Author : Mai Dambu Category : Complete Novels
yadda ya saka Ni cin abinci. Ya Ado da Tahir suka iso. "" Mr Turaki!! "" Hannu ya saka a bakinshi, suka yi shiru nima kallonshi nayi ya ce min."" Ci abinci! "" A hankali nake ci ina kallonshi, na kasa dauke idanuna a kanshi, sannan na kasa daina cin abincin ba, a hankali na ajiye spoon din. "" Na koshi!"" ""Good!"" Ya dauki sauran yana ci, yana faɗin. ""Ba kome yake bukatar ayi magana akan"
"shi ba, je ki wurinsu Mama."""
"Tashi nayi na bar wurin ya ce musu, "" zauna San."" Ya nuna musu akan su zauna. Sai da ya ci abinci ya"
"goge hannunsa. ""Kun ga sakon kamfanin KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY ko?"" Gyada kai suka yi, "" gobe muna da board meeting, Hindatu ta wuce da Luna Bauchi, gobe idan muka gama meeting din zan tura muku sako. Ita kuma abinda ya sa na ce ta koma can, saboda wasu abubuwan zasu faru kai ma baka"
"tsira. "" Daga haka ya mike, ya musu sallama."
"Basu tab'a fuskantar crisis a kamfanin ba kamar wannan lokacin, idan har kana niman dan kasada,"
"Turaki ya dauki wani irin kasada, abin da yake so dole sai anyi zama da duk masu hannun jari a kamfanin ayiwa Lubnah sassauci, xa a dawo mata da 75% na kayan Abba sannan zata yi aiki a kamfanin na tsawon shekaru babu albashi, shine yake son ayi vote a cire aikin nata, sannan yana bukatar goyan bayan kashi hamsin da biyar na masu hannun jarin, ta haka ne zai samu goyan baya, shi kanshi kudin da zai biya kamfanin domin a sake kayan ba karamin kudi ba ne, don ma Allah ya taimaka akwai dukiyar mahaifiyarsa na wurin kakanshi, wannan ya taimaka, ya bada kusan rabi da kwata shine 75 yadda za a dawo da kayan Abba cikin ruwan sanyi. Amma koda yayi haka bai zama dole ya iya haka ba, domin sai da"
"goyan bayan abokan kasuwancinsu. """
"Don haka ya koma ya samu Jasminah da Uncle Auta da Ubaid wanda shima ya shigo cikin tafiyar, domin"
"yasan kaf duniya babu abinda zaka yi yanzu ya burge Turaki kamar ya goya mishi baya akan Lubnah, da ya zauna yayi nazari sai ya ga babu riba, don haka ya zauna yana zaune aka fara tattaunawa, a daren suka yi ta tura sako da kiran masu hannun jari da rokon alfarma sannan suka gaya musu akwai sako su duba, kafin dangin mahaifinsa su san abin da yake faruwa mutane hudu din nan sun gama kome basu bar gidan ba sai karfe biyu na dare, kwanciya yayi a parlourn. Maganar gaskiya zuciyarshi ta gaji a yanzu"
fa ya dace ace ya ajiye iyalinsa na kansa ne...........
(Ku yi hakuri yau nayi baki ne)
"[12/10/2025, 11:24 AM] Maman Walid: 8"
"""Hmmmm!"" Ya furta a hankali, ai yanzu kome ya lalace, domin bai isa ya ce zai tun kari. Maganar"
"aurenta babu shi tunda yanzu yasan duk abinda zai yi cewa za ayi don yana da alaka da abinda ya faru ne. Washi gari har da makara tun yana Sallah asuba da ya dawo madadin ya motsa jiki sai ya kara kwanciya, har sai da aka yi ta buga mishi kofar parlourn ya farka ya shirya a gurguje, a lokacin da suka isa kamfanin dayawa masu hannun jari a kamfanin sun iso shi yake da kashi sittin da biyar amma yana bukatar goyan bayansu a kowani hali, Tarik ya gani tsaye yana murmushi, ya ji dadin ganin Tarik domin shima zai bada nashi gudunmawarsa, amma kuma ta wani gefe yana bala'in shakkar kada Tarik ya kuma shige mata, gaskiya yayi farin ciki amma kuma gefe guda yana bakin cikin da zuwan Tarik domin yanzu zai dagula mata lissafin da yake ƙoƙarin daura mata, haka yayi ta bin manyan baki yana musu godiya domin bai kawo zawo bashi hadin kai har haka ba, ai kuwa daga nan suka wuce asalin conference hall din da suka shirya don baki. Haka kuwa suka hadu bakiɗaya, babban adduarsa ya ga Uncle Auta da Kakanshi, kuwa wurin minti goma da fara faron suka shigo da yan uwan Babansa, ajiyar zuciya suka sauke aka fara meeting din, cikin ikon Allah da girmamawa, ake gabatar da kowacce bayani da kuma dalilin taron, har aka zo wurin da ya kawo maganar Lubnah, shiru hall yayi da yake ba shi yake bayani ba, Taj ne. Ya cigaba da cewa. ""Idan har da muna son yin gaban kanmu ne da ba zamu tara ku a nan ba zamu yi gaban kanmu amma manufar ita ce mu samu haɗin kan kowa yadda zamu fitar da sakamakon kome, sannan yarinyar bata bukatar tayi aiki a kamfanin mun dauki duk wani abun da ya dace, wannan Madadin kamfani muna niman abokan hulda su bamu damar basu 75% na abinda aka karba daga gare su, zamu biya kudin"
"sauran kuma zamu rike izuwa reshenmu da yake garin Gombe!"""
"Shiru aka yi Alhaji Mudansir ya ce. ""Gaskiya ban amince ba, idan har sai lallai anyi haka tow sai"
"dai a kada kuria idan ka fimu tow shine zamu amince idan kuma baka fi mu ba, zaka hakura da tsarin jin kai ga dan kamfani sannan zata cigaba da aikinta, ai ƙaddara ce kuma tana kan kowa."" Bai san me Alhaji Mudansir ya taka ba, amma kuma sai yayi zuciyarshi ta karaya, kuma abinda ya fada din sai mutane suka bashi goyan bayan haka, dakin taron ne ya samu halartar Hajiya Sameerah da Hajiya Khaulatu, sai Khamis da Badr, Mimi da sauran yan gidan kumo da suke garin lagos, suna tare da Alhaji Mudansir, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana kallon yadda suka taru kuma duk sun zauna, bakiɗaya sai ya karaya."
"Chairman na kamfanin wanda ya kasance Alhaji ELYakub Kumo, yana kallon yadda Turakin yake"
"faffutukar tsayawa kanshi, ba tare da ya nuna musu karaya akan idanunsa ba, ya kuma kalli bangaren"
"iyalinsa wanda yasan sun zo ne domin saukar da Turaki daga matsayinsa.""yadda za ayi shine duk wanda yake tare da Mr Bilal Haris kumo Turaki, zai d'aga wannan White paper din, wnada baya tare da da shi ba zai ya d'aga ba, zamu kirga da mutanen da suka d'aga ne."" Duk aka amince, sannan ya cigaba da kai taka takardun gaban jama'a, bayan ya gama sai ga wasu bakin turawa suna zuwa Uncle Auta ya tafi ya gaisa da su, sannan suka samu wuri suka zauna wannan yasa murnan Alhaji Mudansir da Abbas ya koma ciki domin basu tab'a zatan haka zai faru, taron ya tara mutane, kuma aka sake jawabin abinda ya wuce."
"Koda aka gama sannan aka fara kuri'ar, Jikin Turaki bai bashi zai nasara ba, don koda yayi nasara yan'uwan Babanshi da alamar zasu iya kawo wani hargitsi, saidai cikin ikon Allah, zaben ya zo da ban mamaki domin daga cikin yan uwan Babanshi, Hajiya Khaulatu ta mike tare da bashi goyan baya, wanda tun da aka ga tayi haka, yar ta Yaranta suka bada hadin kai ta hanyar mara mata bata ba, kafin wani lokaci ya samu kashi saba'in da bai bukata ba, haka yasa bangaren da basu amince ba, suka tashi a kaso"
talatin.
"Cikin girmamawa da kome Alhaji ELYakub ya mike tare da cewa. "" "" Idan aka yi vote din dole"
"waɗanda suka bawa inda ake bukata kuri'a zasu samu kashi biyar cikin dari na hannun jarin da suka saka za a basu wato zasu samu kari na alkhairin da suka mana, mun gode da taimakon da kuka mana, mun gode da bamu hadin kai. Mun gode da zuwa da kuka yi wasu ma basu cikin garin nan amma kun mana adalci kun taso gari ya gari domin halartar wannan zaman gaskiya mun gode ni yanzu tunda an gama xan tafi, sai kuma batu na gaba dangane da wanda zai rike matsayin Chairman yana da kyau ku fara nazarin abin! "" Ya fada yana shafa kujeran da ya tashi a kai. "" Na tsawon shekaru talatin da biyar ina nan, na gaji ina bukatar hutu, don haka lokaci yayi da zaku sallame ni na huta nima."" Gyada kai duk suka yi suna tafa mishi. Uncle Auta da Ubaid tare da Turaki suka rako shi waje, har inda motar shi take ya kalli Turaki cikin kulawa ya ce mishi."" Saura me yanzu?"" "" Abubuwa dayawa amma wannan shine gaba, sauran kuma zan"
"tsayawa kaina in sha Allah!"""
"Make kewayarshi Uncle Auta yayi yana faɗin."" Yarinyar da baka iya tsayawa kallonta ce zaka tsayawa"
"kanka kai dai!"" Murmushi yayi ya kalli kakan nashi ya ce mishi. "" Naji ka fara batun chairman ai ni tuntuni"
"na turawa boardship zaben sauran fitowar sakamako ne, amma ai tuni na isar da abinda nake buƙata."""
""" Kada kayi wani abu da zai tab'a ka don Allah!"" ""Babu abinda zasu iya domin Allah yana tare da mu!"""
Daga haka ya shiga motar su kuma suka shige shi da Ubaid domin Uncle Auta ya jima da shiga cikin
"kamfanin, anan aka cigaba da bayani ai kuwa kowa ransa ya b'aci a bangaren gidansu. Suka sallami baki da suka zo tare da godiya da fatan alkhairi, wannan abin ya saka kowa jikinsa yayi sanyi."
"Bayan baki sun tafi Alhaji Mudansir ya saka aka kira Turaki, lokacin da ya same shi a office ɗinsa, zama"
"yayi ya kura mishi idanu. ""Kana ganin abinda kake yin nan adalci ne? Taya zaka dauki dukiyarka, ka zuba shi akan wata mace? Shin zata aure ka ne? Waye zai baka auren yarsa ba tare da yayi bincike ba. Kasan dai abinda ya faru itama yarinyar da kake yaki akanta bana tunanin zata aure ka akan tasan kai din!"" Sai"
"yayi shiru kuma, murmushi yayi ya ce mishi."" Ka gama ko akwai saura?"" Ya san tunda ya tambaye shi ya"
"gama ko a kwai saura zai fita ne, haka yasa ya juya abinsa ya fita ya ce mishi. ""Yarinyar da naji ance"
"bazawara ce!"" Juyawa yayi ya kalle shi kafin ya ce mishi. "" Eh wani ta aura,ba wani kato ya gama da ita ba!ita iyayenta suna tsaye a kanta ba,wasu yaran kuwa abin kunyar da suke da inda suke kwana suke tashi hala iyayensu basu sani ba."" Daga haka ya bar office din don ya gaya masa maganar da shima zai"
jima yana jinta.
"An gama taro lafiya, ya kuma turawa Adamu duk yadda aka yi. A lokacin da sakon ya Isa Ya Ado yana"
"karanta wata jarida da aka fitar da labarin babban Lauyar nan me gaskiya an samu labarin mahaifinsa ya ci bashin kamfanin banki har an kwace kadarorinsa shin zai yi yaki ne don samuwar Mahaifinsa adalci ko zai yi shiru ne, a daya page din hoton Lubnah ce aka saka, kanwa ga Babban lauya kuma ana zargin budurwa ga CEO na KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY, ana kyautata zaton saurayinta CEO zai hakura da dukiyar da ya amsa nasu. Ya gaji da yiwa mutane bayani, kuma ai Mr Turaki ya gaya mishi haka dai"
"faruwa, sakon da ya gani ne ya turawa Umar da yake Bauchi, sannan ya gaya masa yadda suka yi."
Lubnah
"Mama muka bari a lagos, mu kuma muka dawo gida, Gidan Ya Umar muka sauka da Yadiko, yan"
"Jama'are suna can wai sun zo mana jajje da abinda ya faru. Zance ban tab'a fuskantar bakin ciki irin na wannan lokacin, domin dayawa yan Jama'are ba don Yadiko ta wanke su ba, gani suke ni ce da laifi, koda yake biri yayi kama da mutum sai da Hajiyarsu Ya Hafiz ya zo, take cewa ai ni ce mai laifi, Hafiz ya gaya mata ni ce na saka hannu kudin yana wurina, da yake kamun Allah ne ba na mutum ba, sai gashi yayi ta fadar abinda Hafiz ya gaya mata, babu wanda ya ce mata kome, har Ya Umar ya dawo yadiko ta gaya mishi yadda aka yi da Hajiya, dama Ya Umar akwai daukar zafi, sai da ya fara huce takaicinsa a kaina kafin ya wuce office din Yan sanda na CID ya shigar da karar Hafiz daga nan aka tura a dauko shi, ai kuwa kwana ɗaya sai ga Hafiz abu kamar wasa dai ga katamin magana ya zama Babba domin kuwa case ce babba aka buɗe wanda Hafiz ya ce shi bai san kome ba ni ce na aikata kome, yan sanda suka ce idan har case ce to dole a dauko ni, sai lokacin sauran yan uwana suka san case ɗin, wannan abin ya raba kan Yan gidanmu har da wasu a can Jama'aren haka ina ji ina gani Hafiz ya kara makala min tsanar da tsangwama har aka kai ga an kama ni nima, lokacin da Ya Tahir ya ji lamarin abin ya mishi ciwo domin baya gari ya tafi Gombe akan case ɗin. Yan sanda su bada belina suka ce ba zasu bada ba domin case ɗin ya shiga bangaren zaman da cin amana, ni ce na saka hannu kuma da aka tambaye ni ban iya magana ba, sai dai a duk lokacin da Ubangiji ya jarabce ka sai ya kawo maka mafita, amma kafin mafitar Ya zo ne akwai"
abinda yake tab'a zuciya da rai.
"Hafiz ya cutar da ni, ya zalince ni domin kuwa a lokacin cewa yayi nice na bashi shawarar ya cuci"
"Abba domin na san yadda yake sign, sai da aka kusan bawa hammata isa tsakanin Ya Tahir da Umar domin abin ya bawa Ya Tahir ya haushi, sannan ya samu yadiko ya nuna mata akan me zata gayawa Umar me yasa bata kira Adamu ba, tasan yadda abin yake da zata gayawa Umar ? Gashi nan ya kwaba kome, domin ba za a bada belina ba, babu wanda ya gayawa Mama domin an san zata iya daukar zafi,"
"kuma burin wasu ne ya cika, abin bai yiwa wasu dad'i ba."
"Yan sanda wasu cikinsu azzalumai ne, yayinda wasu a cikinsu suka kasance mutanen kirki, akwai wasu"
"guda biyu da ban san me nayi musu ba. Suka saka ni a gaba Macen har sai da ta mare ni, na mijin kuwa sau biyu yana zuwa zai min tashin mutunci, sau biyu yana min haka. Ina tsugune a dan dakin da yake tsukuku ni daya ce mace, yar sanda ta shigo tare da cewa. ""Zaki fito ko sai na fito da ke?"" A hankali na taso, na fito abinci aka kawo min, ga sauro da kudin ciwo uwa Uba zarni da warin da dakin yake, idanuna sun yi jajjur yau kwana na biyu kenan, kaina a sunkuye. ""Lulu ki yi hakuri, wallahi bana gari ne, amma na gayawa Adamu ina ganin gobe zai iso?"" Murmushi nayi mishi, ban ce kome ba, ya ce min. ""Ki ci abinci."" Girgixa mishi kai nayi na yi shiru, tunda nazo ko sallah ban samu damar yi ba, ina kallon kasa, matar ta ce mishi. ""Malam zata koma!"" Ya ja hijab dina zuwa cikin dakin kamar shara ta zubar ya ce mata. ""Abin da"
"kuke yi babu adalci meye laifinta?"""
"[12/11/2025, 3:53 PM] Maman Walid: 9"
"Ai yadda suka rufe shi da fada yasa shi yayi shiru, ya fita da abincin matar ta ce ya samu Hafiz ta gaya"
"mishi. Abinda yake faruwa, ya ce mata. ""Ki taimaka a kai mu kotu zan baki wani abu ki taimaka!"" ""In sha Allah zan yi iya bakin kokarina!"""
"Bayan tafiyar Ya Tahir wurin karfe biyar na yamma, ina durkushe a wurin daya dan sanda ya shigo cikin"
"muzurai, ya kai min wani irin damka, sai da na saka ihu tare da kamo ni ya fara ƙoƙarin goga ni a jikinsa, na ture shi ina me fashewa da kuka. Kamar zai fadi ya gyara tsayuwarshi. Sannan ya fito na biyo bayanshi. Mr Turaki na gani, kasa kallonshi nayi ya mike tare da wasu mutane uku masu bakaken gaya, ashe har an gama magana kawai gida zamu wuce. ""Lunah"" d'ago kai nayi na kalle shi a hankali, kafin na sunkuyar da kaina kasa ina kuka, takowa yayi ya riko hannuna tare da zaunar da ni ya ce. ""Ki yi hakuri kin ta jira na ko?"" D'ago kai nayi na kalle shi, sannan na sunkuyar da kai. ""Lunah ki ce wani abu?"" Murmushi nayi mishi hawaye na zuba daga idanuna, na gane hawayen bakin ciki ne ko na farin ciki ne, ""lunah wani abu ya"
"faru ne?"" Girgixa mishi kai nayi, "" amma naji kin ƙara lokacin da dan sanda nan ya shiga, Lunah wani abu ya faru ne!"" Kifa kaina nayi akan cinyata nayi ta kuka taya xan gaya masa cewa mutumin sau uku yana kokarin keta min haddi? "" Gaya min baki yarda zan baki kariya ba ne a duk inda kike a duniya?"" Kallonshi nayi cikin shashekar kuka na ce mishi."" Don Allah ka kai ni wurin Mama ka ji don Allah bana son zaman Bauchi. "" Yadda na fada ina me durkusawa a wurin ina kuka, shima durkusawa yayi yana faɗin. ""Gaya min me aka miki?"" Haka nayi ta kuka can ya ce min. ""Me kike so nayi to?"" ""Na gaji ne, wari nake wancan azzalumin shi da matar sun ta zalintatta bayan bani da laifi idan ma ina da laifi na cancanci ya taɓa ni ne ko ta dake ni? Me nayi da zafi haka? Me yasa sai ni?"" ""Shiga mota a kai ki gida!"" A hankali na mike Taj ya bude min kofar na shiga, sannan muka bar police station din, bayan wasu minti waya yayi kamar minti goma zuwa ashirin commissioner of police ya tawo, mika mishi hannu yayi yana faɗin. ""Don Allah kayi"
"hakuri, wallahi ban san me ya faru ba. Sannan basu san cewa matarka ba ce, kasan akwai b'ata gari a"
"cikin hukumarmu"" kafin wani lokaci karamin al'amari ya zama babba, domin kuwa sanadin abinda suka"
"yi ya janyo aka kore su a aiki bayan an kama masu da laifin cin zarafin mace tare da yunkurin keta alfarmarta, sannan sun karbi cin hanci da rashawa. Inda aka rufe Hafiz ya nufa ya tsaya yana kallonshi irin kallon wulakancin nan, ya ce mishi. "" Ka zauna anan zai fi maka alkhari idan ka sake ka fito wallahi sai na sauya maka halitta."" ""Sai me? Matukar ina raye bata isa aurenka ba, sai na bi duk wata hanya na cusa mata damuwa da tashin hankali yadda zata ji auren ya fita mata a kai, a yanzu ma kawai na kyale