kam Hajja."
"Yauwa, to ku jira zan fara watandarsu tunda na ga ku kun yi sanyi." Dariya Daddy
ya yi ya kalli Nayla ya ce, "Ya gidan babu wuta? Naga kina gumi ki kunna ac mana."

Nayla cikin shagwaɓa ta ce, "ba solar ta lalace ba har yanzu ba a gyara ba." Daddy
ya ce, "Subahanallah! Har yanzu ba a gyara ba daman? Ke Salma meye amfaninki da
baki faɗa min ba?" Ya faɗa yana ɗauko waya tare da kiran masu aikin solar suka
tabbatar da zasu zo a lokacin. Nayla murna kamar tayi me saboda zata samu chaji
yadda take so. Daddy sallama ya yi musu bayan ya basu kuɗi ita da Salma ya tafi.

Omar kuwa a safiyar yana zaune a falon Didi yana cin indomie ita kuma ta
kitchen tana wanke-wanke. Sallama akayi tare da shigowa falon ya ɗago yana kallon
wanda ya shigo. Ɗiff yayi ganin wanda yake tsaye a bakin ƙofar shi bai shigo ba
kuma bai koma ba. Omar bai amsa sallamar ba sai ma ɗauke kai da ya yi. Didi jin
sallama kuma bai bada amsa ba ya saka ta fito falon tana kallon inda yake kallo.

Da Yayan Mahaifiyarsu ta haɗa ido Baba Adamu sai kuwa ta saki fara'a ta ce, "Lah
Baba kai ne tafe? Sannu da zuwa." Ƙarasowa tayi shima ganin ta sai ya shigo yana
murmushi ya ce, "Ni ne Aisha."
"Sannu da zuwa, Ka zauna mana Baba."

Ya zauna yana satar kallon Omar da yake cin indomie kamar bai san ma ya shigo ba.
Gaisawa suka yi da Didi ya ce, "ya kike ya sana'ar taki? Fatan komai Lafiya."
"Lafiya lau Baba, ɗazu nake zancen gobe juma'a zan zo mu gaisa in sha Allah."
"Allah sarki, Allah ya baki ladan niya." Ta amsa da amin ya kalli Omar ya ce, "Omar
ina kwana."

Wani iri Didi taji na rashin jin daɗi ganin babban mutum kamar Baba Adamu shine
yake gaishe da Omar. A sanyaye ta kalli Omar da kamar bai ma ji abinda aka ce ba ta
ce, "Omar magana ake maka, ka gaishe da Baba."

In bowl ɗin da yake hannunsa ya amsa shima ya amsa. Didi ta ce, "Omar!."
"Na'am" ya amsa ba tare da ya kalle ta ba.
"Baka ji abinda nace ba ne?."
"Naji mana."
"To ka gaishe shi." Ya kalle ta ya ce, "bazan ba."

Zata sake magana Baba Adamu ya girgiza mata kai alamun tayi shiru ya kalle shi ya
ce, "Omar ina kwana." Nan ma ya sake yi masa banza Didi zata yi magana Omar ya ce,
"Bana iya girmama wanda bai girmama mahaifiyata ba, bana iya girmama wanda bai
tashi nuna min mu masa bane sai da haƙora talatin suka fito a bakin mu. Kar ki ɓata
bakinki Didi, kema kin san bazan yi ba."

Baba Adamu ya ce, "Omar kayi haƙuri, kuskure ne an yi shi a baya kuma na nemu
afuwar ku."
"Ita wacce ƙasa ta rufe idonta fa, itama ka nemi afuwarta ne?"Omar ya faɗa yana
kallonsa da rikitattun idanunsa. Baba Adamu ya ce, "Ina yi mata addua'ar samun
gafara a wajan mahaliccinta." Omar ya ce, "yadda bakwa son mu wallahi nima bana son
ku, yadda ku ka wulaƙanta mahaifiyar mu dan kawai tana auren mahaifin mu babu wanda
zan iya ganin darajarsa wallahi, kum...."
"Omar!" Didi ta katse shi da ƙarfi tana kallon sa.

Kallon ta yayi sai ya fasa faɗar abinda zai ce kuma bai tashi daga inda yake ba,
dan bai isa yazo ya same shi ya tashi ya bar masa wajan ba. Baba Adamu ya ce,
"ƙyale shi Aisha. Daman magana ce nazo da ita akan sabon company na da na buɗe, in
Omar ɗin yana so sai yazo mu fara aiki gabaɗaya." Kallon ƙasan ido ya yiwa Baba
Adamu kamar zai yi magan sai ya fasa ya cize bakinsa cikin ƙunar zuci.
Didi ta washe baki ta ce, "Lah yaushe aka buɗe Baba?."
"Satin da ya wuce."
"Allah ya sanya alkhairi ya sa albarka, Me zai hana ya zo? Zai ma yi aikin...."
"Gwara na koma bara akan titi da dai nayi aiki a ƙarƙashinsu wallahi" Omar ya katse
a yana ɗaga mata hannu.

Zata yi magana ya ce, "Didi! Ke kin san waye ni, babu ɓoye-ɓoye, babu kare,
wallahil azim bazan yi ba. Wato nayi aiki a ƙarƙashin su a samu damar wulaƙanta ni
a zage ni ko? Kema kin san bazai yu ba, ai ko rahama ake rabawa a company na amince
ta wuce ni na samu a wani wajan daban. Hanyar samun ta ai yawa ne dashi."

Baba Adamu ya ce, "babu laifi Omar. Amma duk lokacin ka ji kana da ra'ayi ƙofa buɗe
take, Kuma har abada baza ka taɓa goge mu a rayuwarka ba, mu ɗin dai mu ne gatanka
saboda mu ne jinin mahaifiyarka."

Omar ya taɓe baki ko kaɗan baya jin nauyi da girman Baba Adamu duk da ya girma
sosai. Ya ce, "Allah ne gatan mu gaba da baya, babu wata halitta da zata zama gatan
mu a duniya in ba Allah ba." Murmushi Baba Adamu yayi dan ya san shine ya jawo kuma
ya san halin Omar da shegen riƙo da taurin kai, shekara sama da goma sha ana abu
ɗaya amma har yanzu yaƙi sakin jikinsa.

Baba Adamu ya ce, "Aisha zan tafi, akwai abinda ki ke buƙata ne?." Didi cikin
sanyin jiki ta ce, "Babu komai Baba, in akwai zan sanar da kai a waya."
"To akwai kayan abinci da nazo miki dashi, zo mu je yara sai su shigo dasu" ya faɗa
yana miƙa mata rafar ƴan dubu-dubu guda biyu ta saka hannu biyu ta karɓa ta ajjiye.
Omar ya kalle shi ya ce, "duk wanda ya ganni ya ganta ya san ba ma tare da yunwa."
Babu wanda ya kula shi Didi ta kalle shi sannan ta bi bayan sa tana hararar Omar
saboda kallon da ta ga yana yi mata.

Ba jimawa aka shigo da madara da milo da sugar da butter, kwai, taliya, doya,
dankali, platain, da sauran abubuwa. A guje yaran suke ajjiyewa suna fita saboda
Omar da yake kallon su daga falon.

Tana shigowa gidan yana fitowa daga parlon ya ce, "babu abinda za a ci a cikin
kayan nan, ko ki mayar masa da tsiyarsa ko kuma na kwasa na zubar wallahi." Ta
Harare shi ta ce, "wallahi bazan mayar ba, kuma baza a zubar ba Omar ba. Yayan
mahaifiyata ne ya bani ba wani bare ba."

Da mamaki yake kallon ta ya ce, "ba gwara ace wani baren ne ya bayar akan ace shine
ya bayar? Didi kar mu yi haka dake, ba za a ci abubuwan nan a gidan nan ba."
"Wallahi sai an ci!" Ta bashi amsa a kausashe tana kallonsa. Idanunsa sun yi ja
saboda ɓacin rai ya kalle ta ya ce, "Akwai abinda babu a gidan nan ne? Faɗa masa
aka yi yunwa tana tare damu ne da zai kawo mana wannan tarkacen?."

"Omar wai meye ya sa baka yafiya ne kai?." Ta kalle shi ganin sai wuci yake kamar
zaki, idanun nan nasa sun yi ja haka jijiyar kansa ta miƙe kana kallon sa kasan ran
masa ya ɓaci. "Tambayarka nake, meyasa baka yafiya ne?."

Bai iya yi mata magana ba sai wuce zai fita tayi saurin riƙo hannunsa ta ce, "Yayan
mahaifiyarka ne in ka saka aka yi masa wani abun tamkar Mama ka yiwa, sannan ka
tuna Mama baza ta taɓa alfahari da kai a yadda ka ke ba Omar. Zata yi alfahari da
kai in ka kasance na gari, amma a haka baza taɓa alfaharin haihuwarka ba." Runtse
ido yayi cikin ƙunar zuci ya zame hannunsa daga riƙon da tayi masa ya bar gidan da
sauri.

Da kallo ta bishi bayan ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ya Allah ka shirya min
ƙanina Omar, Allah ka yaye masa wannan baƙar zuciyar da yake fama da ita, Allah ka
bashi ikon manta abinda ya riga ya wuce ya kama abinda yake gabansa, Amin." Kayan
take ɗauka a hankali tana shiga dasu dan ta san in zasu shekara a wajan bazai taɓa
ba, gabaɗaya jikinta ya gama yin sanyi itama, abubuwan da suka faru a baya suna yi
mata yawo a zuciyarta.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️


*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️*Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.


https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t

*Book 1*
*P 07.*

*Abuja.*

Zaune suke a babban falo na alfarma su biyar suna cin abinci cikin yanga da iyayi,
kai da ka gansu ka san kuɗi da ilimi ya gama zama a jikin dukkan su. Duba da irin
shigar da take jikin Narma zaka tabbatar da wayayyun ƴan boko ne.

Dad ya kalli Nabil ya ce, "Nabil ka san lokacin lissafi a store ya kusa ko?." Nabil
ya kalli mahaifin na su ya ce, "Yes Dad, na sani."
"Ya kamata a dakata da karɓat kaya sai mun kammala lissafi."
"Okay Dad za a yi." Ya kalli Najwa ya ce, "Najwa yaushe zaki koma London?."

Najwa ya kalle shi ta ce, "Sai nan da three weeks Dad." Kafin ya bada amsa Mum ta
ce, "My Dear tunda dai sun samu hutu lokaci ya yi da zamu je Paris. Akwai birthday
party ɗin friend ɗina, za a yi surprising ɗin ta a can, so ina so nayi attending."

Narma ta kalli Mum tana turo baki ta ce, "Mum ni babu inda zan je gaskiya, beside
ni Kano zan je." Najwa ta ce, "Yaya Narma wai me zaki yi a Kano ne?."
"Samra's wedding."
"Friend ɗinki sai aure suke yi amma ke kin tsaya wasa." Narma tayi murmushi ta ce,
"na kusa."

Mum ta ce, "to ke ki tafiyar ki Kano ni da Najwa zamu je Paris." Najwa ta ɗan ɓata
rai ta ce, "Paris Mum?."
"In baza ki je ba kin huta, ai ba hanya ce ban sani ba." Najwa tayi dariya ta ce,
"dole na ma." Mum ta kalli Nabil ta ce, "Nabil ka faɗawa Zuhra sai mu je tare, I
hope Asim sun samu hutun school?."
"Yes Mum, sun yi hutu."
"Okay" ta furta tana cigaba da cin abincin ta.
Dad ya kalle Narma ya ce, "Yaushe zaki je Kano din?." Narma ta kalle shi ta ce,
"Ranar Sunday zan tafi." Dad ya kalle ta ya ce, "Ranar yaushe zaku fara events
ɗin?."
"Wednesday."
"Okay. Narma ban da yawo ke kaɗai ba, kin yanayin Kano ba wani security ne dashi
ba. Dan ma kin takura ne da babu abinda zai saka na bar ki ki je." Narma tayi shiru
bata ce komai na dan kar ma tayi magana a hana ta zuwa.


*Kano.*

Didi share Omar tayi dan ta san yinin ranar a ɓacin rai zai yi shi in tace zata
biye masa itama ranta ne zai ɓaci. Aikace-aikacenta ta cigaba da yi gabaɗaya
abubuwan da suka wuce suna yi mata yawo a kanta, duk yadda ta so ta kawar itama ta
kasa hakan ya sanya idanunta zubar hawaye tunawa da iyayen su da suka rasa a
shekarun da suka wuce.

Bata sake tunanin Omar ba dan ta san bazai dawo ba ransa a ɓace yake da ita sosai
ta fi kowa sanin hakan. Ta kuma san in ba dan ita ɗin babu babu halittar da yake
ɗagawa ƙafa, shi bai san kara ba, bai kuma son alfarma ba. Haka ranar ta yini
sukuku bai dawo ba har yamma, ko da ya shigo bai ce mata komai ba daman ta san
bazai ce ba ɗakinsa ya shiga bai jima ba ya fito ya sake fita.

Sai bayan sallar magriba kamar yadda ya saba shigowa ko yaushe sannan ya shigo
kamar baza ta yi masa magana ba ganin ya haɗe rai sai kuma ta ce, "Baza ka ci
abinci ba ne?." Kallon ta yayi yana shan ruwa ya ce, "Na daina cin abincin gidan
nan har sai abinda ya kawo ya ƙare." Ta rausayar da kai ta ce, "Omar! Omar!! Wai
wacce irin zuciya ce da kai ne don Allah?."

"Wacce Allah ya yi min Didi."
"Shikenan naji. Amma abinda na dafa yau ko abu ɗaya a cikin abinda ya kawo ban taɓa
ba. Kazo kaci abincin ka." Ya kalle ta alamun bai yarda ba ta ce, "da gaske nake,
ka san ai bazan maka ƙarya ba. Ka je ka ɗauko abincin, ka kira su Tukur su ci ga na
su." Shiru yayi kamar zai ci ɗin sai kuma ya girgiza kai ya ce, "su dai zasu zo su
karɓa, ni kam bazan ci ba."

Duk sai Didi ta damu a tausashe ta ce, "in baka ci ba me zaka ci?."
"Assalamu alaikum, Damisa na dawo." Jin muryar Bashir a cikin yaransa ya saka shi
ya fita tsakar gidsa sai ga shi ya dawo da packs da alamun abinci aka siyo masa.
Didi ta kalle Bashir ta ce, "Bashir ku zo ku ɗauki abinci." Bash ya ce, "An gama
babbar Yaya, godiya mu ke Allah ya saka da alkhairi." Kitchen ɗin ta shiga ta ɗauko
musu ta bashi shi kuma ya fita.

Lokacin da ta dawo ta tarar grill tilapia fish ne da chip a cikin pack ɗin irin mai
sauce ɗin nan da ake siyarwa yana ci hankalin sa kwance. Daman ta san shi masoyin
kifi ne sosai, bai damu da cin nama ba akan yadda yake son cin sa ba. Numfashi ta
sauke ta kalle shi kamar zatayi magana sai ta fasa ta zauna akan kujera.

Wani pack ɗin taga ya miƙo mata sai tayi murmushi, daman ta san bazai taɓa siyan
abu bai siya da ita ba, koda a waje ne in ya ci itama sai ya kawo mata. Ganin bata
karɓa ba sai ya ajjiye mata ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ya maganar saurayinki?."

Dariya ya bata sosai, wai saurayinta a ganin ta ai sai dai ace bazawari ba saurayi
ba, ita mantawa da take itama tana cikin sahun wanda za a kira da budurwa. Ganin
tana dariya sai ya kalle ta ya ce, "me ya baki dariya?."
"Kaine ka bani dariya Omar, wai saurayina. Ina laifin ka ce mai neman aurena?
Saurayi ai sai dai irin ku masu neman yara su aura."

Shima sai ya ɗan saki fuska yana kallon ta ya ce, "Yaushe zai zo ɗin?." Ta ce, "ba
ka ce gobe ba? ya ce goben zai zo in sha Allah."
"Ya yi" ya faɗa yana ɗauko waya yana dannawa. Abinda ya faɗo ƙasa ta kalla garin
ɗauko wayar ya faɗo daga aljihunsa. Ta kalle shi ta ce, "Omar me nake gani a kusa
da ƙafarka?." Kallon wajan ya yi sannan ya kalle ta ta ce, "Omar baka daina shan
sigari ba daman?."

"Na daina Didi, ɗazu ne da raina ya ɓaci shine...."
"Shine ka sha?."
"Uhum."
"Omar ba ka ce min ka daina ba?." Ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "Didi na daina
wallahi, ɓacin rai ne kawai." Shiru tayi alamun ranta ya ɓaci, ya kalle ta ya ɗauke
kai ya cigaba da abinda ya ke yi. Jin shirin na ta yayi yawa ya sake kallon ta ya
ce, "Didi yau ne kawai, kuma daga yau har abada bazan sake ba."

Kawai sai ta fara kuka ta ce, "amma ka ce min ka daina ko? Ka san bana so. Yaushe
ka fara yi min ƙarya? Ina yarda da duk abinda ka ce min saboda na san ƙarya ba
ɗabi'arka ba ce, amma gashi ka fara Omar." Ya tausasa murya ya ce, "ai na faɗa miki
dalilina Didi, kuma bazan sake ba faga yau nayi miki alƙawari, ki daina kuka."
Ajiyar zuciya tayi ta kalle shi bata ce komai ba.

Ɗauke wacce ta faɗi ƙasa tayi ta miƙe ta ce, "Zan shiga na kwanta." Ya miƙe shima
yana kallonta ya ce, "ki daina kuka to, bazan sake ba in sha Allah." Ya share mata
hawayen da kansa ta kalle shi tace, "na daina Omar." Da hannu yayi mata alamun tayi
murmushi sai tayi murmushin shima yayi murmushi ya fita ya barta a wajan. Ajiyar
zuciya tayi ta shiga ɗaki bayan ta kashe hasken falon.

Washe gari.

Kasancewar Juma'a ce da wuri ta tashi dan tana yin abincin sadaka duk ranar, nan da
nan ta haɗa shinkafa da wake da dafaffan kwai ta zuba a disposable packs kamar
yadda take yi in an idar da sallah ta fita da kanta ta rabawa yara. Lokacin da ya
shigo ta gama tana zubawa a packs ɗin ya kalle ta ya ƙaraso ya ce, "Didi wai ba za
a samu mai taya ki aikin nan ba?" Ya faɗa yana karɓa tare cigaba da yin abinda yake
yi.

"To Omar ko wacce mace tsoron shigowa gidan nan yake yi saboda kai, kai kanka in
kaga baƙuwa ka dinga faɗa kenan taya zan samu mai ta ya ni aiki?."

"Gabaɗaya mutanen unguwar nan munafukai ne, musamman ma matan." Jin abinda ya ce
sai tayi murmushi ta bar masa ya cigaba da abinda yake yi dan tasan bazai barta ta
cigaba ba. Sai da ya gama sannan ta kalle shi ta ce, "Amma dai ba da ƙananun kaya
zaka je masallaci ba?." Zai yi magana ta ce, "Don Allah ka saka manyan kaya, don
Allah na don ni ba." Hannu ya wanke bai ce komai ba ya shiga ɗakinsa.

Sai gab da lokacin sallah sannan ya fito yana fitowa ta fito itama daga falo ta
bishi da kallo tana murmushi. Ya yi mata kyau cikin yadi milk colour, abin ka da
namiji mai kyau, duk da bai saka hula ba amma yayi kyau sosai. Murmushi tayi ta
ƙaraso inda ya ke ya ce, "ƙanina mai kyau ne wallahi, Allah ya sa kayi budurwa
yau." Taɓe baki yayi bai ce komai ba kuma bai yi murmushi ba.

Ta kalli gashin kansa ta ce, "ya kamata ka ɗan rage gashin nan na kanka, kalli
fuskar ka ma, gashin yayi yawa kamar wani buzu."
"Shi ne" Abinda ya ce kenan yana juyawa ya fita ta bishi da kallo tana murmushi.

Hijjabi ta saka ta fita bayan ta rufe ƙofar gidan ko makulli bata saka ba dan ta
san babu wata halitta da zata iya shiga gidan da sunan sata. Kai tsaye gidan Hajja
ta shiga a lokacin Nayla tana zaune kusa da Hajja sun saka ta a gaba ita da Salma
sai wai ta basu labarin lokacin haihuwar Salma.
Sallamar Didi ya saka suka amsa Nayla ta ce, "Didi." Didi ta harare ta ta ce,
"daman kin ce min baza ki sake zuwa ba gashi kin tabbatar." Nayla tayi dariya
sosai, Didi ta kalli Hajja ta ce, "Hajja ki shaida mun yi faɗa da Nayla." Hajja ta
ce, "ko ɗazu sai da tayi zancenki, amma wai baza ta shiga ba saboda Omar. Na ce
Omar ya raba Yaya da ƙanwarta."

Didi tayi dariya suka

8 / 28