Author : Mai Dambu Category : Complete Novels
da mamaki, yaushe wadanda bayin Allah suka koma baka?! ""Bilal me zasu kawo maka!"" ""Mama yanzu naci abinci, sai dai ko Lunah."" Shi bai jin kunyar kiran sunan nan ne agaban mutane. ""Uncle lunar kuma?"" Shiru yayi bai ce mata kome ba, can ta ce mishi. ""Uncle lunar ana samun shi ne a"
"watan biyu duk bayan shekara tara."""
"""Yes My Lady haka nake nufi but ita I found her after many years na same ta?"" ""Uncle ai lunar a sama"
"ita kuwa Uncle a kasa take."" ""It's miracle"" ya fada yana barin wurin sai lokacin Mama ta ce min. ""Kika ce kina jin yunwa ko?"" Me Jasminah zata yi ban da dariya, kwalla ne ya cika min idanu na ce mata. ""Mama ni me nayi kike min rikon Uwar wata shi kuma har da tambayar shi me xai ci ni kuma na fadi na mutu ko."" ""Yaushe na ce haka?"" Ta fada tana murmushi. Hawaye ne ya zubo min na tashi na bar su a wurin don na ji haushi, sai da na tsaya na amshi abincin sannan na koma dakinmu, a hanya muka hadu da shi zai koma kasa, tun daga nesa nake watsa mishi harara domin ya janyo na rasa kulawa daga Mama."
"Murmushi yayi ya wuce ni. ""Kome sai ka raba ni da shi ne? Itama da take tausayina yanzu ta daina kula"
"ni haka xan rayu duk mazan da na zauna a kasan su sai sun raba ni da dangina suke jin dad'i."""
"Murmushi yayi ya cigaba da tafiya, ""ka kyale min Uwata don Allah!"" Murmushi yayi bai kara min"
"magana ba yayi tafiyarsa, karshe da na shiga dakin abincin ajiye a nayi ban ci ba, na kwanta da takaicin kowa. Lokacin da ya isa ya samu tana hira da Jasminah. "" Mama me yasa baki saka an kawo mata abincin ba? Idan ta kwana da yunwa fa?"" Ya fada cikin yanayin rashin jin dadi. Baya kaunar abinda zai"
"saka tayi kuka har kuka har cikin ranshi yake jin haka. ""Lubnah ba yarinyar ba ce ka kyaleta"
""" ""A'a Mama Lunah yarinya ce a gaban kowa ma yarinya ce. Idan bata ci abinci ba ciwo zai kamata."
"Mama anyi min laifi abar matar turaki da yunwa?"" Tashi yayi ya koma kofar dakinsu ya buga kofar yayi har lokacin ba a bude ba. Tura kofar yayi ya ganta kwance. "" Ke tashi ki abinci bana son bakin ciki, ki bawa jikinki azaba kafin aurena."" D'ago kai nayi ina kallonshi murguda mishi baki nayi na juya mishi baya. Ja iska ya fesar. ""Zaki gaya min ranar da na kama ki, yadda kika murguda min baki isa kin gaya min wanda kike yiwa rashin kunya."" Share shi nayi na cigaba da kwanciyata. ""Tashi ki ci abinci wallahi kika sake na shigo da kaina, abinda zai faru ba zai mana dad'i ba."" Jin yadda ya rantse yasa na tashi da sauri na fara niman abinci na fara bude madara na sha sannan na fara cin ganyen da wani tsokar bana, ina ci ina kallon inda yake, gani nake kamar zai shigo da gudu ya turmushe ni cikin rawan murya na ce mishi. ""Ka tafi kada a ganka a dauka wani abu ne?"" Tab'e baki ya ce min. ""Allah yasa ni ne mutum na farko da na fara wanke miki period dinki, babu abinda wani dan banza zai nuna min tunda ni a can baya mai kwaila nace ina so ba budurwa ba, balle yanzu da kika zaka uwar mata."" Ya fada yana kallona, ni dai sake baki nayi wannan mutumin dama haka yake bai da kunya, sai da abinci ya kusan kware ni. "" Ci a hankali, naga kina Min kallon zargi ne me zanyi da macen da babu igiyana akanta. Tsawon shekarun da nayi ina tattalin samartakana ya tashi a banza kenan, ke ni ba dan iska bane ki sani kamar yadda kike da kamun kai haka nake kome na barwa Allah idan kika shigo gidana zaki fahimci ni saurayi ne, gal a leda. "" Da gudu na wuce ban daki ina faɗin. "" Don kaunarka da mai ka'aba ka fita wallahi ba zan iya jin maganarka"
"ba. "" Shi bai ga wani abu da ya fada mara kyau ba, asalima gaskiya ya faɗa da ace shi dan iska ne da tuni"
"bai tara yara a layi ba, duk yadda ya ga mata masu manyan kaya bai taɓa jin ya je gare su ba, sai yanzu"
"wata kwaila da ita zata na mishi kallon tuhuma, yana hango yadda yake mishi kallon zargi. Shi kan Allah ya tuba ai da rayuwar bata mishi dadi ba ace sai yanzu zai farwa matar da zai aura. Amma itama she too shy, kamar irin yaran da suka fara zama yan mata. Sai kuma abin ya bashi dariya ya sake murmushi......."
(Da alamu shi kuma na shi salon kenan da maganar banza saurayi yake gal a leda)
"[12/15/2025, 4:48 PM] Maman Walid: 15"
"""Allah na tuba!"" Na fada lokacin da na shiga ban daki, ina ji kamar kirjina zai buɗe zuciyata tayi waje. Shi"
"dai bai da kunya. Motsin da naji a dakin yasa na ce. ""Waye?"" ""Ke bana son gulma fito uwar me kike a ban dakin?"" Goge hannuna nayi na wuce na kwanta. ""Kin ci abincin?"" Tura baki nayi ina kallon gefe. ""Kin koshi ko Yaya?"" Ban ce mata kome ba, ta gama yar fadarta sannan ta kuma shiga rarrashina da nuna min kada na ƙara wasa da da cikina, zan samu matsala idan ina wasa da cikina zai haifar min da matsala. Ni"
dai ban ce mata kome ba har barci ya dauke ni.
"Kwanakin da muka yi bana shiga harkansa koda kuwa ya samu ina wurin tashi nake na basu wuri, don"
"na fahimci matuƙar yana wuri Mama mantawa yake da tab'a haihuwar mutum irina, ni kuwa kishi da haushin baya wani kula ni, nima haka kusan Mama ta fahimci haka ta ce min na je yana kirana a kasa, tunda na zo ma zauna mutumin nan yake danna wayarshi. Kusan minti talatin bai da lokacina, haushi ya kara kama ni na mike zan tafi ya ce min. "" Can we walk? "" Juyawa nayi ina kallonshi, ya d'age min gira daya. ""Na miki kyau ne?"" Murguda mishi baki nayi, tare da juya mishi kai. ""Ina tara duk wannan yanayin."" Ya fada yana murmushi, tsoron da nake dannewa ne ya kara cika ni, kaina na kawar don bana son mu haɗa idanu yadda yake wasu abubuwan yasa ni na fara shakkar shi, anya ba wani abu yake bukata da ni ba. Kamar yasan abinda nake tunawa ya ce min. ""Kina min kallon dan iska ko?"" Da sauri na ce mishi. ""A'a!"" Sai ya ce min. ""Ok ya kike kallona?"" Gaba nayi ya ce min. ""Kila sake, kika shiga gaban wadancan mazan wallahi sai ma dauke ki cak!"" Ya fada yana kallona, kamar nayi kuka haka na tsaya muka cigaba da tafiya. ""Allah yana gani ina da zafin kishi, kuma ina kishin duk wani abu da yake nawa, amma ba zan cigaba da ganin kina tafiya kamar doya ba, daga yau, idan da hali abayar nan a bashi a cikin gidan auren babban hijab da nikab is ok, ba takura miki zan yi ba amma ni ina da kishi, kuma ina son nayi koyi da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama. Don ya ce duk mutumin da baya kishin iyalinsa ba zai ji kamshin gidan aljannah ba."" Yana kai aya na kame kaina na tsaya a gefenshi. Muka cigaba da tafiya wani shagon yan Indonesiya muka nufa yayi ta saya min manyan hijab da masu haɗe da riga, wanda babu"
"shape, kallonshi nake ina mamakin yadda yake jidar kayan."
"Wani ikon Allah, bai bar ni na dauki ko daya ba, shi ya riko kayan muka je wani shago wurin cin abinci,"
"ya saya min abinda zai saya min sannan ya kawo muka wuce. "" Fuskarki tana da tsada, ni ban da Uncle Auta ya so ai ko dinner ba zan yi ba, iya walima ce ta maza. Domin bana son shigar nan da kowa zai ta"
"kallon surarki, bayan biki kuma na ce na kaso mutane ana saka hijab."" Abin mamaki ya bani yadda yake"
"magana kamar bashi ba. ""Baki ce kome ba!"" Share shi nayi na cigaba da tafiya."" ""Idan har zamanmu ya"
"samu albarka da Yara, tow ni dai kada ki so yara dayawa domin zan iya kishi akansu."" Sai lokacin na kalle shi kafin na ce mishi. "" Ranar Hafiz ya gaya maka ai ba dan iya haihuwa ba domin ina da matsala, sai dai idan zaka kara aure."" Na fada ina cigaba da tafiya naki na kara magana. ""Ni kuwa ina ji a jikina rabona ne ya dawo dake gare ni."" Ban kula shi ba, na cigaba da tafiya. Shima ganin yadda na dauke kaina akan shi yasa shi share ni. Abin namu kamar masu aljanun, kowa yana iya share dan uwansa ba wai don baya son alaƙar ba ne a'a kawai wani yare ne da nasan iya zuciya ke bada labarin ga juna. Kallona yayi, aka yi dace nima shi nake kallo, murmushin gefen baki yayi ya ce min. ""Kina gulma ko?"" ""Me yasa baki son magana bayan kin mai da ni kanari?"" Ban ce kome ba, idan ka tuna rayuwata da Ya Hafiz yadda xan ta mishi hira da surutu amma shi baya ma ta ni, aikin gabanshi yake idan ya gaji ya ce na ishe shi da magana. Shafa bakina nayi, a hankali tuna yadda wani lokaci da jimawa ya marin bakina wai na cika surutu. ""Wani abu ne?"" Girgiza kai nayi, ""Lubnah yaushe zaki bani labarin aurenki na baya?"" Kallonshi nayi, ""kana son sanin past dina ne?"" Gyada kai yayi, shiru nayi ina kallonshi, kafin na ce mishi. ""Idan na gaya maka kai ma zaka daura naka azabarka ne a kai?"" Murmushi yayi ya ce min. ""I'm not that type!"" Cigaba nayi da tafiya, idan na gaya mishi labarina ba mamaki shima ya shirya nashi wulakanci ko kuma ya hango tumemmen abinda na aikata na shiririta ya juya min baya. Domin ni duk abinda zai dakatar da wannan auren ina tsoronshi."
"""Zan baka labari amma ba yanzu ba!"""
"""Ki barshi sai ranar da aka kawo min ke?"" Kallonshi nayi wata zuciya ta ce min. *Daga nan ya dankara"
miki saki ko?*
***
Lagos
"Hafiz ne gaban Manyan Yaran Alhaji ELYakub Kumo,"
"Mudansir, Khaulatu, Sameerah, Abbas da Zeenatu. Sai Yaransu. Yana shan ruwa ya kalle su da kyau kafin"
"ya ce musu. ""Ni Lubnah nake so bani da wata alaƙa da ta wuce ita. Idan har muka iya tafiya a boat daya,"
"za a dace idan kuma kuka ce ba zaku ban goyan baya ba, da sauki amma a farmake ni ba zai mana dad'i ba. Yaron nan dai naku ne, ni kuma Matar da zai aura ce tawa."""
Shiru suka yi suna kallonshi yadda yake kallon tsarin gidan. Dariya yayi irin wanda ya san kanshi.
"""Gayen nan yasan kanshi, baya wasa da ibada ko wani abu da ya shafi ibada, mutum ne da duk bala'inka haka zaka barshi, ba dai tsafi ko sihiri. Allah ya bashi sa'a, amma auren Lubnah shine kuskuren da zai yi, domin ba zan iya kallon tayi gaba ina tsohon mijinta ba."""
"Shiru suka yi a hankali ya zauna yana kallonsu daya bayan ɗaya. "" Ina son na kunna mata masifa ne"
"daga ranar aurensu zuwa ranar da zan mallaketa. Wannan aikin ba zai samu ba, dole sai da goyan bayanku, kafin nazo nan sai da na san kome a kanku, kowa da inda yake tsaye da kuma abinda yake nima. Ni kuma ita yarinyar nake so, idan har zaku bani damar haka tow ai zamu tafi a jirgi guda."" Mikewa yayi zai bar parlourn ya kalle su, murmushi yayi ya ajiye musu wani takarda ya ce musu. "" Ga shi nan number wayata ce. "" Daga haka ya juya ya bar parlourn, yana fita suka dauke ajiyar zuciya lokaci guda, kowa sai kallon dan uwansa yake domin bakiɗaya sun kasa nutsuwa da shi, da ace yau a cikinsu yake da sauki amma bako ne taya zasu yarda su bashi amana idan tazo ta ci amanarsu fa? Duk da sun ga farauta a"
cikin idanunsa da kalamansa da alamu ba kudi ko wani abu ya kawo shi. Kuma baya bayan kudi.
""" Ni dai na yarda da shi! "" Inji Khaulatu mahaifiyar Badr, domin ita Allah ya gani duk hanyar da za a raba"
"lamarin nan tana cikinsa. ""Nima ina tare da shi!"" Inji Hajiya Sameerah mahaifiyar Batul. ""Nima ina tare da shi!"" Inji Hajiya Zeenatu, ""ban gane kuna bayanshi ba? Kuna nufin idan aka fasa auren Bilal da Lubnah zaku aura mishi Yaranku ne?"" Shiru suka yi ya sake murmushi ya ce musu. ""Ku nutsu dai amma maganar"
"a fasa aure ba zai taso ba!"""
"Tun daga nan suka shi shiru, amma kowacce da yadda take hada gwaraman da zai fitar da ita."
Haka suka watse babu tsayayyen ra'ayi a tsakaninsu domin kowa yana ji da son rai a cikin lamarin idan
"aka lalata auren da yarshi zaa yi. After like three suka nemi Hafiz don s cikin kwanaki uku nan Alhaji Mudansir yayi kokarin ganin shawo kan Mahaifinsu, amma yace aure ba fashi duk abinda Hafiz ya gaya masa ya gayawa Alhaji ELYakub amma tace eh ya sani don ya kara tabbatar mishi har takardun asibitin Lubnah ya fitar mishi da su, ya ce. ""Ka gani sun gama nasu na turawa musu da na Turaki,saura ranar"
"muke jira tunda daga amaryan har Angon basu kasar sun tafi Umara."""
"Wani abu ya tsaya mishi a rai haka yasa shi ya kullaci lamarin a ransa, ya kuma zauna da Hafiz"
"bakiɗaya ya ce mishi. ""Ban san me zaka yi ba, amma ka taimaka mana a lalata lamarin nan!"" Murmushi yayi yana faɗin. ""Wannan aikin nawa ne fa taimakawan mata, ni nasan Lubnah ba kuma san rauninta, ku kuma sai ku nimo raunin naku."" Haka yasa duk suka yi shiru, murmushi yayi sannan ya ce musu."
"""Harkalla ta fada amma ku sani duk abinda zaku mata ku jira ni na baku shawara yadda kome zai tafi."""
"Tun da ya fadi haka ya mike abinsa, ya bar su da nazarin yadda kome zai zo musu. Alhaji Mudansir ya"
"ce musu.. ""kasancewar Badr da ita aka fara ku sauran Yan mata ku goya mata baya, idan ta samu Turaki kamar mu ne, muka same shi, idan har ciki tayi da shi to ku sani namu ne, babu amfanin rigima duk abinda zaku yi ku tuna Shari'a mace daya zata bashi damar aura a cikinku, sai kuma ita Lubnah take! """
"Yadda yake magana tare da tsara kome, ya kuma gaya musu shi zai dauki duk wani abu idan ya faru."
Tabbas sharrin da tuggun da suke daukarwa kansu Babba ce kuma ba karamar da zaa ce zata lalace nan
"kusa ba, Babban al'amari da zai tab'a zuciyar kowa suke dauka. Don haka ya basu shawara da su kwantar da hankalinsu a hada kome a nutse a yi kome yadda ya dace."
"Bangaren Alhaji ELYakub Kumo, wata yar kanwarsa da take England tana aure ita ya turawa duk wani"
"abinda ake bukata na. Kayan aure ya ce yana so kafin daurin auren, domin ango da amarya zasu tafi Dubai yin hoton pre-wedding picture. Lokacin da labarin lefen da za a hada Hajiya Safinah zata hada, abin ya zo musu bazata, sun shirya zalunci gashi wai pre-wedding picture din ma a Dubai za ayi wannan abin ya tsaya a ran Hajiya Khaulatu, domin kuwa tayi amfani da wannan damar tayi ta sake wasu kananan magana da habaici a status dinta domin Hajiya Safinah ta gani, ita kuwa irin mutanen masu bala'in niman na kansu ne daga can take hada kayan aure ta turo nan Nigeria, ai kuwa kannenta suna"
"gani, suka shiga bawa Hajiya Khaulatu amsa, musamman da suka san kome."
"Wata cikinsu mai suna Hajiya Kulsum ta daura hoton Ango da Amarya a gaban Harami, ta rubuta."
"*Zabinsa ce, bai duba me take da shi me iyayenta suke da shi ba kawai soyayyar yarinta ne tun tana yar"
"mitsitsiya yake jiran wannan ranar, na ga na dating Ina jiran Pre-wedding da kuma After wedding a Ka'aba. Ya Allah ka kai mu ranar da zan ga auren Bature!*"
"Da yake haka wasu suke kiranshi a cikin family ɗinsu, wai Bature duk da bai da kalar fatar"
"Mahaifiyarshi, amma kuma yana da yanayi da turawa. Musamman i"
Ƙwayar idanunsa.
***
"Ranar da muka gama Umara, Mama take gaya ai zan bi Mr Turaki da Jasminah, dubai akwai hoton da"
"za'a yi a can, Aunty Hindatu da Aunty Innah suna can, ya biya musu kudin tafiya da kome da kome. ""Mama sai!"" ""Allah ya shirya ki!"" Ta fada sannan ta cigaba da hada kayan tafiyarta gida, haka kuwa aka yi Mama ta bar Saudiya, koda Mama bata nan, na kame kaina kada ya ga babu Mama ya sauya halinsa, sai dai wani ikon Allah, bai taɓa kallona ya ce yana son wani abu ba, har wani nuna mishi rashin yarda nake idan ya zo kusa da ni, amma wani murmushi yake, mun ya ce min. ""Ni fa bana da ra'ayi ne akan zina, da ina da shi wallahi ban san iya adadin matan da suke kawo min kansu ba, don haka ki daina min kallon Kasungurmin dan iska. Ko a kasar nan idan ina son mace har dakina zata biyo ni."". Hararanshi nayi."
Domin na lura ba ruwansa da kunya.
"Kwanan Mama biyu da barin kasar muka wuce Dubai, su Aunty Hindatu suka zo daukata da Ubaid da"
"Matarshi, wacce na ga yanzu ta sake kamar ba ita tayi ta haukar zubar da mutuncinta ba. Sai da na wuni"
na huta kafin muka je inda Ubaid ya kai min dinki kayan pre-wedding din. Sai da na huta domin mai
"hoton daga kasar China aka dauko shi, ranar dai hoto kala goma goma muka yi da kaya ɗaya, muna gamawa aka ce kanwar Mamanshi ta iso daga Germany da wani cocktail gown, wanda aka zuba mishi wasu pearl masu bala'in kyau da daraja, yadda ta rungume ni tana faɗin. "" Lunah ko?"" Gyada kai nayi, tana murmushi ta ce mishi. ""Kayi sa'ar mace gata da kunya!"" ""Ni kuma mara kunya kawai ki ce Bilyl