Author : Mai Dambu Category : Complete Novels
baka da kunya sai na sani, Lunah zaki sammin kunyarki?"" Shi dai bai da ta ido, haka ta wuce dakin da ya kama mata, washi gari muna karyawa muka wuce wurin gyaran jiki da gashi. Ina jin wata baturiya tana tambayar ko ina son wig ne? Nace a'a ina da gashi na dai-dai gwargwado ina zan kara da gashin doki, haka muka gama wurin karfe biyar sai da muka yi sallah sannan aka min kwalliya muka fito, yau kan da Laffaya shi kuma jamfa fari tass laffayar fari ds ratsin golden, maganar gaskiya mun yi kyau a yadda ake hoton kamar mutumin yasan kan aikinsa, a rana na hudu muka saka wannan cocktail gown shi kuma suit ya saka baki, a wannan ranar ne muka yi hoton da har ya tab'a jikina wato hannunsa a kan kuguna, sai kallonshi nake a sace. ""Ai da mutane ni ba shaidani ba ne."" Ya fada yana murmushi, ni kuwa sai kunyar su Aunty Hindatu nake ina ta astagafarallah, har aka gama na yau yana sake ni na sauke ajiyar zuciya kamar wanda ya cakume ni. Sai satar kallonshi nake. Bayan mun koma masauki yake bawa Ubaid"
"labari sai dariya suke lokacin da muka fito cin abinci ya muka hada idanu, d'aga min gira yayi na daukr kai. Sako ta turo min da cewa. *Kin yi kyau* kallonshi nayi, ban san lokacin da na sake murmushi ba, na tura"
mishi da cewa.
_Hmmm_
"Sai da ya d'ago kai ya kalle ni, sannan ya cigaba da abinda yake."
***
Bauchi
"A Bauchi kuwa ba karamin shiri Mama take ba, duk da bangaren Maza sun gaya mata basu bukatar"
"kome akwai kome a gidan, amma Mama ta ce a'a ita fa ajiye kwarya a gurbinta...."
"[12/15/2025, 10:14 PM] Maman Walid: 16"
"Kaya irin wanda ba a zata ba, shi ta saya domin kudin da ta bada aka mata sayayya a kano aka kawo,"
"kwana biyu da dawowarta Ya Ado ya zo da wasu key guda biyu, ya ajiye mata yana faɗin. ""Mijinta ya sayi gida anan Bauchi yace kayan da kika mata a zuba anan gidanta na Gombe akwai kaya yanzu haka jiya aka saka wasu an kawo su daga kasar waje. Nan kuma an barshi idan sun zo ganin gida zasu sauka anan ko ita idan tana bukatar haka."" Shiru Mama tayi domin abin Turaki ya fara bata tsoro, kada fara gulmar sun samu me kudi sai tatsarshi suke, bata son tashin hankali da surutun mutane. ""Baki ce kome ba?"" Girgiza kai tayi kafin ta ce mishi.""Ni lamarin Bilal ya fara bani tsoro, kada Yaron nan ya wulakanta min Yarinya, kada ya kashe kudi ya fanshe da tozarci."" Girgiza kai Ya Ado yayi yana faɗin. ""Ban ga yayi kama da haka"
"ba, mutum irinsa kwanciyar hankali yake bukata ba tashin hankali ba."" Gyad'a tayi amma lot of thinks"
"suna zuwa a ranta, tana tsoron kada ta sake jiki a dawo ana musu dariya."" Tashi tayi ta nufi dakin Yadiko"
"ta gaya mata abinda yake faruwa, kusan sai lissafinsu ya zo ɗaya, hankalinsu ya tashi."
"Yadiko ta kira Baban wansu da yake wani gari a misau wato belaye ta gaya mishi halin da ake ciki, ya ce"
"su bashi kwanaki uku kafin nan zai musu magana. Amma yanzu su bada sadakar Pure water, bata gayawa Mama ba, ta saka sayo mata ruwa jaka goma aka kai masallaci da wani Islamiyya a nan dutsen tanshi, aka yi ta addu'a kuwa. Zuwa yamma ta gayawa Almajirinsu akan ya turo musu Yara akwai abincin sadaka. A yammacin Ya Ado ya bada kudi ayi cefane aka sayo har da nama, aka tashi aiki ba ji ba gani."
"Store Yadiko ta shiga ta fito da ledar takeaway ta fito da shi tana faɗin. ""Wannan na hidimar biki ne, amma gashi zan yi amfani da shi, Ya Allah ka shiga lamarin nan!"" Ta fada tana ajiyewa Abba da ya zama sai mishi kome ya turo keken da yake zaune a kai ya fito ya ce musu.. ""Saboda naki Lubnah shine na zaku aurar da ita baku gaya min ba?"" Shiru suka yi kafin Mama ta katse shirun da cewa. ""Tunda aka zo tambayar aurenta nake binka na gaya maka amma me kace min? Cewa kayi kada na ƙara saka ka cikin abinda bai shafe ka ba. Yanzu kuma saboda kafi kowa adalci zaka ce munki saka ka cikin hidimarta."""
Murmushi tayi irin wanda kana gani zaka fahimci yadda take jin zafin abin a ranta.
"""Amma ina da hakki akanta? Idan aka cigaba da yin haka waye zai dauke ta da daraja. Duk wannan"
"rawan kafar da kuke yi ku sani bare ne ba dan uwanta ba."" Ya fada ranshi yana jin zafin abin, basu kula shi na can ya ce musu.""idan har albarkata ce zata rike auren Lubnah ba zan saka mata ba."" Murmushi Mama tayi ta ce mishi. ""Tabbas rayuwar auren Lubabatu yana bukatar albarkanka amma ka sani ko ka saka ko kada ka saka aure babu fashi, kuma ka rike albarkanka ai naji Talatu da Uwani zasu bashi Jalilah da wannan nake son ka sani kamar yadda Lubnah tayi gaba har abada Hafiz da Jalilah ba zasu tab'a tarda da ita ba. "" Daga haka ta wuce dakinta ba zata kara miishi magana, haka. Yayi ta fada har yana faɗin saboda abin duniya suka likewa turaki! Yadiko ta ce mishi."" Eh kai tunda ya fitar da kai kunyar kallon mutane da bashin da Tsinannen Yaron can ya ciyo maka, dole ka samu bakin magana ko kunya baka ji ba."
"Ka zauna kana dabbawa kanka wuka. "" Tayi tsaki ta cigaba abinda take yi."
"A can Jamaare fa haushin Yayun Lubnah sun tsaya kai da fata ba zata koma gidan Hafiz ba, shine suka yi"
"zuciya tare Da bawa Hafiz auren Jalilah, wannan shine mafarkin Jalila ta sami Hafiz kuma burinta ne gashi"
"nan ya cika zata samu Hafiz yadda take so, sai dai Hafiz shi baya ta ita domin kuwa zuciyarsa bakiɗaya tana can ga son zuciya. Hatta hada auren bai san anyi ba domin ya je kulla nashi makircin."
***
Kwanaki goma sha biyu muka dawo daga Dubai a matuƙar gajiye da tarin tsaraba. Wanda muna isowa
"aka yi ta tura kayanmu wurin ɗinki, har gida matar ta zo tayi ta amsa tana, duk da ya cewa su Aunty Hindatu akwai kayan biki daga Russia za a kawo don kome booking yayi daga can, mun dawo da"
"kwanaki uku. Wanda yayi dai-dai da bikin saura kwanaki,"
"Da safe Aunty Hindatu suka zo gidan ina zaune a daki ina karyawa suka shigo, kallonsu nayi na ce"
"musu.. ""Lafiya kamar an koro ku?"" ""Gobe zasu kawo kaya!"" Wani zabura nayi tare da nufar daki suka biyo ni da yake Mama tana dakin Abba, daga nan ina jin yadda suke sa'in'sa da alamu maganar auren ne, sai da ta fito muka fahimci, ai akan auren ne domin kuwa ta ce ya bada abinda za ayi hidimar bikin ya ce shi ba zai bada ba, ya rigada ya tura Jama'are shi yanzu ya tura daurin auren Jama'are, shine take fada wai ayi bikin a can, ita kuwa ta ce ba yarda ba shine fa abun ya kai ga sa'in'sa. Shi ya ce idan ba a Jama'are ba sai dai a fasa auren ita kuma tayi tsalle ta tuma ta ce babu wnada ya isa ya mata wannan rashin adalcin. Karshe sai ga gidan ya cika da Yayuna dakyar aka lallaba Mama ta amince, amma kuma da Ya Umar ya zauna da Abban ya gaya mishi abinda yake faruwa domin har gidan Ango sun buga katinsu gobe za a kawo kayan aure, sai jikinsa yayi sanyi dama daga can aka zuga shi da yake bai da lissafi"
ya zauna a kai.
"Dakyar aka kashe maganar a daura auren Hafiz a can, Lubnah za ayi bata a gwallaga, sannan shi Hafiz"
"ranar juma'a ne yayinda lubnah ranar asabar ne. Wani ikon Allah a masu zuwa amsar kayan har da Jalilah tazo ganin kayan auren, da yake gulma da munafunci ya kawo su. Karfe daya na rana suka iso lokacin gidan ya cika a gidan nan Aunty Zakiyah da Aunty Munah basu nan, amma har Raliyah daga Jos sun zo yan kaduna ma sun zo, suna sallah dangin Mr Turaki suka iso wurin karfe biyu da minti talatin. Tun daga bakin kwananmu aka rasa inda za a ajiye motar yan kawo kaya, abinda nake gani a blogs yau shine a kaina, yadda aka yi ta fitar da kayan ana shiga da shi kai rakiyan kawo kayan har da yan sanda da civil defense, aka kawo kayan aurena. Wato ba iya jijjiga table nayi ba karya table din nayi, domin har"
daga makotan unguwarmu shigowa ake zuwa ganin kayan.
"Ni kan tunda na shige uwar dakin Mama ban fito ba, a babban parlourn baki aka karbe su, koda yake ba"
"abinda xan cewa Yayuna sun fitar da ni kunya ba zan iya cewa kome ba, a cikin waɗanda suka kawo kayan har da wata baturiya anan suke cewa kanwar Mamanshi ce ita ce autarsu wato Miss Herlim, bayan an karbi Kayan an kuma bude anyi addu'a, sannan aka yi addu'a, kafin suka ce. ""Tow mu dai zamu wuce ba kwana zamu yi ba!"" Ita Miss Herlim ce ta bukaci ganina, Aunty Hindatu ta ce mata tazo, ina zaune a dakin aka shigo da ita, ko bata gabatar fa kanta ba nasan Yar uwar Mamansa ce. Tana shigowa ta rungume ni, tare da kama hannuna ya saka min wani abun hannu. ""Inji Mamanmu, tace a sakawa Labubu wannan."" Shafawa nayi ina kallonshi murmushi na ce mata. ""Na gode!"" Murmushi tayi ta ce min."
"""Mafarkin Son zai tabbata, don Allah ki mishi adalci yana sonki so na hakika, mutumin kirki ne bai taɓa"
"niman matan banza ba, na kirkin ma baya bi, bai taɓa shan giya ko wiwi ba, balle kuma taba. Mutumin"
"kirki ne sosai. Zai kula da ne, ki rike mana shi amana maraya ne bai da Uwa bai da Uba sai kakanni. "" Sai yanzu na tuna mun yi fada ashe bar muka bar Dubai a tare muka sauka a lagos, mu kuma sai muka sake bin wani jirgin zuwa Jos, bana son tuna abinda ya fada mu, domin raina bacci yake. Koda yake ba laifinsa ba ne na me hoton ne, da kuma nima, Kodayake ai ba wani abu bane, awurin daukar hoton ne ya min tashin ɗa'a, na kusan gaya mishi magana, amma ya dauko duk laifin ya daura min domin kuwa bai yarda yayi kuskure ba, har sai da Auntynshi ta shiga lamarin, nasan ya hanani saka turare mai karfi amma"
Aunty Innah ta saka nu sawa. Shine ya nime yayi min rashin mutunci.
"Har yau mutumin nan ya ki kirana ya bani hakuri bayan yasan shi ne da laifi, murmushi nayi nace mata. """
"In sha Allah!"" Haka ta fita duk wani abinda muka yi sai da aka hada musu tas suka tafi, bayan tafiyarsu Yadiko ta ja kofar ta rufe. Domin kuwa bata ji a ranta a bude parlourn ba, haka kowa ya gama son gani sai bayan tafiyarsu aka bude tare da zuba idanun akan kayan aka gama gani aka rufe parlourn, bayan isha aka tattara kayan sai gidan Ya Umar aka kai can, karshe aka bar gidan da kamshin yan gayu, wurin karfe tara Ya kira Mama suka sha hira yayi ta godiya. Tare da farin ciki an karbi danginsa da mutunci an"
karrama su..
"Ni dai ban san yadda suka kare ba, domin barci ya kwashe ni sai wurin karfe biyu na dare na farka nayi"
"alwala na gabatar da nafilla, ban kwanta ba sai karfe hudu saura na kwanta."
*
"Washi gari mota Ya Tahir ya kawo aka mai da yan jama're, suna barin gidan nima Aunty Raliyah ta kai ki"
"saloon, muka je aka gyara min kaina, ana wanke min kai kalman Jalilah ya dawo min inda take cewa. ""Na ga sai wani murna kuke kasa dai a zurma dayawa domin dai kaf duniya babu me iya miki kirkin da Hafiz ya Miki!"" Ta fada tana murmushi, nima na ce mata.. ""duk wnada ya goyi kare yasan yadda zai da bakinsa,"
"Malama ina miki farin ciki, zaki auri abinda kika jima kina jira."" Daga haka ba barta a nan."
"Murmushi nayi kawai ganin Ya Hafiz take, haka aka wanke kaina da kafana aka gyara min farce na. A"
"ranar da muka dawo gida. Mama ta bani ruwan zam-zam take gaya min cewa. Yadiko ta biya aka hada min daga can Belaye, aka kawo min. Shi dai bai ce musu kome ba, ya ce a cigaba da shiri aure za ayi shi kuma akwai haske d duhu amma hasken tafi yawa, Tunda ta fadi haka suke sadaka kome badawa suke sadaka, kamar zasu zauce saboda kawai Allah ya bada zaman lafiya, haka yasa kowa ka gani a hidimar da"
aka fara hankalinsa kwance.
"Ranar Juma'a Goggo Alti tazo, ta ce ta bar Goggo Uwani da Talatuwa a can, musamman ita da zata yi"
"auren yarta, amma wani ikon bayan isha sai fa Goggo Uwani, kamar an wurgota daga daka, abinda ya bawa kowa mamaki an daura auren Hafiz da Jalilah."
"Ranar Juma'a daren saukar kur'ani aka yi, ba ayi kome ba. Washi gari kafin daurin aure aka yi walima"
"wanda karfe goma aka yi shi, ana gamawa sha daya saura muka aka kara shirya ni. Tun daren jiya aka kawo mai lalle da asuba ta zana min yayi kyau ya zauna das a hannuna."
"Da yake a masallacin gwallaga ake daurin auren, dubannin al'umma suka shaida daurin aurena."
Bilal Haris ElYakub kumo
Da
"Lubabatu Usman Umar Jama'are, akan sadakin sisin gwal, guda ashirin da biyar. Lakadan ba ajalam ba."
"Idan ka ganshi a wurin kowa sai ya san an daura aurensa domin yayi wani irin zuru-zuru. Bayan an gama aka dauki hoto da manyan baki sannan aka wuce gidansu amarya. Ina sanye da wata farar doguwar riga wacce aka kawo daga wurin kakanshi a can Rasha, sai mayafin da na rufe kaina da shi aka fara guda alamar angwayen sun shigo sai da suka gaida aka yi addu'a, sannan aka kira ni parlourn baki, koda na isa gabanshi na je, wani irin rungume ni yayi kirjina yana buga tara-tara, ya ce min. ""Finally Mrs Bilal Haris"
Turaki.....
(Allah ya gani page biyu na so baku amma ciwon do da gefen kaina zuwa goshina ciwo yake min sosai
kuyi hakuri zuwa gobe don Allah)
"[12/16/2025, 1:37 PM] Maman Walid: 17"
"Yadda ya rungume ni naji haka a jikina, sai yanzu nake jin kamar ina safe place, he became mine, kara"
"rungume shi nayi hawaye na zuba min tabbas mutumin nan yayi hakuri ya jira har Allah ya bashi, duk wanda ka gaya ya jima yana nima to kada ka ga dare daya ya samu kace ta wata hanya ya samo hakuri da juriya. Dakyar aka janye shi sai guɗa ake mana, kafin aka fitar da shi. Parlourn Mama suka shiga ya zube akan gwiwarshi, da sauran yan uwansa ta ce mishi. "" Bilal ga Lubabatu nan na baka, Bilal idan ka gaji da Lubabatu kada ka wulakanta min ita ka kira Ado ko Tahir ka ce su zo su ɗauki Kanwarsu, Bilal kada ka tozarta min Yarinya idan tayi maka laifi ka kawo min ita ni nan nasan abinda zan mata, Bilal don Allah idan ba zaka zauna da ita kada ka kore ta, ka. Kira a zo a dauketa. Ku shaida na roke shi da kada ya"
"wulakanta min Yarinya don Allah kada ka wulakanta min ita wallahi tana maka ba dai-dai ba, ka gaya,"
zan zo har gidan na iso kota. Ka yi hakuri ka duba rayuwarta na baya ka rike min ita da adalci. Zata maka
"biyayya ba zaka tab'a hanawa tayi ba, kayi hakuri don Allah."""
"""In sha Allah Hajiya babu abinda zai faru, idan yayiwa Lubnah wani kawunansa ni zan fara sare"
"mishi kai."" Inji Uncle Auta, Ubaid ya ce mata. ""Hajiya in sha Allah haka ba zai tab'a faruwa, Hajiya ya iya zaman jiranta duk ya tsufa ya zama Kasungurmin tuzuru kafin baiwar Allah ta amince mishi ai kin san baba tsoho zai rike yar Matarshi da amana!"" Ai kuwa aka yi ta dariya sannan aka yi addu'a. Suka nufi dakin Abba, kasancewar yana jin nauyin Turaki da irin abinda ya mishi, mika mishi hannu yayi Turaki ya riƙe ya cewa Ya Ado. "" Kira min Auta!"" Ya Ado ya zo, abokan wasa sun saka ni a gaba wai a bamu fili kawai tunda sun ga mijin ya gagara boye zallamarsa a fili nima har da wani cusa kaina kai Jama'a, wata abokiyar wasana yar kawuna kenan take min wannan tsiyar.."" Hindatu fito da ita Abba yana kiranta?"" Ya fada a gaggauce, bakiɗaya muka kalli juna, wani irin tsoro da tashin hankali muka shiga dukkanmu haka muka fito musamman yan uwana. Haka muka fito aka shigar dani har gaban Abba tsoro ya gama cika ni. "" Bilal Turaki ga Lubabatu nan na baka ita, Bilal Turaki kada ka saka min Y'a kuka, idan ba zaka iya ba ka dawo min da ita don Allah, don Allah kada ka cutar da ita, ta sha fama da rayywarta na baya idan har bata maka ba, ka kira ni na tura Yarana su daukota. Y'ata yar dangi ce soyayyar da suke yiwa juna Allah kaɗai ya sani, idan har wani zai yi kuka tow kuwa dukkansu zasu yi, bakiɗaya suka goya min mata baya don tayi farin ciki, Yarana basa bayan abinda kake da shi, damuwarsu Kanwarsu tayi farin ciki, nasan suna son kanwarsu zasu iya tsayawa sun yake ka akan Kanwarsu don Allah ga amana mun baka."" Ya turo kekenshi, nima ba matsa kusa da shi, ya dauki hannuna ya mikawa Mr Turaki, ya rike ya d'ago kai yana faɗin."" Allah ya saka da alkhairi, in sha Allah ba zaka tab'a samuna da laifin akanta ba, in sha Allah ba zaka kama ni da laifi a kanta ba, idan ka ga wani abu ya faru tow a cikin kaddaranmu ce, Abba ni yar da ka bani kawai ka min gata, idan ka ga na dawo na butulce maka, ka girmama dalilin haka, Abba ni ba iya y'a ka bani, rayuwa ka kara min domin na kara akan nawa. Abba iya wannan alfarman fa