Author : Mai Dambu Category : Complete Novels
ya wuce wurin da na ajiye yar ya dauke ta, yana faɗin. ""I miss you Mommy."" ""Nifa!"" ""Allah ya baki hakuri duk nayi miss dinku."" Ya rungume ni yana murmushi. Sai da naji ina ma rayuwarmu ya tsaya"
"haka kada wani ya shiga cikin rayuwarmu, kada wani ya hana mu farin ciki."
"""Muje kaci abinci, sai ta tafi sallah isha."" ""Bani tea na sha sai na fita, idan naci ba zan mori kaina ba!."""
"Haka kuwa aka yi na wuce na cigaba da hada mishi, sannan nan kawo mishi na zauna ina kallonshi, ya sha yana kallon yarshi. Yana gamawa ya ajiye ya nufi masallaci, nima nayi a gidan bayan na idar, na kara gyara jikina na sha zuma na, na gyara jikina da turare. Dakinsa na wuce na gyara dakin kayan da ya dawo da shi, na shiga cirewa. A hankali na gama sai dai me lipstick na samu ban tab'a ba. Na mai da kome wurin zamanshi da zan wuce na ga wayarshi tayi haske. Ban yi niyyar dubawa ba, na hango sunan Adaa. Komawa nayi na shiga duba wayar ya saka mata security code yaushe ya fara saka security code a wayarshi? Abin sai ya bani mamaki nayi ta kallon wayar hoton yarshi ce a kai, nayi kasa da kaina ina"
"mamaki. Kafin na sare ban kara magana ba, na ajiye na fita."
"Har ya dawo ya ci abinci, muna ta hira sama-sama. Tashi yayi ya shiga cikin dakin, bai fito ba nima"
"kuma ban yi wani yunkurin zuwa dakin ba, na wuce zuwa dakina na gyarawa Yarinyata wurin kwanciya, na kwanta barci ya dauke ni. Har zuwa sha biyu ko zai zo wallahi ban Ganshi ba, karshe na tashi na rufe kofar na kwanta ina kuka, sai wurin karfe daya da yaji kukan yarinyar ya zo yana buga kofar ban bude ba, haka ya gama buga kofar ya hakura. Washi gari tun asuban fari na mata wanka na bata nono, na fita na hada kome na ajiye mishi nasan ba zai fita ba, amma sai na zabi shiru na zuba mishi idanun, wurin karfe goma na safe ina barci ya shigo dakin, ganin ko ina tsaf-tsaf sai ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kwanta a baya, duminsa ne yasa na juya ina kallonshi. Ban wani damu ba amma zai san ya tab'a har mutanen"
Bauchi. Yadda nayi kuka shima haka zai koka...........
"[1/8, 7:41 PM] Maman Walid: Mikewa naso yi amma ya me da ni, kallonshi nake shima kallona yake."
"""Nayi miki wani abu ne?"" ""Me ka gani?"" Shiru yayi yana kallon yadda na haɗe rai na fara ƙoƙarin tashi ya mai da ni. ""Wai me ke damunki ne?"" A gajiye na ce mishi. ""Ban shirya wani haihuwar ba ne, kuma naga kai kana da damar karo wata macen ni dai oho!"" Tun a zamanmu na fahimci shi mutum ne da bai maka dole akan abinka, shiru yayi yana cike da mamaki, ko yayi tunanin yayi amfani da karfi ne, ai kuwa dai gashi ya saka min karfi na ce mishi. ""Don't try rape me!"" Yadda nayi maganar ya kara kokarin aiwatar da abinda nake hangowa a kwayar idanunsa. Cikin rawan murya na ce mishi. ""Ex dina bai taɓa using karfinsa a kaina ba, bai taɓa ba bai taɓa amma kai da yake kana da kudi kuma kana da kyau yan mata zasu iya bibiyarka har ka bibiye su, karewa har da lipstick a kayanka fine kayi yadda kake so da ni, kayi tunda godiyar da zaka min kenan a kwanakin haihuwar Yarka da take da daraja sama da kowa kayi min fyade kayi Bilal ka yi yadda kake so da ni!"" ""Ke wai meye matsalarki ne?"" Watsa mishi harara nayi na dauke kai, haka ya mike tare da cewa. ""Wai me nayi ne? Idan kuma akan abinda ya faru jiya ne sorry."" ""Sorry fa!"" Na fada tare da fashe da wani irin kuka har cikin raina, naji wannan kalmar sorry Sorry wannan kalmar ya min ciwo, kuka nake har Nana ta farka kuka nake itama kuka take, haka ya fita zuwa kitchen ya dauko nonon da muke tarawa, ya dawo ya zo ya saka a abin dumama mata, yana yi yana"
"kallon yadda nake kuka, wayarshi da take kusa da ni tayi ƙara naga Adaa, sake kallonshi nayi wani irin"
"baƙin ciki. Dauka yayi saura kiris ya sake min yarinya ta fadi na fasa ihu. Ina cewa."" Bani y'ata"
"womanizer"" shiru yayi yana kallon yadda nima maganar tayi affects dina balle shi da na gayawa, na kuma saka hannu na amshi yarinyata. ""Ka je wurin budurwa wacce take da abinda bani da shi, ka je ita babu abinda ya ragu a tare da ita, tana da kome full options, ka je bata haihu tayi bellypot ba, ka je bata bude kamar ni ba ka je bana son ganinka, kuma ka sani tafiya zan yi gidanmu wallahi ba zan iya zama da kai ka kashe ni da yata ba."" Tunda na fara maganar har na kai karshe bai ce min yi hakuri ba, bai tanka min ba bai kuma ji a ransa ko a fuskarshi abinda nake ya b'ata mishi rai ba, duk fadar da nake kallona yake, karewa abinda yayi min ya saka ni frozen shine tab'a goshina da wuyana, sai kaina jin babu inda yayi zafi, sai ya rungume ni tare da Yar. ""Baki fita kaina da zan fara hango wata mace ba, na gode sosai da kika nuna min kishina, ban tab'a zatan zan ga kishina a ƙwayar idanunki haka ba."" Wani irin kuka ne ya kara kwace min na ce mishi.""Fita min a dakina!"" Na nuna mishi hanya, a hankali ya nufi hanyar fita, kusan wannan yayi breaking duk wani zaman lafiyan gidana, duk yadda yaso na zaffafa shima ya tattara"
lamarin ya zuba min idanu. Nima haka da yayi sai ya kara tunzura ni. Na kara jin zafinsa.
"Muna cikin wannan yanayin, ranar da muka cika sati daya da tashin hankalin. Yadiko tazo nayi ƙoƙarin"
"boye kome, amma da yake wanda ya haife ka, ya fika wayon duniya sai da ta yi magana domin na zube sosai saboda rashin barci da b'acin rai, tayi ta tambayata ko da wani abu ne nace mata azumi nake kawai na bar zancen, haka ta wuni domin washi gari zata koma gida, sai da zata tafi ne na fara kuka ni kawai zan bita, haka da nayi yasa ta fahimtar akwai abinda nake boyewa, haka tayi ta kallona ta ce ko da wani abu ne nace mata Babu kawai zan bita gida ne. ""Ki yi hakuri nan da kwana ashirin zai kawo ku, lokacin Nana tayi wata biyu kenan!"" Wannan maganar da ta gaya min kamar na mutu, domin nasan ba zai kai ni gidan ba, haka nayi ta kuka har ta tafi. Shima da yake baya dawowa Sai wurin karfe sha biyu saura, haka ya same ni a parlourn ni da Nana na sha kuka har na godewa Allah, tunda ya shigo yaji ajiyar zuciya na a kai a kai, har ya wuce ya dawo ya ajiye jakarshi ya zauna bayan ya kunna wutar parlourn, idanuna ne ya sauka akan kwalar rigarshi shatin jan bakin mace, ""Lubnah!"" Tashi nayi na bar shi a wurin, ina shiga dakina ns rufe kofar dakin ban kara kula shi ba, na yanke duk wata hanyar da zai samu damar min"
magana.
Washi gari.
"Wurin karfe biyu na rana Hajiya Zeenatu suka zo ita da wasu mata sai wata very pretty lady, fara ce tas"
"har kana hango koren jijiyar jikinta, tunda suka zo Hajiya Zeenatu take min murmushi, kallonta nayi a hankali na gaishe ta kafin na shiga kawo musu kayan tab'awa. Hango karfen da nake motsa jiki yarinyar tayi ta ce min. ""Na ki ne ko na, Sir Turaki?"" ""Both!"" Na fada ina kallonta, murmushi tayi tana magana da yarbanci. ""Au da gaske ya saya miki irinsa, ai na gaya miki."" Kawai sai naji kirjina tayi nauyi. Sai nayi kamar ban ji su ba, can yarinyar ya ce min. ""Ina Yata?"" Kallon gadon kwanciyar yarinyar da muka saka a parlourn nayi ta nufi wurin tana faɗin. ""Alaja kin san da ni ce uwar Yarinyar nan!"" Yanzu na fahimci abin sarai, na kuma kara hango abinda take nufi, sai na sarke hannuna a kirjina ina kallonsu. ""Wannan ita ce"
"Adaa yarinyar da Turaki yaso ya aura!"" Murmushi nayi na ce musu. ""Ina ta shiga na mata overtaken?"""
"Na fada bayan na gyara zaman da nayi akan kujera. ""Kamar ya? Bai gaya miki labarinta ba ne?"" Inji"
"Hajiya Zeenatu, ""bai gaya min ba saboda ba ta da muhimmanci a rayuwarsa, da tana da shi da ba zai manta da ita ba,sannan da kowa yasan da zamanta."" Yadda nayi maganar ina murmushi, ta ce min. ""Yanzu ai ta dawo mai wuri tazo."" ""Hajiya ni sai nake ganin kamar kishin da kike da Uwar Bilal ne ya dawo kaina, domin dai na ga Bilal dan tsohon mijinki ne, sannan uwarsa ta tsamo ki daga duhun talauci ta kawo ki cikin hasken arzikin, yanzu babu ita babu wanda ya baki damar shiga kumo ni Lubabatu ina ruwa da ke? Ban ga dalilin da zai saka ki shigo min rayuwar gidana ba. Idan kuwa kuka ce zaki shiga rayuwata, zan takura miki zan kure miki gudu zan tabbatar kowa yasan yadda kika dame ni, ita wacce kika janyota gidana idan naso sai na rufe ku na watsa muku ruwan zafi, wannan fatar da take nunawa mijina, sai na kara toyashi yadda zata cigaba da bibiyar lamarin Mijina, Hajiya focus matsalarki ki fita hanyata da gidana, turaki bai shirya auren wata ba, idan mijina ya shirya auren wata ni da kaina zan"
"tsaya mishi domin nasan ya shirya. """
"Dariya tayi ta ce min."" Yarinya kenan, ni da ke shege kafasa, Allah ya baki sa'a. Ita wannan yarinyar"
"Uwarsa ce ta nime mishi aurenta, kuma akwai document na yarjejeniyar haka, aure zai yi domin nice a tsakiyar."""
"""Hajiya kenan Allah ya baki sa'a, ya kuma bamu lafiya da nisan kwana. """
"Daga haka suka nufi hanya yarinyar ta ce min. "" Da alamu baki ga sakona ba ko?"" Murmushi nayi na ce"
"mata. ""Ba mamaki ni nawa sakon zai zo lokacin da ya dace."""
"Daga suka fita, raina a idan yayi dubu ya b'aci."
---
""" Alaja ni fa ba zan iya ba, Yarinyar nan tsoro take bani kin ga confidence da na hango a cikin idanunta?"""
"Murmushi Hajiya Zeenatu tayi ita fa dole yadda tayi a gidan Uban turaki da Mijinta Alhaji Mudansir take so tayi a gidan Turaki, ta ce mata. ""Kwantar da hankalinki, duk abinda take fada karya ne, waye bai san yadda ta samu Turakin ba, asalin asiri suka mishi. Idan har su bokonsu kasa yake bugawa zan nuna mata nawa akan dutse yake."" Ita kan Adaa sai ta shiga damuwa domin kuwa bata son tashin hankalin da zai"
dagulawa ranta.
***
"Bayan tafiyarsu na rasa yadda zan yi. Ko yan uwana bana son su san halin da nake ciki, don haka na kira"
"Mama. Cikin kuka nace mata. ""Mama Turaki!"" Shiru tayi kafin ta ce min. ""Ki dawo gida to! "" Shiru nayi"
"kafin na ce mata. ""Ba fada muka yi ba, asalima narasa yadda xan yi ne?"" Murmushi tayi, ta ce min."" Gaya min me ya haɗa ku?"" "" Mace yake kulawa."" "" Kina sonshi?"" Cikin shashekar kuka na ce mata. "" Mama"
"shine mahaifin Nana A'ishah Boɗɗo, shine ya so ni tun ban san ciwon kaina ba!"" Murmushi tayi ta ce min."
""" Good to me kike so? Gaya min me ya faru?"" A hankali nake gaya mata abinda yake faruwa, shiru tayi kafin ta ce min.. ""Lubnah!"" ""Na'am Mamana!"" ""Mijinki ya shiga tarkon matar ubansa duba da yadda ta kawo miki yarinyar gidan. Mijinki babu wata mace a gabanshi. Domin ko juma'a da ta wuce yazo Bauchi. Kuma ya zo har gidan nan, abu daya nake son na gaya miki, Mijinki yana sonki yana girmamaki, kada damuwar wasu ta dame ki, sannan ita uwar Mijinki, zan gaya miki abinda zaki mata, amma ki nutsu da kyau. Ba mamaki mijinta bai san me take yi ba, idan kina son nasara akan mutane kaima tunaninka kake budewa sai ka tafi da daidai da kai, kishiya take so a miki. Mijinta Uban Mijinki ne ke kuma yarsa duba da yadda suka dawo jikin Mijinki, sai ki san hikima da dabara. Ba a ciwon mummuni sau biyu a wuri daya don haka ba zan kara barin wani ya cutar da ke a gidan aurenki ba."" Cikin shashekar kuka na ce mata. "" Mama to ya zan yi? Matar nan shaidaniya ce, na rasa yadda zan yi da ita!"" "" Ki hada da azumi zan miki sadaka anan, in sha Allah zata barki miji ai naki ne, idan Turaki ya tashi aure ko kina so ko bakya so mune nashi kuma zamu tsaya mishi, amma yanzu lokacinki ne da Yaranki ku samu soyayyarshi da kaunarshi, shine babban abinda nake nufi da fata, sannan kin san ni bana bin boka ko Malam Allah nake bi tare da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, don haka ki cigaba da addu'a mu nime tsarin Allah akan duk wani mai sharri!"" Sai naji kamar nafi kowa dace a duniya da na samu Mama a matsayin Uwata, ta tsaya min ta kuma sa na daina kuka. Wani abun da ya kara bani mamaki yadda ya iya zuwa Bauchi bai gaya min ba, sannan kuma bai kamata karana ba, asalima abin da yake gabanshi yayi sai na ji"
tausayinsa............
"[1/12, 1:52 PM] Maman Walid: 39"
"Bai kai karata ba, sannan bai nuna min ya damu da abinda nake yi ba, asalin adalci Yayi min domin ni dai"
"ba san yadda zan yi da abin kunya ba, haka yasa nayi shiru ina sauraren Mama. Har ta gama min bayani sannan muka yi sallama, bayan isha da ya dawo ina kwance a dakina ya leko zai fita da gaggawar. ""Zaka tafi wurin Adaa?"" Cak ya tsaya yana kallona. ""Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya."" Shigowa Yayi min a zauna zai dauki yar nayi maza na kwace Y'ata. ""Me yasa kike min haka? Ni ma fa y'ata ce, sai ki hana ni daukarta idan na zauna bakya kula ni gaya min me nayi miki da zafi?"" Hawaye ne ya zubo min na ce mishi. ""Ka damu ne da mu? Ai dmuwarka yana kan Adaa."" ""Ki tsaya mu yi maganar gaskiya."" ""Wani irin maganar gaskiya bayan na samu jan bakinta a cikin kayanka, na biyu na ga sakonta yadda ka mata a daren da kuke tare na ga layin jan bakinta a jikin rigarka, sannan ta zo gidan nan ita da Matar Kaduna tsohuwar Step mother dinka me ya rage da ban gaya maka ba? Akwai ko babu? Duk abinda na gani shima ba hujja ba ne? Zaka iya amfani da ita amma ka sani ni da kai Y'a mace muka haifa ka rufa min asiri kada a lalata min y'a wallahi ban tab'a zina. "" Ya dauke ni da mari wanda ya janyo nayi shiru tare"
"da rike fuskana. ""Marina ka yi?"" Na tambaye shi, ina kallonshi hawaye na zuba min daga idanuna. ""Na"
"cancanci kyautar mari daga gare ka?"""
"Kura min idanun yayi idanunsa sun yi jajjur, tashi yayi ya bar gidan bakiɗaya na sha kuka, kamar ya"
"bana son na kira Ya Ado domin zan d'aga mishi hankali a daren na sayi ticket na Jos, kamar ya san abinda nake shiryawa, da safe sai gashi tare da Kakanshi, suka shigo na gaishe su. Na koma dakin na dauko musu yar da na gama shiryata na mikawa Kakar ita, sannan na koma dakin na cigaba da hada kayana na fito da su waje, na ajiye. "" Y'ata ina zagi da wannan kayan?"" ""Baffa gidanmu zan tafi"" shiru yayi kafin ya"
"ce min. ""Gaya min me suka miki shi da su?"" Ai kuwa na fara kuka, na rasa yadda zan mishi bayanin"
"wulakancin da yake, ganin har lokacin kukan ya ki karewa Ya ce mishi. ""Allah sai ya bi mata hakkinta,"
"domin ka zalunce ta sosai."" Yadda yake mishi fada ba nan yake fita ba, har da cewa. ""Ban da ita wacece zata zauna da kai tsakaninta da Allah ba tare da ta tuna cewa kai wani ne, tayi maka alfarmar zama da kai har da haifa maka zinariya me yasa zaka wulakantata?"" ""Datti rashin kunya take min wallahi ban mare ta don bana sonta ba, ranar ta kira ni manemin mata jiya kuma tana ƙoƙarin kirana da maxinaci kawai don ta samu wani abu da tabbatar mata muna tare Adaa!"" ""Ban rabaka da yarinyar nan ba?"" ""Amma Datti!"" ""And so what? Abubuwan da kake yi yasa take zarginka, ai nima ba yau na ce ka rabu da ita ba nayi karya? Bari ka ji idan ka sake ta bar nan ta je har gidan dan uwanta ko iyayenta wallahi ba zan je biko ba. Kuma ba zan tab'a shiga lamarinka ba, ba ruwana da kai, wallahi xan gayawa Kakarka. "" ""Datti don Allah kayi hakuri!"" "" Ita zaka bawa hakuri domin ita ka cutar matarka ta rufin asiri babu wanda ta kaiwa kukan kayi mata laifi bs kasan ana jiran a ga ta kuma kuka akanka ba ne a ce damar ba sonta kake ba."" Sai naji bawan Allah nan ya biya ni, cikin shashekar kuka na kara kai min kukan na ce mishi."" Baffa Mommy Zeenatu ta ce matuƙar tana raye sai ta aura mishi Adaa ni ba auren ne bana so ba, a zo a raba da Y'ata, ni na yafe mishi duk abinda yayi min Daada mutumin kirki ne, kawai ya je yaji auren shi ni ban damu ba kuma ban yi bakin ciki ba, abubuwan da yake yi kada wata rana a cutar min da ita tunda har gidanta yana zuwa da sunan soyayya duk anan suka gaya min. Kayi hakuri Alhaji amma lokaci yayi da dole na hakura da zama da shi."" "" Ita Zeenatu ta ce miki zai auri yarinyar ko? "" ""Eh tace akwai baiko da Mahaifiyarshi ta tabbatar za a yi aurenshi. Allah ya basu zaman lafiya gara na tafi wurin Iyayena sun fi kaunata ba xan zauna bakin ciki ya kashe