Advertisements
Chapter 307 Reading ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu

Author :  Mai Dambu Category :  Complete Novels

Chapter   307 / 321

918K to 921K   out of 962.4K words

ka min na bani abinda kuka fi so, yafi kome min dad'i nasan da Iyayena suna raye sai sun fi kowa farin ciki. Amma nasan Kakanina kowanni bangare suna cikin farin ciki. Na gode na gode!"" Ya fada yana kara damke hannuna, hawaye ne ya shiga zuba min tun daga fara maganarshi, wani irin so yake min haka? Kamar yasan tambayar da nayiwa kaina ya cewa Abba..""Abba ni ba so ya kawo ni gare ta, gaba da kaunarta ya kawo ni gare ta! Abba ina kaunar Yarka ina kaunarta sama da kaunar da nake mata, ita din wata bangaren rayuwata ce."" Addu'a Alhaji Sa'idu ya rufa da shi, haka Aunty Hindatu ta fitar da ni, mutumin nan yayi confessing yadda yake kaunata, ya faɗa abinda yake ranshi abinda na jima ina jira, da muka fito aka fara hoto, ban tab'a gani ko ji a rayuwata akwai irin kaunar da yake min ba, hatta a wurin hoton kowa ya shaida shin kaunar kauna yake min, haka yake kare ni, tare da kallona lokaci zuwa lokaci. Yana murmushi. Idan ya ga kamar xan yi kuka, rike hannuna yake yayi ta murzawa, murmushi yake min ko ya saka bakin shi a kunne. ""Kada ki yi kuka!"" D'ago kai nayi ina kallonshi, shima murmushi. Wani irin kuka ne yake zuwa min, amma haka nake shanyewa yaddA muke hoto da dangi, kafin nayi da yayuna mata, ina tsakiyarsu Aunty Munah tayi missing na Bauchi koda yake a lagos akwai dinner. Kuma ta ce zata ta can, haka ba koma aka yi min da Yayuna maza musamman Ya Ado da na kwantar da kaina arm dinsa ina kuka, sannan aka yi min da shi da Ya Ado, sun saka ni a tsakiyarsu. Kaina yana kafadar Ya Ado, shi kuma"
"yana rike da hannuna. Murmushi yake. Sannan aka gama ya rike hannuna yana faɗin. ""Sai yaushe zan"
"kuma ganinki?"" Ya fada yana murmushi, ""Malam dalla sake ta bayan rungume ta da ka gama a gaban"
"Jama'a."" Inji Ubaid, haka ya kyale ni. Wurin karfe daya aka gama shirya ni cikin wata laffaya, danginsa da suka zo aka basu ni tare da tsaraba, Yadiko da take cikin tafiyar ta shiga parlourn Abba ta fito da ni,"
"Mama kin fitowa tayi don itama zuciyarta yayi rauni, a hankali na kwace na wuce dakin Mama da"
"take uwar daki ta zauna tayi shiru, rungume ta nayi ina kuka. ""Mama ki zo muje!"" Murmushi tayi tana"
"shafa bayana. ""Kada ki damu zan zo na ga gidanki, idan turaki ya miki laifi ko gaya min zan ɗauki mataki akan shi."""
"""Ke bana son sakarci, Mama kyale ta mu tafi! "" Inji Ya Umar, da hannu tayi mishi alama da ya tafi, ta"
"cigaba da buga bayana, can Aunty Hindatu ta shigo ta mata alama ta tafi. Sai wurin karfe biyu saura sannan ta ce min. ""Muje ki tafi gidanki in sha Allah!"" ""Mama!"" Hannu ta saka min a baki tayi, tare da riko hannunta muka fito ta mikawa Yadiko ni, ""Ubangiji ya baki zaman lafiya da zuriar dayyiba, ya albarkaci rayuwarku, Rahama da Ni'imar Allah ya lullube rayuwar gidanki, Allah ya shirya zuriar da zasu zo bayanki."" Haka tayi ta min addu'ar har wurin motar da zan shiga, kafin a tashi motar na rike hannunta, murmushi ta sake, sannan ta cire hannunta tayi musu alama su tafi ina ji ina gani aka raba ni da gidan, ko aurena na farko ban ga wannan gatar ba, domin Ya Tahir mota guda ya dauka wa dangi bayan wanda gidan ango suka kawo, aikuwa dayawa sun bi motar domin kuwa sun zata a can zan zauna. Duk da akwai gida a can, amma ni da Gombe maybe sai ko sallah ko wani abu, ba ƙaramin kuka nayi ba, tafiyar awa biyu tare da rakiyar sojoji da yan sanda muka isa garin Gombe, an karbe mu da hannu bibbiyu, abinci aka kawo mana, muka yi sallah da ya wuce muna, sannan aka hada min ruwan wanka na shiga nayi aka kawo wani lace wanda aka yi mishi dinkin doguwar riga yayi kyau gashi fari tas, sannan mai kwalliya ta zo ta min kwalliya wurin karfe hudu da rabi aka fito dani zuwa kofar fadar Gombe, aka yi kilisa, domin an bashi dan malikin Gombe. Yadda aka tsara hawan yaji kyau ga shi ashe tun jiya aka bashi sarautar aka yi bikin, sai karfe shida muka dawo gidan. Anan Gombe sun yi yar karamar liyyafa, yayi kyau ba na wasa ba. Da"
"na dawo dakin dakyar nayi barci domin bai taɓa min irin wannan abin ba, sai wannan karon magana yake faɗa min masu nauyi da saka jin kunya, don haka naki biye shi, karshe yaja can yana baro min magana har nayi barci, tun da muka yi sallah asuba, na kwanta na gaji sosai. Wurin karfe takwas muka tashi nayi wanka na saka wata Holland, sannan na shirya bayan na saka Aunty Innah ta daura min laffaya muka fito zuwa parlourn aka shiga dani cikin gidan na gaida manyan gidan suka saka min albarka, sannan muka dawo muna karyawa waɗanda suka rako ni suka fara shirin komawa Bauchi muka fita nayi musu sallama sai Godiya suke, bayan sun tafi Aunty Raliyah take cewa. ""Gaskiya Mijinki nan yayiwa bikin nan shiri na musamman, kowani mutum daya ta samu kyautar dubu hamsin da jaka na kayan biki."" Murmushi kawai nayi ba tare da nace kome ba, har zuwa lokacin da na gama karyawa, ya shigo sanye da wata yadin material na kasar Sweden sai daukar idanu take, yana shigowa ya gaishe su sannan ya ce min.. ""ko zaki sauya kaya mu shiga kunyi hoto da yan gidan."" Yadda ya tsare ni da idanun taya zan ce mishi a'a, haka na koma cikin dakin na saka wata shadda na fito, da babban mayafi sai takalmi da pose muka shiga cikin gidan aka yi ta hoto da manyan gidan har da kannen kakanshi, sannan ya riko hannuna"
"muka nufi wani gida wnada ko bai gaya min na san nan ne wurin zaman mu, ashe akwai mutane a gidan"
"mai kwalliya da mai taya ni sauya kaya, haka muka yi ya hoto har ya kira su Aunty Hindatu suka zo aka yi"
"da su, sannan aka fita. Ina zaune a gefenshi har kafad'arshi yana gogan nawa, waya yake hannunshi yana cikin nawa. Yana gama wayar, zuba min idanu. ""Wa na kama?"" Ya fada yana sumbatar goshina. A hankali wasu abubuwan da zuciya ta jima da binne su, yau ita Mr Turaki yake tono min, tare da jefa min kwadayi da son na kasance da shi, tabbas kowani namiji da yadda yake daurawa mace karatunsa. A wannan ranar Mr Turaki ya daura min wani karatu me nauyin dauka. Domin sai yanzu na fahimci yadda mace take ji idan ta hadu da shu'umin namiji, musamman wanda ya san yadda zai zautar da zuciyar mace, dakyar na iya kame kaina tare da fara ƙoƙarin kwace kaina, ina hakki tare da niman mayafina hawaye na zuba min. Da sauri na dauki mayafina zan fita ya fisgo ni. ""Ba jikinki nake bukata ba, amma na gaya miki kada ki zo gare ni da turarenki nan domin Allah ya gani duk lokacin da zan ji kamshin ki tow ina jin mafi kololuwar buƙatar kasancewa da ke, kada ki yi kuka kin ji domin akwai ranar da zaki roki na kyale"
naki........
"[12/16/2025, 8:08 PM] Maman Walid: 18"
"Da sauri na bar parlour ina gyara zaman mayafina, ina zan iya irin wannan rashin kunyar, shi bai da"
"kunya bakiɗaya da aka zo rabon ina ga nashi bawa wasu aka yi, "" hi Mrs Turaki jira ni na kai ki ai baki isa ki tafi ki bar ni ba, salon wani dodo ya kama min yar Chika ta!"" ""Chika?"" Na kara maimaitawa a raina nace. *Allah yasa ba wata kalmar batsa ba ce!* Domin shi duk abinda ya fito a bakinsa fada yake, sarkafe hannunmu yayi ya d'ago tare da sumbatar hannuna ya ce min. ""Muje ko? Chika na!"" A hankali nake binsa yana kallona yayi murmushi. ""Sai naji kamar mu yi ta tafiya haka, babu kowa a tsakaninmu. Babu wnada zai dame ne mu, babu tashin hankali."" Riko ni yayi na dawo gabanshi, ya hade goshinmu wuri guda. ""Ina ji a raina ni nafi kowa sa'a a wannan rayuwar duniya, ina kuma rokon Allah yasa kada nayi danasanin akanki har karshen rayuwata."" Hannunsa naji akan kuguna na bude idanuna. ""Ke hakkina ne fa, da zaran na taɓa ki sai ki razana kamar wacce aka ɗoɗɗana mata wuta, ki sani Mijinki jarumi ne ahto ba zan yarda ina taɓa ki, kina zabura kamar wacce aka saka mata lantarki ba."" Wayarshi ce tayi kara ya"
"ɗauka yana faɗin. ""Ok kuna airport kenan?"""
"Take na ga fuskarshi ta sauya, a hankali na kai hannuna kirjinsa ina ɗan tab'awa, a hankali kamar"
"rarrashi. Zuba min idanun, ni kaina ina jin abinda ake fada tsaki yayi ya ce mishi."" As you wish!"" Rigima suke da Kakanshi akan ya zauna a part din iyayensa musamman na mahaifiyarsa shi kuma yace ba zai zauna ba, shine ake ta kai ruwa shi ya nace sai gidansa. Kallon kwayar idanuna yayi kafin ya ce min. ""Zaki iya zama a wancan jahannamar?"" Lumshe idanuna nayi kafin na bude akanshi. ""Duk inda ka kai ni zan zauna."" Bakinshi ya kai tare da sumbatar goshina, ""Muje su Auntynki sun tafi fa!"" Zare idanun nayi ina faɗin, ""me yasa suka tafi?"" ""Ji gulma da kika samu Mijinki, kika manta da wasu aunty a can!"" ""Ni ba ruwana kai ne ai!"" ""Amma yarinyar nan kin ga girmana, lallai ma dole na shiga lamarin nan ayi mana Shari'a akan wannan sharrin da kika min."" Ya fada yana murmushi, har muka isa inda motar da xata mai mu airport an saka kome na mu, ya bude min na shiga sannan ya zagayo ya zauna a kusa dani. Rike hannuna yayi yana shafa lallen hannuna. ""Kin yi kyau! Amma. Jiya don wulakanci kika yi ta kuka har naji tsoron kada Mama ta ce an fasa tarewar da sai na ce kowa ya tafi mun gode anan zamu cigaba da"
"zama!"" Kifa kaina nayi ina dariya, ashe haka yake da surutu, an kira shi ya kai sau biyar karshe kashe"
"wayar yayi, ""idan suka gama bidiarsu dole na dauke ki mu tafi honeymoon!"" Murmushi nayi wato ina ga"
"ko Radio sai zuba yake min, har muka isa airport ɗin Uncle Auta yayi ta mishi fada akan bata lokaci da yayi ya ce musu. ""Ni fa bance a shirya wani biki ba, yawwa don da na san da wani bikin nan da na wuce honeymoon da matata ni bai dame ni ba, kowa ya zo ya kwashi gara yayi tafiyarsa ko Lunah!"" Ya tambaye ni yana kallon fuskana, kasa motsi nayi Ubaid. ""Amma kai dai daga dan iska sai kai, Allah yasa ka wuce bangon duniya ba honeymoon ba."" ""Tow ina ruwana, lunah kina jin yunwa na kawo miki wani abu?"" Wato shi dai haka Allah yayi shi da bala'in niman magana, har muka shiga jirgin a wurin zama ne fa ni zan zauna da su Aunty Hindatu da Goggo Alti, sai Ummanmu, suka janyo ni na zauna a wurinsu. ""tsayawa yayi ya ce musu, ku bani matata, ni na muku alƙawarin zuwa aikin hajji in sha Allah, muna"
"sauka zan tafi da ita idan kafin a fara zan dawo muku da ita."""
"Kallonshi nayi kamar zan yi kuka na dauke kai, yadda yayi ta tsara su har suka bada hadin kai, na sha"
"mamaki. Kafin mu isa lagos ya shawo kansu, muna isa airport na lagos wata mota ta zo ta dauke shi da ni."
Ina kallon yan uwana cike mamaki su kansu lamarinsa kara basu mamaki. Duk jikina ya ɗauki rawa.
"Haaka muka isa wani gidanshi a can victory Island, gidan yayi kyau, ya riko hannuna muka shiga avinda muka fara shi ne sallah, muna idarwa ya fita can sai gashi da abinci, kusan a tare muka ci yana bani ina kauda kai karshe ya janyo ni kamar yarinya karama haka yayi ta dura min, har na ji na koshi. Kafin ya riko hannuna zuwa parlour ya zaunar da ni akan kujeran parlourn, sannan ya fito ya zo ya zauna ya saka ni a gaba yayi ta kallona. Kafin ya kwantar da kanshi a cinyata, hannuna ya ja ya daura akan kirjinsa, tun yana min hira har barci yayi gaba da shi. Zama nayi ina kallonshi. A hankali nima na daura kaina kan kujeran na cigaba da nazarin rayuwa, kafin barci yayi gaba da ni. Wasa-wasa sai karfe shida saura muka farka, shi ya fara tashi ya zuba min idanu. Ji nayi an sumbaci hannuna, a hankali na ji dumin lips dinsa, bude ido nayi na kalle shi na ce mishi. ""Kin tashi?"" Gyada mishi kai nayi ya ce min. ""Sorry ko ni na tashe ki?"" Murmushi nayi na tashi zuwa dakin da muka cin abinci a cikin na shiga ban daki biyo ni yayi, zuba min idanu yayi da yatsu biyu ya nuna min abinda zai yi. Juyawa nayi zan fita ya riko hannuna na tsaya, ya gama yayi duk abinda Muslunci ya shara'anta sannan ya fito nima nayi nawa na fito na zo na samu yana jirana, a bayanshi na tsaya ya jamu sallah, bayan mun idar ya dauki Babban rigarshi ya ce min. ""Muje kin ji suna can suna ta Bala'i!"" Ya fada yana murmushi, gyara zaman mayafina nayi yana gamawa ya riko hannuna muka fita, har waje ashe dA mutane a gidan a harabar gidan na gansu suna taya shi murna."
"Motar ya bude min na shiga, sannan ya zagayo ya shiga yana zama muka bar gidan kafin mu isa har an kira Magariba, muna shiga can cikin gidan. Ya bude min na fita ya riko hannuna sai da ya ja min mayafina ya rufe min fuska, sannan ya rike ni gam, muka shiga tafiya kasancewar gidan ana ta hidima ga mutane sun taru, hotonmu da muka yi aka saka a wurin da za ayi taron, a hankali muke tafiya saboda tun da muka shigo gidan ake daukarmu hoto, lokacin da muka fito aka mana caa, sai da na ji bakiɗaya kome ya tsaya min har cikin gidan muka shiga hannun shi rike da nawa, gam lokacin da zamu shiga yan matan family din sun fito, hannunsa ya kai kuguna, ya kara janyo ni jikinshi, kallonshi nayi murmushi yayi min da wani karamin murmushi, haka muka shiga cikin gidan ana rangad'a gud'a, kaina a sunkuye har gaban Kakarshi ta wurin Uba wato Daddah tare da Kakarshi ta wurin Uwa. Guɗar da ake yasa ko ina na gidan ya amsa, riko mishi kunne wata babbar baturiya tayi tana mishi fada. ""Aunty Mom barci nake ji. Idan na ce"
"ku bari mu yi barci ba zaku yarda ba, amma gata Lunah bayan barci akwai wani abu da na.."" ture"
"keyarshi tayi tana faɗin. ""Allah ya shirya ka wuce masjid;"" ta tura shi waje, daga nan ta riko hannuna ta"
"kara kawo ni gaban Mamarsu. ""Mum ga Lubnah!"" ""Labubu!"" Kaina a kasa ta rike hannuna, ta rasa bakin magana sai kuka, Daddah tsabar dad'i wani abun wuyarta na gwal ta cire ta saka min, ""tunda turaki ta kawo ka da sunan tana sonka, nasan bai yi zabin tumin dare ba."" Ba ta kara cire warwaronta, ta saka min a hannu. Yan uwan Mamanshi da suke zaune da kawayensu ba sai gashi anata zuba min kudi fa kyauta kamar ana hidima. Da yake an tura a kira su Aunty Hindatu, sai gasun nan, haka suka d'aga ni zuwa vangaren da xan zauna aka hada min ruwan wanka Aunty Zakiyah ta hada min kayan kamshi nayi wanka na gyara jikina na fito nayi sallah, sannan na gabatar da sallah da ya wuce min, sannan nayi isha domin za a yi min kwalliya, bayan na gama aka kawo min wani kaya irin na mutanen Ethiopia, haka saka min kayan tare da mayafinsa sannan aka gyara min gashina, ban ji dadin wannan kwlliyar ba. Ana cikin kwallyar ya shigo yana ganin gashin a bude ya ce bai san wannan zancen ba, hular da aka daura akan gashin ya kara fitar da ni, kasancewar Kakarshi Kirista ce har yanzu don haka kayan akwai Cross amma sai aka cire na kan hular, sannan muka fito bayan an gama shirin, su Aunty Zakiyah sun jima da barin"
gidan domin tas zai kunyata su.
Tunda aka ce zamu fito aka haska wani fitila da camera wanda suke can baya suna hango mu a
"majigi, sai suka huta da mikewa, flower girls dinmu Yaran Jasminah ne da Yaran mazan Uncle Auta, suka bude mana hanya muka cigaba da tafiya, Nusaiba yar Aunty Nuratu Kafaya ita ce da wasu yan Gym dinmu suka fito a bridesmaids, suka take mana baya a mazan da suka rufa mishi har da Ubaid. Haka"
muka isa wurin zaman muka zauna.
"Gashi an saka wakarsu ta can wanda suke yi da kafada, wasu daga cikin danginsu na can, sai wurin"
"yayi kyau. Haka akayi ta gabatarwa har aka gama kafin aka kira Ubaid ya bada labarin abokinsa, a hankali yake bada labari har ya gama sannan aka kira Nusaiba ta bada labarina, tun daga bude taron da Addu'a zuwa yadda take ba da labarina, kallon Aunty Zakiyah da ta d'aga min hannu nayi murmushi, bayan ta gama aka saka waka musamman namu na yan arewa, kafin aka saka wakarsu na Fulani. Kallona yake yana murmushi, bayan an fito da ni da shi. Aka yi ta zuba mana kuɗi, daga shi har ni ba gwanayen rawa ba, haka muka tsaya musamman inda ya ɗan saka hannunshi a kuguna da kuma rike hannunsa ina kallonshi. Wani abun da ya kara tashin hankalin a wurin masu adawa da aurenmu, musamman Badr ban ganta ba, na samu kyautar abin arzikin da abin duniya baa tashi ba sai karfe daya saura sannan aka raka su Aunty Hindatu zuwa gidan Ya Ado ango da yan uwansa, ni kuma aka wuce da ni bangaren fa aka gyara shi tas, aunty Innah har da cewa. ""Yanzu ba mamaki fitar nan har

307 / 321

Chapters