Advertisements
Chapter 308 Reading ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu

Author :  Mai Dambu Category :  Complete Novels

Chapter   308 / 321

921K to 924K   out of 962.4K words

kin bashi hadin kai ko? Tow wallahi ba wani ɗoukin da zai yi akanki."" Tura baki nayi ina faɗin. ""Wallahi ba abinda muka yi barci kawai yayi fa!"" Na fada ina jin haushi ko me na bashi ai hakkinsa ne, tun da muka dawo take fada, kamar nayi wani zunubi, bayan sun tafi Aunty Mom ta bani wasu abubuwan har da tarkacen mata irin na turawa, muna nan zaune da ita har suka dawo da yake har da Matar Ubaid da Uncle Auta, ana ta hira sama-sama, na lura matar Ubaid tana jin kanta ita wata shegiya ce, nima na nuna mata ni iyaka ce, suna shigowa kai tsaye wurina ya nufo ya cire min mayafin yana faɗin.. ""zaki cutar fa fatarki da wannan uwar bargon wanda ko ita Momma bata isa yafa wannan abin ba."" Ya wurga da shi can kasa ya maza ya duba kafana da yake muna dawowa na goce da kafar, yana d'agawa yaga yayi ja. Rike baki yayi tare da dama a"
"kujeran ba juyawa Kanwar Uwarsa baya yana faɗin. ""Yanzu kin san kafar tayi haka shi ne baki kira ni kin"
"d'aga min hankali ba, Innalillahi wainnalihir rajoun, wannan wacce irin masifa ce da tayi min asarar daren"
"amaarci."" Zuba mishi duka Kanwar Mamarsa tayi tana faɗin.. ""kai dai baka da mutunci sai ka san yadda zaka yi da kafar."" Wallahi tsakaninsa da Allah ya kore kowa a gidan. Ya kuma nace sai ya cire gocewar."
""" Yanzu Lunah hakuri zaki yi na cire wannan abin domin wallahi ba zai hana ni sakat ba.""zare idanun nayi"
"na ce mishi."""" Ban isa ba wallahi ba zaka cire min masifa ba, ina zaman lafiya. "" Ai kuwa ya dauki wayarshi ya dokawa Kakanshi kira akan akan me zai shirya taron da na goce. Kafin wani lokaci tsofaffin nan sun iso gidan, ba sai gashi Uncle Auta ya dawo ba aka je a daren aka dauko me gyaran karaya, yayi tsalle ya tuma ya ce musu.. ""Malam gayan mun yadda ake cirewa amma ba zaka taba min matata ba!"" Sai da Uncle Auta ya ce mishi.. ""ka rungume ta domin idan kai ne waye zai rungume ta, haba don Allah."" Gyada kai yayi yana dawowa kusa da ni ya zauna, tare da rungume ni mutumin ya kama kafar ya latsa da"
kyau kafin ya ja wallahi ban san lokacin da na gantsara mishi cizo ba..........
"[12/17/2025, 7:29 PM] Maman Walid: 19"
"Shafa bayana tare da ce min. ""Shiiiiii!"" Sake fatar nayi tare da cewa. ""Don Allah ka ce ya bari na huta don"
"Allah ka gaya mishi ya bari na huta;"" ""Sake kafar ta huta!"" Ya fada yana bubuga bayana, ""sannu."" ""Boy dare yayi fa saura minti hamsin a kira sallah farko kai da matarka kun hana mu barci wallahi!"" ""Look at my eyes bari ya ja!"" Zare idanun nayi zan girgiza mishi kai, ya saka kaina a kafad'arshi, yana buga bayana, mutumin na jan kafar na fisge kaina zan yi ihu ya cilla min wani sweet a bakina na fashe da wani irin kuka. Tare da rungume shi. Kuka nake yana shafa kaina. Har aka gama jan kafar ina kuka, Daddah tayi ta min"
"sannu, anan barcin wahala yayi gaba da ni."
Haka suka watse a gidan kowa yana tausaya min. Cak na ji kamar ina yawo a iska na bude idanu me
"cike da barci na kalle shi, murmushi yayi min sannan ya ce min. ""Yi barcinki, my chest is your special bed, don haka rufe idanunki."" Ya fada yana tafiya a hankali har dakinshi, ya kwantar da ni a hankali, ajiyar zuciya na sauke ya shiga ban daki yayi wanka da alwala sannan ya fito, ya ja min bargo yayi sallah. Kafin ya kwanta. Sai da yayi sallah nafilla kafin ya ɗan kishingida, yana addu'a gyangyadi yana fisgar shi ya ɗan kwanta. Ai kuwa barci ya dauke shi, sai jin shigar sallah yayi da sauri ya shiga yayi alwala ta nufi masallaci, bai fito ba sai da garin ya fara haske. A hanya ya hadu da Kawunsa da Mijin Goggonsa kallo daya ya musu ya shiga shafa gemunsa cikin murmushi irin na tantiran yan duniya, ya d'aga musu gira irin tow ya nima haka nake, don iskanci goya hannu yayi a baya ya cigaba da tafiya yana murmushi. Tabbas yana shiga musi hanci da kudundune. Yasan su ne suka shirya aka dawo da shi gidan don haka sai ya fitine su da rashin kunya da rashin mutunci yadda da kafarsu, zasu zo su ce ya bar musu gidan. Duk yadda aka tsara ya sani amma yafi son su fuskanci guilty din tare da shi, yadda suka yi amfani da damarsu. Sai da ya isa"
kofar gidansa ya fara wani iyayi irin na zumudin sabon ango.
"Ai ko da ya shiga cikin gidan, dakinsa ya wuce ya samu tana barci abin ya burge shi, amma ya zauna a"
"bakin gadon yana wani murmushi yana jin wani irin dad'i da nutsuwa. Kayi mafarkin kai Gwauro ne ba karamin masifa ba ce, shafa kaina yayi sau biyu na bude idanuna. Da suke cike da barci a hankali ya ce min. ""Good Morning Queen!"" Murmushi nayi na tashi zaune kafin na ce mishi. ""Kayi hakuri ban yi sallah ba."" Na dauko a hankali na daura kafar a kasa, sai naji babu zafin sosai zan mike naji ya janyo ni, sumbatar goshina yayi yana faɗin. ""Kin yi kyau!"" Murmushi nayi na kara mikewa, ya dawo da ni na zauna ina kallonshi. ""Lokaci yana kurewa!"" ""Ok muje na raka ko!"". Ya fada na mike a hankali, zai dauke ni na ce mishi. ""Don haka ka yi hakuri wallahi xan tafi da kaina."" Murmushi yayi ya ce min. ""Nayiwa Mama alƙawarin kula da autarta!"" Haka ya dauke ni har ban daki. ""Ni dai ka fita xan iya kome da kaina."" ""Tow!"" Ya fita ni kuwa nayi wanka da alwala a gurguje, na fito nayi sallah. Ina idarwa ya shigo da mug na tea, mika min daya yayi ya ajiye na shi ta fita can sai ga shi da Pjym riga da wando ya mika min."" Kwanta muyi barci!"" Kallon kayan nayi sai kuma na amsa na nufi ban daki na saka, ina fitowa ya zubawa kofar ban dakin idanun kuri, kunya ce ta rufe ni na saka hannu bibbiyu na rufe fuskana. Tasowa yayi ya balle gaban"
"rigar yana murmushi ya ce min ""haka nake son ganinki!"" Ya janyo ni zuwa bakin gadon ya zaunar da ni."
"Yana sonta yana kaunarta amma baya son ta ga kamar don jikinta, baya son ta ga kamar bai da hakuri"
"akanta. Ko dama can yana kwadayinta ne. Zama ya kara yi ya daura kafa daya akan ɗaya, ya janyo ni jikinshi. Haka yasa na daura kaina a kafad'arshi. Murmushi yayi. ""Na jima ina addu'ar wannan ranar, yau ni ne Matata ta daura kanta a kafadana! Alhamdulillahi alakulli halin."" Ya furta yana murmushi, ina gama sha ya amshi kofin ya fita da shi, can ya dawo ya kashe wutar dakin, sannan ya zo ya riko hannuna muka kwanta. Janyo ni yayi kan pillow shi, ya kuma ja bargo ya rufe mu, ya ce min. ""Ki yi barci domin nima barci zan yi!"" Daga haka na sauke ajiyar zuciya, ""ki yi barci hankalinki kwance domin kina tare da Mijinki ne."" Gyara kwanciya zan yi ya gyara min tare da daura kaina a kirjinsa. ""This is your place, wurin naki ne ke ɗaya!"" A hankali ya cigaba da shafa bayana, tun ina jin wani irin yanayi har barci yayi gaba da ni, sosai wunin ranar muka yi barci, da alamu kowa ma yasan cewa muna hutuwa, karfe daya na rana muka tashi saboda yadda ake buga kofar gidan daga waje, sake lumshe idanuna nayi na bude a hankali, zame jikina nayi daga nashi na nufi ban daki fitsari nayi sannan na wuce waje bayan na saka doguwar hijab har kasa, bude kofar nayi yan matan nan ne, na zuba musu idanu. Ban ce musu kalla ba, sai jin shi nayi ya rungume ni ta baya.""uban me kuka zo yi?"" Hannunsa ya sakalo shi ta kan cikina. Daura nawa hannun nayi akan nashi. ""Maybe sun zo ganin wuri ne, su shigo mana!"" Na fada ina juyawa cikin gidan. ""Before na je na dawo na ga wata Yarinya sai na mata rashin mutunci."" Ya fada tare da banke kofar, ai kuwa bamm kofar tayi kara. Wato shi dai kome na shi daban ne. Kitchen na nufa ya biyo ni, cire hijab din yayi yana faɗin. ""Yanzu da zance mu yi wanka!"" Rufe mishi baki nayi da hannuna ya shiga sumbatar hannun na kwace ina faɗin. ""Me yasa baka jin nauyi ne?"" Kallon sama yayi kafin ya kalli gefe da gefe yana niman wani abu can ya ce min. ""Nauyin wa zanji? Naki?"" Ya nuna ni da yatsa sai kuma ya janyo ni yana faɗin. ""Gaya min yadda ake jin kunya sai na fara akanki?"" Na jima ban ga tantiri irin wannan mutumin ba. ""Ina wayata take ne ma? Na ji su Aunty Innah zasu shigo ne?"" ""Eh kai zasu shigo da karfe biyar na yamma."" Sake baki nayi na ce mishi. ""Au kasan da haka daman?"" Na tambaye shi, jingina yayi da wall din kitchen din, yana faɗin. ""Eh kai na sani hala sai kuma ki yi kuka?"" Ya fada yana jan hannuna zuwa waje dakin da"
"nake tsammanin shine nawa ya kai ni, ya ce min."" Ki yi wanka ga Ni nan zuwa."""
"Ban daki na wuce nayi wanka da alwala, sannan na fito ina daure da towel, shigowa yayi sai kuma ya"
"juya ganin nima na diririce, ai kuwa yana fita na yi maza na saka kayana, sannan na fito na same shi yana tsaye, murmushi yayi min ya ce. ""Muje mu yi sallah."" Haka na bishi har dakinsa, muka yi sallah. A lokacin yunwa ya dame ni. Riko hannuna yayi muka bar gidan bayan na koma dakin na gyara fuskana, hannuna cikin nashi muka isa har gidan kakanshi, tun da muka shiga ake min sannu har na samu wuri na zauna ina gaishe su, abinci aka kawo mana na ji yana ta fulatanci, ai kuwa Daddah ta rufe shi da fada aka shiga kawo min abinci, kafin wani lokaci an cika min gabana da abin karyawa. ""Kayi hakuri Turaki bata jin magana ashe haka ya barka da yunwa har yanzu."" Murmushi nayi ina kallonshi, hada min abin karyawa yayi ya mika min tea din na fara sha, da zafi na ajiye mishi ina hura bakina. Dauka yayi yana d'aga min har yayi huce na dauka na fara sha ina murmushi. ""Sha Chika!"" Haka na karya shima ya ci kaɗan, kusan sai da naci na bar mishi sannan ya ci. Ganin yadda na zaɓi wasu abubuwan wasu kuma na bari ya sake murmushi yana faɗin "" kina loss weight ko?"" Ci yayi yana faɗin ""cigaba da rage kiba, kin ga ni na ci Abinda kika bari ina laifi."" Haka muka gama sannan aka kwashe ya riko hannuna muka tafi dakin da Kakarshi ta wurin Uwa take, ina shiga ta rungume ni tana faɗin. ""Labubu kin ji sauki kenan?"" Gyada mata kai nayi ya ce mata. ""Granny meye matsalarki da ni yanzu bayan na yi aure kina min kallon banza ko kishi kike ne don nake na yi ba?"" ""Allah ya rufa min asiri."" Ta fada tana buga mishi sanda ya kauce yana dariya sannan ya fita ya barmu a dakin, mun sha hira da ita kafin ta ke gaya min ""an jima zamu koma gida ma yaushe zaki zo mana!"" Murmushi nayi na ce mata ""Sai ya kawo ni!"" Haka muka yi ta hira jife-jife har na tayata hada kayanta, ta dauko kudi me yawa ta bani, nayi ta Godiya. Shigowa yayi ya ce mata. ""Ki fito gashi an zo ɗaukarki!"" Ai kuwa na rakota zuwa waje, a lokacin suke gaisawa da sauran mutanen gidan, haka ya rakata har wurin motar ta kira ni. A hankali na isa wurinta na tsaya, riko hannuna tayi ta saka min abu a cikin hannuna. "" Ki kula da Mijinki da kyau, ki kuma kula da kanki."" Ta rike hannuna alamar tana bani abu me muhimmanci, sannan ta sake hannuna yazo gefena ya rufe mata kofa yana faɗin. ""Granny yarinyar nan ta kwace min ke!"" Murmushi tayi tana faɗin. ""Ka taimake ni ka rike musu yar mutane!"" ""In sha Allah!"" Ya fada, bayan ya ja hannuna baya, suka tashi motar suka bar gidan, yana d'aga musu hannu. Sannan ya mai da ni can parlourn Alhaji ELYakub Kumo, muka zauna a rough carpet din parlourn, mika min wani album yana faɗin. ""Wannan hoton zuriarki ne!"" Amsa Yayi ya mika min, a hankali na fara bude shafi zuwa shafi. Hoton Babanshi ne na farko ya matso kusa da ni. ""Wannan shine Papa!"" Juyawa nayi ina kallonshi. ""Kuna kama!"" Bakin shi na ji a kan hancina. ""Sosai kai!"" Ya fada bayan ya sumbaci hanci. Sosai ya matso kusa da ni, kamar zai boye ni a jikinsa. Wani hoto na bude, hoton"
"Mamanshi ce. "" Mammy ko?"" "" Ya aka yi kika san Mammy nake kiranta?"" Ya fada yana sumbatar kuncina. "" Bari mana Chairman yana nan fa?"" ""Tuni ua gudu parlourn wurin Matarshi."" Da mamaki na kalli wurin da yake babu alamar shi. Gira ya d'aga min. ""Ai na gaya miki, ni lamarina mai karfi ne!"" Tura baki nayi, yayi maza ya rike bakin da yatsarsa guda biyu. ""I like this lips!"" Ya fada yana sakewa. ""Kika kara tura min baki sai na ciza!"" Hoton bikinsu ba buɗe. ""Lokacin ina zero kafin na zama plus."" Shi dai bai da kunya ya more, ture shi nayi ina hararansa. ""Me yasa kake da matsala?"" ""Saboda ni ne gidan haya!"" Murmushi nayi ya kai hannunsa yana tab'a ni, ""don Allah kada ka hanani kallon!"" Ihun da muka jiyo a waje yasa muka kalli juna sannan muka kalli kofar, Badriyyah ce sanye da wasu kananan kaya a jikinta. ""Idan ka ce ba zaka aure ni ba it's ok, but ka auri wannan karuwan yafi kome disguise a cikin wannan Familyn wallahi sai na kashe ka na kashe ta, sannan na kashe kaina. "" Ya fada tana nuna mu da wuka. Mikawa yayi ya nufe ta, ta fasa ihu tana faɗin. "" Kada ka matso kusada ni"" ta fada da karfi zata yanka hannuna, kafin ta"
"d'ago daga kallon inda ya dace ta yanka ya rike hannunta. "" I don't care idan kika min wani abu, kuskuren"
"da kika yi shine involved din Matar turaki cikin lamarin shine kuskurenki!"" kwaɗa mata mari sai da ta"
"sake fitsari, ai wannan katakon hannun nashi nasan za ayi haka.........."
"[12/18/2025, 3:54 PM] Maman Walid: 20"
""" Bilal kashe ta zaka yi?"" Inji Uwarta, ta fada da hargowa. Bawan Allah nan ya shafawa idanunsa toka"
"yana faɗin. "" Kika sake riko wani abu da sunan matata don ubanki sai na binne ki da ranki ina wasa da ke? Mara kunya ni nayi maka da wadancan sakarkarun da suke bin ki ne? Na kara ganinki da sunan kin zo gidana ko wurin Matata da sunan hauka sai na rufe tarihinki!"" Ya hankad'a ta can, t faɗi tana kuka."
"Kallon Uwarta yayi ya ce mata. ""Ba ita ba ke kanki, ki fita idanuna wallahi idan wani abu ya samu matata sai na baku mamaki."" Ya dawo inda nake ya zauna ya barsu da bakin ciki kallonshi nayi ya sake murmushi. ""Yi kallonki kin ji ai namiji na gefenki babu karen da ya isa ya miki haushi na kyale shi."" Ya fada yana rike min habba na. Sai da suka fita ya ce min. ""Lubabatu?!"" Na sha mamaki da ya kira sunana domin bai taɓa yin haka ba. "" Dangina ne, kada ki rena min su. Zan yi iyakar kokarina na ga sun miki adalci. Tun ina yaro na taso bama shiri da su, sai Uncle Auta."" Murmushi yayi ya kwanta tare da daura kanshi a cinyata yana faɗin. ""Ina kewar Mammy sosai!"" ""Papa fa?"" ""Not yet!"" Kallonshi nayi na tuna abinda Granny ta gaya min, wato ba iya fusata yake da kowa hatta mahaifinsa bai bari ba, Innalillahi wainnalihir rajoun, wallahi sai naji ya ban tausayi. ""Papa ya bata abubuwa dayawa."" ""Bai bani ba, ya bani ya kwace je betrayal me."" Sai na rasa bakin magana, nayi shiru lokacin da aurena ya mutu Abba fushi yayi da ni ya kuma zare hannunsa a kaina, a lokacin ni kaɗai nasan yadda nake rayuwa. Ganina ake but ina matukar shiga damuwa. Dakyar ya fara amsa gaisuwar da nake mishi. Shafa kanshi nayi na ce mishi. ""Ba kyau fushi da iyaye! Kowani irin Yanayi zaka tsinci kanka kada kayi fushi da su, ba ina son na ce kayi hakuri ba ne, amma ina son na tuna maka hakkinsu akanka ne. "" Wato akwai wani abu da na fahimta a rayuwa ba zuwa Islamiyya ka haddace kur'ani ake buƙata ba, yaro ya san waye Allah da hakkin Allah shine ake bukata, sannan yasan soyayyar Allah da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, kafin ahalul Baitu da"
"Sahabbai, har zuwa kan iyaye. Mafi kololuwar daraja na wannan matakai uku ne, kafin zuwa ga Iyaye."
"Shafa kanshi nayi ina jin tausayinsa har cikin raina, duk yadda aka yi yana da trauma akan Iyayensa."
"Hawaye ne ya shiga zubowa daga idanuna yana d'iga akan fuskarshi. ""Me kuma aka yi?"" ""Ba kyau fushi da iyaye!"" Cike da mamaki yake kallona bayan ya tashi zaune. ""Me ya kai ki personal life dina?"" Rike hannunsa nayi, kuka na saka mishi.. ""ka janye fushinka akan Mahaifinka ba haka yake bukata ba!"" Zuba min idanu yayi ina iya hango yadda fuskarshi tayi ja. ""Ke idan aka miki haka zaki ji dadi? Ko da yake kema ai kin yi min karya na rashin gaya min baki da aure me yasa rayuwarku take cike da karerayi ne?"" Kallonshi nake na kai hannu zan rike shi ta kwace hannun. ""Na gaya miki gaskiya, kada ki kara tab'a ni!"
"Kannena uku da mahaifiyata hudu suka mutu bai iya kiran Makarantar ya gaya min ba, ya boye min haka bai ishe shi ba sai

308 / 321

Chapters