Advertisements
Chapter 310 Reading ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu

Author :  Mai Dambu Category :  Complete Novels

Chapter   310 / 321

927K to 930K   out of 962.4K words

ba, ai na gaya miki ke tawa ce ba xaki tab'a tsare min ba."" Ya rike wukar kamar wanda aka jefo shi haka ya shigo parlourn, wani irin daukar Hafiz yayi ta baya ya buga shi fa kasa, kishi ya rufe mishi idanu. Dukanshi yake kamar zai kashe shi, na rike shi ina faɗin. ""Don Allah kada ka kashe shi!"" Ture ni yayi na fadi akan hannun kujera. Shi kuwa Hafiz ganin yadda ya Turaki ya fita hayacinsa ya ce mishi. ""Ai na gaya maka, indai ina raye ba zaka tab'a kasance da ita ba, bari"
"ka ji sai da na taɓa kuma ita ta kira ni, shine na biyo ta. Kai baka isa ka ce zaka raba ni da ita ba, ko ka"
"kashe ni nan Hafiz Ni ne mijinta wanda ya fara bude mata idanu!"" Naushi ya kai mishi. ""Don Allah ka"
"kyale shi wallahi karya ne!"" ""Wallahi ba karya nake maka ba, ka duba wayarta da whatsp dinta da Email dinta, ni dai take bi."""
"Wani irin kuka ne ya kwace min nayi ta kallonshi. ""Allah ya isa Hafiz! Me yasa kake son lalata min"
"rayuwata!"" Kai mishi duka Turaki yayi a gabanshi sai da ya suma ya kalle ni. Kafin ya ja shi ya fitar da shi a"
gidan yayi wayawa yan sanda aka zo aka dauke shi. Ni kuwa madadin ya min magana sai ya saka kai ya bar gidan.
"Haka na kwana na wuni, babu shi babu alamar shi, haka na kwanta washi gari. Mutumin nan baya nan,"
"sai karfe biyu na yamma Ubaid da Matarshi suka kawo min ziyara, a bakinsa nake jin labarin business Trip din da yayi, haka na bawa kaina hakuri na shanye na cigaba da hakuri. Sai da ya shafe sati uku cib ranar na shiga gidan Uncle Auta. Na samu wani labarin wai ashe an d'ago da maganar aurenshi da badr,"
akan idanuna suke fadar zata shigo ta kwace mijinta.
"Haka na fita na tafi gida, na kira Hindatu ina kuka, na gaya mata duk abinda yake faruwa. Nace mata. """
"Ni zan koma gidan Ya Ado ba ni da sa'a da aure!"" Fada tayi min sosai sannan Aunty Hindatu ta shiga bude min sirrin zama yar bariki a gidan miji, sai nayi ta jin kunyar kuma maganar Allah gaskiya ta gaya min, haka muka yi sallama da ita, da safe Uncle Auta ya kawo min cefane, na yi girki don daga ganin haka nasan yana hanya, haka na shiga nayi aiki wurin sha biyu ya shigo gidan, kallo daya nayi mishi, na wuce na rufe kofar gidan na dauke key na saka a kitchen, sannan na gama abin da nake na shiga ban daki nayi wanka, wurin karfe daya da rabi na fito na daure da towel. Shigowa yayi na kalle shi fuskarshi a haɗe ga"
"alamu yayi ya ce min. ""Key nake bukata!"" ""Babu inda zaka sai ka gaya min me kake nufi da ni?"""
"""Bani da lokacin magana bani key?"" Ya nuna min hannu, gyara zaman towel din nayi na dauko baby oil"
"dina na cigaba da shafawa a hankali cikin wani salon jan hankali. Yaki kallona, ne saboda baya son ya dauko amma kamar an ce ya d'ago kai idanunsa suka yi farin gani......"
"[12/19/2025, 9:58 AM] Maman Walid: 22"
"Da wani irin sauri ya dauke kai yana.. ""Kin ga saura minti uku a shiga sallah ba ni!"" Yana kallon yadda na"
"mike, ""Ya Ilahi."" Ya furta a hankali, ya rasa me yake mishi dad'i. Turare na dauka nayi ta shafawa har aka shiga sallah, sannan na wuce na daki doguwar riga da abin sallah na shimfida mana na ce. ""Zo ka jamu sallah, tunda na masallaci ya kwace maka!"" Yadda nayi maganar a sanyayye tare da wata Ja'iran murya yasa shi, shiga gaban sallah. Haka ya jamu, amma zuciyarshi kamar ta fito don azabar karfin turaren nan"
dakyar yayi addu'a ya fita a dakin murmushi nayi ina bin shi da idanun. Oh dai.
"Bayan na idar da addu'a, na nufi kofar dakinsa na buga, shiru yayi ya ki amsa min. Na kara buga kofar"
"ina kiranshi. ""Malammmmmmm!"" Haka nayi ta bugawa har ya gaji ya buɗe, murmushi nayi mishi. ""Food"
"is ready!"" Kallona yayi yana mamakin. ""Ba zan ci ba!"" Riko hannunshi nayi nace mishi. ""Wallahi nan ne"
"kan nace na zai yiwu ba, oya muje!"" Na ja hannunsa, ina faɗin. ""Oya muje ka ci abinci, ba zai yiwu a bani amanarka azo a ga wani abu ya same ka, na shiga uku ba."" Na ja mishi kujera ya zauna sannan na shiga zuba mishi abinci kome daidai cikinsa. Sannan na ajiye mishi na saka cokali. ""Ke yanzu baki ji kunyar kayan jikinki ba?"" Kallon kaina nayi dress ne irin na yan makaranta, skirt da riga, ko gwiwa basu kai ba nace mishi. ""Ina zan ji kunya tunda gidan mijina ne!"" Na fada ina murmushi, tabbas yayi kewar abincinta,"
amma kuma fushin da yake da ita har yau ba daina jin zafi ba.
"Sai da ya ci ya koshi sannan na bashi ruwa ya sha kafin ya mike. ""Yawwa Goodluck;"" na ce mishi"
"sannan ya wuce abin dariya a fusace yayi tafiyarsa. Haka na gyara table din na kai kome kitchen, sannan na wuce dakina. Ina waya da Mama muka gaisa sosai har da Yadiko. Kafin muka yi sallama.. ina zaune wani idea ya fado min wata rigarshi na dauka na saka, yau ko da karfi sai mun shirya wallahi na gaji. Ni ko labarin Hafiz ban kara ji ba, ina zaune ina karanta wasikar jaki ya shigo ya shirya zai fita ya ce min."""
"Bani key zan je KUMO FAMILY MANSION!"""
"""Sai gobe yau lokacina Better go to your room, babu inda zaka na gaya maka."" Daga haka na cigaba da"
wasa da kafana.
Sake baki yayi yana kallon yadda take mishi tsirfa kala-kala. Abin ya bashi mamaki. Haka ya koma dakinsa
"can naji ana buga min kofar gida kofar na je na tsaya ya zuba min idanu ganin Hijab har kasa na ce. ""Waye?"" ""Uncle Auta ne "" aka bani amsa. ""Ai sannu me kake bukata?"" ""Wurin Turaki na zo!"" ""Ayya sai dai gobe amma yau turaki nawa ne ni ɗaya."" ""Ki yi hakuri ki bani aronsa."" ""Ina ka je kawai da ya tafi har tsawon sati uku ka tambaye ni ya gama amarci ko bai gama ba, amma haka na zuba mishi idanun don haka sai ya biya kwanakin da yayi baya tare da ni wuce wurin Maman Daddah kafin na kira ta na gaya mata kun fara niman sabin yan mata!"" ""Tow haka abin ya koma!"" Ya juya yana faɗin haka juyawa nayi na kalle shi yana rike da hularshi. Cike da mamaki yake bina da kallo. ""Kayi lokacinka yanzu nawa ne!"" Na"
wuce dakina.
"Fitowa yayi da sauri daga ban daki, jin yadda aka shiga sallah, ya sa shi kara nufar kofa a zafaffe domin"
"yana tsoron kada ta kara sashi rasa sallah Asr kamar yadda ya rasa ta Dhur, sai dai kash kicibs suka yi da ita cikin hargitsetsan yanayi da yake kara karayar mishi da wasu kwarin gwiwa da yake da shi, kin kallonta yayi domin haka na iya Dragging dinsa into wani part da bai shiryawa ba, cikin makirin muryanta da rabonsa da ya ji muryan kusan sati uku kenan, ta ce mishi. ""Malammmmmmmmm!"" Jin wani abu yayi ya tsaya a tsakiyar kansa ban da ita da tasan tasirin da muryanta yake da shi, da ba zata tab'a kiranshi da wannan yanayin ba, hade rai yayi ya cigaba da tafiya don baya son ya kara kallonta ba tare da ya nufi masallaci ba, ada idan aka ce mishi mata dangin shaidan ne baya tab'a amincewa, dawowarta gida yau a karo na biyu ya amince ita din tafi kowa sanin hanyar da zata kashe shi, kafin ya gama tunani"
"ta kara cewa. ""Malammmmmmmm yunwa nake ji!"" Raka'a na biyu da aka kai ya saka shi dafe goshinsa"
"tare da watsa mata harara, ai kuwa ta shiga buga kafarta. ""Shi kenan kamar yadda ta min dazun ta kara"
"yanzu dole nayi sallah a gida "" ya rasa yadda zai yi da ita tare suka ci abinci amma yanzu tana kara mishi wani abu wai yunwa take ji. Zuba mata idanun yayi ya juya zai tafi, na bi bayansa har dakin ya shimfida abin sallah, nima na fito naje nayi alwala na dawo dakin na samu ya fara bin bayanshi nayi muka yi sallah tare. ""Yunwa nake ji!"" Na fada a hankali ina matsawa kusa da shi. ""Malammmmmmm!"" Juyowa yayi ya"
"rufe min bakina. ""Naji!"""
"Tashi nayi a hankali zan fita daga cikin dakin ya ce min. Na yarda so halitta ce, ya ratsa zuciyata,"
"amma ba zan jure abinda ya faru ba , ki min bayani Lulu... ina sauraronki ya aka yi Hafiz ya zo gidan nan?"""
"Murmushi nayi tare da zuwa na zauna a gabanshi, hannuna na kai gaban rigarshi na shiga balle bottom"
"din. Bai hana ni ba sai ma kallona yake. ""You like it?"" Gyada kai nayi a hankali ya cire rigar tarin kwanji da tsokoki suka bayana. Daga nan labarin ya sauya, wasu abubuwan dai sirrin Turaki ne da ni, domin na fahimci wata rayuwar daban take da lissafin mai karatu, shi bako ne a bangaren, yayinda ni yar gari na kasancewa wacce take rayuwa a wani bangare na garin, kamar yadda ake cewa mata suna suka tara haka ma mazan suna suka tara, a daren nan namiji gwarzon mijina, y goge min hadda bakiɗaya ya bude kaina ya zuba min nashi iya nashi shi dayansa. Ya daura ni a lissafinsa wanda iya ni kaɗai ya daurawa, akwai rana mai matuƙar daraja irin wannan ranar? Akwai wata rayuwa mai dadi irin wannan rayuwar?"
Mutumin nan ya wanke min duk wani abinda nake ji ko nake gani. Mutumin nan ya dasa min so da
kaunarshi tare da buƙatarshi a kodayaushe.
"Sai bayan kome ya lafa ya kara rungume, yana shafa bayana kamar za a kwace mishi ni! ""Thank you"
"Lunah!"" Kwantar da kaina nayi a kirjinsa, ina jin wani irin yanayi yana ratsa tsakaninmu. Mun fi awa a makale da juna, kafin ya tashi ya haɗa mana ruwan wanka, kin shiga mu yi nayi amma haka ya tilasta min na shiga muka yi wankar muka fito. Kunyarshi kuma sai ya cika ni, riga da wandonsa ya dauko min na saka, ya gyara gadon ina kallonshi. Bayan ya gama ya janyo ni jikinshi muka kara kwanciya, kanshi ya daura a kirjina, na rungume shi. Furfura kanshi na kai hannuna ina tsige su ya ce min.. ""Kin ga furfura ko? lokacin da na ganki ina talatin da wani abu, yau gani ina bawa arba'in baya, tunda kika amince kika aure ni, zan gaya miki, ina da lafiyar da zan jiyar dake farin ciki a ranan da muka kasance! kawai ki kaunace ni ki bar jin kunyana domin ni bani da kunyar!"" Tabbas bai da kunya, amma sai na tsinci kaina da kasa"
magana na cigaba da wasa da gashin kanshi. Ina murmushi da jin wani farin ciki a raina ya ce min.
"""Ki ce min wani abu? ina jiran kalmanki ko da ta a'a ce."" Murmushi nayi ya d'ago kai yana kallona, wani"
"irin tartsatsin kauna nake hangowa a cikin idanunsa. He like me, sama da yadda nake tsammani."
"Chakulkuli ya fara min nayi ta kaucewa, daga karshe yayi nasarar daukata ya daura ni akan kafarshi yana"
"faɗin. ""Shi yaren soyayya ba ruwansa da yare ko kabila, ba ruwanshi da jinsi mace ko namiji, shi wata halitta ce da take wanzuwa cikin zukatan masoya imma mutane imma wasu halittun na daban, ya kike"
"fahimci haka? Ni na fahimci haka ne lokacin da na hadu da ke."""
"Akwai wani irin dad'i da nutswa idan ka ji namiji yana fitar da abinda yake ransa. ""Ina sonka Malam,"
"sai dai ina tsoron kada ka juya min baya, ina tsoron kada ina murnan na rabu da Hafiz!"" Rufe min baki yayi yana girgixa min kai. ""Allah ya min tsari na zama kamar Hafiz Allah ya rufa min asiri na zama irin Hafiz, Ubangiji ya hanani ranar da zan zama kamar Hafiz. Kai Allah ya nuna min mutuwata sama da ranar da zan ga na zalunci matar da nake aure ba."" Kifa kaina nayi a goshinsa na ce mishi. ""Na gode!"". "" Me yasa kike godiya! "" "" Ai kai mutumin kirki ne kuma me cika alkawari ne, shi yasa nake maka godiya domin"
"zaka cika alkawarin da ka ɗauka. """
"Haka kawai na zauna ayi min sakiyar da ba ruwa, mijina yana sona nima ina son mijina, akan me zan"
"bar wani ya shiga tsakaninmu, a ranar duk a gida yayi salollin, wurin karfe tara aka buga gidan ya kalle ni, murmushi nayi na nufi kitchen na dauko key na mika mishi. Ya je ya bude Kofar. "" Ka fito daga prison kenan?"". Murmushi yayi sannan ya amshi ledar kafin ya kara magana ya banko kofar, Uncle Auta ya ce mishi."" Ni ka wulakanta?"". "" Sorry Uncle!"" Wato mu fa sai yau muke cin kazar amarci, muka ci muka yi"
"nak, sannan muka baje a parlourn muna hira da kallon wani film."
"Daren ranar dai dayawa zasu so jin labarin amma kuma, ai lamarin Babba ne fa. Domin ni kaina sai da"
"naji kamar na gudu mutumin nan wayo ne da shi, amma kuma duk abinda zai yi tausayi yake ba ni domin ya jima bai yi auren ba, ni kuma sai na mishi uziri, sai da muka kwashe sati daya cib sannan ya fara zuwa office shima din dakyar na lallaba shi, har da cewa Uncle Auta da Ubaid zasu mishi dariya ya ce musu sai ya rama min kwanakin da baya nan, riko shi nayi nace mishi. "" Wato bazani kayi kana gaya musu sai yanzu muke amarci! "" "" Ai ke kika gaya musu! "" Zare idanun nayi na ce mishi."" When?"" "" Kin manta kenan. "" Yana tuna mun ranar na ji kunya ta kama ni da gudu zan fita ya riko hannuna. "" Ban da gudu don Allah!"" Kaina na daura a kirjinsa ina murmushi. ""Kin yi kyau kullum kara kyau kike min!"" Ya fada min wata katuwa magana a kunnena, kunya ta sa na kifa kaina ina faɗin. ""Yaushe zaka fara jin kunya?"" ""Hala ranar da tsufa ya cimma ni!"" Girgiza kai nayi na raka shi har wajen sannan ya shiga mota ta bar gidan nima na dawo parlourn, tunda na dawo na shiga aikina, karfe uku saura na wuce lokacin na kusan gama hada sobo, da yake yace zai zo da baki tuwan shinkafa miyar Egusi nayi, ina ta aiki na ji an buga gidan na zata shi ne ina zuwa na bude Matar Uncle Auta da Ubaid sai wasu mata biyu da yan mata uku. Murmushi nayi na ce musu.."" Barkanku da zuwa ku shigo!"" Na wuce kitchen na kawo musu ruwa. Na juya zan tafi na ji daya tana faɗin. ""Dazun na ga posting din wata arewa dairy wai Yan Bauchi suna da rowa, basu iya baka kyauta daga ruwa sai ruwa."" Murmushi nayi na wuce kitchen, na hado musu snacks da nayi na karban baki na fito musu da shi, sai lokacin juna suke. Na koma na hada abinci a kula guda, sannan na kawo musu na ce musu. ""Don Allah ku yi serve kanku, bari na sauya kaya."" Na koma dakina na watsa ruwa na sauya kayan jikina, ina kasa kunnena ko zanji dirin motarshi, amma ina sai ji nayi yana gaisawa da matan, kafin ya shigo dakin.. ""ina ta son na maka oyoyo!"" Zungure min goshi yayi yana faɗin. ""Kin san dai da baki zan zo!"" Na dauko wata hijab dina har kasa na daura akan riga da zanin da yake jikina. ""Kina kyau da riga da zani."" Haka ya riko hannuna ya ce min. ""Waye dai taya ni shiryawa?"" ""Muje na gaishe su sai na raka ka, ka sauya kayan ko?"" Haka muka yi na fito na gaishe su, sannan na cewa Matar Uncle Auta"
"da Ubaid. ""Kuci abinci!"" Na raka shi dakinsa, ya watsa ruwa ina tsaye na fito mishi da wasu kananun kaya,"
"ya saka sannan ya saka turare na riko hannunshi,. Muka fito a lokacin da su Uncle Auta da Ubaid suka"
"shigo gidan, ashe matan biyun nan mazajensu ne da Yaransu, haka mazan suka koma dinner table, su kuma matan suka zauna a parlourn na koma kitchen na yi ta fito da kayan abinci, shi kuma yana karba idan na kawo sai ya sumbaci hannuna, ko ya ce min. ""Sannu da ƙoƙari!"" Ina kawowa zai sumbaci goshina. ""Allah ya miki sakayya da gidan Aljanna!"" ""Amarya ko Falisha zata taya ki ne?"" Inji daya matar. ""A'a mu yan Bauchi, mun iya aiki da kanmu ko Malam?"" Gyada min kai yayi bayan mun gama na wuce kitchen, sai gashi ya biyo ni da abincinsa. Ajiye min abincin yayi. Ya saba muci tare don haka na wanke hannu ya zauna a kan wani kujeran kitchen din nima haka, muka shiga ci tare. ""Wani abu ya faru ne?"" Ya tambaye ni bayan na tura mishi loma. ""A'a babu abinda ya faru!"" ""Akwai mana baby gaya min."" Murmushi nayi"
"nace mishi. ""Zance ne irin namu na mata."" Gyada min kai yayi yana kallon yadda nayi ta tura mishi abinci, sai da muka gama ya wanke hannu ya taya ni wanke kwanon, muka fito ina cewa. ""Dauko tissue please!"
""" Wurin cin abincin ya nufa Uncle Auta ya ce masa. "" Sai ka gaya mana matarka ce ta baka abinci a baki!"""
"""Kai dai da baka iya romantic ba, a barwa newly couples kayansu!"" Ya tawo lokacin har na shigo parlourn,"
"yana zuwa ya mika min. Na amsa tare da goge mishi ina faɗin.. ""Malam gashin baki da kasumbar nan suna bukatar gyara fa."" Na faɗa kasa kasa. ""Tow idan suka tafi ba sai ki gaya min ba, ai tun jiya nake bin ki, amma kika share ni."""
"""Ok bari mu sallami baki!"" Na fada ya koma wurin mazan. ""Duk wannan soyayyar kafin a haihu ne"
"idan aka haihu shi kenan sai ya zama tarihi."" Murmushi matar Uncle Auta tayi ta ce mata . ""Da don haihuwa ne, da tuni ya tara goma na yara. Kauna ce dai da bata tsufa ba, sannan bana jin idan zasu

310 / 321

Chapters