Author : Mai Dambu Category : Complete Novels
albarka a aurensu, kai kuma mara kunya kana kishin"
"jahilci, Iyayenta sun kira suna bukatar yarsu da takardar shaidar saki."""
Hankalinta ne yayi mugun tashi tare da jin kamar yayi gagarumin kuskure amma taya zai gyara? Idan
"har ya ce zai gyara taya kenan? Kiran Granny yayi ya gaya mata halin da yake ciki itama ta ce mishi.. ""amma baka da kunya, Allah yasa su karɓe yarsu tunda baka da mutumcin mutumin banza kawai."""
"Cin mutuncin sosai dattijon nan yayi mishi, shi kanshi ya rasa ta ina zai fara. Ina zai fara zuwa, kakaninsa"
"sun juya mishi baya, domin kuwa sun samu labarin irin zaman da nayi a baya, sannan kuma shi da"
"bakinsa ya gaya musu abin da ya gaya min , kuma na bar shi ba tare da wani alama ba. Wannan abin ya tsaya mishi a rai."
"Kusan ana niman sati uku kenan, babu wanda yayi tunanin zuwa Bauchi ko Gombe as ko na tafi can!"
***
"Yau Laraba, yadiko da Mama sun gama abin sadaka kenan, Yadiko ta kalli Mama yadda tayi shiru wanda"
"ya bata damar cewa. ""Ina ga Lubnah tana kusa tunda bata wurin Yan uwanta, ina ji a jikina tana matukar kusa damu, wallahi naji haka a jikina. Tayi haka ne domin wani dalili mai karfi. Kai bari na je gidanta na"
"G.r.a."""
"Ta shiga daki ko minti biyar bata yi ba, ta fito Mama ta ce mata. ""Bana jin tana nan kusa."" Girgiza kai"
"yadiko tayi ta ce mata. ""Bari dai na dawo!"" Ta fita."
"Sai da tayi tafiya sosai kafin ta samu keke napap, ta fada mishi inda zai kaita. Ya fada mata kudin ta ce"
"su je. Bakinta dauke da Addu'a zuciyarta na bugawa saboda tsoron kada ta samu, bana nan har zuwa"
"unguwar da yake tazo lokacin da ake kawo kaya, kofar gidan ba kowa da alamu me kula da gidan ya shiga cikin gidan, don haka ta shiga gidan kai tsaye tana sallama."
"Muna tsaye da shi ina mishi lissafin abinda zai sayo min, kawai na ga Yadiko akanmu, jikina ne ya dauki"
"wani irin rawa, abinka wacce bata saba laifi ba, kallonshi nayi taya ya bar gidan A buɗe? ""Hajiya lafiya? "" Ya cewa Yadiko, "" Uwaki Lubnah! "" Ta min dakuwa da hannu bibbiyu, "" Nace kin ci gidanku! Haka muka"
"miki tarbiyya?"""
"Idanuna ne ya cika da kwalla shima mai gadin ya ce min. ""Kiyi hakuri Hajiya mantawa nayi da gidan a"
"buɗe!"" ""Maza dauko Hijab dinki mu je gida mara mutunci!"" Kiran wayar Mama ya shigo wayarta. Sai da ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce mata. ""Tana nan bata je ko ina ba gamu nan zuwa da ita."" Daga can Mama ta ce mata. ""Ki tawo min da ita!"" ""Tow shi kenan."" Haka yadiko ta saka ni a gaba muka nufi gidanmu, kunya duk ya kama ni. A lokacin da muka iso gidan, wani matsiyacin kallo Mama ta min tana faɗin. ""Allah ya ganar dake!"" Sai bayan isha suka min fada sosai, kafin Yadiko ta gayawa Ya Ado shi kuma"
"ya kira Uncle Auta ya gaya mishi, a ranar labarin ya tafi kunnen Turaki.."
"Har dare Yadiko fada take min, sai da lokacin kwanciya yayi ta ce na je dakin Mama, haka na wuce dakin"
"na je na kwanta, duk da haka bata tambaye ni ba, nima ban gaya musu kome ba, sai washi gari ina karyawa ta ce min.""idan bakya son auren ina ga ku rabu mana?"" Kallonta nayi kafin na ce mata. ""Ai ni dashi bamu yi fada ba!"" ""Amma ya gaya min dalilin barin gidan ko?"" ""Wannan ai ra'ayinsa ya fada ni dai Bauchi nake son zama yayi aikinsa a can ni na zauna nan, sannan ki roka min shi yayi aure don"
Allah............
"[12/23/2025, 7:46 PM] Maman Walid: 26"
"""Kin san illar haka kuwa yayi aure fa?"" Kallonta nayi, kafin ka dauke kai ina tura kosai bakina. "" Ko dai"
"yana miki wani abu ne?"" "" Ba kome!"" Na fada mata, na cigaba da cin kosai na har na gama bata kara magana ba, "" yanzu ya kike so nayi?"" Juyawa nayi kamar zan yi kuka na ce mata. "" Ki ce mishi yayi aure na amince!"" Murmusa min tayi irin na manya, ta ce min. ""Shi kenan!"" Na ci gaba da karyawa bata kara magana ba, ina jin suna magana da Yadiko na zata maganar auren ne amma bata mata ba, wurin karfe"
"daya ina barcin rana, gidan ya kaure da hayaniyar da ya tilasta min farkawa. Na sauko daga saman"
gadon Mama na fito parlourn kaina babu dan kwali. Shine zaune a parlourn yana waya kamar ba zai yi
"magana ba, kallo daya nayi mishi, duk ya fada kamar mara lafiya. Kurawa juna idanu muka yi. Daga yadda ya motsa lips ɗinsa na fahimci abinda ya ce min.. wato ""kin kyauta min!"" A hankali na juya zan bar parlourn. ""Ok! Sannu!"" Ya fada har zan shiga cikin dakin ya ce min. ""Haka ake amsar bako?"" Juyawa nayi ina kallonshi, komawa ciki nayi na saka hula na fito na samu Yadiko ta shigo suna gaisawa, Mama da su Uncle Auta suna parlourn Abba. Fita nayi na kawo mishi ruwa da sauran abin karyawa, ya sauko daga kujeran ya fara ci yana faɗin. ""Ayi hakuri!"" Tashi tayi ta fita, ta barmu a parlourn shiru ya wanzu a parlourn. D'ago kai yayi yana kallon yadda nake danna wayata hankali kwance. ""Nasan nayi kuskure amma me yasa ba zaki fahimtar da ni ba? Kowa ya daura min laifi eh nayi kuskure amma barina a wannan lokacin kin san illar da kika min?"" ""Saboda ba ni ba ce na gaya maka maganar da ya fito bakinka ba, Yes nasan haka kake baka iya boye abinda yake ranka, shi zaman da zaa yi shi babu yarda meye amfaninsa? Ni da ce min kai yi je ki na sake ki zai fi min sauki, amma ka gaya min don waninka ya aure ni kake gaya min magana ba zaka iya kasancewa da ni ba, tow me kake so na maka yanzu? Na rantse da"
"Allah kai da kanka na gaya maka haka sai ka ji kamar babu amfani na cigaba da rayuwa da kai!"""
"Daga haka na mike zan tafi dakin ya ce min. ""Idan ke ce kika tsohuwar matata take kiranki tare da tura"
"miki hotuna da bidiyo dinmu da wanda muka yi tarayya ya zaki ji?"" Juyawa nayi na kalle shi murmushi nayi na ce mishi. "" Shi yasa nace mu rabu kowa ya kama gabanshi, ai babu amfanin zama da zargi, har na gama zama a KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY, wani ya tab'a yunkurin keta min haddi ne bayan cousin dinka? Ba laifi bane idan ka ce ba zaka zauna da ni ba, zuwa yanzu na fahimci waye kai! A da can ina kallonka a matsayin wanda ko a gidan karuwai ka dauko ni zaka iya aurena a haka ka zauna da ni, tow tsaya idan bai cusa maka bakin ciki ba, taya zai fahimci nayi mishi nisa, ku dai maza kullum abinda ya muku kawo kuke ɗauka akanku wanda bai kai a dauka ba, ba zaku dauka ba."" Na wuce na barshi, waya na ji yana yi sannan ta fita, can Mama ta zo ta kira ni na isa parlourn. Ya fadi abinda yayi min ya ce shi yasan abinda ya kawo na bar gidan kenan, Kallona Abba yayi na ce mishi. ""Ni bai min kome ba!"" ""Karya ne wallahi nayi miki, don Allah ki fada kome wannan shirun naki gara azaba da shi, Abba nasan nayi laifi amma naso na dauke kai amma Hafiz ya dame ni, Hafiz ya takura min zuwa yanzu hatta email din Lubnah yana da iko da shi. Hafiz hatta wurin aikina ya tura sako marasa dad'i, Hafiz ba yaro bane na saka hannu a jikinsa amma kamar bai san inda yake miishi ciwo ba, nayi ƙoƙarin gano me yake bukata, sai na gano kawai Lubnah ce da take tsakaninmu, har ga Allah nayi kuskure da nake jin haushinsa ina kauracewa Lubnah, wallahi. "" Tashi nayi na bar parlourn, domin da gaske bature ne bai da kunya yanko magana yake kawai, sai da Uncle Auta ya dakatar da shi, daga Abba har Mama sai aka rasa me magana domin ya fada musu shi fa rayuwar aurenshi lafiya lau kawai Hafiz yake mishi kutse har hukuma ya shigar Hafiz ya ki dainawa, yana gudun abinda zai taba mutumcinsa da kimarshi ce. ""Har yau Hafiz bai rabu da Lubna ba dama? Ka dauki Matarka ku je gobe da bayan sallah isha ku dawo da ita. "" Inji Abba, haka Mama ta fita daga parlourn ta saka na hada kayana, tunda na ga haka haushi ya kama ni hijab dinta na saka ko kaya ban ɗauka ba, muka wuce Uncle Auta sai hakuri yake bani, ya kuma hada ni da Alhaji ELYakub. Ya bani hakuri sosai sannan ya kara min nasiha, har muka isa gidan na wuce kitchen na gyara na fara ƙoƙarin daura abinci, ya shigo. ""Ki bari nayi takeaway. Don jibi zamu wuce lagos."" Wani irin kallo na mishi, ""me zan ya a can? Ka daina ma tunanin xan kara binka, ka je ka auri Virgin ka ajiyeta a Lagos."" Shiru yayi yana tuna Kalaman Abba da ya ce mishi. ""Kana da Chance da zaka gyara alakarku, ka tafi da ita"
"kishi kuwa kowa yana da ita, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya auri Khadijah yana da shekaru"
"ashirin da biyar ita kuma arba'in sannan ya zaune da ita har ta haifa mishi Yara, kana kuma ita bazawara"
"ce da ta girme shi. Don haka idan kana da ra'ayi kafin gobe ka goge kuskurenka da laifinka, idan kuka dawo bata iya goge laifinka, Hafiz yayi nasarar juya maka lissafi domin ya fi ka sanin wacece ita, ya kuma"
"san zaka dauki kishi da zafi ita kuma zata ga babu amfanin aurenka."""
"Fisgo ni yayi ya saka hannunsa bibiyu a kafadata. ""Look at me? Me kike so?"" "" Zaman Bauchi!"" Na"
"fada mishi haka kai tsaye, ""ok! "" Ya fada bayan ya rungume ni, shiru nayi a hankali na ji kwalla yana zubo min, sake rungume ni yayi ya ci-gaba da bani hakuri. A hankali na fara kuka mara sauti, yana bubuga bayana, daga nan ya dauke ni cak, zuwa dakina. Sauke ni yayi ya daura ni a kan kujerar dakin ya gyara dakin. Kafin ya janyo ni gadon muka zauna, a hankali yayi ta rarrashina har labarin ya sauya na rasa wani munafuncin ne ya janyo ni na bashi damar yin abinda na ce ko me zai min ba zan kara yarda da shi, na kuwa san nayi yaji domin har barkono sai da ya gaya min yadda ake nomarsa, kiran sallah la'asar ya saka ni mikewa zuwa ban daki nayi wanka koda na fito yayi barci, dama da Alwala na fito na shimfida abin sallah, na shiga gabatar da sallah. Bayan na isar nayi addu'a, zuwa inda yake nayi na tashe shi yayi sallah, ya janyo ni na fada kanshi yana shafa fuskana. ""Tashi nayi sallah"" ""hmm but ban koshi ba!"" ""Cab yunwa nake ji!"" Na fada ina kwace kaina na fito na daura abinci, ina ta aiki ya shigo da Jallabiya. Sumbatar wuyana yayi ya zagayo da hannunshi kan cikina, ina aiki yana hana ni sakat. ""Ka rufa min asiri kada na kone, dama ina bazawara kaga sai ka auro budurwa Virgin!"" Shiru yayi ya daina sumbatar ya dawo gefen firj din yana kallona. ""Allah ya baki hakuri."" Ban kula shi ba, na gama girkin sannan na fito zuwa waje yana biye da ni na shirya abincin, kiran sallah Magariba ya fitar da shi, wurin karfe takwas suka shigo sanin halinsa yasa na ki fitowa, sai da ya zo don kanshi ya fito dani, na zuba musu abinci, haka dai na gama abinda ya dace musu na dawo dakina na kwanta, har wurin ƙarfe tara sannan Uncle Auta ya mana sallama gobe zai wuce Jos. Ya koma lagos. Ba kunya ya ce mishi. ""Allah ya tsare ka gaishe su ni kan sai"
"kun gani."""
"Daga haka ya mishi sallama, tunda ya shigo daki wurin karfe goma saura, ya haura gadon da nake"
"zaune ina karanta hisnul Muslim. Ya kwace ya fara kallona kamar zai hadiye ni, a hankali labarin dai fushi na rasa inda na kai shi, dazun na zata ina masifar kewarshi amma a yanzu dai na gane bakiɗaya rayuwata zan bada saboda shi, domin yadda kome ya wakana ya kasa barin cikin kaina da zuciyata, abin ya tsaya a idanuna ba zan tab'a mantawa da wannan daren ba, ina kwance a jikinshi shafa kaina yayi ya ce min. ""Kin hakura zamu koma Lagos idan muka huta anan?"" Kwantar da kai nayi a kirjinsa, nayi shiru kafin na d'ago ina kallonshi.""idan muka koma ka cigaba da ƙyamar wani ya taba kwanciya da ni? Kayi ta gaya min ni ragowar wani ne?"" Rufe min baki da yayi da nashi, sannan ya kashe zancen babu yadda zaa yi na kara tunawa da mun yi wani rigima, kusan a tare muka yi wanka muka dawo ina kwance a jikinshi. Har barci yayi gaba da mu, kusan washi gari makara muka yi, ya zuba min idanun ina barci. ""Tashi gari ya waye!"" Da sauri na bude idanun, muka shiga muka yi alwala sannan muka fito a tare, bayan nayi sallah na fita waje, fitowa yayi shima yana waya bayan ya idar ya shigo ya samu ina ƙoƙarin kunna gas, riko hannuna yayi ya ja ni zuwa daki, anya mutumin nan lafiyarshi kalau kuwa? Kusan ranar yana manne da ni, bini bini, abu daya da na fahimci zai lalata min lokacina na tuna mishi zamu tafi gida yau, sai ya hakura ya kyale ni na huta, har muka ci abincin rana, don sai karfe biyu muka karya abincin rana kuwa sai yamma"
la'asar likis.
"Karfe shida yayi mana a gida, da yake ana sallah Magariba da wuri sai da ya bude min kofar na fita don"
"muna isa cikin harabar gidanmu muka hadu da Hafiz. Haka muka shiga cikin gidan yana rike da jakata, ni kuma ina lafe a kafad'arshi, don bana son kallon Hafiz ma. A tsakar gida muka sami Mama da Yadiko, kasancewar ranar juma'a ce ranar, muka gaishe su. Daga yadda muka tawo Mama ta fahimci mun shirya, haka ma Yadiko sannan ya ce min.. ""Bari na je sallah ko?"" Gyad'a mishi kai nayi, yana fita suka hadu da"
Hafiz sai shigo murmushi suka yiwa juna. Kowa ya wuce. Dakin Yadiko na wuce na shiga nayi alwala.
"Bayan na idar da sallah, na cigaba da azkar har bayan isha, sannan na na fito saboda Yadiko ta min"
"magana, muka shiga ban tab'a sanin haka Abba yake faɗa ba, sai da ya saka Baban Jama'are a gaba ya wanke shi tas, sannan ya koma kan Hafiz ga Ya Umar ga Lauyar da aka dauka da yarjejeniyar kada wani abu ya kara shiga tsakaninmu da Hafiz, Abba ya ce mishi. ""Banda rashin kunya da rashin mutunci, yarinyar nan har hauka ta kusan yi kai nima sai da ka kusan kashe ni, a haka ban rabu da kai ba, ka lalata min suna ka ciyo bashi da sunana duk na rabu da kai Hafiz idan kai ba Tsinanne asararre bane ka fita hanyar Lubnah idan na kara jin wani abu ya kara tasowa akanka, zan ajiye zumunci da kara na daure ka sai igiya ya saura mara kunya, Ali yau na dawo maka da karar danka, idan ya lalata min auren Y'a wallahi zan dauki matakin da sai an rasa mai bani hakuri, ka ja mishi kunne idan ya har dan halak ne shi ya kara bibiyar rayuwarta sai na lalata mishi nashi rayuwar maciji da bai da ramin kanshi sai na wasu."" Tass Abba"
ya mishi tare da buga mishi kashedi........
"[12/24/2025, 10:15 PM] Maman Walid: 27"
"Sannan ya juya ga Baban Jama'are ya ce mishi. "" Na zata kasan yakana ne, amma na fahimci baka fahimci"
"haka na, idan na kara jin labarin Hafiz a bakin Lubnah ko mijinta da sunan ya shiga rayuwar aurenta, na rantse da Allah zan yi abinda zai baka tsoro. "" Murmushi yayi kafin ya kalli dan uwansa ya ce mishi."" Da gaske nake ba da wasa ba, rayuwarta da aurenta yafi min kome muhimmanci ban damu ba ace don tana auren mai kudi ne ba kome, na ji kuma na amince"" yayi fadar ni kaina sai naji kamar an yantani daga wani kunci zuwa jin dadi, ya juya ga Turaki ya ce mishi. ""Idan ba zaka iya zama da ita a haka, ka sake ta yanzu nan!"" Ya ajiye mishi takarda da biro, ba Turaki ba hatta ni sai da gabana ya fadi, muka kalli Abba da yake wani muzurai. Alamar no mercy a cikin lamarinsa, kallon Turaki nayi da yake Allah bai mishi burbushin kunya ba, janyo ni yayi ya ce mishi.""Wai Alhaji i love my wife, zan iya kome domin tayi farin ciki. Daga yau ka kuma ganin Lubnah a gidanka matuƙar ba dalili bane babba kayi karana kotu domin a nima mata hakkinta, Alhaji a dokar ƙasashen duniya idan tayi ƙarana duk abinda na mallaka sai an raba biyu, a nan kuma ka bani takarda da biyo, wai ina son Matata wallahi idan zan fada maka ita mace ta biyu mai daraja a rayuwata, ni ba gara ka fille min kai zai min sauki da na sake wannan abin!"" Ya shiga rattaba bayani, zamewa nayi na barshi ya yi ta rashin kunyarshi, na rantse bai da kunya har cewa yake. ""Ni fa naga ƙoƙarin Lubna da ta xauna da mai furfura irina, waye ya sani ko hakuri take da ni, amma Alhaji ina kula da kaina! Ina cin abinci me kyau ina. "" Da gudu na shiga parlourn na riko kunnenshi, ya kuwa taso. "" Ya zaa yi, ai haka zan bi Umarninki! "" Muna fita waje na ce mishi."" Wai kai baka da kunya"
"ne?"" "" Da nayi me?"" Ai ban yarda mun kara shiga cikin gidan ba, na ja shi muka bar gidan. Wannan tarin"
"rashin kunya nashi. Sai da muka dauki hanya na ce mishi."" Ba kyau rashin kunya, ba kowani magana ake"
"fada ba, wani ana shiru a gaban manya ko mutane, ba laifi bane