Advertisements
Chapter 318 Reading ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu

Author :  Mai Dambu Category :  Complete Novels

Chapter   318 / 321

951K to 954K   out of 962.4K words

sake ta saboda baka haihuwa?"" Girgiza kai Hafiz yayi kafin ya ce mishi. ""Idan na sake ta ba zata samu wanda bai kai ni ba, ta zauna da ni a haka har ta Allah ta ishe ni, nisan da Lubnah tayi min har abada babu wata"
"macen da zan iya samu irinta."" Kasa yayi idanunsa sun yi jajjur ya d'ago yana kallon Jalilah ya sakar mata"
"murmushi, ya ce mata. ""Ina fama da laluran rashin lafiya na jima ina amsar magani, yanzu ciwon da yafi"
"damuna shine cutar hanta. Kuma ina kyautata zaton kema kina da shi, tunda mun yi mu'amalar aure da ke!"" Wato da Jalilah ta fasa ihu tare da yankar jiki ta fadi, sumarta uku kafin ta farka, tana ganin Hafiz ta fashe da mugun kuka tana yi tana buga kanta da bango tare da jin kamar ajalinta ne ya zo. ""Yanzu Hafiz ka kyauta abinda ka aikata?"" ""Abba wannan shine karshen azalumai irinmu, Abba kasan yadda suka yi ta tura ni ga na saki Lubnah. "" Hawaye yake zuba mishi, tabbas yayi asara babba da ya rasa Lubnah, haka yayi ta kuka kamar yadda yake jin ciwon da yake damunsa ya d'ago kai ya ce. ""Ta bani kudinta na ci na hanata, sau uku kana biya mata Umara nace ba zata ba, na amshi kudin na kashe akan matan banza ban da Jalilah da kin Allah sau nawa kika cewa zaki Jama'are, na kama miki gida ki zauna mu ta abinda bai dace ba, nayi duk abinda kike so saboda kawai mu kunttawa Lubnah ba wani, kina daga cikin mutanen da suka bani shawarar na daura Lubnah akan kwaya, idan ba haka ba zata cika min gida da Yara ashe yau don bana haihuwa kece mutum na farko da zaki fara zama da ni, kece kika hada ni da Karimah yau kece kike guduna saboda bana haihuwa, Haba ai idan na kyale ki Allah ba zai bar ni na kare rayuwata lafiya ba, gara mu karasa abinda muka fara, a jikina me ye baki yi ba, meye ban baki ba wai har kece zaki guje ni, kin ga yanzu idan duniya tasan halin da nake ciki sai naga yadda zaki kashe auren, hmmm na san haka zai"
"faru. """
""" Allah ya isa tsakanina da kai, Azzalumi dama can halinka ne ni ce zaka yiwa sharri."" Jalilah ta cigaba da"
"zaginsa da ci mishi mutunci da cewa ko me zai yi sai ya sake ta wallahi bata zama da shi."" ""Goggo ko na sake ta wallahi ba zata sami me aurenta ba, duk inda zata ni zata dawowa."" Ya fada yana kuka yana kallon kasa. Ya cigaba da cewa. ""Ko sau daya babu wanda ya daura ni akan hanyar da ta dace akan Lubnah, kowa so yake na kuntatta mata idan na cire Goggo Alti ita ɗaya ke ce min ka rike aurenka da daraja, Abba nan suke zuga ni da cewa ai morata kake don haka ka bani auren Yarka, duk yadda kuka juyawa Lubnah baya basu gani ba, nima ban gani ba, anya zan samu rahamar Ubangiji kuwa? Har wurin Dangin Mijinta na je na lalata mata suna da kome, amma da yake Allah ya kafa aurenta ba kafi irin namu na, Na gaji zuciyata kamar zata fashe idan na tuna ni da kaina a lalata lamarina, Hajiyata tayi kokarin gini"
min mugun nufina.......
"[1/6, 8:28 PM] Maman Walid: 34"
"""Amma yau gashi mugun nufina ya dawo! Na zalunci kaina da kaina, duk abinda nake yi duniya ta juya"
"min baya, ina ji ina gani na kashen kaina da kaina. Na saka dabi'ar niman mata a gaba, bani da aiki sai yadda naso, Abba kasan na tab'a kawo mace gidana ta kama mu amma."" ""Ya isa haka Allah ya kyauta."" Baban Bauchi ya fada yana kallon yadda Hafiz yake girzan kukan kamar yaro karami, girgixa kai yayi kafin ya ce mishi. ""Me kake gani zaka sake ta?"" Murmushi yayi hawaye na zuba mishi ya ce mishi. ""Na sake ta saki ɗaya."" Ya mike s hankali, har ya kai bakin kofar fita ya juya yana kallon Baban Bauchi ya ce mishi. ""Ina son Lubabatu ina sonta, ina sonta azzalumai da ni kaina mun cutar da ita, ji nake kamar nayi ta ihu ina masifar kaunarta ina kewarta da dukkan rayuwata. Kace mata ta yafe min."" Daga haka ya fita a"
"parlourn, mamaki ya kama kowa a parlourn ga dama kamar jira ake kiris maganar da aka yi a cikin"
parlourn har an fara lekowa ana kallon Jalilah da take ihu abinda ya janyo hankalin masu zuwa gaisuwa
"kenan, gidan ya rikice da tashin hankali."
"Haka Baban Bauchi ya bar can hankali a tashe, bai ga ma dan uwansa ba. Amma yasan yana cikin tashin"
"hankali. A hankali yake kara godewa Allah da basu juyawa Lubnah baya ba, yadda suka yiwa Lubnah rashin adalci. Koda ya iso Bauchi yake gayawa su Mama da Yadiko, abin bai basu mamaki ba domin sun san haka zai faru. Ai ba yau aka fara ba, kuma ba yau za a gama ba."
Fatan ta sauka lafiya suka mata kawai domin yanzu shine babban damuwarsu ta sauka lafiya.
***
Lubnah
"Tabbas yanzu na fahimci yadda kowacce mace take ji idan cikinta ya tsufa, wayyo Allah na, sai na ji kome"
"ya tsaya min a rai. Duk yadda zan bada labarin hankali ba zai dauka ba, sai ka shiga wannan yanayin zaka fahimci mata jarumai matukar jarumai ne, domin kuwa kullum zan kwana da ciwon baya, mai cin rai amma gari yana wayewa zan nime ciwo na rasa, tunda na shiga 38 weeks nake fahimtar wannan yanayin. Yau ma ina kwance yana shiryawa. Tsayawa da saka agogon hannunsa yayi ya ajiye sannan ya dawo gabana ya zauna yana kallon yadda nake kallonshi, abu biyu yake damuna na farko haushinsa nake ji, na biyu yadda yake wani shiri alamar ko a jikinsa halin da nake ciki, ai kuwa yana riko hannuna na rufe idanuna sai ga hawaye sharr. Ba yau ya fara ganin wannan sabon halin nawa ba, amma ya dauka a matsayin yanayin ciki ne, tunda shekaranjiya kusan tsiwa nayi mishi, har da kuka ni ya bar ni na tafi Bauchi na gaji sai da Umma tayi ta fada kamar zata duke ni na yi shiru, sai kuma na fara kuka. Sosai nayi kuka fa sannan nayi barci, Umma ta ce mishi. ""Kayi hakuri fa wasu matan haka suke idan cikinsu ya tsufa gani suke kamar basu da wani amfani a wurin namiji, wasu ma sai su ji basu son zama da mijin ina ga bata samu matsalar haka lokacin laulayi ba ne, shi yasa yanzu take maka haka kayi hakuri."" ""A'a ba kome ai na bincike kuma ina bin rubuce-rubucen masana da likitoci ba wani abu ba ne."" Wannan bayanin da tayi mishi sai ya samu natsuwa har ya shirya ya fita, to yau ma haka yadda nake kuka duk sai ya damu. ""Sorry!"" Ya fada yana shafa hannuna. ""Nasan kin gaji, ki yi hakuri zan kasance a gefenki har Allah ya baki ikon rabuwa da shi."" Ya fada yana shafa kaina. ""Na gaji!"" Hannunshi ya kai bakina. ""Na sani ba sai kin fada ba, Allah ya baki hakuri da lafiya kin ji."" Gyada kai nayi ya rike min hannu nan tashi zaune. "" Sannu!"" Ya fada min, sannan ya fita daga dakin can sai gashi dauke da tire na abincin, wayarshi ce tayi ƙara ya kalla sai kuma ya cigaba da aikin da yake ya zuba min abinci ya nufi toilet ya dauko min brush, da toothpaste ya dawo. Sai da ya saka min na yi sannan ya bani ruwa na wanke bakin ya koma ban daki ya zubar, ya dawo ya taimaka min na ci abinci. Ina ci yana bani labarin aikin da yake gabanshi. ""Amma ina ga yau zan hakura da shi sai gobe ayi meeting din!"" ""Da dai ka tafi;!"" Jan kumatuna yayi ya ce min. ""Ina kan magabata!"" Bayan na gama ya kai kayan waje, ina zaune ina kallon kofar, bai tashi shigowa ba sai da wata Indonesia gown har da top ga material din roba ce tana budewa idan aka saka, ajiye min yayi ya"
"mika min hannu, murmushi nayi na mika mishi nawa ya riko ni a hankali na sauka a gadon ina murmushi."
"Dan rungume ni yayi sannan ya sake ni, ya kuma riko hannuna muka wuce ban daki. Da taimakonshi nayi"
"wanka muna fitowa ya taya ni shafa mai a jiki ba wani mai bane blue seal ne, ina gamawa ya bani comb na tace kaina, ina gamawa ya riko hannuna muka fito parlourn girgiza kai Umma ta ce. "" Na shiga uku ni Aminatu! Anya ba zan koma Bauchi na bar ku da mugun abu ba."" Murmushi yayi kawai ya koma dakin ya gyara sannan ya fito, dakina ya wuce ya shiga ciro kayan baby yana shiryawa, jin shiru na tashi na nufi dakin na same shi yana saka pants. ""Me kake yi?"" ""Ina shirya kayan haihuwar ne!"" ""Nace maka haihuwar"
"taxo ne?"" ""But ai an kusa!"" Gyada kai nayi, na zauna ina nishi."
"Ajiye kayan yayi yazo ta gyara min zama, ina murmushi nayi, ina son nayi magana amma ya hana ni,"
"bayan ya gama ya riko ni zuwa parlourn. Kitchen ya shiga ya haɗa min fruit ya kawo min parlourn Umma tana kallonmu, wayarshi ce tayi ƙara ya ɗauka yana faɗin. ""Barka ds safiya Abba!"" Kallonshi nayi ina murmushi. Mika min wayar yayi, ""Barka da safiya Abba!"" ""Yawwa ya kike?"" ""Lafiya lau!"" Na fada ina jin shi, ""Hafiz yana son baki hakuri amma baya samun number!"" Kallon Turaki nayi gyad'a min kai yana murmushi.""Abba duk abinda zai fada ya kafada maka, ina haka yafi saboda ba dad'i idan shi ya fahimci"
"wani abu a tsakanina da Hafiz ko nice ba zan ji dadi."""
"""Eh haka ne shi yasa na fara kiranshi, don ina son ya san Hafiz Dan."" Daga can naji Yadiko tana faɗin."
"""Ba dai kashe mata aure zaka yi ba? Dan uwa aiko mahaifa daya suka haɗa dole kowa ya kama gabanshi, idan don ta yafe mishi ne ta yafe a kyaleta ta ji da kanta."" Daga haka muka yi sallama da shi, ina kallon yadda ya kafe ni da idanu. ""Waye ne shi?"" Yadda yayi maganar sai ya bani dariya, jan kumatunsa nayi na ce mishi. ""Kai mana!"" Na fada ina murmushi, jan kumatuna yayi haka muka cigaba da hira har na samu aka kira shi ya fita, wurin karfe daya bayan nayi sallah aka kira da wani number, ina dauka na ji muryan mace ce. Nayi mamaki bayan nayi shiru can na ce mata."" Ban gane ki ba."" ""Eh ba daki gane ni ba, dama nima na samu number ne a wani wuri."" Kashe wayar nayi don zan iya dura mata zagi, can ta kuma kirana."
"Dauka nayi ta ce min."" Ban san ki da wulakanci ba, ki yi hakuri Jalilah ce."""
""" Kina lafiya? "" "" Lafiya lau! "" Daga haka muka yi shiru bakiɗaya kowa ya rasa yadda zai ce, domin wani"
"irin nauyin da muka yiwa juna, can ta ce min."" Dama na kira na gaishe ki ne!"" ""Ok na gode!"" Na kashe wayar, ba zan mata da abinda tayi min ba, duk abinda Hafiz yayi min Jalilah tana da kaso a cikinsa."
"Wurin karfe biyar Daddah suka zo da Badr, sosai suka cika min gidan suna zuwa kowa kallon cikina"
"yaƙe. Ko minti goma basu yi ba sai gashi. Tunda ya shigo yake hararata, dariya ya bani haka ya zo ta zauna yana matsa min kafana suna Magana da Daddah jife-jife, har kusan awa guda kafin suka yi sallama, ni dai ban tab'a sanin mai ciki tana zama abin kallo ba sai a family kumo. Shi kansa dariya yake min idan ya ga yadda nake nuna ina tsoron abinda da yake faruwa. Ce min yake ba kome zasu dai ma don ba zai"
dauki renon hankali ba......
"[1/6, 8:28 PM] Maman Walid: 35"
"Haka muka yi ta fama, ranar wata laraba da yamma muna hira muka ji ihun Falilah. Sai da gabana ya fadi."
"Ina zaune a wurin Umma ta fita ta duba ashe har sun kaita asibiti. Haka ta dawo tana jajjanta abinda ya faru wai a bakin masu aikinta ta ji haka kawai ta fadi ba tare da kome ba. Ni dai rabona da ita tun wani zuwana awo na hango ta tare da matar Uncle Auta, ban Kuma ganinta ba, karfe shida matar Uncle Auta ta shigo suka gaisa da Umma ina kan abin sallah, ina jiran a kira sallah kawai nayi sallah, ta shigo tana shigowa kuwa ana kiran sallah, tashi nayi na gabatar sallah, sannan na cigaba da azkar, bayan na idar muka kara jajjanta abinda ya faru na Falilah shiru tayi kafin ta ce min. ""Kwanaki da Turaki ya kwanta, ta zo min da wani magana ta ce min ai idan ka duba yadda turaki yake rawan jiki akanki ba hakan kika barshi ba."" Kallonta nayi da kyau, kafin na ce mata. ""Ina ga kamar maganar nan bata da amfani anan ko?"" ""A'a yana da amfani dalilin da ya kawo ni kenan, ina son ki sani nayi kuskuren da na biye mata muka yi ne!"" Sanin cewa zan iya samun kaina da bakin ciki idan naji labarin sai na ce mata. ""Kin san me?"" Girgiza kai tayi, ""ki bar labarin nan na yafe maku, ku je wallahi na yafe."" Cike da mamaki take kallona. ""Baki san me muka yi miki ba amma kin yafe mana?"" ""Idan nasan me kuka min xan ta kallonku da shi har karshen rayuwarmu, amma idan na yafe ba tare da na sani ba zuciyata zata samu natsuwa babu wnada na rike ba wanda ya rike ni. Kuma har gaban Ubangiji ban kwana da kowa a raina ba."" Wannan maganar"
da bayi ta samar min da kwanciyar hankali.
"Kasa magana tayi don na hanata ta, Umma ta zubo mata abinci, taki ci. Bayan ta bar gidan na sauke"
"ajiyar zuciya. "" Kada ki sake damuwarsu ya taɓa lafiyar cikinki."""
""" In sha Allah! """
"Hmmm ashe tana kasa tana dabo, ita dai Jalilah abu ya ki na asibiti, dole aka wuce da ita Gombe, a can"
"ne aka yi ta wani irin rigima da gurmi fa, na farko aka ce kishiyarta tayi mata asiri, abin tausayi yarinyar nan haka suka d'agawa iyayenta hankali, dole ta shiga wani hali, aka yi ta fama."
"Sati daya da mai da ita Gombe, na tashi da ciwon nakuda. Cikin dare haka aka wuce da ni asibiti. Tun"
"karfe sha biyu muke abu daya har asuba gari ya waye. Ban haihu ba. Karfe tara na safe Umma tana waya da Mama ciwo ya taso gadan-gadan, dama ni da shi ne a dakin itama ta kawo min ruwan Lipton da sugar ne ta fita kenan tana faɗin. ""Wallahi har yanzu!"" Kawai sai jin kukan jariri tayi ta leko, ganin yadda haihuwar tazo a dakin da aka kwantar da ni kiran Nurse tayi ai kuwa sai gasu nan a tare lokaci guda na sauke mishi ƙatuwar diyarshi, jajjur da ita. Wani irin kallona yake domin bai zata zan haihu a yadda na ke din nan ba. Komawa nayi na kwanta aka gyara Yarinyar tas, sannan nima suka duba ni ko na karu babu"
kome.
"Karfe goma suka gyara dakin har yan gidansu sun fara zuwa kafin wani lokaci labarin ya karaɗe ko ina,"
"Ya Ado yana office aka gaya mishi ai kuwa sai gashi a asibitin. Har da Aunty Nuratu Kafaya da yarta Nasiba. Karfe biyar anan yayi musu. Daga ni har Babyn muna cikin koshin lafiya. Karfe shida na yamma aka sallame mu, muka dawo gidan duk da an yiwa yarinyar wanka acan muna shigowa Umma ta kwab'a lalle, tazargaje, ganyen magarya, ta mutsike yarinyar da shi. Ta lullube ta. Wurin karfe takwas bayan na fito wanka. Ta shigo da kayan wanka tayiwa yarinyar wanka tas, a lokacin wata budurwa da ban santa ba,"
"ta shigo dauke da tiren abincin. ""Sannu Aunty kin samu kai lafiya!"" ""Alhamdulillahi!"" Matar Ubaid a"
"bayan yarinyar suka shigo. ""Sannu Husnah!"" ""Sannu ashe kin sauka!"" Murmushi nayi mata yarinyar bata"
"da matsala kamar Falilah.""Alhamdulillahi!"" ""Nur ajiye mata taci Aunty ga abincin nan nayi miki da kaina, Allah yasa ki ci!"" Murmushi nayi na ce mata. ""Zanci kai!"" Umma da take gyara baby ta ce mata. ""Me zai hana!"" Bayan Umma ta gama kintsa Baby ta fitar da kome zuwa toilet sannan ta dawo da ta zuba min abinci, na fara ci a hankali. Ina jin wani irin dad'i yanzu na gane dalilin da Ubaid ya makalewa Yarinyar na daya gwana ce a wurin girki, domin kakar yarinyar tayi sana'ar tuwo-tuwo a gadar Lagos, na biyu yar"
gayu ce tsaf-tsaf da ita. Ga iya magana da salo. Dole na miji ya tare wurinta.
"Dama basu samu haka ba ma ya aka kare balle kuma sun samu ai magana ya ƙare, sai sha daya suka"
"tafi tayi ta kallon Yarinyar. Bayan tafiyarsu Umma ta ce min. ""Ba mamaki Mijinki ya zo nan domin na lura ba ruwansa da kunya idan yazo shi kenan idan bai zo ba ki kira ni!"" Gyada mata kai nayi na kwanta. Ina me addu'ar barci yarinyar nan sai barci take. Wurin sha daya ya shigo da katon leda, sai da ya kaiwa Umma sannan ya kawo min dakina. Kallona yayi lokacin da ya kunna wutar dakin. ""Sannu ko"" murmushi nayi, ya fita ya dauko plat ya juye min namar. ""Uncle Auta ya ce ana son kici!"" A hankali na fara ci shi kuma ya koma wurin Babyn. ""Kece kika haife ta?"" Gyad'a kai nayi, ya dauke ta yana sumbatar goshinta. ""Wani suna kike so a saka mata!"" ""Mammy!"" ""Sai dai ko Mama!"" ""Mammy sunanta Ummuna Aisha!"" Na fada ina kallon namar gabana. Ajiye Babyn yayi ya zo ya zauna a gefena. ""Thank you!"" Sai naji abin wani iri, a wani lokaci maza har wani isa suke nunawa akan Yaransu amma yau saboda nace ya saka sunan Mamanshi yake gode min, fita yayi ya hada min tea Mai kauri ya kawo min na fara sha a hankali, ina cin namar wurin sha biyu saura muka kwanta,. Muka sakata a tsakiyarmu, karfe biyu yarinyar nan ta ce garinta ya waye, daga ni

318 / 321

Chapters