Advertisements
Chapter 14 Reading KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA

Author :  NANA HALEEMA Category :  Complete Novels

Chapter   14 / 28

39K to 42K   out of 83.2K words

ma'aikacin gwamati ne ko hamshaƙin ɗan kasuwa. Dan ƙananun
kaya ya saka harda takalmi sau ciki, kai baza ka kalle shi kace Damisan da ke zance
bane.

Narma kuwa tsaf ta shirya cikin riga da siket ɗnkin straight siket, ya kamata sosai
ɗakyar take jefa ƙafarta saboda yadda ya kamata, ta yafa mayafi babu laifi ta saka
da ɗan saka mai girma amma chantily ne gabaɗaya ana ganin jikinta. Wayarta taji
yana ƙara ta duba ganin mai kiran sai ta ɗauka aka yi mata magana ta kashe ta ɗauki
wayar ta ta sakko daga saman.

Harabar gidan ta fito duk ma'aikatan gıdan suka ƙarasa suka gaishe ta maza da mata,
shi kam yana zaune abin sa gefensa Tk shida kunama. Kallon agogo ya yi yaga saura
mintina biyar a lokacin da ya bata ya tashi ya tawo wajan Tk da kunama suna take
masa baya, ya buɗe motar ya shiga ya yi mata key bai ce mata komai ba.

Narma sai da gabanta ya faɗi ganin yanayinsa a yau ya saka taji wani iri a
zuciyarta, gudun kar abinda ya faru jiya ya faru ya saka ta buɗe bayan motar ta
shiga Tk ya shiga gaba shi kuma ya ja motar suka fita. Ƙhamshin turarenta ya gama
cika motar, ga ƙhamshin mai daɗi da tsayawa a rai bai ce mata komai ba itama bata
ce masa komai ba.

"Tk."
"Allah ya ja da zamanin Madugu."
"Ina ne Arewa24?."
"Nan gaba ne babu nisa." Bai sake magana ba ya cigaba da tafiya Tk na nuna masa.

Yadda ya furta magana ta biyu sai ta kalle shi tana mamakin wai shine ya yi maganar
ko ba shi ba, ganin shi ne yake maganar sai ta girgiza kai tana tunanin anya wannan
ɗan daba ne kamar yadda Dad yake faɗa? Anya shine Tiger ɗin da ake faɗar
tsagerancinsa a duniya?. Kai gaskiya da sake tana tantama akan sa.

A bakin gate suka tsaye ta kalle shi kamar zata yi magana sai kawai ta fasa dan so
take taga iya gudun ruwan sa. Fita tayi ta shiga ciki kamar yadda bata yi magana ba
babu wanda ya kula ta.

Suna zaune shi da Tk duk da ba magana suke yi ba kowa harkar gabansa yake yi, shiru
babu ita babu alamun ta kusan mintina talatin. Agogo ya kalla ya ga sha biyu na
rana har ta kusa ya sake kallon inda ta shiga ya yi tsaki. Mintina goma ya ƙara
mata in bata fito ba zai yi tafiyarsa ai ba driver bane ba shi da zata ajjiye shi a
waje bata fito ba. Ita kuwa an jima da gama interview tana sane tayi banza dashi
tana so taga ƙarfin iskancin sa shiyasa tayi zaman ta.

Gajiya tayi da zaman ita kanta, bacci take ji hakan ya saka ta fito a lokacin ya
kunna motar zasu bar wajan kenan. Ganin ta fito ya saka shi ya dakata ta buɗe ta
shiga tana cewa, "wai da ban fito ba kenan tafiya zaka yi?." Tk ya ce, "to Damisa
yaron ki ne da zai zauna yana jiran ki?." Narma ta ce, "kai ba da kai nake magana
ba, kayi min shiru kafin na ɗauki mataki akan ka."

"Mataki akan wa? Wai ni Tk? Gaskiya....." Kallon sa Omar yayi hakan ya saka ya ce,
"Tuba nake Madugu ta zo ta rainin hankali ne." Narma ta zo iya wuya saboda ɓacin
rai cikin masifa ta ce, "Kai wai waye kai? Me ka ke dashi da ina magana zaka yi min
banza?. Me ka ke dashi da zaka tafi ka barni a kan titi iyeee!" Ta faɗa da ƙarfin
gaske wanda hakan ya saka Omar taka burki da ƙarfi.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️*Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 12.*

Yadda ya taka burki da ƙarfi sai da tayi gaba kamar zata kifa kafin ta koma daidai
ta zauna, ya jiyo ya kalle ta suka haɗa ido bata ɗauke idonta shima bai ɗauke ba ya
ce, "in kika sake yi min magana a motar nan wallahi sai kin sauka, ki aikata ki
gani." Mamaki yake bata da tsoro, ita da motar gidan su shine yake cewa in ta yi
wani abun ba daidai ba sai ta sauka? Lallai wannan anyi ɗan rainin hankali, rainin
hankali mana, in ba haka ba ita zai kalla ya ce in bata yi shiru ba sai ta sauka
daga motar da babanta ya siya.

Sai kuma ta kasa magana tayi shiru ya cigaba da jan motar yana aiyana wallahi in ta
sake masa magana sai ta fita daga motar sai dai ta hau abin hawa ta koma. (Omar
akwai ƙarfin hali).

A haka suka koma gida motar tsitt babu wanda yake magana a cikin su sai ƙhamshinta
da ya cika motar gabaɗaya. Yana tsayawa a gidan ta buɗe motar ta fita, ta kalle shi
bayan ta fita shima ya fito ta ce, "zan ga abinda ka ke taƙama a duniyar nan, zan
ƙure maka gudu, zaka fahimci ni ba sa'ar wasan ka bace ba." Tk ne ya zabura ya yi
kanta Omar ya ɗaga masa hannu alamun ya ƙyale ta, ya juyo ya kalle ta ya ce,
"cigaba."

Wani irin baƙin ciki ya zo ya tokare mata a maƙogwaro, kenan ya mayar da ita
shashasha mara hankali kenan ta cigaba da magana mahaukaciya. Juyawa tayi a fusace
ta shiga cikin gidan ta cillar da mayafin jikin ta a haukace. Wayarta ce tayi take
ƙara ganin sunan Ashraf ya saka bata ɗauka ba ta tashi ta hau sama a guje raina a
ɓace matuƙa.

Da wannan ɓacin ran tayi sallah sannan ta yi wanka ta kwanta bacci zuciyarta nayi
mata saƙa da kwancewa akan abinda zata yiwa Omar dan ta huce. Bata farka ba sai
bayan la'asar, ta tashi ta sake sabon wanka ta sako riga da wando na shan isaka ta
sakko ƙasa da niyar cin abinci. Kamar yadda ta zata mai dafa mata abinci ta dafa
abinci ta ajjiye, ta a dining table zauna ta zuba abinda take so ta fara ci.

Wayar ta ce ta sake yin ƙara ganin mai kiran sai ta ɗaula ta ce, "ina ciki." Abinda
tace kenan aka yanke wayar ba jimawa aka shigo falon.

Kyakykawan saurayi ne fari tass siriri mara jiki ya shigo yana kallon ta daga inda
take zaune tna cin abinci. Kallon sa tayi sai ta miƙe ta ɗauko plate ɗin abincin ta
shigo cikin falon tana cewa, "Welcome Baby." Ƙare mata kallo yake yi dan shigar da
tayi ta yi masa kyau a idanunsa sosai. Surar Narma tana daga cikin abinda yake
ɗaukar hankalinsa a kan Narma, duk lokacin da zai yi arba da ita sai yaji shauƙin
son kasancewa da ita cikin yanayi na soyayya. Ya so hakan ya kasance tsakanin su
amma taƙi ba da haɗin kai, da ya yi magana sai ta ce ya jira sai bayan auren su,
shi kuma gani yake kamar bazai iya jurewa ba.

Ɗan hugging ɗinsa tayi daga gefen kafaɗarsa kana ta zauna a akan kujera ta ɗora
ƙafa kan ɗaya tana cigaba da cin abincinta. Zama Shima ya yi yana kallon ta cikin
yanayin da ya ke kasancewa da duk lokacin da suke tare, yanayin sa na sake yin gaba
in ta yi hugging ɗinsa ko ta yi masa kiss sai ya ji kamar zai zauce. Ajiyar zuciya
ya yi sannan ya ce, "What wrong? Naga fuskarki da alamun damuwa."

Yatsine fuska tayi ta ce, "Wani banzan driver Dad ya haɗa ni dashi yake raina min
hankali, wai ni yake ɗagawa murya har yana cewa in na sake magana sai na fitar masa
a mota." Ashraf ya ce, "Like Seriouly? Ke ɗin yake faɗawa haka?." Bata amsa ba sai
murmushin takaici da tayi tana girgiza kai.

"Waye shi haka?."
"Wani ɗan iskan mutum ne dan daba wai shi tiger, ni yake yiwa tsawa saboda Dad yana
son ya dinga kai ni ko ina nake so."
"Kuma Dad ɗin ya san da haka?."
"Yes he knew, but today i won't inform him, i want to take action independently and
how him my capabilities." Ashraf ya ce, "That's good my Love, you should teach him
a lesson so he understands you deserve respect and won't tolerate any nonsense."

Kallon sa tayi taga yana kallonta ba, iya fuskarta yake kallo ba duka jikinta yake
kallo sai tayi murmushi ta ce, "zan koya masa hankali."
"Nima zan taya ki." Murmushi tayi tana kallonsa tace, "yaushe ka zo Kano?."
"Ɗazu." Kai ta girgiza ya ce, "yaushe zaki fara event ɗin Samra?."
"Lahh ka tuna min, gobe ne fa, ko makeup artist ban nema.

He looks into her eyes yana wani lumshe ido then he say, "My Narma event without
makeup you looks magnificent." Tayi murmushi ta ce, "Duk da haka dai zan yi
kwalliya." Ya bita da kallo ta ɗauki waya ta kira tana magana da turanci nan da nan
ta yi booking makeup artist za a zo har gida ayi mata home service.

Ashraf ya jima suna hira kafin ya tafi dan shima a gajiye yake ya tafi ya huta da
niyar in anjima zai dawo. Narma bayan ya tafi sama ta hau ta buɗe balcony gidan
tana kallon ma'aikatan gidan ɗaya bayan ɗaya tana mamakin rashin ganin Omar, wato
ko ya taimaye ta ya ji babu inda zata je shine yayi tafiyar sa kamar itace take
aiki a ƙarƙashin sa. Wayarta duba taga number sa Dad ya turo mata kawai ta dubawa
number ido kafin ta girgiza kai tare da yin tsaki ta koma cikin falon.

Omar kuwa ko da suka bar wajan shi da Tk ba gida suka koma ba sai da suka je
wani wajan bai koma gida ba sai bayan la'asar. Yana shiga kai tsaye wajan Didi ya
shiga, ya same ta a zaune tana shan magani ya ƙarasa ya zauna ya ce, "Ya jikin?."
Ta kalle shi ta ce, "Jiki da sauƙi sosai, na sha magani." Ya girgiza kai ya ce,
"kin tabbatar babu abinda yake damın ki?." Ta ɗaga kaii alamun eh.

"AbdulHamid zai zo in anjima, ka zauna ku gaisa." Da to ya amsa mata a taƙaice
kafin ya tashi ya fita daga falon. Ba jimawa AbdulHamid ya ce masa gashi ya zo ta
ce ya shigo ya shigo da sallama ya samu ta ajjiye kujeru gıda biyu kamar wancan
lokacin.

Zama ya yi suka fara gaisawa cikin girmama juna ya faɗa mata duk yadda suka yi da
Kawu da jiran sa da yake yi dan ya ce zai neme shi. Ta girgiza kai ta ce, "Kawu ya
faɗa min komai, bayan ka bar wajansa ya kira ni a waya."
"Haka nake so naji. Amma Aisha na tambaye ki." Ta kalle shi ta ce, "ina ji."
"In Kawu ya baki dama kina ganin zaki iya aurena?." Murmushi ta yi ta ce, "Allah
nake roƙa ko yaushe ya zaɓa min mafi alkhairi, sai gaka kazo, in dai har kai ba
alkhairi bane Allah bazai bani ikon zaɓarka ba."

Ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya ne, Allah ya tabbatar mana da alkhairi baki ɗaya."
Ta amsa da amin. Omar ne ya zo wajan ya ƙaraso yana kallon su ta kalli Omar ta
kalli AbdulHamid da yake kallon sa ta ce, "AbdulHamid ga Omar ƙanina kuma Yayana."
AbdulHamid ya miƙawa Omar hannu suka gaisa ya ce, "Omar ya aiki?."
"Alhamdu lillah" ya bashi amsa a taƙaice yana sake kallon sa dan haka kawai ya ji
ya burge shi.

Didi ta ce, "Ina zuwa haka?." Ya girgiza kai ya ce, "akwai inda zan je." AbdulHamid
cikin wasa ya ce, "ko wajan ƙanwarta mu zaka je?." Kallon sa ya yi ya ɗan saki
fuska amma bai ce komai ba kuma bai yi murmushi ba.

Barin wajan Omar ya yi AbdulHamid ya kalli Didi ya ce, "ma sha Allah, babu wanda
zai ce ƙanin ki ne, kallon farko in aka yi masa za a ace Yayan ki ne dan ya
cancanci zama yayan naki. Yana da kwarjini sosai kana kallon sa kaga jarumi."

Didi tayi murmushi ta ce, "Omar kenan." Shima murmushin ya yi yana mamaki dan shi
yadda ake bashi labarin Omar ɗin sam bai yi kama da haka ba, ba dan ya sani ba ma
da bazai ce shine Omar tiger dake bashi labari ba.

AbdulHamid bayan sun yi sallama da Didi ya fito zai shiga mota sai ga wani babban
mutum mai ƙaramin jiki ya ƙaraso inda yake, ya yiwa AbdulHamid sallama ya amsa da
girmamawa. Mutumin ya kalle shi ya ce, "Bawan Allah don Allah wajan Aisha ka zo?."
AbdulHamid ya ce, "Eh, wajan ta nazo."
"Neman aurenta ka ke yi kenan?."
"Haka ne." Ya girgiza kai ya ce, "kuma ka san duk abinda da suke faruwa a akan
ta?."

Abdulhamid ya ce, "a'a, sai ka faɗa min." Sai kuwa ya gyara tsayuwa cikin son isar
da gulma ya ce, "Ko da naji, da ganin ka yaro ne ɗan mutunci baza ka kawo kan ka
gidan nan ba sai dai rashin sani. Wato Aisha da Omar da ka ke gani abinda suke
aikatawa a gidan nan Allah ne kawai ya sani, ya hana kowa shiga gidan ko almajiri
baya shiga ya yi bara, da shi sai ita kullum su kwana su tashi. Baligi mara aure da
baligar mace a waje ɗaya ai dole a samu matsala, zan iya yi maka rantsuwa da Allah
masha'ar su kawai suke aikatawa a cikin gidan. Shiyasa ba ya barin kowa ya shiga
gidan, irin yaran nan ƴan mata na unguwa ko kallon ƙofar gidan basa yi saboda shi.
Gashi tantirin ɗan iska ajin ƙarshe, kai da ka gashi ma ai ka ga zubin ƴan iska."

AbdulHmaid kallon sa kawai yake yi cikin tsananin mamaki ya ce, "Baba ba ƙaninta ba
ne? Aka ce uwa ɗaya uba ɗaya suke."
"Hmm ƙaninta ne mana, amma zama suke yi kamar mata da miji. Kuma bayan shi ma ta
kan kawo wasu cikin gidan shiyasa take samun kuɗi tana siyan abinda take so. To in
ba mazan banza ne suke bata kuɗi ba wannan sana'arta ta ta siyar da abincin order
wata riba ce da ita da zata dinga wannan kashe-kashe kuɗi? Ai kana gani ka san da
walalin giro a miya, ba a haka kawai ta kai wannan shekarun bata yi aure ba. Akwai
mai biya mata buƙatarta daga gefe."

AbdulHamid ya sake kallon sa ya ce, "to Baba yanzu me ka nufi da labarin nan da ka
bani?."
"Ina nufin ka rabu da Aisha kaje ka samu yarinya ƴar mutunci ka aura, gabaɗaya
unguwar nan babu wanda ya sana salin su, kwatsam suka tare a cikin ta kuma wayi
gari dasu. Ba a ganin dangin uwar su dana uban su balle a saka ran suna da dangi.
Kaga a haife na haife ka, kamar ɗana ka ke bazan ga abinda zai cutar da kai na bari
ba, kayi gaggawar daina zuwa wajan Aisha kafin girman ka da mutuncin ka ya zube a
idanun mutane."

Yayi murmushi ya kalli gefensa kawai idanunsa ya faɗa cikin na Omar da alama duk
yaji abinda suke tattaunawa. Sai kuwa ya ce, "Yauwa Omar ƙaraso ga Baba yana bani
bayani akan ku." Mutumin yana ji an ce Omar ya kalli wajan da sauri ya ganshi kuwa
a tsaye yana kallon sa ya Kalli AbdulHamid murya na rawa ya ce, "Aisha ai mutuniyar
kirki ce, ga sanin ya kamata, ga girmama na gaba da ita. Don Allah ba abinda nake
faɗa maka kenan ba?."

Ba AbdulHamid kaɗai ba Omar ɗin kansa sai da yayi murmushi jim abinda Baba ya ce,
bai nuna ba haka ya tako cikin ƙasaita yana zuwa ya kalli mutumin ya ce, "Waye kai
a layin nan?." Jikinsa ya soma rawa kar kar kar saboda tsoro. Omar ya kalli gefe
yana girgiza kansa kafin ya sake kallon sa fuska babu walwala ya ce, "nace maka
waye kai a layin nan?." Murya tana rawa ya ce, "Malam Salihu."

"Mai kiran sallah?" Omar ya tambaya yana kallonsa. Jiki na rawa ya amsa AbdulHamid
ya ce, "Yanzu Baba kana da matsayin mai kiran sallah ma a unguwar nan amma ka ke
faɗar irin wannan maganar akan yaran wasu? Ko baka da yara matsayinka na babba
wannan ba girman ka bane balle na tabbatar kana da yara kaima da ka ke burin aurar
dasu. Ko da da gaske abinda ka faɗa gaskiya ne ka taɓa gani da idon ka?."

Shi dai yayi shiru sai hannunsa da yake rawa sosai. Omar ya kalle shi ya ma rasa
abinda zai yi masa, baya son yiwa manya wani abun ko ya yi niya sai ya kasa amma
babu abinda zai saka ya ƙyale Malam Salihu, sau biyu kenan yana kama shi da irin
wannan munafurcin a kan su.

Malam Salihu ya ce, "Ni fa wasa nake maka yaro, so nake naga ko maƙaryatan unguwar
nan sun faɗa maka haka, dan Aisha mutuniyar kirki ce." Omar ya ce, "Zaka tabbatar
da mutuniyar kirki ce in nayi maka illa yanzun nan."

Malam Salihu ya ce, "Ka bashi haƙuri don Allah" ya faɗa yana kallon Abdulhamid.
Shima ya kalle shi ya ce, "Baba ai ko ya yafe nima bazan yafe ba, matar da zan aura
ka ke yiwa ƙazafi a gaban idanuna. Ko shi ya ƙyake ka ni sai hukuma ta raba mu da
kai."

Tk da goje Omar ya hango da ido yayi musu alama su riƙe Malam Salihu, caraf Tk ya
kamo shi daman haushinsa yake ji shekaran jiya ya yi masa munafurci hakan ya saka
ya ce, "Malam Salihu yau ka zo hannu, ƙarshen munafurcin ka ya ƙare."

AbdulHamid ya kalli Omar ya ce, "Omar ka ƙyale shi kawai kar ka yi masa komai, ka
bar shi da halin sa." Omar kallon sa ya yi jin yana bashi umarni kamar wani wanda
ya haifa. Omar ya ce, "ai ba a dakatar dani in nayi niyar abu sai nayi." Ya yi
murmushi ya ce, "kar ka manta kamar yayan ka nake tunda yayar ka zan aura."
"Ko ita bata faɗa maka bana bari ba?." Ya yi murmushi ya ce, "a yi min wannan
alfarmar." Kallon sa ya yi zai sake magana sai kawai ya fasa ya kalli su Tk da suke
tsorata Malam Salihu ya masa alama da su ƙyale shi ya juya ya shiga gida, shi kuma
ya hau mota ya tafi yana mamakin munafurci irin na mutane.

Omar yana shiga gida wayarsa ta fara ƙara ya duba ya ga number ce ya ɗauka,
ana fara magana ya gane Yahya ne ya sanar dashi Narma zata fita in anjima. Bai amsa
ba ya yanke wayar dan ransa a ɓace yake sosai ko wajan Didin bai koma ba.

Sai bayan sallar i'sha yaje gidan ya tarar da Narman ma ta hau mota ta tafi wai ta
gaji da zaman jira ita ba baiwarsa bace ba. Tsaki ya yi da ya san hakan mai zai
fito dashi daga gida yanzu. Gabaɗaya zuciyar saa cushe take akan kalaman Malam
Salihu, duk da ba haka aka saba ba amma ya ji zafi sosai. Ɓacin ran da yake ji ya
saka shi takowa a hankali yana tafiya

14 / 28