Advertisements
Chapter 296 Reading ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu

Author :  Mai Dambu Category :  Complete Novels

Chapter   296 / 321

885K to 888K   out of 962.4K words

ya shiga anan ya sayo abubuwan da ya ga take bukata, daga dangin kayan tea, bargo asalin bargo safa wanda har ya wuce ya dawo saboda ganin yadda jan lallen da aka mata yana daukar idanu, sai wata ƙatuwar rigar sanyi da ya hango don ya ji inda suke akwai sanyi, takalmin roba domin da na adonta tazo, yasan bata ci abinci ba, a hankali ya gangara skycrown ya saya mata gasashen kaza, yana komawa kuwa mai da ita vip za ayi ta kwanta, sai fruit da ya shako a ledar, lokacin da ya iso asibitin bai cire kayan ba, samun likitan yayi ya ce mishi."" Sam Please a tura ta vip nan akwai sanyi!"" "" Ok sir!"" Ya nufi office dinsu can kuwa aka tura gadon aka daura a wata yar mashin suka wuce da ita Amenity, sai da aka bata babban daki, ya koma waje ya shigo da kayan da ya zo da shi, ba ruwansa da wnai yan uwanta suna kallonshi bude jakar bargon yayi ya lullube ta da shi, ya dauki Safar ya gama kallonsu kamar ya basu kawai wata zuciyar ta saka shi sai da ya saka mata sannan wata munafukar kunya ta kama shi, amma sai ya wani waske kamar bashi ba, ya mike tare da cewa. ""Tow ni zan koma ma sauki. Idan ta farka ta ci abinci Please idan sun shigo zasu bukaci a sayo magani gashi nan!"" Ya ajiye wani katinshi, sannan ya fita daga dakin yadda ya daure su sai aka rasa me ce mishi."
"An gode, da gudu Aunty Innah ta fito ta ce mishi..""sir ga key ɗin motar ka je da shi........"
"[12/8/2025, 11:21 AM] Maman Walid: 2"
"Dama yana tunanin yadda zai hau mashin, amma tana kawo mishi sai ya kasa amsa ya ce mata. "" Tow ke"
"fa?"" "" Zan kwana da ita?"" Ta fada, amsar key ɗin yayi yana faɗin. ""Thank you!"" Ya juya har zai tafi ya ce mata. ""Please ki kula da ita!"" Daga haka ya bar asibitin, zuciyarshi cike da nutsuwa domin yanzu hankalinsa ya kwanta. Lokacin da ya isa hotel wanka yayi ya sallaci sallah isha, sannan ya kwanta. Barci"
yayi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Har ya so ya makara.
***
"Yunwa na farka da shi tun karfe shida na safe na farka na sha tea da Aunty Innah ta haɗa min, na ce"
"mata. ""Yaushe aka dawo da ni nan?"" Tana azkar bata kula ni ba, sai da ta idar lokacin ta cire min ruwan da aka kara sakawa karfe biyu na dare. ""Sannu kin ji, Allah gayen nan yana sonki."" ""Hmm!"" Na ce mata, sannan na sauka na je nayi alwala na zo na gabatar da sallah isha da na asuba, ina idarwa ta haɗa min tea da kazar jiya naci kaɗan, kafin na koma na kwanta, ina mamakin yadda aka yi be bar garin nan ba, barci ya kara gaba da ni, wuraren tara na bude idanu saboda likitoci sun zo duba ni, haka suka yi ta min yan tambayoyi ina basu amsa karshe sai da aka binciko tsohon file dina, shine basu hada mana tea kamar ina dauke da cutar kansa. Bayan sun gama suka kara rubuta min magana daya ya cewa Aunty Innah gobe in sha Allah za a sallame ni. Bayan sun fita ta haɗa min ruwan wanka, na shiga nayi na fito tare da gyara jikina. ""Ina su Aunty Hindatu basu zo ba ne?"" ""Tazo kina barci duk sun zo ai!"" Gyada kai nayi ina mai zama sai ga Yadiko ta shigo Ya Sani yana bayanta, ""Gawa taki rami!"" ""Yadiko ki ce ya bari."" ""Ai bashi da girma sai na jikinsa"" ta fada tana hararanshi, abinci aka ajiye min na fara murmushi. Aka zuba min na fara ci a hankali, ina jin wani dad'i. Kafin karfe sha biyu dakin ya shiga, duk da haka sai naji ina son ganinsa ko ya tafi ne? Domin Sani ya kai Aunty Inna gida, wurin karfe daya da rabi dakin su Aunty Hindatu an cika ya turo kofar daidai na dauki farfesun kayan ciki ina ci ya turo kofar, ji nayi kamar zuciyata zata faso daga kirjina, na kasa saka tsokar a bakina. Jikina yana wani irin kerma ta ciki, a tausashe ya yi sallama, da cikakken muryanshi ta asalin jarumin namiji, aka amsa mishi a hankali na mai da cokalin na ajiye tare da janyo hijab dina da ya zame a kaina, gyararren gashin kaina yadiko ta tufke"
"min shi a baya. Gaida shi suke amma idanunsa yana kaina, duk yadda nayi motsi ina jin idanunshi a kaina. A hankali na d'ago kai sakamakon tambayar da yake min na ya jiki. Muka yi ido hudu da shi, shi dai Allah ya mishi baiwar wanka idan ya saka kaya cikin ikon Allah sai ka ga kamar a jikinsa kayan aka yi su. ""Da sauki"" na furta ina jin kamar amsar bata kai zuci na gaya mishi ba. ""Turaki ka karya kuwa?"" Sosa kai yayi yana kallona. ""Umma ai ina sitta shawal!"" Ya fada idanunsa har lokacin yana kaina. Ban san yadda aka yi ba nake ji kamar wani abu a tsakanin kirjina yana motsi ba, jinin jikina kamar ana zagaye min shi da wani abu, hatta kaina wani irin motsi yake wanda ban tab'a jin haka ba sai a yau. ""Ke Hashiya bashi kujera don gidanku, zauna turaki."" Bashi kujeran da yake kallon gadon Hashiya tayi ya zauna yana mai daura kafa daya akan ɗaya, wannan kamar halayyarsa ce, wannan zaman. Kaina a kasa.. ""Yadiko me suka ce?"" Ya tambaye ta, ""Ga Hindatu nan ni basu gaya mana kome ba."" Juyawa yayi wurin Aunty Hindatu. ""Jininta ne ya hau dama tana da shi, amma wai damuwar da ta shiga ya saka ya hau."" Ta fada tana wani dauke kai"
"ita fa yanzu gani yake kamar yana haka ne don yana da kudi. ""Allah ya bata lafiya!"" Kallon agogon hannunsa yayi ya kuma kalle ni. Mikewa Yadiko tayi tana faɗin.. ""Kuzo ku raka ni duba jikin jikar amaza!"" Ba musu suka taso, ""Nima yanzu zan tafi fa!"" Da sauri na d'ago kai ina kallonshi, ""a'a muma yanzu zamu dawo!"" Inji Yadiko, suna fita ya janyo kujerar zuwa jikin gadon ya zuba min idanu. Yana kallon kafana, ganin safar da rigan sanyin da ya kawo jiya ne a jikina yasa shi cewa.. ""yanzu ya kike ji?"" Ya tambaye ni yana kallon hannuna da nake ta wasa da cokalin, daukar bowl din yayi ya fara sha a hankali. Sake baki nayi ina kallonshi. ""Yunwa nake ji, kuma da kunya na bude cikina na ci!"" Abin mamaki ya bani, a hankali na dan motsa kadan na sauko da kafana kasa, na dauko kofi na shiga haɗa tea. "" Lipton is ok! "" Na saka mishi suga zan kara ya ce min.."" idan kika kara sai nayi gudun awa biyu kafin ya fita a jikina!"" A hankali na mika mishi na janyo daya kular na zuba mishi dankalin turawa da agada, ya fara ci yana kallona. Kara"
"mishi farfesun nayi ya ci sosai.. sannan ya ajiye kofin ya cigaba da sauke numfashi, tissue ya dauka ya"
"goge bakinsa. Kome nashi abin burgewa ne, idan ya yi ado kamar wata macen. "" Nayi miki kyau ko?"" Ya"
"tambaye ni, murmushi nayi na dauke kai. Shafa sajenshi yayi da yake dauke da yan furfura. ""Ina ta tsufa!"" Ya mike, yana hamma. Kallonshi nayi a hankali na ce mishi. "" Ba dai tafiya ba?"" Kaina a kasa, a hankali ya ɗan rankwafo ya kai ɗaya hannunsa jikin karfen gadon daya kuma saman gadon bar ina jin hucinsa ya ce min. ""Na zauna ne?"" Wani irin diriricewa nayi tare da dan matsawa baya na ce mishi. ""A'a ka je abinka!"" A hankali yayi kasa da kanshi daidai kunnena ya ce min. ""Zan tafi gaida Mama ne!"" Da sauri nayi baya sai da gadon ya motsa, na kasa hada idanu da shi, murmushi yayi yana faɗin. ""Ni ba mutumin banza bane."" Ya fada yana barin dakin, a raina nace dan renin hankali kawai, waye mutumin banza. Ashe da ya fita motar Aunty Innah ya jira su Yadiko suka zo ya mika mata key ɗin yana ta bata hakuri ya fasa mata motar, murmushi tayi ta ce mishi. ""Kada ka damu zata gyara."" Har ya tafi inda motarshi yake Malam Hamza ya kawo mishi, ban san me ya sani nake murmushi ba, amma har suka shigo sun samu ina murmushi, hannuna biyu a kumatuna, kawai abinda ya faru ne yake dan mintsini kawai sai naji wata irin kunya da ta rufe ni, kasa magana nayi Aunty Zakiyah sai dariya take tana faɗin. ""Yarinya gaya min gaskiya."" ni dai banza na mata, can Yadiko dasu Aunty Zakiyah suka tafi. Aunty Hindatu ta kalle ni a hankali, tana faɗin. ""Yana da kirki ko?"" Ban iya bata amsa ba, nayi shiru ina wasa da hannuna.."" Kina sonshi har haka ne? "" Zare idanun nayi nace mata. "" So kuma? Ni ban ce ba, sannan ai oga na ne a wurin aiki!"" ""Ina jin tsoron kada ya cutar dake kamar Hafiz?"" A hankali naji zuciyata tana motsi tare da jin kamar magana ta gaya min. Amma sai na danne na ce mata. ""Shi din zaki ne, duk inda ya tsaya sai ya nuna gaskiyarshi. Mun tafi Japan tare da ko rike hannuna bai taɓa ba, tunda Mama ta iya bude mishi zuciyarta bana tunanin zai iya cutar dani, sannan batun soyayya ni har ga Allah babu shi a cikin tsarina. Yana da kirki amma bana jin Matarshi zata zo ya zauna da wata mace bayan ita?"" Da mamaki take kallona. "" Yana da mata dama?"" Na kirkiro haka ne don kada su saka burinsu akanshi."
"Amma nasan bai da mata kuma bai taɓa ajiye ta ba. Haka muka gama hiran take bani labarin abinda ya faru da kashe kuɗin. "" Kuma na ga kamar kina farin ciki da ganinsa fa."" Ban ce mata kome ba har zuwa yamma sai gashi tare da Mama, yadda suke hira da Mama sai nayi ta mamaki, gayen nan ya iya shiga jikin mutum, Sallamar Ya Sani da Taj muka amsa na rike baki ina faɗin. ""Kai ne a Bauchi?"" "" Eh kai Hajiyata gani nan nazo cin masar Bauchi koda yake mutumina ya bani na ci. "" Sai nayi ta kallon Taj ina murmushi. "" Lallai ka ji dadin ka, shine kazo asibiti ganina?"" "" Oga na zo ɗauka! "" Ya fada yana nuna min shi da idanu, sai lokacin na lura da haɗe rai, tare da shiru kuma da hira yake yiwa Mama. Itama ganin yadda yayi shirun sai ta zuba min idanu. Sai na diririce bakiɗaya na rasa me yake min dad'i. Shi kanshi bai ji dadin yadda nake sake da Taj ba. Mikewa yayi na ji yana yiwa Mama magana da fulatanci, am surprised da naji Mama itama ta amsa mishi suka fita ko kallona be yi ba ya saka kai ya fita abinsa. Ban san lokacin da na leka na ga da gaske tafiyar yayi sai kuma wata zuciya ta ce min sai me? Da wannan kwarin gwiwa na cigaba da jiran fadar Mama ai kuwa da ta dawo na sha fada, shigowa Aunty Innah tayi tana faɗin.. ""Ke a ina kika samo mutumin kirki haka? Dubu dari biyu ya bani na gyara motar fa."" Yadda tayi ta zuzuta shi Mama tana wani blush, irin ya mata abinda ya dace. Washi gari aka sallame ni cike da farin ciki kusan wani ikon Allah bakiɗaya sai a bar min katinsa. Haka muka dawo gida na samu Baban Jama'are ya zo shida Goggo Uwani, nan san me suke tattaunawa a kai ba, amma na sha jinin jikina, sai dai ba ayi nisa ba, Mama ta musu tass haka suka kwana washi gari suka koma Jamaare, nima washi gari muka bar Bauchi Mama ta ce gara mu wuce kawai domin zamanmu a Bauchi kara fitina yake amma bamu tafi ba, yankari muka wuce da su Ya Umar da Tahir, Aunty Hindatu da Aunty Innah, suma su Ya"
"Umar kowa da Matarshi, bakiɗaya muka wuce har da Sani, mota guda muka dauka. Hankalina yana kan"
"wayata har muka isa dinduma anan muka hadu da wasu motoci, muka shiga cikin garin yankari. Tunda"
"muka isa gate din Yankari ja hango kamar shi ne, ya fito a motar yana. ""Kambu kamar Mr Turaki?"" ""Eh shine kai!"" Inji Aunty Innah tana dariya, ""ai shi yayi invite dinmu nan!"" ""Shi din?"" ""Eh kai!"" Shiru nayi ina kallon yadda suka ci amanata da shi, har ciki muka shiga cikin, sai da muka fito ja gyara zaman mayafina, na fito ina kallon inda yake waya alamar magana ce mai muhimmanci, yadda iya daura hannu daya a kirji, daya yana waya kunnen. Janye idanuna nayi da sauri saboda yadda ya kama Ni ina kallonshi. Na shiga cikin mutane. Haka kawai ya kama ni ina kallonshi. Haka muka shiga cikin kafin ya iso suka bashi hannu aka gaisa, Yaran Yayuna suka gaishe shi ya amsa yana fadar sunansu kamar an bashi irin sunan kowa."
"Kallonshi nayi a fakaice. Da wutsiyar idanu ya kalle ni, ai kuwa muka kama juna, dauke kai yayi ya shafa kanshi wanda yake dan dauke da ratsin fari alamar furfura. ""Wannan mutumin ya tsufa amma sai wani abu yake kamar yaro!"" ""Waye?"" Aunty Zakiyah ta tambaye ni, kallonta nayi ina faɗin. ""Ban ce kome ba!"" ""Munafuka cikin ƙananan kayan ne ya tsufa Allah ki sake ranki bature ni ba ruwansa da wani harkar al'ada kada a kashe mishi rayuwa. Irinsu zasu jima suna ririta mace musamman."" Tura mata baki nayi ina"
"faɗin. ""Ni ban tambaye ki ba!"" Nayi gaba abina, domin na lura.........."
"[12/8/2025, 11:21 AM] Maman Walid: 3"
"Ta saka min idanu, tunda mutumin nan ya fara zuwa gidan Ya Ado na lura da Aunty Zakiyah Yar sa'ido ta"
"koma, tura baki nayi na naki kulata haka muka shiga cikin wurin shakatawar, masu karban baki suka shiga mana jagora, zuwa dakunan da zamu zauna. Wani karamin jaka aka kawo min, ""inji Mr Turaki ya ce a kawo miki."" Amsa nayi ina kallon jakar na shiga cikin dakin, ni daya ce kamar mayya. ""Tow me zanyi da jakan nan?"" Na yi magana ni ɗaya, wayata ce tayi ƙara ma ɗauka don number bakuwa ce. ""Lubabatu ce?"" ""Eh waye?"" ""Hmmm Hajiyar Hafiz ce, na kira na gaishe ki ne na kuma gaya miki Hafiz tunda ya ganki"
"bai da lafiya!"" ""Ayya Allah ya bashi lafiya,"" na kashe wayar tare da kallon kofar dakin da na ji ana tab'awa, shine ya bude a hankali ya ɗan tsaya tsakanin kofar dakin da kuma ciki, wayar ta kara yin kara kamar ba zan daukar ba, na saka raina a inuwa na dauka. ""Luluna ki saurare ni? Luluna ki yafe min."" ""Allah ya yafe mana bakiɗaya amma don Allah ka kyale ni saboda kai ba zan sauya layi ko nayi ta b'ata lokacina ina blocking dinka Please ka daina kirana."" ""Luluna ki dawo gare ni, zan daina kina dawowa ne kawai zai saka na daina bibiyarki?"" ""Idan naki fa?"" Na tambaye shi cikin masifa da tsiwa na ce mishi.. ""idan naki fa?"
"Kashe ni zaka ko hana ni aure zaka yi kamar yadda kake fada? Tow ka sani kafin kayi wani ya rigaka."" Na"
"kashe wayar baki daya koda na d'ago kai babu shi babu dalilinsa, fitowa nayi na samu baya nan wurin, haka na koma na zauna."
"Wurin karfe Bakwai na dare, Aunty Hindatu da Innah suka shigo sai matan Yayuna suka bude wannan"
"jakar da aka turo min suka ciro wata doguwar riga mai kyau suka bani na saka. ""Me yake faruwa?"""
"""Muje zaku gani?"" Inji Aunty Zakiyah, ni sai abin ya dame ni zan kara magana ta saka min hannu a bakina. ""Shiiiiii!"" Haka nayi shiru tare da bin duk abinda suke aikatawa, har aka gama muka fito lokacin anyi sallah isha domin sai da muka yi sallah, kallon kaina nayi tayi ina mamakin yadda nayi kyau ba wani"
"kwalliya nayi ba amma sai nayi na dan yi kyau, fitowa muka yi zuwa wani babban hall, abun dariya wai"
"birthday aka shirya min, kasa magana nayi ina kallon abin kamar irin how dai ayi maka abinda baka zata"
"ba, in fact sai abin ya zo min wani iri ban tab'a kawowa ni za ayi min wannan abin ba. Idanuna ya cika da kwalla. A hankali suka fara waka idanuna cike da mamaki. Har suka gama. Wukar suka bani na fara yankawa. Kallon wurin baki daya nayi ga shi ne bako a cikinmu, a hankali na mika mishi cake, murmushi yayi ya saka hannu ya amsa tare da cewa. ""Happy birthday Lunah!"" Hawaye ne suka zubo min, anya wutsiya rakumi bata yi nesa da kasa ba? Haka na bi Yayuna na basu, wani hoton majigi ya bayyana a hall, a ina aka samo hotona. A hankali na taka zuwa wurin da yake zaune na dan tsaya a jikin bangon da yake gefe shi. Shima tashi yayi ya jingina da bangon. Shiru ya ratsa tsakaninmu, kusan rabin hankalinmu yana kan majigin, yayinda yake ta fama da wayarshi. Satar kallonshi nayi kafin na ce mishi. ""Baka da lokacin kowa sai na wayarka."" Murmushi yayi ya ce min. ""Tunda kika zo kin duba aikin office dinki?"" Kallonshi nayi kamar bashi yayi Maganar ba hankalinsa yana kan wayar. ""Ina da meeting ki zo muje?"" A dan razane na ja da baya. ""Ba zan tab'a wuce iyakata ba, yayunki xan tambaya."" Dan ajiyar zuciya na sauke ya tambayi Ya Umar suka ce bi shi, tabbas sune mutanen da na gani yadda muke tattaunawa tare da abinda ya kawo su, har muka gama yana fama wayarshi, wurin karfe goma ya rako ni, sai xa muka fara tafiya ina gefenshi na ji ya riko hannuna tare da fisgo ni, kwace hannuna nayi cike da mamaki, ""hmm!"" ""Hmm what? Ka dauka ni don bani da aure nima yar iska ce kamar yadda ake yiwa sauran zawarawa kallon, kada ka kara kai hannunka jikina, I'm not whore kada ka ga ina aiki a kamfanin ka, ka zata ni yar iska ce, ka bani kunya kada na

296 / 321

Chapters