Advertisements
Chapter 304 Reading ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu

Author :  Mai Dambu Category :  Complete Novels

Chapter   304 / 321

909K to 912K   out of 962.4K words

da Ya Ado ya hana shi shiga gidan amma yadda ya haukace sai da naji kamar nayi mishi wani kuskure mai girma domin kuka yake wiwi yana rokon ko za a kashe shi ne ya yarda fatanshi ya mutu ina tare da shi, akwai wani abu da na kasa rabuwa da shi a tsakanina da Ya Hafiz shine tausayi, ina tausayinsa wanda na fahimci cewa har yau zuciyata tana tunawa da shi, sai dai da ba tuna da tarin laifuffukanshi a tare da ni, sai na ga bai"
"cancanci nayi wasa da rayuwata ba, amma kuma shi Mr T zai zauna da ni bana haihuwa ne?"
"A rana na biyu da yake zuwa gidan na fita, wanda sai da nayi danasanin fitar da nayi. Domin kuwa"
"lokacin da na fita na same shi yana tsaye ya zuba min idanun Ya Hafiz da na sani ɗan gayu ne na fitar hankali amma wannan na gabana kamar wanda aka kamo shi daga cirani, gashi ya yamutse kamar wanda aka biyo bashin masifa, kallonshi nayi na tuna yadda yake min dariya a baya. ""Me kake bukata?"" ""Ki yi hakuri!"" Shiru nayi ina kallon kasa ashe akwai ranar da Ya Hafiz zai bani hakuri? Ashe akwai ranar da zai zo ya ce min nayi hakuri? Na zata shi mutum ne me ra'ayin kansa ba a saka shi ba ya ji kuma baya gani. ""Amma kasan na amshi sadakin wani ko?"" Tsayuwar motar Mr Turaki a gaba damu ya kashe ya fito, ya tsaya yana kallonmu. ""Ya Hafiz kayi hakuri ka rabu da mu, ban san me ciwon kai ba sai da na haɗu da shi, ban san yadda zuciya take ji ba sai da na same shi a rayuwata, nasan kuruciya tasa na amshi"
"soyayyarka amma shi zaman jirana yayi har wannan lokacin, ina jin wani abu a kanshi."""
"""Karya kike yi, wallahi karya ce bakya sonshi kudinsa kike so don ya biya muku bashi."" Ya cigaba da zage -"
"zage. ""Wuce ki shiga cikin gidan."" A hankali na juya ina kallonshi, hawayen dake ta danne shi ya sauko da gudu, na saka bayan hannu na goge. """
"A wancan ranar da ya tsaya a gabana, rawan kai da rashin sanin ciwon kai yasa naki kulawa da tarin"
"Alkhairinsa, amma a yau da yake gabana sai nake ganin kamar banbanci sabon rayuwar da yake bibiyata da shi ba, nayi laifi amma haka ba yana nufin daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaki ba ne, wancan da ya tsaya min a wancan rayuwar kama yake da gardi irin almajirai da aka ɗauki nauyinsu. Madadin yau"
"wanda yake gabana, CEO ne guda mai cike da kammala da nutsuwa, ba kamar wancan na baya mai"
yawan murmushi da fara a ba. A yadda nake kallonshi tsaf zan buga kirji nace shi din masoyina ne amma
"kalaman Ya Hafiz da ya fada ya saka ni jin wani irin abu ya tsaya min. "" Kana ta murna ka kai sadaki shi sadaki ba aure ba ne, kuma idan har a Bauchi za a daura auren in sha Allah ta haramta maka. Domin kuwa ni ne mijinta a duniya ni ne a lahira!"" "" Ya Hafiz wannan rayuwata ce, me yasa sai ka lalata min rayuwata ? Me na maka kake son saka ni a damuwa? Na zata duk tarin alkhairin iyayena da suka maka sai ka tozatani?"" Murmushi yayi alamar ya samu nasara ya a kaina sai ya juya kan Mr Turaki ya ce mishi. ""Ka sani baya haihuwa, domin!"" ""Waye ya gaya maka kowa yake bukatar Haihuwar? Ni ita nake so, ba"
"wani abu ba, idan don wani abu nake bukata baka isa ka aure ta a farko ba, ka. Ji na gaya maka kul!"""
"""Wallahi baka isa ba! Lulu ki dawo gare ni hatta Arzikin Abba yana tare da aurenmu tunda muka rabu"
"masifa suke ta faruwa baki gane ba ne? "" Cikin wani irin baki ciki. Na juya zan fita suka fara fada kamar zasu kashe kansu."
"Kasa magana nayi ina kallon maza biyu a gabana, na rasa yadda zan yi da rayuwata. Ban gama nazarin"
"abinda zan fa musu ba, sautin muryan Ya Hafiz ya daki dodon kunnena. ""Ke ce silar farin cikin iyayenmu, ki dawo aurenmu domin kaf duniya babu namijin da ya isa ya zauna dake, don ni nafi dacewa da ke."
"Luluna ki sani babu wani namijin da zai so ki sama da yadda na so ki!"""
"Sautin murmushin CEO na ji yana mai kallon agogon hannunsa ya ce min. ""Think wisely, ba zan raba"
"ki da Ex ɗinki ba. Amma ki sani ten years ba ten months ba ne, ba kuma ten weeks, ba ten days ba ne ba"
"kuma ten hours ba ne. Ba kuma ten minutes ba ne, na ajiye kome dominki duk lokacin da kika shirya ina nan ina dakonki."""
Sai na shiga rud'ani CEO ko Ya Hafiz waye zan komawa...........
"[12/14/2025, 9:16 PM] Maman Walid: 14"
"Ji nayi kaina yana wani irin juyawa, da karfi na ce musu. "" Ya isa nace ya isa haka. Ka je ka amshi"
"sadakinka kai kuma na kara ganinka sai na kashe kaina sai ka auri gawata."" Na juya cikin gidan da sauri"
"don na gaji da maganarsu. Muryan Hafiz ya kara tsayar da ni. ""Idan baki dawo gare ni ba. Wallahi haka zaki kare rayuwraki babu namijin da ya isa kallonki!"""
"""Ai kai ba Allah ba ne muna nan zaka ga tayi aure, don abu kazan kazanka ubanka!"" Inji Ya Ado da ya fito."
""" Kuma wannan da yake gabanka shi ne Mijinta. Aure kake cewa ba zata yi ba? Kai ne zaka hana auren,"
"kambu tow Bismillah macuci azzalumi mara imani. Ina ga sai an shiga tsakaninka da Lubnah tunda abinda kake nufi kenan katon dakiki jahili."""
"Tas Ya Ado ya wanke Hafiz sannan ya bawa Mr Turaki hakuri. Tun daga nan na kara shiga damuwa,"
"lokaci zuwa lokaci ina ganin sakon kudi da kati da kuma data, tow me zanyi da shi? Ni ire-iren waɗannan abin basu wani burge ni. Amma haka na share na cigaba da harkan gabana, Ya Hafiz ma bai daina kirana ba tare da barazana, har na rasa yadda zan yi da raina, a gefe kuwa Mr Turaki ya zuba min idanun bai kara bin ta kaina ba, sai dai abinda na fahimta shi irin mutanen nan ne masu iya dafa mutum da ruwan sanyi ba faɗa ba zagi amma wallahi gara yayi min hargowa irin na Hafiz amma ina ko da wasa bai ƙara bin ta kaina ba, har ranar da na bar lagos, sai da na isa gida na huta na ji yana ta waya da Mama da Yadiko, zuwa yanzu na fahimci yadda Turaki ya samu fada a gidanmu, yadda ka san su kwanta ya bi ta"
"kansu, Mama kuwa tasa ni tayi a gaba tana min gyaran jiki da jike jike take min, tare da dauke min huta."
"Ban san inda ta hadu da wata yar maradi, matar nan har gida take zuwa ta min gyaran jiki. Ko waje"
"bana fita saboda gyara da kulawa. Sai abin Yadiko nake jin an saka auren wata guda, tab'e baki nayi kamar wacce ta ga kashi na ce mata. ""Kuna ta wani damuwa bayan shi ba sona yake ba!"" Na fada ina tura baki, rike baki Yadiko tayi ya ce min. ""Inji waye? Waye ya gaya miki baya sonki? Ko kafin ki zo sai da ya zo kwanansa daya ya koma ko garinsu bai je ba, a tsohon dakin Sani ya sauka. Mijin da kika samu ba karamin mutumin kirki ba ne, har wurin danginmu sai da ya zaga ya gaishe su. Ke ki godewa Allah."" Tura baki nayi na ce mata. ""Ba wani sona yake ba kawai ganin haka kike kawai."" ""Soyayyar ta daki hancin kaniyarki, baya sonki kuma haka za ayi auren idan kin shiga ko sha piya-piya ki mutu ja'ira kawai."" Inji"
"Mama tana mai sake labulen, tana mita akan Yadiko take biya min nake iskanci kala kala."
A daren Hafiz yazo gidan yayi ta kuka yanzu zai cika baki zuwa anjima zai koma yayi ta bada hakuri.
"Zuwansa na uku kenan, babu wnada yake kula shi. Ganin haka Yadiko ta fito ta ce mishi."" Amma kasan haramun ne nima a cikin nima?"" "" Yadiko ina son Matata, aka raba ni da ita."" "" Uwarka ta rabaka da ita! Ita ta kawo khulu'i amma bata kai kotu ba, uwarka da yan uwanka suka kai kotu, don mune marasa zuciya sai mu dauke ta mu dawo maka da ita, sakarai kenan ai Lubabatu ta wuce lisafinka abinda baka zata ba ne ya same ka, tunda baka so ta samu miji irin wanda take tare da shi, sai ga shi bata cutar da kai ba, ta samu mijin kere sa'a shine bari ka lallabo kazo da wata fitinar da zata janyo a dakatar da auren"
"ko?"""
"""Ai kuwa ko Hasiya da ifritai take yawo bata isa ba wallahi, lokacin da ka rabu da ita ai cewa kayi mata a"
"gari kamar jamfa a jos, ina zaka kai kayan wanki, da Allah ya tashi sakayya sai gashi ita da kake mata kallon ba zata samu mijin da bai kai ba, sai gashi Allah ya bata wanda baka isa ka tsaya a gefensa ka ce ka tab'a auren Lubnah ba, kai ko a lahira ka ga Lubnah ka ce kasanta sai Allah yayi mana hisabi, fita kafin na watsa maka ruwan zafi dan iska mara mutunci idan na. Ganka kamar na ga mutuwata haka nake ji."
"Yanzu ka kawo kara ta auri wanda ya fika saboda bakin ciki sa mugunta. """
"Kusan abinda Mama ta fada gaskiya ne, yanzu Ya Hafiz ya dawo ne don yaga xan auri wnada ya fishi,"
"da ace baya ne ko a jikinshi tunda yasan wanda zan aura bai kai shi ba, amma a cikin lokaci kalilan yaji"
"labarin wnada zan aure haka yasa yake jin kyashi da hassada, yana niman hanyar da zai bata kome kowa"
"ya rasa. Wannan abin ya d'aga mishi hankali. Shi yasa yake ta wannan koke -koken Mama kuwa ta rantse ya sake zuwa sai ta mishi babu dad'i, ya kullaci auren nan a ransa kuma duk inda ya zane, zai lalata auren"
nan sai yayi.
Hafiz
"Tunda ya bar gidan yake kiran Hajiya amma bai same ta ba, ya kirata yafi sau uku. Amma bai same haka"
"ya koma gefen titi ya kira Nana, ta dauka. "" Ina Hajiya?"" "" Bata nan"" ta bashi amsa, "" Nana ya zanyi? Ba zan iya barin Lubnah ta auri wancan mutumin ba, idan ta aure shi wallahi ko na fada na taɓa aurenta karyata ni za ayi. Na gayawa mara mutunci cewa har hauka tayi ya ce shi ma mahaukaci ne zasu zauna cikin kauna da soyayyar mahaukata. Nana kamar xan mutu don Allah ki gaya min yadda zan yi?"" Ya tambaye , har da kuka kamar yaro. Shiru tayi ta ce mishi. ""Ni dai ina kyale su, ka kyale musu rayuwarsu, rayuwata ma ta ishe ni ina cikin tashin hankali ba zan iya tsayawa ka kara cutar da Lubnah ba, domin duk sharrin da Hajiya ta tura mata gashi nan akan nawa Yaran, mijina ya sako ni a gaba ni ba sakakkiya ba ni ba mai aure ba, sannan kai kanka kana cikin arzikin Lubnah ne tunda har yau babu wnada ya ce ka bashi key ɗin motar da ake tukawa ashe kuwa dole ka barsu su rayu cikin kaunar juna, idan kuwa ka dage sai"
"ka raba su, wallahi karshe rabon da yake tsakaninsu ya kashe ka."""
"Sai yau yake wani irin danasanin hana Lubnah haihuwa yasan yadda Uwa take akan Yaranta, ba zata"
"tab'a hakura da Yaranta, ta auri wani namiji ba, yau gashi yana ji yana gani wani zai dauke mishi Lubnah, yau da yana da Yara da ita wallahi ko da iya Yaran zai saka dole ta dawo, kuma ya daura daga inda yatsaya. Amma bai san wani abu yasa ya ki hada jini da ita ba, a yanzu idan kalle ta sai yaji kamar bai taɓa mu'amala da wata mace bayan ita ba, sai ga ita ɗaya ce zata iya daukar laluranshi, ita ɗaya ce zata so shi zata iya hakuri da shi, wani shegen kishi ne ya kama shi ya kira Hajiya sai lokacin ta dauka tana faɗin. ""Lafiya dai?"" ""Hajiya so nake a nakasa min mijin da Lubnah zata aure tun kwanaki nake gaya miki a yi abinda zai hana auren, kamar yadda aka binne zancen bashin nan amma kin ki yin kome!"" Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce mishi. ""Hmmmm Yaron nan da zai auri Lubnah Kakaninsa akanshi suke, suna tsaye akanshi yadda baka zata ba, ita kanta Lubnah Uwarta tana tsaye a kanta babu yadda za ayi wani abu na sihiri ko tsafi ya same su, domin suna cikin kariyar Allah. Sannan idan aka matsa mutum zai iya fuskantar gagarumin lamarin wanda mutuwa ce.."" shiru yayi duk da wannan bala'in tsoronshi da"
"mutuwa a fili take, duk abinda za'a kawo mutuwa a cikinshi yana gudu."
""" Hajiya a nakasa shi ya koma ba namiji ba!"" Ya fada yana kallon titi. ""Baka gane bane? Ba fa abinda za a"
"iya mishi domin Yaron jikinshi a tsare yake itama Lubabatu babu wani abunda zai iya zama a jiknta, da kamar da ne zaka iya amfani da yadda za a zuba mata abincin da zata ci, in sha Allah za a dace amma a yanzu ko me ka bata ba zata tab'a karba ba."" ""Hajiya a hada a kayan gudunmawar da zaku basu, na"
"hakura amma wallahi sai ta fito saboda matsala. """
""" Ka shirya mutuwa?"" Ta fada mishi cikin kosawa da maganarshi, "" sannan ka sani irin wannan aikin ba"
"karamin kudi yake ciki ba, idan ka shirya sai ka turo kuɗin aiki da na yanka, amma ka sani ba zanje na amso kayan aikin ba, kai zaka ne can ka amai kayanka ni nawa na shiga tsakani ne! "" Bai ji ya fasa abinda yayi niyya ba, dan kudin da ya samu a wurin wani abokinsa ya tura mata akan kafin ya iso Jama'aren sai ta je ya amso. Haka ya cigaba da tafiya yana ta sake sake. Yadda idan aka yi aikin Lubnah zata kasance"
"da shi domin auren maza biyu zata yi, yasan abinda ya shirya mata."
**
Washi gari
"Da safe aka yi kosai sadaka aka raba da kunu, da rana aka yi yankar katon rago. Haka aka raba makota."
"Ashe Mama ta saka ayi min saukar Alqur'ani ne, kwana biyu a tsakani ta ce maza na shirya zamu tayi abuja, haka na shirya sai abuja. A ranar da muka isa aka gama mana kome muka tayi Umara da ita, jajjirtacciyar uwa irin Mama dakyar za a samu irinta, domin kuwa tana tsaye a kaina kamar hasken rana. Sati biyu da nayi muna addu'a da rokon Allah sai ma ji bakiɗaya na sallamawa Ubangiji kome nawa yayi duk abinda zai yi a kaina. Ranar daren Juma'a, ina dawafi, sai naji kamar Mr Turaki yana filin ka'aba ko da na juya ban ganshi ba, amma jikima ya bani yana nan, amma ba yadda xan ina cewa ga inda yake. Haka na cigaba da ɗawafina, sau biyu sai na zo inda nake jin yana nan zan ji alamar yana kallona amma da zaran na juya zan ga babu shi, haka nayi karo na biyu muka yi ido huɗu da shi, gefenshi Jasminah ce da Yaranta, Yaran suka tawo da gudu suka rungume ni, sai ya saje da turawan da suke gefenshi. ""Ilham Nadiya!"" Na riko hannunsu muka zauna, ""Aunty Lunah!"" Buge mata baki yayi yana hararanta. ""Lafiya lau Maman Nadiya!"" ""Ina wuni Sir!"" Wani irin kallo ya min irin na rud'anin nan, ina hango yadda yake maimaita kalmar Sir a lips dinsa, ya kara maimaita kalmar yafi sau uku. ""Baby Il nayi kama da cow?"" Ya tambaye ta, da yake Yarinyar bata san me yake nufi ba, ta ce mishi. ""Uncle wani irin cow milk cows?"" Wani irin kallon ya watsa min ya cigaba da biye mata suna maganarsu, ""Yaushe kuka zo?"" Na tambayi Jasminah. ""Yau kwana biyu kenan!"" Shiru nayi tsakaninmu kwana uku kenan, na saci kallonshi waya yake yana raba idanunsa a ko ina, can muka yi ido huɗu da shi, so nake na kare mishi kallo. Rigar jikinshi jallabiya ce amma ta wani kwanta a saman kirjinshi, wanda ya fitar da six figures dinsa, a inda nake ina iya hango bakar singlet din da ya saka. A hankali nake binsa da kallo har idanuna ya sauka kan zoben da Mama ta bashi, yayi mishi kyau. Koda na d'ago kai na zuba mishi idanun, mikewa yayi zai bar wurin na cewa Jasminah. ""Bari na shiga Masallaci."" Sallah zan yi na kara godewa Allah da ya haɗa ni da irinsa. A lokacin da ban zata ko na kawo zan samu irinsa ba. Amma me yasa yanzu nake jin tsoronshi? Wayyo Allah duk wancan maganar da na gaya mishi ne, haka na tafi ta ce min. ""Muma masauki zamu koma."" Sallah na je nayi sannan na fito zuwa gida a hanyar komawa ta masauki ni daya ce mace dayawansu maza ne sai daidaiku masu mata, kuma fararen fata ne. Ina tafiya naji wani ya bangaje ni, ya wuce da Matarshi. abin ya bani mamaki, tsayawa nayi ina kallonsu, tsayawar da suka yi na ga sun juyo tare da nufo ni, kallonsu nayi Mijin ya ce min. ""Don Allah ki yi hakuri ban lura ba ne, Mijinki ya ce ba zai yarda ba."" A hankali na kalli inda yake ya wani haɗe rai. ""Kiyi hakuri mun bar Yaro ne da Mahaifiyata kuma nasan ya tashi yana kuka a masauki "" murmushi nayi nace mishi. ""Ba kome ku je."" Juyawa suka yi zuwa"
"wurinsa suka bashi hakuri sannan suka tafi suna juyowa suna kallonmu, sai da na iso wurin da yake ya"
"cigaba da tafiya kamar yadda wadancan ma'auratan suke tafiya, har zuwa masaukinmu. Mama na hango"
"suna hira da Yaran Jasminah. Wurinsu na nufa na zauna a hankali ina faɗin. ""Wash Mamana yunwa nake ji!"" Shima zama yayi ya gaida Mama yana mai latsa wayar cikin kulawa ta ce mishi. ""Bilal ka dawo?"" Kallon yadda matar nan ta juya min baya zuwan wannan gardin nake. ""Eh Mamana!"" Sake baki nayi ina kallonsu. Cike

304 / 321

Chapters