Author : Mai Dambu Category : Complete Novels
har shi aka rasa wanda zai yi wani abu, karshe saka min ita nayi na bata nono, sannan na koma na kwanta, bayan na kwanta shi ya cigaba da kula da ita, har ta koma barci. Karfe hudu na asuba ta tashi, ya fita da ita zuwa dakin Umma itama ta daura da ita har zuwa hudu da rabi ta kawo ta na bata nono. Na koma na kwanta ita kuma ta kwanta. Dakinsa ya wuce ya kwanta sai karfe biyar ya fita sallah yana dawowa ya shiga bude kayan da aka kawo mishi last week daga Russia, duk wani abin bukata ya saya. Ina wurin karfe shida na shiga wanka ina fitowa yana hado min tea, na sha Umma ta min dumame naci, ya dauko belt ya mika min na daure cikina, na saka wata Flora gown. Ina gamawa na ya fita zuwa kitchen sai gashi da wasu bottle, Umma tana kallonshi ya mika min tare da gaya min yadda zan yi amfani dashi, ya mika min Babyn ina daura ta akan ɗayan nonon wannan da muka saka abin zuba sai ga shi ya fara zuwa, a cikin bottle din. Kafin wani lokaci ya taru na sauya mata na bata ɗaya ma, sannan"
Umma ta mata wanka.
"""Amma nonon bai miki zafi ko kamar na asibiti."" Dariya nayi na cigaba da fito da kayan da zaa saka"
mata. Ya shigo da fruit dakin.....
"[1/6, 10:23 PM] Maman Walid: 36"
"Ajiyewa yayi a stool sannan ya amshi kayan ya ce min. ""Zauna ki ci."" Na bar mishi aikin ya cigaba ni kuma"
"na zauna ina ci, ina kallonshi cikin kulawa. ""Daada ka karya kuwa?"" ""Bari a shirya my queen sai na je na ci ko!"" Gyada mishi kai nayi, a hankali na zame jikina ganin suna ta hira, na nufi kitchen, da kaina na fara hada mishi abinda zai ci, ina tsaka da gasa dankalin turawa naji ya rungume ni ta baya. ""Yanzu aiki kika zo yi ban sani ba?"" Murmushi nayi nace mishi. ""Meye amfanin zaman da nake yi kana aikin kula da Mammy ni kuma sai na bawa dan Mammy abinci ko?"" Janyo kujeran kitchen din yayi ya zaunar da ni yana faɗin. ""Hutawa ya dace ki yi ba aiki ba."" Murmushi nayi nace mishi. ""Na sani amma kuma ai kafi ni buƙatar abinda zaka ci, ni ina gida ne kai kuma zaka office.!"" ""Inji waye ya ce zan tafi office!"" ""Wai kana nufin ba zaka office ba?"" ""Sai dai su kore ni!"" Kallonshi nake a hankali, yayi murmushi. ""Mace aka haifa min kuma ina fatan irinsu goma, don ina sonsu da dukkan rayuwata."" ""Haihuwa da wahala idan kana son sai ka ka..."" Yatsarshi ya daura min akan bakina. ""Never!"" Dariya ya bani, lekowa Umma tayi ta ce min "" ungo naki, da jegon zaki tare a jikin namiji? Kai ma ka daina shiga mana wallahi ba zan iya jegon turawa ba."" Ta fada tana mika min yarinyar da take barci. ""Umma jego fa ba addini ba ne, ki yi hakuri ku kyale ni a jikin Matata da Yarana, idan ma gida zaku kai su, wallahi xan bi ku. Amma batun kada ta manne min bai taso ba, Uwata ta haifa."" "" Wallahi ban isa ba, sai dai na kira Yaya Salamatu na gaya mata."" Kallonshi nayi, a hankali na koma daki na samu tana mita, kwanciya nayi, can kuwa sai gashi da abincin, ya kawo duk yadda take mita sai gashi ta barmu mun ci tare har ya fitar da kayan na kwanta aka saka room heater, barci yayi gaba damu. Wurin karfe daya sai ga Alhaji ELYakub Kumo haka aka ƙara gyara yarinyar aka fitar da ita, na shirya cikin abaya, shigowa dakin yayi ya tsaya a bakin kofar tare da jingina da kofar, yana min wani irin kallo daga kasa har sama. Murmushi nayi mishi. Matsowa yayi ya rungume ni, "" thank you!"" Murmushi nayi na ce mishi. ""Da aka yi me?"" ""Da kome kin yi min kome, kin bani kyauta daga gare ki, kin min kyautar da ba kowacce zan samu daga gare ta ba, na gode sosai na gode sosai na gode. Please kada ki musu murmushi me tsadar nan, yake zaki musu kin san yadda nake jin zuciyata tana wani irin pounder kamar zata buga."" Murmushi nayi haka ya riko hannuna muka fita har wajen. Muna isa parlourn na zauna a daya daga cikin kujerun, na gaishe su. ""Sannu Lubabatu!"" Murmushi nayi ina satar kallonshi. Shima kallona yake yana magana da fulatanci, ban tab'a ganin kyautar gwal a zahiri ba sai akan Mammy, box din ya mikawa Uban ya bani, sai kudi dollars. ""Gashi nan ki saya mata pampers wannan na barka na ne."" Sai da suka dauki minti arba'in sannan suka mana sallama, komawa ciki muka yi na kwanta na huta, dauke yarshi yayi wurin karfe ya kawota lokacin ciwon ciki da ake bayan haihuwa ya dame ni, sai fama nake kamar zan mutu. Ganin haka yasa shi shirya ni muka wuce asibiti,muna zauna aka kwantar"
"da ni, allura suka min da drip aka min. Wurin karfe goma da rabi muka dawo gida."
"Washi gari da safe sai ga Jasminah da Yaranta, tunda suka zo suka mannewa Babyn da suke kiranta"
"Boɗɗo, kowa sonta yake ni kuma Jasminah muna dakin, zuwansu ya sa shi tafiya Office a can ma ya kira ni ya kai sau goma, har ya dawo gida kirana yake, lokacin da ya dawo na kai mishi, ina shiga dakin na same shi yana cire takalmi, karasawa nayi na ajiye mishi abinci, sannan na shiga taya shi ya cire kayan, tausayi ya bani kamar wani maraya. ""Sorry!"" ""Yau duk nayi kewarku!"" Rungume shi nayi tare da shafa"
"kanshi, ""Sorry baby mun yi kewarka."""
"Ban tsaya biye mishi ba, na hada mishi ruwan wanka, sannan na fito na saka shi dole ya shiga wanka, ai"
"kuwa yana shiga na gyara kayan sannan na ciro mishi kayansa na saka turare na ajiye mishi. Ina me barin dakin, lokacin da na koma yana cin abinci yana ganina ya mika min hannu yayi na isa wurinsa, zama nayi ina kallonshi. ""Ina sonka!"" Murmushi yayi tare da sumbatar goshina, ya cigaba da cin abinci. Yana gamawa ya rike hannuna a cikin nashi, mun jima a haka ya ce min. ""Kin san Allah!"" Kallonshi nayi, ""da kin haihu da Hafiz ko!"" Kallonshi nake a hankali ya ce min. ""Da har abada ba zan daina kukan cutar da yayi min ba, Alhamdulillahi Ubangiji ya min kyautar da ba zan iya saya ba, ya bani d'a guda daga gare ki, iya wannan nayi mishi nisa, sannan ni ne Uban Uban Yaranki ni daya da Yarana zamu more ki, ba tare da mun raba da wasu ba, babu wanda ya riga Yarana iya su kaɗai zasu kalle ki su ce Mamarsu ce su daya ba tare da wasu yaran ba, iya wannan ma babban sa'a ce da nayi, kai Alhamdulillahi Alhamdulillahi Ubangiji ya gama min duk wani arziki a duniya, Aisha Bilal Haris Kumo, Aisha Turaki, ke ni fa na gama Sa'a, Ubangiji ya sallame tun daga nan na sannan Allah ya sallame ni, Ina godiya ga Allah da ya min wannan kyautar da babu wanda ya isa ya ce shi ya bani, babu wanda ya isa ya min gori sai dai ya ce min ban samu haihuwar da wuri ba, Alhamdulillahi."" Yayi hamdalla ya kai sau nawa yadda yake maganar yana kara jajjantawa kanshi irin wannan kyautar da Allah ya miishi, har na gaji na bar dakin na wuce dakina."
"Mika min waya Umma tayi na saka a kunne, daga can Mama ta ce min."" Wallahi kika sake ya kara dirka miki ciki zaki sani wato ke wacce irin sakarya ce kin biye mishi sai nanike mishi. "" Yadda Mama take faɗa kamar na je nayi wani abu da shi, sai na kame kaina ban kara biye mishi ba, karshe da ya ishe ni sai na tura mishi sakon don Allah kada ya damu da rashin kula shi, mu biye musu a wannan lokacin, a bisa al'adar bahaushe ana kwanaki uku, a ranar aka kawo mana gero buhu ɗaya, rabin buhun barkono, citta rabin buhu, kanunfari rabin buhu kome sai da suka yi shi na alfarma, sai zabbi guda talatin, lokacin da Umma ta gayawa Mama, addu'a tayi kawai tasan yanzu kan Allah ya bani gidan auren da rufin asiri. Da yamma sai ga kan saniya a gyarenta aka saka a firji, iya haka da ya faru ya kara min wani irin yanayi na"
musamman.
"Washegari Aunty Zakiyah tazo, ita da su Aunty Innah, Wai Aunty Hindatu sai ana gobe zasu tawo, ita da"
"Sunyi Simah. Cikin kankanin lokaci gidan ya fara ciki, Aunty Raliyah ma tana hanya, tare da Yadiko duk sai naji kaina ya kara girma. Yayuna sun min adalci sun turo matansu, shima sai godiya yake ta mana, ana jibi suna ya kira ni na hada mishi kayanshi, ya tattara ya koma gidansa na Agege, sannan muka samu damar sakewa su na bar musu dakina da sauran dakunan na koma dakinsa na kwanta, a ranar da Aunty"
Hindatu suka iso har da su Yadiko aiki aaka yi ta yi kamar zasu tashi saboda aiki kawai.
"A ranar wuni nayi a wurin gyaran kai da lalle shi yazo ya kai ni, sai da muka biya ta gidansa na agege"
"sannan muka wuce ana gama min muka dawo gidan bai dawo da ni ba sai dare anan muka yi wanka muka ci abinci yayiwa yarshi wanka ya gasata, ina sanye da rigar wanka kallonshi nake nace mishi. ""Anya zaka iya aurar da Yarka kuwa?"" ""Zan iya mana, a duniya babu wata Y'a mai darajar Nana Fatimah amma Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya aurar da ita, don haka zan iya kawai mijin zai ga dan iskan"
Uba ne domin ba zan iya kwana biyu ban ganta ba ne.......
"[1/7, 8:05 PM] Maman Walid: 37"
"Ban san me zance akan son da yake yiwa yarshi ba, amma tabbas kaunar ta kai wani mataki da baya iya"
"boye shi, haka ya gama shiryata yayi sallah sannan ya tattaro ni zuwa gidan, harara yadiko ta watsa min ni dai na wuce kamar wata munafuka zuwa wurin Yayuna, a wannan daren anyi hira sosai, washi gari a can family house ɗinsu aka yi raddin sunan domin ya fita da wuri ya kira ni ya ce min zasu tafi radda sunan Yarinyar, yadda ya sha wanka zaka rantse daurin aure zai je. Wurin karfe tara sai ga manyan raguna a gyare aka kawo min guda biyu, mu babu abinda muka yi a gidan domin an bada aikin abincin sunan ne, namar ne aka dauko wani mahauci ya gyara aka dauki daya aka saka min a firji daya kuma aka shiga aikinsa. Wurin sha daya da rabi mai kwalliya da Jasminah suka iso, ta zo ta min make-up bayan ta gama bata tafi ba domin aikin wannan ranar ya biya bakiɗaya, sai da na shirya cikin wata lace me laushi, na fito sai gashi tare da su Aunty Mom da Granny, wayyo Allah tun anan ta fara kiran yarinyar Annah, wani irin kauna take yiwa yarinyar mara iyaka, ni dai ban san me zancewa Ubangiji ba, hoto muka yi sosai, karfe biyu aka sake min kwalliya muka wuce family house ɗinsu, haka ya ce min na shirya mu tafi, sai da na je muka fahimci ashe anan ake bikin sunan domin an cika wai baki har daga Ethiopia, ban da na Gombe. Hajiya Zeenatu ta gaya min magana da sai da na kusan kuka amma nayi yake, domin cewa tayi. ""Duk wannan hidimar akan y'a mace, ni na zata da ake boye cikin saboda d'a namiji za a ahaife ashe"
"duk mu ne."" Ban ce mata kome ba, domin idan nayi magaja nawa sai yayi zafi."
"Bayan tafiyarta sai ga ta tare da wasu mata kamar yan boko irin Lagos Alaja din nan, suka zo yarbanci"
"ta juya musu suka yi ta yin wasu abubuwan da ya sa na ce mata. ""Hajiya hala baki da tarihin jahar da na fito ko? Ni yar jahar Bauchi ce, ina kuma alfahari da cewa ni namar kai ce ga kitse ga tauri, idan kika sake na saka ki a corner."" Wani devilishly smile na mata, ina kallon cikin kwayar idanunta. ""Kada ki saka na kai ki inda ba zaki ji dadi ba."" Ina fadar haka ta bala'in shiga hankalinta, fita suka yi ita da kawayenta. Haka Yarta Mimi suka shigo kamar wani abin arziki, ta dauki Yarinyar sai da ta gama kallon yarinyar ta ce min."
"""Anya wannan jinin KUMO ce kuwa ban ga tayi kalar fatar Kumo Family ba."""
"""Ba mamaki an saba number ta yadda kika kasance daban a cikin kumo family, domin duk kumo"
"muna da manyan idanun naki kuwa kamar ta kwad'i."" Inji Jasminah tana kallon Mimi, sai tayi shiru, tana kallon yarta. ""Yes kalle ni da kyau duk wani jinin kumo yana da dogon hanci dogon gashi, kai everything yaran kumo suna da shi hatta Boɗɗo da aka haifa jiya kalli gashi har yatsun hannunta sun nuna zata yi gashi, amma ke kuma ko goruba ys sallama miki rashin gashi, shima hasken fata baki ga lura cewa mai kike ta labtawa akanki ba."" Duk Jarabar son ayi fada Jasminah ta sani, sai da ta kunyata yarinyar nan ta fita kuka, atow ka fada ne tsakani me baki mara kunya, haka ta fita daga parlourn, ni dai na zuba idanun ai kuwa can sai ga Hajiya Zeenatu ta shigo tana huci, kallonta Jasminah tayi irin kallon nan ne mara daɗi, zata yi magana na rike hannunta. Girgiza mata kai nayi ina murmushi, haka uwar ta gama zage-zage ta sannan ta fita a parlourn, abin bai yi dad'i ba domin Hajiya Khaulatu ta je ta ci mata mutunci wanda ya janyo katon tashin hankali a cikin gidan kamar zasu yi doke doke, dakyar aka gama lafiya Kannen"
"Babanshi sun zo sun bani hakuri ni a lissafina kamar zasu kara biyo min ta baya ne, har muka dawo gida"
"maganar ake nanatawa sai da Yadiko ta musu fada suka yi shiru, ashe wannan zuwan yadiko zama zata yi"
"Umma zata koma Bauchi wai mijinta yana ta sintiri, duk sai naji ba dad'i. Haka na tura mishi sako, aikuwa washi gari sai gashi da akwati ya shigo da shi suka gaisa, da yake kayan da aka mana na sunar basu kawo ba, kome ayin parkage dinsa ne, haka ya kawo mata ya saka dubu dari biyu a kai, tare da da godiya, dukkaninsu da suka zo sunan sai da aka musu shatara na arziki, suna da kwana biyu suka bar Lagos, a"
ranar kuma aka kawo kayan Yadiko tayi ta saka albarka.
"Yanzu nasan ina wanka wato Yadiko sosai take wanke ni, Umma ai ni nake yi da kaina, Yadiko kuwa"
"haka ta saka shi nimo mata ganyen lim, tayi ta zane ni da shi da sunan tana min wanka, ai sai da naji kamar zan yi hauka domin wankan ya saka ni jin wani irin tsoro da damuwa, sati uku nayi wani irin kwari sai yanzu na fahimci wankar tana gyara min lafiyata, domin kuwa idan nayi barci sosai, yarinyar ma idan ta sha ruwan zafi tuni take barci sai dai kukan dare da rikici. Shima Yadiko take nuna min yadda zan yi, shima ganin Yadiko bata bada fuska sai ya kame kanshi ya daina nimana, abinci idan muka gama da ita xan jera zan koma daki yana dawowa zan zo na gaishe shi. Bayan nan zan koma daki shima haka ta ce"
"min, sauran kuma yayi da kanshi."
"Sakon kewar da yayi, wani abun da yadiko take kara burge ni da shi da ta fito kiri ta gaya mishi gaskiya"
"tare da cewa idan aka gama wankar da kanshi zai fahimci dalilin haka. Sai bai kara nuna takura da yake ciki ba, haka muka cika wata guda, ranar Jasminah suka zo mana wuni ita da wata yarinya baka"
"kyakyawa da ita anan take gaya min budurwa Taj ce, yarinyar ita ta yi mana abinci, da dare suka tafi gida, ya rage saura kwanaki goma yadiko ta sauke mana wanka. Haka yayi ta sayayya yana kawowa gidan,"
"idan na tambaye shi dalilin haka sai ya ce ina ruwana ranar da na mishi magana ban gane me yake nufi ba, budar bakinsa ya ce min.. ""aure zanyi ko akwai matsala ne?"" Daga ranar ban kara mishi magana ba, ana saura kwanaki uku ta ce min. ""Kina takure ko?"" A kunyace na ce mata. ""A'a Yadiko!"" Murmushi tayi ta ce min. ""Ki kula da kanki da Yarki, idan kin gama wanka jini ya dawo, ki kula da kwanakin kyankyasan kwanki, domin zaki kuma ciki. Ki kula da kanki da Yarki don kin ga tana da lafiya da kuzari don Allah kada ki dauko wani cikin saboda wannan rawan kan da kuke da shi zaku iya samun wani cikin nan kusa wallahi."" Ni dai ban kara magana ba, kuma ban kara motsi ko wani abu ba, sai dai na kara fahimtar cewa shi fa kome na rayuwa yana tsarin Ubangiji, ranar da muka cika kwanaki arba'in, muka ajiye wanka, sannan shi da kansa ya ce mata. ""Yadiko ki yi hakuri wata sati sai ki tayi don Allah!"" Bata so ba, amma"
haka ta hakura.
"Tafiya ce ta kama shi har na tsawon kwanaki biyar, a wannan lokacin yadiko ta shiga hada min wani"
"hadin gyaran jiki da kanta ta shiga kasuwa tare da rakiyar Aunty Munah da tazo min, kamar nayi kuka haka tayi ta haɗa min magani har da tsumi tare da maganin sanyi ta hada min na fara sha, sai nayi ta fitsari na tsawon kwanaki uku, kafin ta bani gumba da zuma na cigaba sha, ranar da ya dawo tare da ita muka sha aiki da Aunty Munah, yana dawowa ya shigo suka gaisa, a daren ashe ta kira Ya Ado ya zo ya"
"dauke su, sai gashi nan kuwa ya zo suka tafi sai da nayi kuka don takaici, shima bai san sun tafi ba, fitowa"
"yayi ya ga ina kuka. ""Lafiya?"" ""Sun tafi mana!"" Shiru yayi kafin ya ce min. ""Sorry zan bisu kin ji!"" Gyada"
"kai nayi