Advertisements
Chapter 299 Reading ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu

Author :  Mai Dambu Category :  Complete Novels

Chapter   299 / 321

894K to 897K   out of 962.4K words

ba, ni nayi mamaki me yasa Hafiz yaƙi hakura da ke ashe wannan ta'asar yayi. Allah mun gode maka!"" Daga haka tayi shiru sai kuma tayi kwafa. Ni kan tun da ta fadi haka na rasa nutsuwata. Haka nayi ta zama karshe zuwa yamma Ya Ado ya zo ya mai damu gida, a kofar gida na hango motarshi yana tsaye ya harde hannunsa a kirjinsa. ""Auta ga mutumin ki!"" Lokacin da motar tayi tsaya na fito tare da fitowa daga cikin gidan na nufe shi, yana ganina ya tako har indA nake. ""Ya mai jikin?"" ""Da sauki sosai!"" Na fada mishi, ""Na bawa SAN offer ko zai kawo shi Kumo clinic amma yaki."" ""Alhamdulillahi mun gode!"" Na fada ina kallon kasa. ""Ki taimaka min da takardun hannunki!"" Ya fada kamar yana shakkar abinda zai fito bakina, murmushi nayi mishi tare da cewa.. ""A'a adalci ne na tsaya a basu hakkinsu, idan na ce zan bi bayan ahalina ban yi adalci ba sannan suma bankin sun yi adalci da suka yi hakuri har zuwa wannan lokacin. "" ""Ni zan biya kuɗin ku bani takardun please!"" Ya fada kallonshi nayi da kyau kafin na ce mishi."" Mun gode! "" Na juya zan tafi sai kuma na juyo na ce mishi. "" Ina son na kasance a cikin masu tafiya Bauchi da Gombe, please saboda ina son ganin kome!"" Na saka a raina matukar na dawo daga haka zan ajiye aikin na hakura ban tab'a fahimtar yadda mutane suke ji ba sai yau da ta fado kaina. Yau na ji yadda mutanen da banki take kwace kayansu, Abba ya rasa hatta gida daya da zai zauna, hadiye kukan nayi ina ji kamar zuciyata zata buga."
"""Am sorry!"" Ya fada a hankali. Juyawa nayi na kalle shi, sannan na shiga cikin gidan."
"Shiga motar yayi ya bar kofar gidan, burinsa ya hango Khamis, har ya isa KUMO FAMILY MANSION, a"
"kofar gidan iyayenshi ya hango shi, cikin wani irin fushi ya nufe shi, cikin fushi bai gama tsayar da motar ba ya fita kamar wanda aka cilla shi, ya rufe Khamis da mugun duka, shi da ya san me ya aikata dariya yake mishi yana nuna shi da yatsa alamar yayi nasara abinda yake bukata. ""Wallahi ko zaka kashe ni, sai na hana soyayyarku tasiri. Kai ba haka ba baka isa ka yi aure ba matuƙar ina raye!"" Duka kamar ya samu jaki. Dakyar aka kwace shi ya ce mishi. ""Yarinyar nan har abada ka rasata, ai duk abinda kake so matukar zan gani sai na haramta maka ita, ka saka idanun ka gani."" Rike hannun Turaki Ubaid yayi yana jan shi har cikin mota bakin ciki ya hana shi magana. ""Ka sani ko zaka mutu ita din ta haramta a gare ka"" ""Sake na kashe dan iskan Yaron nan! "" Fisgar motar yayi da ƙarfi kofar gidan Alhaji ELYakub ya nufa, wani irin naushi ya kaiwa glass din motar sai da yayi tsawa, ya fita tare da nufar cikin gidan Alhaji ELYakub, ya zauna shiru sai a lokacin Alhaji Sameerah ya shigo tare da nufar Turaki kamar zata rufe shi da duka, wani irin d'ago kai yayi ya kalleta da jajjayen idanunsa. ""Me ya faru?"" Ubaid ya gaya mishi abinda ya faru wanda ya gani da idanunsa. A lokacin Khamis ya shigo ya danna fuskarshi da tsumar ƙanƙara. Kallonshi"
"Alhaji ELYakub yayi ya ce mishi. ""Khamis me ya faru?"" ""Kawai don na nunawa sakatariyarsa takardun da"
suka yi daidai da sunanta na banki sun yi gwanjon kayan Babanta shine ya rufe ni da duka ni me na mishi
"da zai dake ni?"""
"A fusace ya sake mikewa Ubaid ya mai da shi, ""Please!"" Ya fada, yana taping bayansa a hankali"
"alamar yayi hakuri. Cikin fushi Hajiya Sameerah ta ce. ""Baffa Marin Khamis yayi a gaban jama'a? Marinsa yayi a gaban kananun ma'aikata, marinsa yayi da akan mace? Baffa haka bai yi mishi ba sai da ya zo ya kara Dukanshi s gaban jama'a, ka yi wani abu domin wallahi abinda Bilal yake ya fara wuce makadi da"
"rawa."""
"Kallon Bilal Alhaji ELYakub Kumo yayi rabon da ya ganshi haka tun rasuwar Iyayensa, yadda ya zauna"
"ya sunkuyar da kai tare da dunkule hannunsa yayi murmushi ya ce mishi. ""Lubnah ce ko?"" Bai d'ago kai ba amma ya damke hannunsa sosai, alamar Eh. ""Me yasa zaka je gaban Macen da yake so da irin wannan al'amarin?"" Murmushi yayi mai sauti sannan ya cigaba da cewa. ""Ita din Matar da yake so ce, ba yau nake jin labarin kana kazamin rayuwa da matan kamfanin ba, na tab'a maka magana? Sameerah da kike ihu na tab'a yiwa Khamis magana akan abinda yake aikatawa? Ita yarinyar rabin rayuwarsa ya b'ata yana jiranta, sai ya zuba idanu wani ya lalata mishi damar shi? A kodayaushe kuka tashi magana kuna mantawa cewa Uban Bilal shine ɗana na fari rabin da karin kamfanin dukiyarsa ce gadonsa ce, me ya dace yayi? Ya kare dukiyarsa da ta al'umma. Sai kai Khamis ka manta da cewa kana da aure ne? Kalli matarka da Yaranka biyu amma baka daina tsalle tsalle ba, na maka iyaka da Lubnah ba ruwanka da ita sannan ruwan Bilal ne ya mai da musu kadarorrinsu ruwansa ne ya cigaba da rikewa. Daga yau kada na ƙara ganin wani ya zo da maganar Bilal da Lubnah idan har ya faru dan barranta kaina da shi, idan ba zaku taya shi niman soyayyarta ba, ku kyale shi yayi yakinsa shi ɗaya. Ban haka kowa yayi yadda yake so ba amma shiga rayuwar Bilal kamar cewa ne za ayi yaƙi da ni. Bana son wani ya kara shiga rayuwarsa, Turaki kai kuma ka rage zafin rai ko fushi don Allah. Nasan ya maka ba daidai ba amma yana da kyau ka iya sarrafa fushinka kada ka zama abin dogara mutane suna amfani da fushinka wurin cutar da abinda"
"kake so!"""
"Haka suka yi shiru Hajiya Zeenatu ta ce mishi. "" Amma idan da adalci ga mata a cikin gidan, har sai Bilal"
"ya fita ya hango wata can kuma wacce suka fuskanci karayar arziki?"" Ganin parlourn babu wanda ya amsa mata, ta cigaba da cewa. "" Waye ya sani ko don abin duniyarsa take bi, tunda a wannan age na shi bai zama dole ya samu haihuwa ba, tunda an gama watsar da yaran a kwaroro da lungu da sako."" ""Amma baki da kunya, amma Sam baki da mutumci a kan idanuna kike fadar haka? Kin manta Uwar Turaki daga titi ta wanko ki, zuwa kamfaninta bayan ta mutu kika auri mijinta, wai matar da take da boyayyen manufa ita ce yau take fadar abinda bata da sani akai."" Inji Uncle Auta da ya shigo yana kallon Hajiya Zeenatu, shiru tayi tana kallon shi, zama yayi yana fadar abinda Khamis yake sannan ya ajiye takardan koran da Turaki ya mishi. ""Koranshi kuka yi kenan? Haba Mujitafa, amma dai daga Bilal har Khamis Yaranka ne me yasa kake nuna fifiko akan su, idan da Bilal ne yayi haka, shima haka zaka kyale shi ne haka? Ai nasan ba zaka tab'a kin goyan bayanshi ba, ka duba lamarin idan Khamis ya bar aikin a"
"ina zai ci-gaba da aiki?"" Shiru parlourn yayi Alhaji Abbas yana rokonsa amma bai ce kome mikewa Bilal"
"yayi ya bar su a parlourn, idan aka ce bai ji zafin abinda aka yi ba, yayi karya kawai ya san idan ba sa'a ba"
ya rasata kenan. Bakiɗaya yaji tsoron Allah da tsoron rasata. Haka ya shiga motar ya wuce gida. Tare da kiran Taj ya gaya mishi ya saka idanun akan kamfanin zai dauki kwanaki bai zo ba.
"Tunda ya shiga gidan ya kwanta bakiɗaya yaji kome ya tsaya mishi, sallah ya samu yayi ya sha tea kawai"
"ya kwanta. Yana nazarin yadda zai da matsala, a yanzu duk yadda zai fito da bukatarsa na aurenta abu"
"daya ne saboda case ɗin ne zai musu rufa-rufa, duk yadda zai yi bai san yadda zai shawo kan danginta ba........"
"[12/9/2025, 8:05 PM] Maman Walid: 7"
Washi gari
"Da wuri na shirya na nufi office, ban yarda abinda ya faru ya hana ni sakat ba, na saka a raina zan tafi"
"aikin ko don kada a ce don tazo kaina ne, ina isowa abinda na fara aikina. Takardun na fara aikinsu sannan na turawa Lauyar kamfanin da ya saka hannu, wayata ce tayi ƙara na ɗauka number Tarik Mustapha Takai, murmushi nayi na dauka ina faɗin. ""Ina ka shiga kwana biyu bana ganinka?"" ""Sorry Baby girl na ji abinda ya faru, na turo 50% please na san Uncle zai bada sauran."" Murmushi nayi na ce mishi. ""Kul ka turo min kome, wato don ni ce taku shi yasa zaku kare ni? Me yasa baku tab'a yin haka akan kowa ba?"" ""Baby ina zuwa in sha Allah gobe zan tawo!"" ""A'a ka zauna ka ji ni bani da matsalar kome zan ji da kome in sha Allah."" Duk yadda ya so ya tausaya min naki, bana son wani ya tausaya min bana son na ga tausayi na a idanun mutane, haka na cigaba da aikin baya. Na gama na haɗe takardun na turawa Mr Turaki, kafin kan na fashe da kuka, tare da kifa hannu a fuskana, ban san lokacin da ka dauka"
"ina kuka ba, ina d'ago kai muka yi ido hudu da shi, share hawayena nayi tare da cewa. ""Good Morning sir, na tura maka sakon zaka duba sai kayi sign zan turawa bankin UBA an jima!"" Na fada ina fitowa daga table din zan wuce ya ce min. ""Am sorry!"" Juyawa nayi na sake murmushi na ce mishi. ""Har yaushe zaka cigaba da bani hakuri? Is not your fault, haka ƙaddara take sai ta haɗa mu boat daya kuma mu fuskanci kaddara daya!"" Na wuce wurin da goran ruwa yake na dibi ruwan na wuce ban dakin da yake cikin office din ya na wanke fuskana, sannan na fito na ce mishi. ""Sir ka tafi babu lokaci."" Kamar wanda na tura shi ya fita, goge fuskana nayi na cigaba da laptop wanda sunan Abba da kome akan file din, ina ji kamar mafarki ne, wayata ce tayi ƙara ma duba Ya Ado ne. ""Lubnah!"" ""Na'am!"" ""Don Allah ko zaki duba wani sako na tura miki ko zaki iya printing ɗinsa ki zo min da shi."" ""Ok Ya Ado!"" Haka na shiga aikin na fara, a hankali nayi ta duba takardun har zuwa wanda na gama printing sai na ga kamar na tab'a ganin takardan"
"da jimawa, haka nayi ta kallon takardan."
"Kiran wayar Ya Ado nayi na ce mishi. ""Ya Ado a ina ka samu takardun nan?"" ""Yanzu na saka Ibrahim da"
"yazo daga kaduna ya turo min!"" Hawaye ya zubo min. Na ce mishi. ""A dakin Abba aka samu kenan?"" ""Eh a nan aka samu!"" ""Kin san shi kika ce?"" ""Bari xan kira ka an jima!"" Ka kashe wayar na fashe da kukan da"
"ya fi farko, nayi ta dukar table din gabana, wannan wacce irin masifa ce, nayi ruined family na bakiɗaya."
"Me yasa na kasance azzaluman, suka nayi a kan kujerar nayi ta buga kaina da bango domin ta haka ne zan ji sanyi a raina. Ina kuka ina ji kamar gara na mutu ko zan wuta, rike ni yayi tare da cewa. ""Ya isa haka!"" Janye jikina nayi na fashe da kuka bayan kifa kaina da gwuiwata na ce mishi. ""Nayi ruined rayuwar family, na saka kowa cikin tashin hankali, Ni ce na aikata kome ni ce nayi kome. Don Allah ka saka a rufe ni saboda useless halina, gashi nan family suna suffering a kaina. Abba yana can cikin wani hali, Mama da Yadiko sun rasa inda zasu zauna, gaya min me nayi haka? Ni saboda ni kowa yana bakin ciki. Saboda ni, ina ji kamar na mutu ma kowa ya huta idan bana raye kowa zai yi farin ciki."" Yadda nake zaune a kasa haka yake durkushe a gabana, ""ki yi hakuri!"" Ya fada a hankali, ""Ba laifinki ba ne, ƙaddara ce idan kika ce zaki kalubalenci ƙaddararki kamar baki yarda da Allah ba ne, put Allah a gabanki kome zai zo da sauki."" Dafe kaina nayi na cigaba da kuka ina jin shi, a hankali na mike tare da hada kome na tattara sannan na ce mishi. "" Excuse me! "" Na bar shi a durkushe, ganin yadda na fita da sauri ina kuka zaka ɗauka mutuwa aka yi min saboda kukan da nake sosai, ina ta son bin elevator amma na ga zai bata min lokaci stair na bi, shi kuma yana fitowa ya biyo elevator kusan a tare muka iso yadda na fito da sauri, ""ki dakata hakan"" cak na tsaya ina jiranshi, ""muje na ce!"" Ya fada a kausashe, haka na bi shi har wurin motar ya bude min na shiga. ""Daga yau na dakatar dake zuwa aiki sai na nime ki!"" ""Sir don Allah kada ka hana ni zuwa Bauchi!"" "" Na yanke hukunci!"" Kuka na saka mishi ya da ki gaban motar, wani irin tsoro ya kama ni na ce mishi.""am sorry Sir!"" Kunna motar yayi ya bar kamfanin yana tuki har asibitin. "" Kin san Allah, idan kika yi wani abu da zai nuna kin san dalilin faruwar lamarin a will deal with you, don haka just keep follow me and my order, kin ji ko?"" Wallahi yadda ya bude min idanun sai na ji bakiɗaya ya cika min idanu, kasa nayi da kai tare da gyad'a mishi, murmushi yayi mai sauti ya ce min."" Good gurl koma yayi tsanani maganinsa Allah."" Haka ya fito y bude min muka shiga Asibitin, yana gaba ina bayanshi ban san an sauya musu daki ba, sai da ya jagorance ni, har inda aka mai da su. Hancina na fara ja ya tsaya cak nayi karo da bayansa. "" Ka yi hakuri Sir! "" Juyowa yayi ya ce min. "" Bana ce kada ki yi kuka ba?""gyada mishi kai nayi. Ya sake cewa. ""Ki yi hakuri kin ji zan yi handle kome in sha Allah."" Gyad'a kai nayi, sannan ya ɗan matsa kaɗan ya bani wuri muka cigaba da tafiya, har muka isa, yana zuwa ya mikawa Ya Ado hannu suka gaisa, tun daga nan suka fita, zama nayi na saka Mama a gaba ina ta kuka har, Mama ta gaji ta rufe ni da fada, can sai gasu nan sun dawo Ya ado ya ce min.""Zo muje!"" Tashi nayi na bishi, shi kuma ya zauna yana kallona, tunda na bi bayanshi wurin motarshi na isa shida su Ya Tahir, tambaya suka fara min akan takardan, na shiga bashi amsa, har zuwa yadda aka nasan takardan. Cikin wani irin damuwa na"
"kalle shi,"
"""Lokacin muna tare da shi."" Shiru nayi daga bayana ya ce min. ""Calm down, babu abinda za ayi miki."""
"Ya fada bayan ya karaso ya tsaya a gefena. ""Sorry Barista, kada ku ɗauka na muku shishigi Please ku bita a hankali."" Yana fadar haka ya wuce wurin motarshi ya shiga, wani irin fargaba yasa na rufe fuskana cikin shashekar kuka na gaya musu yadda aka yi har nasan takardan, ""ban san cewa haka zai faru ba, ni dai na gaya mishi na san yadda Abba yake sign, sai ya ce min na gwada mishi, nayi mishi ya kuma je ya ga na Abba sak da irin wanda na mishi, bayan wasu lokuta sai ya kawo min takardu yadda yake azazzzalamin na saka mishi hannu wallahi ban tab'a sanin cewa irin wannan fraud zai aikata ba, don Allah nima ku yanke min hukuncin, wallahi "" na fada ina wani irin kuka me cin rai. Idanun Ya Ado yayi jajjur ya ce min. "" Me yasa Lubnah? Kin san yawan kuɗin da ake bin Abba kuwa?"" Zuciyata ta ce ta tsinke na kalle shi a"
"matuƙar razane, hawaye wannan na koran wannan ina girgiza kai na ce mishi."" Ka rufa min asiri, wallahi"
"ban sani ba, don Allah kada ka gaya min mutuwa zan yi."" Na fada ina durkusawa a wurin, domin a rud'e"
"nake don yadda zuciyata take tsinke kamar zata fado, zai sake magana Ya Tahir ya ce mishi. ""Ya isa haka yanzu ba lokacin magana ba ne, taya abubuwan da aka rasa zai dawo ake magana."" ""Koma cikin asibitin muna zuwa!"" Inji Ya Ado, haka na mike a hankali har na koka can nesa da su Mama ina kallonsu idan har su Mama suka san nice nayi wannan aikin har abada ba zasu daina tsanata ba, zasu jima suna jin zafina, sai yanzu na fahimci me yasa Hafiz yake cewa ba zan tab'a tsere mishi, ashe wannan abin da ya aikata ne, dafe kaina nayi da hannu bibbiyu ina jin tsanar kaina da bakin cikin wannan halin nawa zama naji an yi a gefena, da sauri na kalle shi. Mika min goran ruwa yayi yana kallon yadda nayi zuru-zuru, a hankali na d'aga goran na sha sannan na sauke ina me rufewa, kaina a kasa ina kallon goran. ""Gobe su Hindatu zasu tafi, na ce su tafi da ke!"" Kallonshi nayi a hankali na dauke kaina, ina kallon kasa. ""Yanzu kayan sun riga da sun shiga cikin KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY, har an yi musu stamp ko?"" Na tambaye shi, kura min idanu yayi kafin ya ce min. ""Eh!"" ""Nawa KUMO PROPERTIES take bin mu?"" ""Ba wani kudi me yawa take binku ba!"" ""Kamar ya?"" ""Eh kasancewar kayan gwanjo ne har na mai da musu kudinsu,"" kallonshi nayi cike da mamaki murmushi yayi ya ce min."" Ba wani dayawa ba ne, kudin ruwan da yake ciki ne"
"kawai yayi yawa, Alhamdulillahi an biya dukka."" Shiru nayi ina ta wasa da yatsuna. ""Yanzu ya za'ayi kenan, a cikin gidajen da kumo ta rike ko za a sakawa asalin gidanmu kudi mu saya?"" Murmushi yayi ya gyara zama ya ce min,"" idan kika ce a baku ma dukka dukiyar me sauki ne?"" Ya ciro wayarshi da sauri na kwace wayar na ce mishi."" A'a! "" "" Yes idan har zaki yi dariya ba wani abu ba ne maza ci abinci."" Akwai wani abu da na kasa ganewa akan shi,

299 / 321

Chapters