Author : Mai Dambu Category : Complete Novels
ta mika min muka fita, Tarik ya zo ya dauke ni. Lokacin da muka isa Asibitin Uncle Auta da Ubaid muka samu sai Kakanshi.."" Jiya ina kika tafi?"" ""Naga kamar tana bukatar hutu shine na tafi da"
"ita ku yi hakuri."""
""" Ba kome Hajiya, dama mun damu ne."" Inji Kakanshi. Wucewa nayi dakin da jakar zam-zam, na shiga"
"na same shi a yadda na barshi. Ruwan addu'ar nayi Bismillah na shiga shafa mishi, shigowa Uncle Auta yayi ya ga ina shafa mishi ya zo ya taya ni. Har muka gama ya ce min. ""Addu'a ko?"" Gyada kai nayi, murmushi yayi ya ce min. ""Mun yi da Baffa zaki koma gida zamu tafi da shi Russia!"" ""Zan bi ku!"" Girgiza"
"kai yayi na ce mishi. ""Ni nafi dacewa na zauna a gefenshi."" Na fada ina mai fashewa da kuka, fita yayi ya"
"bar ni a dakin, dA sauri na juya gare shi, na riko hannunshi na kai kan cikina. "" Please wake up ka ji feel"
"your baby a marana, please ka tashi we need you."" Na fada ina kuka. Na rasa yadda zan yi haka na fito na same kakanshi na ce mishi."" Don Allah ka bar ni nan tafi da shi, don Allah ku bar ni, na biku. Mama ki ce su bar ni kin ji Mama ki roka min shi don Allah."" Kallon su Mama tayi a nutse, ta ce musu. ""Ku barta ta bi Mijinta!"" A yadda suka tsara babu ni, amma da yake Allah ya mata baiwar iya sarrafa kanta sai gashi sun amince. ""Shi kenan ta shirya!"" Haka Tarik da Mama suka kawo ni gida na shirya tsaf, sannan na hada kayana na kashe kome na gidan abincin da yake frij na kai cikin gidan Uncle Auta, sannan na rufe gidan, muka wuce asibitin. A daren muka wuce Russia, lokacin da muka isa can Russia har da Uncle Auta. Yadda aka Karbe mu yafi kome dad'i, nima damuwa da rashin hutu yasa ina sauka a jirgin na yanki jiki na suma."
Haka aka wuce da mu asibitin.
"Sai da nayi kwana biyu ina barci na farka, koda na farka Aunty Herlim na gani a gefena. ""Lunah sannu kin"
"farka?"" Gyada kai nayi ina murmushin karfin hali. ""Ya Jikin shi?"" Na tambaye ta ina kallon dakin, murmushi tayi ta ce min. ""Yana dakinsa."" Gyada kai nayi na rufe idanuna. ""Kwanaki biyu kina barci!"" Kallonta nayi na ce mata. ""Kwana biyu?"" Gyad'a kai tayi tana murmushi. ""Amma babu inda yake ciwo na kira likita?"" Gyada mata kai nayi, danna abu tayi sai ga nurse sun zo, tare da likita a bayansu, bayan an gama duba ni suka min tambayoyi, na basu amsa. ""Ki huta zaa yi miki scan nan da dare!"" Bayan sun fita na shiga wanka, na fito nayi sallah. Sannan na wuce dakinsa. Lokacin da na shiga naga sun daura mishi karfuna, zama nayi na dafe kaina. Ina kallon yadda ya koma lokaci guda, wani irin kuka nake ina kiran sunan Allah, tunawa nayi da kayan da nazo da shi, na kalli Aunty na ce mata. ""Ina goran ruwan da yake jakata."" ""Yana gida zan saka a kawo miki!"" ""Ina so yanzu nan!"" Haka ta bar Asibitin, bayan minti ashirin sai gata, dauka nayi na shafa miishi a jikinsa da ko ina. Da dare na je aka yi min scan sannan anan aka gano cikin sati biyar da kwanaki shida, hawaye ne ya zubo min, na koma dakin ina kallonshi yana barci. A bisa ka'ida ba za a zauna da shi ba, amma saboda yadda suka ga koma suka bar ni, sallah biyar sai na saka shi a cikin addu'a. Idan dare yayi kuwa sai gari ya fara haske nake komawa gefensa na kwanta ina"
kuka har nayi barci.
"Ban sare ba, ban tab'a give up ba. Addu'a na saka Allah a gaba. Ruwan zam-zam din na karewa na"
"gayawa Auntynsa suka nimo min har da ganye magariya, anan ne na ga ikon Allah, na kuma. Yarda akwai sihiri a tare da shi, tunda ya kwanta baya motsi numfashi ma da taimakon inji yake yi, amma ina fara ayatul shifa, ya fara motsi. Tunda na fara sai nima na fara jin wani irin abu yana yawo a kaina, idan na kwanta barci zan ga kamar aka bina da gudu. Sau biyu na ga haka, sai na kira Mama ina kuka na gaya mata. ""Bar kuka haka, ki tuna akwai wanda yake bukatar kulawarki bayan Turaki, ki tuna da abin cikin ki ko ba don kanki ba, in sha Allah zan taya ki daga nan."" ""In sha Allah Mama!"" Na fada ina kuka, tayi min"
nasiha sosai sannan ta kara min addu'a sosai.
"Haka na kara kai mi, amma kuma idan na tuna akwai Allah sai na ji bana tsoro. Haka na cigaba da na"
"shi, Turaki bai da Uwa bai da Uba, nice abu biyu zuwa uku. Jasminah tana Kano, bata san me yake"
"faruwa ba. Nan kuwa dangin Uwarsa ba musulmai ba ne. Haka na tsaya ba dare ba rana, ina addu'a."
"Aunty Hindatu ta kira ni ta min jajje take gaya min anyi saukar Alqur'ani da yanka, Abba yasa an tara almajirai, sai na fashe da kuka. Sannan an raba namar sadaka gida gida, abinci kuwa har kofar fada aka kai aka rabawa almajirai. Sannan anan ware tsangaya uku akai abinci da ruwan sanyi aka raba. Nayi kuka kamar raina zai fita, sati daya aka dauka aka addu'a, sati na zagayowa ya fara farkawa, wani bin idan ta bude idanunsa har da tashi da karfi kamar zai tashi sama, sai anyi mishi allurai yake komawa barci, na kira Mama na gaya mata, ta ce min. ""In sha Allah za a ci nasara!"" Likitoci kuwa cewa suke miracles ne"
yasa ya dawo rayuwa domin sun fara tunanin a cire mishi abin numfashin ya tafi ya huta.
"Alhamdulillahi ko kafin satin ya farka ya zauna da daram, ranar da na ga haka kuka na saka tare da"
"rungume shi. Shafa bayana yake yana murmushin farin ciki. Ban kyale shi ya wartsake ba na daura hannunsa akan cikina. Na gyada mishi kai. ""Alhamdulillahi!"" Ya furta a hankali, hawaye na zuba a idanunsa yau na ga yana zubar da hawaye ya ce. ""Zan zama Baba daga gare ki? Thank you for choosing me to be a Daada."" Rungume shi nayi ina cewa. ""Thank you for made me a mother!"" Hade goshinmu yayi yana faɗin. ""Thank you Lunah, thank you for saving me, thank you for protecting me. Na ganki a mafarkina, kin kare ni kin hana kowa ya cutar da ni, thank you for be in my side. Lunah!"" Rufe mishi baki nayi ina faɗin. ""Ya isa ka huta kayi sallah."" ""Jikina yana ciwo!"" ""Bari idan muka koma gida ayi maka"
"hayakin habbatu saudat."" Murmushi yayi yana shafa cikina. Haka na taimaka mishi yayi wanka da alwala, ya zo ta gabatar da sallah. Bayan ya idar ya ci abinci, sannan na bashi addu'ar da nake shafa mishi. Ya sha na kara shafa miishi, yans murmushi ya kwanta. Kwanaki hudu yayi aka sallame shi, muna zuwa gida na hada mishi ruwan addu'a yayi wanka sosai. Bayan ya fito na mishi hayaki da Habbatu saudat, ba sai gashi yana gurnani ba. Can ya tashi ya fara wani irin abu. Yana niman kamani amma yayi baya, na cigaba da zuba garin habbatu saudat, duk da na razana amma kuma aka na fahimci kamar abin da yake tare da shi yafi ni razana, tari yayi ta yi har ya zube a kasa. ""Ki godewa Allah kina da shi a gefenki, Allah yana gefenki, ba wurinsa aka turo mu ba wurinki ne, wurinki aka turo mu amma muka kasa gane hanyar inda kike"
"shine muka shiga jikinshi, shima abinda yasa muka shiga bai yi azkar din yammaci ba ne, ke kuma kina cikin addu'a koda ba kya ibada. Ni dai ki bar ni na tafi domin an daure ni ne da addu'ar da Iyayenki suke miki!"" Kallon wulakanci nayi mishi na ce mishi. ""Sai dai ku tabbata a haka kamar yadda ka bawa mijina wahala haka zaka kare ba zan kyale ka ba!"" Ihu da kururuwa yayi ta yi har Auntynshi tazo, na cigaba da addu'a zata yi magana na ce ta je kawai. Haka na cigaba da addu'a da ruki'a, sai da na wahalar da shi har yana cewa zai mutu na kyale shi, ya fita ta atishawa. Yana samun damar barci na mishi alwala na gyara mishi kwanciya. Na kira Mama na gaya mata, ta ce min."" Akwai abubuwan da aka hada muku dukkanku"
"har da cikin jikinki ya za ayi?"" "" Kada ki damu zan turo Tarik."""
(Kuyi hakuri na gaya muku gaskiya bani da lafiya wallahi gudun kada na tafi break ku ce ban kyauta muku
"ba yasa zan muku koda daya ne, ku yi hakuri kun san yadda nake typing amma wannan karon bana jin dadi sosai?! Arewa gobe xan kara muku update telegram maybe sai Sunday in sha Allah)"
"[12/29/2025, 7:53 PM] Maman Walid: 31"
"Na fada mata tare da rike hannunsa, kwantar min da hankali Mama take tana gaya min magana me dad'i,"
"hawaye ne ya zubo min, na ce mata ""in sha Allah ina tare da shi, ba zan tab'a ja da baya ba."" ""Allah ya miki albarka, ya sauke ki lafiya. Ki kula da addu'a da azkar!"" Daga haka muka yi sallama, na tsaya sosai da addu'a bs dare ba rana, a bangarenshi kuwa sauki ake samu, sati daya da muka yi magana da Mama sai ga Tarik, kusan nafi kowa murna, haka muka yi ta amfani da magani na fara mishi amfani da su, Alhamdulillahi sai gashi lafiya ta samu har an koma duty, bakiɗaya ya koma irin iyaye mazan nan masu matukar damuwa da Yaransu. Tun da yaji na shiga wata na uku ya tattara kaunar duniya ya daurawa cikin, da yake gani kamar bai da wani sama da shi. Tun daga nan na fahimci irinshi, da cikin ya shiga wata hudu nan na kara yarda da cewa zuwa yanzu Allah ya min arziki da ya bani shi a matsayin mijina, domin fita goma shiga goma, zai daura kanshi akan cikin yayi ta bashi labari, surutu kala kala. Ni kuwa motsi"
kaɗan zai tambaye ni me nake so.
"Har ga Allah na gaji da zaman garin, don haka cikin da ya fara tasawa na shiga wani irin yanayi na son"
"gida musamman abincin gida, tuwo, fate, dambu da kwadon zogale, ranar da na tashi da son taliyar"
"murji ban samu ba da mai da yaji, karshe indomie na dafa na jikata tayi manya manya naci da mai da yaji, da dare kuwa ina kwance naji ina sha'awar awara da mai da yaji, kuka ne ya zo min ganin yada nake"
"shiga damuwa Kakarshi da Auntysa suka saka shi gaba ya shirya mana dawowa gida, shi a lissafinshi kada mu dawo gida a kara cutar da abin cikin tunda sun ga ba nasara akanmu, murmushi nayi kawai nace ni"
dai gida.
Haka muka gayawa Mama zamu dawo na gaya mata ranar da zamu dawo. A bakinsa nake jin ta
"turo aunty Hindatu da Aunty Innah da Zakiyah aka gyara min gidan suna gari ma su zasu karbe mu, bai yarda ya gayawa kowa zamu dawo ba, sai dai ganinmu aka yi ranar wata Alhamis da safe muka iso. Uncle Auta da Ubaid sai da suka mishi tsiya, wani ikon Allah ko Yayuna Mama bata gaya musu ina da ciki ba, tace dan duma ne ba aboye shi. Nayi kiba daga sama da kasa, suka yi ta min tsiya ko ciki ne nace su taya mu da addu'a. Duk wani abinda muke bikatA an kawo a gidan babu abinda na rasa sai dare suka bar gidan,karfe tara ya shigo shi ɗaya. Ina daki na ji shigowarshi. Fitowa nayi na same shi yana zaune yana shan ruwan zam-zam. Murmushi nayi na bi kitchen na dauko dabino da ya'yan zaitun ka kwalba, Mama tayi recommended din akan ina ci, bude min jikinshi yayi na shiga cikin na zauna tare da kwantar da kaina a kirjinsa. ""Baby ya My love yake?"" ""Idan na haifi Baby sai a koma Madam ko?"" ""Waye ya gaya miki haka?"" ""Kai mana!"" ""Kada ki min sharri!"" Ni dai ban ce kome ba, na cigaba da cin zaitun din har na gama, muka shiga hira. Da yake bamu ta kowa ta kanmu muke ihun Falilah matar Ubaid muka ji tana faɗin matukar tana numfashi ni da Mijina da muka saka Mijinta aure zamu gani. ""Ta gani akanta!"" Ta kara da cewa. ""Idan na haifu yar halak Lubnah ke da haihuwa sai dai wasu su gani!"" Murmushi yayi bayan na kalle shi. ""Allah ya bamu sai dai taji haihuwa!"" Haka muka tattara ta muka zuba a gefe, sannan ya min kashedi na fita harkan Matar Uncle Auta itama munafika ce, kawai sai naji na samu nutsuwa hankalina kwance ba ruwana da kowa. Babu wanda ya san ina da ciki ma, satinmu uku da dawowa aka yi bikin Badriyyah ta auri wani senator a abuja, yadda bai je ba nima ban je ba, gidanmu baya rabuwa da karatun"
"Alqur'ani, haka yasa muke kara samun kariya daga Ubangiji."
"Lokacin da cikina ya shiga wata biyar da sati biyu na cigaba da zuwa ANC anan Lagos, tare muke zuwa"
"ya rike min jakata. Duk ya lalace a jikina, haka nake zuba kafasiti son raina. Wani ikon Allah cikin bai fito ba duk yadda muke boye shi bai fito din ba, haka matar Uncle Auta ta gama Jarabar shigen min ta kyale ni. Koda na shiga wata bakwai a lokacin muka fara sayan kayan haihuwa muna shiryawa, a lokacin yayiwa Mama magana a zo a zauna da ni, yana da tafiyar da zai yi. Abba ya ce babu wanda ya dace da zama da ni kamar Ummanmu kanwar Mama itama ba laifi akwai ibada da addini. Wannan yasa ya ce ta"
"shirya kwananta biyu a Bauchi ta tawo lagos, muka cigaba da turawa da ita."
**
"Ranar wata laraba ina kwance lokacin cikina ya shiga wata takwas cib, sai ga Maman Badriyyah da Yan"
"uwanta, Ummana tana ɓare min ayaba ina zaune don cikin ya fara fitowa. Suka shigo kallonsu nayi fuskata da mamaki. Suma ganin cikin da ya ɗan fito ne ya basu mamaki, Maman Badriyyah ta ce min. ""Ke yaushe kika yi ciki?"" Kallonta nayi na ce mata. ""Wannan kan ai hurumin Allah ne ba nawa ba naki ba!"" Shiru tayi kafin ta ce. ""Shine kika haka shi aure?"" Dariya nayi na ce mata. ""Shi fa mijin mace hudu ne, akan me xan hana shi aure? Ai na taso gidanmu mata biyu ne akan me zan ji a raina ni daya ce tal, ai na jima da yarda da haka don ko gidan da na fito mu biyu ne."" Na fada ina cin ayaba. ""Amma wannan cikin dashensa aka yi?"" ""Da sauki tunda na Bilal Turaki ne ba na wani ba!"" Daga haka suka bar gidan kowacce"
"magana tana da amsarta, haka suka bar gidan cike da barin kunya."
"Ashe gurmi ne sosai a gabanmu domin danginsa sun ce basu yarda ba, a ina na samo ciki da zan makala"
"mishi. Ai na bar kasar babu cikin sai yanzu da zan dawo da ciki, haka akayi ta gurmi matar Uncle Auta ta zo ina barci Ummana ta hanata shiga, kai ba sai ga yan family ba kowa yana zuwa ya ga da gaske dai ciki ne, kai karewa har Daddah Kakarshi tazo min wuni itama ta ga cikin she was so shocked, matar Ubaid hankalinta ya kasa kwanciya sai ga ta har gida, itama ina jin muryanta na ce a gaya mata nayi barci. Haka kuwa ta fita rai bai so ba. Idan nace ban yi kewar My Man nayi karya, Umma tana tsaye a kaina da addu'a da kome, da yake har Islamiyya take da shi, wani ikon Allah sai gashi tun Babyn yana cikin take bani addu'a da duk abinda xan ci ko xan fada, sauraron karatun Malamai na addini, ta hanani Gulma ko maganar mutanen da muke da matsala da su, ta hana ni saka kome a raina, idan nishadi nake ji ta kan ce min. Ki duba Islamic cartoon. Haka nake budewa nayi ta kallo har na gaji, ranar da na gaya mata zai zo ta ce min ita xata koma gidan Ya Ado na saka mata kuka na ce mata. ""Wurina kika zo ba wurinsu ba, don Allah kada ki tafi!"" Ganin yadda nake rigima yasa ta hakura, amma kusan tare muka yi mishi abinci, tunda muka gama na dawo parlour na zauna ta kawo ruwan zafi ta ajiye min a cikin bawo karami na saka kafana. Muna hira har zuwa wani lokaci ta dauke ta koma daki ta kara hado min wasu sinadarin kamshi ta kawo tare da cewa muje ta haɗa min ruwan nayi wanka, bayan wanda nayi haka kuwa muka je ya haɗa min ruwan nayi wanka sai kamshi mai dadi ruwan yake. Sannan ta turara min kaina, bayan ya gama ta cire min wani riga da wando, ta ce min. ""Saka zaki sake shima zai ji dadin ganinki cikin kayan nan, zai"
"samu nutsuwa ko bai yi kome ba, wani lokaci ganin mace fess yana hana namiji hango muninta, ta bani"
"karamin mayFi na yane kaina. Sannan na fito a hankali zuwa parlour ta kara gyara gidan ta saka turare,"
"ita kuma ta shiga dakin da ta sauka. Karfe bakwai ya shigo bayan mun Isha. Kallonshi nayi a hankali na taso ya sake jakar, ya tawo da sauri ya rungume ni."
""" I miss You! "" Na fada ina shakar kamshin turarensa. "" Baby haka kuka kara girma? Ina Ummana?"""
"""Sannu kai dai ka ji dadinka da fashi da makami, itama Umman ba zaka bar min ita ba!"" "" Tana dakinta ko?"" Na gyada mishi kai, murmushi yayi ya riko hannuna muka wuce dakin tana kan abin sallah da Radio tana sauraren labarin karfe bakwai da rabi na BBC Hausa, rage karar tayi muka shiga ya zauna daga bakin kofar yace. ""Umma na same ku lafiya?"" Ba sai suka juya fulatanci ba, suka shiga zagina (lolz haka Baban Walid yayi min lokacin Babanmu yana raye sai su