Advertisements
Chapter 315 Reading ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu

Author :  Mai Dambu Category :  Complete Novels

Chapter   315 / 321

942K to 945K   out of 962.4K words

ni, gara ka gaya min gaskiya zai fi min sauki da sassauci. Ba zan kara maka magana ba amma ka daina azabtar dani da haka Please."" Na fada ina kuka, janyo ni yayi yana faɗin. ""Am curious da kika ce na kara aure, ni a ganina na auri mace ta haihu da ni ba ke ba, cin amanar kauna ce, ba adalci ba ce ba kome ba ne son zuciya ce. "" Girgixa kai nayi ina kuka na ce mishi."" Ba cin amana bane, adalci ne zaka yi don ka haihu da wata mace mace ba"
"wani abu ba ne. Wallahi ba kome ba ne kyautatawa ce da adalci!"""
""" Ba zan iya adalci akanki ba, zan auro mata nayi ta zaluntarsu, zan ta cutar da su saboda ke ina sonki da"
"bana iya dauke idanuna akanki a kwanakin da nayi hakuri nake, amma ba zan iya son wata mace bayan ke ba. Zan cutar da ita su kuma zasu cutar min dake!"" Rike fuskarshi nayi cikin kuka nace mishi. "" I miss you baby;"" na fada ina shashekar kuka, rungume ni yayi yana faɗin. ""Bana da ra'ayin wata mace Allah ya"
"gani amma idan wata tazo ba yadda na iya ke daya nake so!"""
"Shi kenan fa fada ya kare nayi alkawarin ba zan kara mishi maganar aure ko haihuwa ba, kwanaki biyar"
"tsakani ya shirya mana tafiya zuwa ganin likita ni da shi, kasar Ingila. Dama nasan matsalata ban boyewa likitan ba, ya bamu test ya kai goma, kullum ana mana daya kullum sai da muka yi kwana goma aka tsaya jiran sakamakon. Sai da muka samu kwana hudu kafin aka kiramu likitan ya kalle ni ya kalle shi kafin ya ce mishi. "" Kana da Chance sosai na haihuwa, amma ita gaskiya babu Chance sosai domin duk wani hanya da kwayar halittar zata shiga ta wuce har ta samu kwan halittar ta ya toshe. Don haka zamu iya cewa kai baka da matsala akai haihuwa matsalar ta Madam ce itama da a iya magance ta amma sai ta amince ko nace kun amince sai ayi mata. HSG"" zuba mishi idanun muka yi kafin muka kalli juna yadda kuka san ana mana hisabi, saboda tsananin tashin hankali. Mene ne kuma HSG? Kamar yasan abinda"
"muke nazari ya sake murmushi ya ce mana. "" Ku kwantar da hankalinku ba wani babba al'amari ba ne!"""
(Kuyi hakuri don Allah bana jin dadi amma da sauki sosai sannan masu kodai kodai Wallahi bashi
ba ne hmmm idan shine ai maganar rubutu ya kare wai wata Shekara zan cigaba idan da shine Nagode sosai Ubangiji ya karo zumunci)
"[12/25/2025, 10:02 PM] Maman Walid: 29"
"Sauke ajiyar zuciya muka yi lokaci guda, yana rike da hannuna. Wani irin tsoro yana fisgana. Na kalle shi"
"murmushi yayi min irin na kwantar da hankalina, sannan na mai da idanuna kan likitan. Murmushi yayi ya fara zubo bayani kamar haka."
"""Da farko dai zan muku karin bayani akan yadda ake yin HSG"""
""" A harshen Hausa, HSG (wato Hysterosalpingogram) wani nau'in binciken likita ne na musamman da ake"
"amfani da hoton X-ray da wani magani mai ruwa (dye) domin duba mahaifa da magudanar kwai na mace."""
"""Ga daki-daki bayanin ma'anarsa da kuma dalilin da yasa ake yinsa"" sai da ya sauke numfashi kafin ya"
"kalle mu, ganin yadda na gama firgita, ya kalli Turaki yana murmushi ya ce mishi. ""Na ga kamar kai kafi madam karfin zuciya ko akwai tambayar da zaka yi ne?"""
"Jinjina kai Turaki yayi yana matsa hannua ya ce miishi,"
"""Mene ne Ma'anar HSG?"""
Cikin nutsuwa da kwarewa likitan ya ce mishi.
"""HSG gwaji ne da ake yi a sashen hoton X-ray. Likita zai sanya wani siririn roba ta farjin mace zuwa cikin"
"mahaifa, sannan ya tura wani ruwan magani. Wannan ruwan yana haskaka cikin mahaifar da bututun da ke kai kwai (fallopian tubes) domin a ga yadda suke a cikin hoton X-ray."""
"Gyad'a kai yayi yana me kara kallona, jin irin azabar da za ayi min ban san lokacin da hawaye ya fara"
sauko min ba. Ya share min da hannunsa ya kara kallon likitan ya ce mishi
""" Me ya sa ake yin HSG? (Dalilai)"""
"""Likita kan bukaci wannan gwajin ne saboda manyan dalilai kamar haka"""
* Binciken Rashin Haihuwa:
"""Wannan ne babban dalilin. Ana son a gani ko magudanar kwai (fallopian tubes) a toshe suke. Idan"
"bututun ya toshe, kwayar halittar namiji ba za ta iya haduwa da kwan mace ba."""
* Duba Siffar Mahaifa:
"""Don ganin ko mahaifar tana da wata matsala tun daga halitta, ko kuma akwai wasu abubuwa kamar"
"fibroids ko polyps da ke hana juna biyu zama."""
* Bayan Tiyatar Mahaifa:
""" Idan an yi wa mace tiyata a mahaifa ko an toshe mata magudanar kwai don tazarar haihuwa, ana yin"
"HSG don tabbatar da cewa tiyatar ta yi nasara."""
* Binciken Bari (Miscarriage):
""" Idan mace tana yawan yin bari, ana yin HSG don ganin ko mahaifar tana da rauni ko kuma tana da"
"siffar da ba za ta iya daukar juna biyu ba."" Ajiyar zuciya muka sauke lokaci guda, tare da rike hannun juna gam Turaki ya kara tambayarshi."
"""Yaushe ake yin sa?"""
"""Yawanci ana yin wannan gwajin ne kwanaki kadan bayan mace ta gama al'ada (tsakanin rana ta 7 zuwa"
"ta 10 bayan fara jinin al'ada), amma kafin lokacin da take yin kwan haihuwa (ovulation). Wannan don a tabbatar ba ta da juna biyu a lokacin gwajin."""
Shin yana da zafi?
"Mafi yawan mata suna jin dan ciwo kamar na ciwon mara (cramps) lokacin da ake tura ruwan maganin,"
"amma ciwon baya dadewa."""
"Rike hannun mijina nayi tare da cewa. ""A'a na hakura wallahi na hakura ba zan iya wannan azabar"
"ba."" Gyada kai yayi yana faɗin. "" Bata so ina ga a hakura da shi."" "" Tow shi kenan amma ku yi nazari dai!"" Haka muka fito daga dakin muka bar asibitin. A hanya ya ce min. ""Sorry na saka ki kuka!"" Murmushi nayi na daura kaina a kafad'arshi. Haaka muka isa masaukinmu, bai kara min magana ba har ya fita abinsa."
"Kwanakin da muka na tsawon sati guda, ranar ya fita ina ga akwai wani abu me muhimmanci da ya fitar"
"da shi ina kallo da laptop dinsa, na ga wani sako kamar ba zan bude ba, na buɗe."
*Fisabiilillahi sai ka biye mata ta fasa ganin likitan? Idan ita bata son haihuwa kai zaka zauna ne naka
biye mata tunda bata bukatar haihuwar shi kenan amma ka sani na gaji da dakatar da Daddah akan ita tana son ganin Yaranka*
...... Mujitafa Kumo
"Wani irin abu na ji ya tsaya min a rai, dama haka suka damu da rashin haihuwata, binciken laptop din"
"nayi naga yadda Uncle Auta yake tambayarshi yana bashi amsar a sanyayye, hawaye ne ya zubo min. Da yawan kuɗin da ya kashe. Don na ga likitan, dafe kaina nayi cikin wani irin nadama, wani irin mutum ne da yake bin muradina? Duk abinda nake so kawai zai ko da blind eye, kuka ne ya kwace min domin na rasa wani irin so yake min da yake biye min haka, hada takardun nayi na wuce asibitin nayi sa'a kuwa likitan yana nan, ina ganinsa na fashe da kuka.. ""Doctor bayan HSG babu wani hanya ne? Ka taimaka min mijina yana sona, yana kome domin ni, amma bana son ta fuskanci damuwa saboda ni. nasan yana jin ba dadi ina son na ga nashi babyn ne a tare da ni."" Murmushi yayi ya ce min. ""Dole sai mun san yanayin ciwon da maganin hana daukar ciki ya haifar miki, shi yasa nace ayi gwajin HSG,"" ""Na amince!"" Na fada bakina yana rawa, ""Yaushe ne zaki fara Al'adarki?"" ""Nan da kwanaki uku!"" Na bashi amsa. ""Kuma kina Evolution?"" Shiru nayi kafin nace wani lokaci ina yi wani lokaci bana yi!"" Na fada ina kallon kasa. "" Shi kenan, zan baki magani ya taimaka miki da evolution din sannan idan kin yi sai ki kawo mu san yadda za"
"ayi."""
"Murmushi nayi na ce mishi. ""Sai me kuma?"" ""Ba wani abu ai Mijinki ya biya kome tun farko don har ana"
"maganar za a tuntube shi don mai da mishi kuɗinsa."" ""Na dawo ayi aikin."""
"Gyada kai yayi sannan ya bani takardar magani da wata takarda alamar daga wurinsa ne, ina zuwa"
"aka bani. Koda na koma masaukinmu, na same shi ya zubawa kofar idanu. A hankali na nufe shi bude"
"min hannu yayi ka shiga cikin hannun na durkusa a gabanshi, tare da daura kaina a kirjin shi. "" Waye"
"yake bada haihuwa?"" Ya tambaye ni."" Allah! "" Na bashi amsa, ""ina fatan idan aka yi aikin ba zaki yi fushi ba idan har aka samu fail?"" Nodding kaina nayi alamar eh, shafa kaina yayi yana faɗin."" Good gurl;"" share min hawaye yayi s hankali ya shiga shafa bayana, har barci ya dauke ni, a daren na sha maganin har tsawon kwanaki uku. Kafin na fara period, wani nayi kwanaki biyar kafin ya dauke sannan muka"
shirya ranar Monday muka je ganin likitan anan ma aka kara bani wani maganin na kwana kwanaki biyar.
"Kamar da wasa na sha na kwanaki biyar sannan muka koma a kwanakin na fara evolution, haka aka yi"
"min aikin da na sha matuƙar azaba, koda aka fito da ni kamar bani da lafiya, haka ya tsaya a gefena har tsawon wuni guda. Lokacin da na farka na ganshi zaune ya kura min idanu. Sai ya bani tausayi na mika mishi hannu ya d'aga ni. Kuka na saka mishi. ""Am sorry My Man, am really sorry!"" Na fada ina kara rungume shi, shima rungume ni yayi yana shafa bayana, tare da sumbatar kaina ya ce min. ""In sha Allah ko baki haihu ba, zan zauna da ke a haka ba kuskure ba ne, sai mu yi adopted din Yara biyu mace da"
"namiji ko?"""
"Na sha kukana ni daya amma shima ya sha aikin rarrashi, kafin ya taimaka min nayi alwala da sallah,"
"kafin ya kawo min abinci. ""Ya aka yi nayi barci?"" Kallona yayi kafin ya ce min. ""Kina ta kukan maranki yana ciwo tunda aka yi aikin shi ne ya miki alluran barci."" ""Sorry!"" Na ce mishi. Lakace min hanci yayi, na sake murmushi. Ya hade goshinmu wuri guda, ""ina sonki!"" Hannuna na kai bayanshi na lumshe idanuna. ""Me too!"" Bayan na nutsu ya kira Abba muka yi waya da su. Sannan ya kira Ubaid suka yi magana."
"Wunin ranar ina makale da shi, har washi gari sannan aka sallame mu. Sakamakon ya fito magani aka"
"hada min, wanda ba san yadda zan yi da su ba, sati daya muka kara na warware sannan muka dawo Nigeria."
"Cikin so da kaunar juna, wani irin yanayi nake ji na tausayinsa domin kuwa kwana biyu nan a gajiye yake"
"dawowa daga nan zai fita, ni na zata ko don akan maganar rashin haihuwar ce, ashe wata kullaliya aka"
kulla min. Wanda ya tsaya kai da fata yake faɗa a kai. Watan azumi ne a gabanmu don haka kowani musulmi shirin azumin yake.
"Ana saura sati azumi aka kawo sabbin kaya, aka kwashe tsofaffin aka fitar dasu. Matar Uncle Auta ce"
"ta shigo muka gaisa ta min fatan alkhairi. Har zata fita ta ce min. ""Lubnah kin san me ke faruwa kuwa?"" Girgiza kai nayi ina kallonta. Shiru tayi kafin ta ce min. ""Mijinki za ayi wa auren dole fa da kanwar Matar Ubaid. Wannan ba gyaran tarban azumi ba ne Alhaji ELYakub ya ce a kawo miki kayan fadar kishiya a fara da wannan."" Murmushi nayi na ce mata. ""Wallahi ban sani ba, Allah ya bada sa'a yasa a dace."" ""Amin Ya"
"Allah! Don Allah kada ki d'aga hankalinki anyi haka ne don a bata miki amma kada ki damu;"" murmushi"
"nayi nace mata. ""Wai ai na jima da sanin haka zai faru amma ban kawo ta bangarenta ba ne hankalinta"
"ya kwanta Falilah kenan ina ga da Mijinta nake aure sai ta kashe ni, abokin Mijinta nake aure take kishi da ni wai 'Allah ya kyauta."" ""Amin Ya Allah!"" Daga haka ban kara ba, ai kuwa ban san me aka yi ba itama Matar Uncle Auta ta juya maganar ne sai maganar sai ga case ina zaune sai ga Mahaifiyar Badriyyah tazo inda take shiga ba nan take fita ba, abin har da gorin haihuwa. Sai ranar na fahimci girman illar da Hafiz yayi min domin kamar xan mutu, haka suka tafi har da matar Ubaid din, bayan tafiyarsu Matar Uncle"
"Auta ta shigo, yadda suka bar ni kaina yana ƙasa, haka ta gama surutunta ban d'ago kai na ce ci kanki ba,. Ta fita itama jikinta a mace. Har ya dawo ban nuna mishi abinda ya faru ba, domin shima bai da nutsuwa. Shafa kanshi nayi ina murmushi na ce mishi."" Me yasa kake damuwa ne baka cin abinci sosai fa!"" Jan kimatuna yayi muka saka dariya, yadda muke rayuwarmu haka muka yi kome sannan muka kwanta. Rike hannunsa nayi na ce mishi. ""Me yasa ba zaka amshi tayinsu ba? Yanzu ana niman shekara daya kenan da aurenmu, ban ga laifin Daddah ba."" ""Wasu sun zo nan ne?"" Buga kofar parlourn da ake yi ne. Na kalle shi. ""Hamma Turaki?"" Na ji muryan Falilah a tare muka fito da shi ina sanye da Hijab har kasa, yana budewa ta shigo ita da yarinyar da akace zai aura ta fashe da kuka. ""Hamma Turaki, meye laifina don akan aurenka da Zakiya? Ashe Baban Nihla ya je yana niman auren kanwar Maman Husnah Yarinyar nan"
"walidah kawar Zakiyah. Fisabiilillahi."""
"""Kin san bakya son zama da kishi kika tafi har gaban Daddah kika hada min munafunci, ai ni na"
"bada sadakin karma is bitch shine zai kashe ki, aure babu fashi."" ""Baby ka bani kudin hada kayan leffe please bana son wannan damar ya wuce ni, zan hada muku kai da ita in sha Allah."""
"""Idan har rashin haihuwa ne kema me yasa baki kara wani haihuwar ba, Yan mata zan ki kudin kayan"
"lefe!"" Wani irin mutuwa jikinta tayi ta ja kafa ta fita, kallonshi nayi cike da Mamaki. ""Dama aure Ubaidullah zai yi?"" ""Eh kai ya jima yana son yayi aure shegiya tana hanawa na rasa gane me kika tsare mata take jin haushinki, yanxu zata ga rashin mutumci ganin idanunta ba ita yar iska ba!"" Rike baki nayi"
ashe haka yake da rashin mutunci.
Ai kuwa ba washi gari Ubaid yazo yayi ta bani hakuri Allah sarki sai ya bani tausayi. Idan baka samu
"mace ta gari ba rayuwarka tana cikin garari, wani ikon Allah ni da taso ganin nayi hauka. Da na gayawa Dangina addu'a aka yi ta min Allah sarki saii ga Yadiko tazo ta kawo min maganin wanke mahaifa, da sauransu. Satinta biyu ta koma, a lokacin har na gama hada lefen Ubaid ai yadda ta min kan kara haka zan mata na itacce. Kuma na shiga gaba aka kai kayan auren, muna dawowa tayi ta hauka da ihu zata"
dake ni. A raina na ce ko zaki mutu aure sai anyi shi......
"[12/26/2025, 4:22 PM] Maman Walid: 30"
"Ihu da haukar da take yi, har cikin parlourn ina jinta, hankalina yana kan abinda nake haɗawa don na sha,"
"""wallahi idan ina raye sai ga bayanki!"" Ihu da hauka iri-iri tayi shi gashi an hanata shigowa gidan, a ranar dakyar ta koma gidanta, ina jin yadda yake ihu da tashin hankali."
"Da yake mijina ya tafi wani meeting Abuja sai dare zai dawo haka na hada magani gyaran jiki, wurin"
"karfe shida ya shigo a gajiye, karban jakan nayi kallonshi. Yayi laushi na tab'a goshinsa ina faɗin. ""Anya yau lafiyarka lau kuwa?"" Murmushi yayi ya wuce kitchen yana faɗin. ""I need water!"" Na biyo bayanshi na bashi ya sha, sannan ya sauke ajiyar zuciya can kuwa ya fara wani irin tari. ""Me yake damunka?"" Na rike hannunsa muka wuce cikin dakina, ina shafa bayansa.. sai da na taya shi wanka duk yayi laushi. ""Me ke damunka!"" Masallaci ya tafi bayan ya dawo ya kwanta sai dai dama mishi kunu nayi ya sha, ina rike da hannunsa. ""Meke damunka?"" ""Bana jin dadi ne almost 3-days kenan."" Sake tab'a wayarshi nayi na ji zafi rau. ""Baby you're burning! Muje asibiti."" Girgiza min kai yayi yana mai rike hannuna ya ce min. ""Please sir na da sweater!"" Haka na wuce dakin na kawo mishi, ya saka nace mishi. ""Me kake so!"" Girgixa min kai yayi yana faɗin. ""Bana jin yunwa."" ""Fisabiilillahi haka zaka zauna da ciwo?"" ""Hmm!"" Ya ce min na rasa me yake min dad'i, duk ya rasa kuzarinsa, haka yayi ta zazzaɓi a kwanakin ya daina zuwa office sai da yayi sati s gida, wanda ya janyo aka kai shi asibitin da baya so. Ruwa suka yi ta saka mishi, wani abin mamaki"
sai jikinshi ya rikice sosai. Wanda ya saka ni cikin wani irin tashin hankali.
"Wanda ya kai aka tura shi ICU, dole Mama ta zo. A cikin kwanakin nayi wani irin rama domin bana"
"cin abinci bana kwakwaran barci. Tunda Mama ta zo take nazarin yadda yanayin mu alamata da danginsa idan ya wuce Daddah da Alhaji ELYakub sai Uncle Auta da Ubaid. Kallona tayi ta ce min. ""Kina cikin abinci kuwa?"" Murmushi nayi na ce mata. ""Ina ci!"" Riko hannuna tayi ta ce min. ""Kamar kina da ciki ko?"" Da sauri na kalleta babu kowa a wurin, na ce mata. ""Ciki Mama?"" Gyada min kai tayi, nayi kasa da kaina. Tun last week ya dace period din ya dawo amma har yanzu shiru, sai ciwon gefen ciki da yawan kasala. Na zata ko don rashin lafiyarshi ce. Rufe bakina nayi da hannuna daya na kalleta. ""Innalillahi wainnalihir rajoun! Mama!"" Hannu ta saka min a bakina. ""Mijinki ma kamar hannu aka saka mishi, bani da tabbas amma ki shirya mu koma gida!"" ""Mama!"" ""Ba zan barki anan ba, domin shima a nan din farautar rayuwarshi ake idan har shi ba a kyale shi ba, kema ai baki tsira ba. Waye kika yarda da shi a cikin danginsa!"" ""Tarik!"" Na furta kai hatta Uncle Auta da Ubaid ban yarda da su ba,. Kiran Tarik nayi a waya.. ""My boy ina son ganinka don Allah!"" ""Ina nan tafe gobe in sha Allah!"" ""Muje gidan Adamu!"" Bata gayawa kowa dalilin tafiyarmu ba, haka muka isa gida, dai naji kamar nayi kuka, idan na tuna yadda na barshi. Kusan kwana nayi da zazzaɓi, washi gari Tarik ya iso ban san me Mama tayi ba amma da safe ruwan zam-zam

315 / 321

Chapters