Author : Mai Dambu Category : Complete Novels
dawowa nayi na samu yayi adding another wife, gaya min me kike so nayi?"" Baya na ja musamman yadda ya hayayyako min, na kara fashewa da kuka. ""Matar da ya aura sakatariyar Mahaifiyata ce, taya ba zan tsane shi ba waye ya sani ko sun kashe mahaifiyata ne don su cigaba da abin!"" Da sauri na kai hannuna bakinshi. ""Allah yana ganinka kada ka yi mishi kazafi, kada ka tozarta shi. Sadauki ne da yayi kokarin baka kyakyawar rayuwa. Yayi maka adalci ta hanyar ka fuskanci abinda yake gabanka. Bai d'aga maka hankali ba sai da ya tabbata ka sami abinda yake ganin zai gyara maka gobenka, iya adalci ya maka ya maka adalci bai lalata mutuncinsa da kimarsa ba, ya aurota duk da bata addininsa"
"da ta same ka ta amince da addininsa, ta kuma zauna da shi ba tare da ta hango gazawarshi ba, shi din"
"jarumi ne da babu irinsa har ya koma ga Allah yana son ya zauna da kai ya fahimtar da kai waye shi, ya"
"gaya maka yadda yake jin ka. Amma baka fahimce shi ba. Yayi kuskure wurin auren yar dakinta amma kuma rabon Jasminah kike tsammanin bai isa ya dauki rayuwarta ba ne."" Rike hannunsa nayi tare da matsawa kuwa da shi, kafin na rungume shi ina kuka. Na janyo kanshi na rungumar a kirjina ina shafa bayansa. "" Nasan anyi maka laifi amma kada hukunta shi ta haka, wata rana kai Uba ne da sannu zaka fahimci me yasa iyaye suke hakura da wani abu domin Yaransu. Zaka gano yadda suke tsoron kare yaransu daga wani abin da zai shafi bayansu. Wallahi ban tab'a ganin jarumin Uba irin Papa ba je did him best to protect you! Kuma har yana kan kare ka, ya cusa maka kiyayyarshi domin ka zama dodonsu, kuma yayi haka ne domin ka tsaya da kanka. Yaki nuna maka soyayya domin kada ya saka maka soyayya da kawazuci kamar yadda Mammy tayi yake damunka, ba nan kulawarsa ya tsaya ba, ya bude maka idanunka ka fahimci mutanen da suke zagaye da kai, ya cusa maka niman na kanka domin kada ka jira abinda Mammy da shi suka tara maka. Idan har haka dai saka na zama Uwa ta gari zan yi tsalle na rungume wannan halin nashi. Domin ya nuna min ba koda yaushe ake tafiya a yadda ake so ba."" Kai ya d'ago yana kallona da idanunsa da suka yi jajjur, ga Daddah a kofar shiga parlourn. "" Dubi ka ga mahaifiyarsa ce, kalli yadda take kuka danta ne fa, and kasan yadda take ɗaukar abin a ranta? Kasan yadda Uwa take girmama me kaunar danta? Balle kai son da take yiwa mahaifinka ya shafe ka, shafar da takai har ta rufe idanun ta ki yarda da shi ta baka dukar yarda. Kaf duniya ita ta san waye danta."
"Wadanda bayin Allah ba iya tausayin dansu suke ba kai ne abin tausayi domin kai ne kake raye kaine kake bukatar kome shi na shi ya ƙare yana can amma addu'ar iyayensa dukka biyu yana riskanshi kai fa? Baka da wanda ka ajiye zai maka baka da wanda zai maka addu'a kana fushi da shi! Bayanshi ya kama dahir wani lokaci ba kukan mutuwa muke ba, kukan namu ya zai riske mu muke kuka. Duk wanda ya rasa iyaye shine abin tausayi ba su iyayen da suka tafi ba! "" Ina kai nan na mike na bar shi a wurin, tabbas rayuwarshi a juye take yana bukatar wanda zai d'aga mishi rayuwarsa. Ban daki na shiga nayi kuka nayi kuka wannan shine abinda ba zan manta a rayuwata ba. Ganin har lokacin ban fito ba, Daddah ta ce mishi.""Matarka yaki fitowa, kizo ki san yadda zaki yi da shi!"" Jiki a mace ya zo ya buga kofar. "" Lunah"
"kada ki kirkiro mana wani scenes please ki fito muje gida!"" Haka na bude kofar ina kallonshi. Yayi wani iri, bude mishi hannu nayi ya shiga cikin hannun, na rungume shi. "" Sorry ba zan kara maka magana ba ka ji, amma be a good boy!"" Gyada min kai yayi na shiga shafa bayanshi, ina jin wani irin tausayinsa a raina."
"Mijina ne dole na taya shi yaki da zuciyarsa ya san darajar iyayensa. Wucewa Daddah tayi ta bar parlourn. Sai da na ji yadda yake jin zafi na janye jikina na saka mayafina muka koma gidan mu, aka yi sallah la'asar. Ina dakin ya shigo ya same ni. Kallonshi nayi murmushi nayi mishi tare da bude mishi hannu. A hankali ya tako, wani lokaci namiji ya maka lakar shagwaba wani cinyewa ne, yana zuwa ya durkusa a gabana na rungume shi, ina shafa kanshi. ""Kayi hakuri ka ji!"" Zagayawa yayi da hannunsa bayana ya rungume ni. ""Thank you, Moon!"" Shafa bayanshi nayi a karo na biyu. ""Is ok, ka godewa Allah da sauran lokaci bai kure ba."" D'ago yayi yana kallon yadda nake kallonshi, murmushi yayi a hankali ya d'ago fuskarshi ya haɗa da nawa, akwai wani lokaci da zaka yi mafarki a zahiri amma kuma irinshi bai cika tabbata ba, but today My Man ya cika min mafarkin fiye da yadda ban zata ba, domin ni dai nasan nayi aure amma ban san cewa akwai wani tafiyar da iya yarda da abokan arziki mijin na gari, sai dai kuma yadda labarin zai kasance ne aka samu matsala. Domin ana ta buga kofar gidan. Janye jikinshi yayi yana kallon yadda na lumshe idanuna. ""Ina ga su Auntynki ne ko?"" Ban iya amsa mishi ba, amma kuma na gyada mishi kai wani irin kunya da girmansa suka cika min idanu. Sai da ya fita ka sauka da gudu na bude kayana na dauko riga da"
"skirt na saka sannan na yafa mayafi. Daurin dankwalin a parlourn na karasa shi, shine ma kayansa yayi"
"wani irin squeezing, shigowa suka yi ya musu barka da zuwa sannan ya fita. Ganin yadda yake raba idanu"
"Aunty Zakiyah ta ce min. ""Auta ba dai mun katse muku!"" Wucewa kitchen nayi kunya ya gama lullube ni. Dakina suka shiga yadda suka ga gadon a yamutse Aunty Hindatu ta shigo kitchen din ganin yadda na tsaya a gaban sink ina murmushi, wannan shine first time da aka yi kissing dina. Sai nake ji kamar ina yawo a sama ne ko a iska ne, abin akwai armashi wanda a da can Ya Hafiz bai yarda da kiss ba wai shi baya son kazamta, amma yau abubuwa dayawa sai suka sani jin kamar bani ba, yatsuna na kai bakina. ""He kiss You ko?"" Kallonta nayi a razane domin ta razana ni. ""Wallahi kin bani tsoro!"" Zungure min goshi tayi tana faɗin. ""Kina imagination na abinda ya faru, ki sani babu amfanin hasashe domin kuwa shi naki ne."" Aunty Hindatu kenan bata san yadda na sha mafarkin irin wannan ranar da rayuwar ba, daukar tire din da na saka drinks din nayi na wuce na kai musu na dawo na duba firj na ga namar jiya kasancewar yayi sanyi sakawa nayi a microwave nayi na dumama, sannan na kawo musu yadda nake dan dingishi yasa suka fara min tsiya wai tun shigowarsu nake raba kafa. ""Innalillahi wainnalihir rajoun, gocewa nayi fa jiya! Allah ku tambaye shi!"" Na fada musu kamar xan yi kuka. ""Au don mune yan iska sai muce mishi wai da gaske gocewa tayi?"" Shiru nayi ina share zancen, daga gidan Daddah aka kawo mana manya kulolin abinci, har da fura da nono. Ai kuwa sun ci abinci sosai. Aunty Zakiyah ta ture tare da miko min wata jaka wai muje daki Aunty Innah ta ce. "" Bana son bakin munafunci gaya mata anan!"" Kayan Mata ne na Maman Hidaya da Khairat ne, hadi na musamman ta ajiye min ga turaren tsuguno da na humra, duk kunya ta kama ni tsuminta ta sa nayi ta sha har bayan Magariba suka tafi, bayan fitarsu na gyara gidan na saka turaren wuta, na shiga ban daki nayi wanka na gyara jikina da kyau. Sannan na fito a hankali, na shiga turare jikina ta ko'ina sannan na nufi wurin kayana, na dauki kayan barci masu kyau. Na saka na kara gyara jikina sannan na nufi ban wurin abin sallah na daura sallah isha da shafa'i da wutir, ina cikin addu'a ya shigo gaba yayi ya tare da tadda kabbara, sallah da ma'aurata suke na sunnah shi ya ja mu. Sannan ya dafa kaina yayi ta zuba addu'a kafin muka shafa. Janyo hannuna yayi muka fita parlourn, zaunar da ni yayi sannan ya nufi kitchen, wayata da take hannun kujeran yayi kara, ɗauka nayi."
*Kina ta rawan jiki! Tow in sha Allah wannan daren da kike gani shine na bakin cikinki *
"[12/18/2025, 7:27 PM] Maman Walid: 21"
"Sake wayar nayi ya fadi kasa, daidai isowarshi parlourn ganin yadda na razana tare da zubawa wayar"
"idanu cike da tsoro. Ajiye tiren yayi ya zauna tare da ɗaukar wayar ya kalli rubutun, kallona yayi ya ga yadda duk na firgita. Kashe wayar yayi tare da cewa. ""Oya muci babu abinda zai faru."" Ya fada yana mika min hannunsa na rike tare da saukowa daga gadon, a hankali na mika mishi hannuna. Ya riko ni sannan ya zaunar da ni a gefenshi muka ci abincin wanda ni kaina nasan ba wani abin arziki na ci ba, amma shi ya ci kai. Kallonshi nake na ga shi ko a jikinsa. Bayan ya gama ya ce min. ""Taya ni kai kayan kitchen,"""
"haka muka kai kitchen, sannan ya ce min. ""Mu wanke!"" Ya fada yana me kallona, ganin nayi shiru ya dafa ni a dan razane na kalle shi. ""Tunani kike?"" Girgiza miishi kai nayi, ya janyo ni gefenshi ya shiga bani labarin da ya mantar da ni abinda ya faru, ba a gama wanke wanken , ma samu sauki daga tunanin da nake. Muka gyara kitchen din sannan muka dawo parlourn muka yi ta hira. Sai goma saura na wuce dakina na wanke baki na cire hijab din na kwanta sannan can sai gashi ya shigo, ya zo dakin kunna wutar dakin yayi ga yadda na rungume pillow, kashe wutar yayi ya nufi gadon ya zauna yana kallon yadda nake kwance lumo. Kwanciya yayi a gefena. ""Ya ce min yau ko bani labarin da na jima ina son sani da bakinki!"""
"Bude idanu nayi a hankali na zuba mishi kafin na lumshe idanuna, na fara bashi labarin irin zaman da"
"muka yi da Ya Hafiz, sai da na gama bashi tas kafin ja gyara kwanciyar da nayi na sauke ajiyar zuciya"
"janyo ni yayi jikinshi yana faɗin. ""Sorry ban san irin rayuwar da kika yi ba kenan, amma me yasa kika manta da ni?"" ""Saboda ban tab'a tsayawa na duba waye kai ba, sannan ban tsaya na kalli fuskarka ba, balle har na san cewa kana tare da adalci. Duk lokacin da na tuna na kwari kaina sai na ga kamar ban yiwa kaina adalci ba, sai dai ni fa mahaifata ya lalace bai zama dole na haihu da kai ba, amma kofa a bude take idan zaka kara aure Allah ya baka zuriar dayyiba."" Hannu ya saka bakina yana faɗin. ""Shiiiiii!"
"Nima ban damu da lallai sai na haihu ba, shekaru sun ja!"" Ya janyo ni karo na biyu ya rungume ni da kyau,"
a hankali yake shafa bayana yana rarrashina. Har barci yayi gaba da ni.
"A hankali muka yi wani irin sabo da shi har na tsawon kwanaki uku cib, duk da bai tab'a niman wani"
"abu ba amma na ga alama kamar shiri yake yiwa kansa. Sai dai ranar da na cika sati da yake su Aunty Hindatu sun tafi washi garin ranar da suka zo. Ranar da na cika kwanaki bakwai a ranar ya shirya min gagarumar tarbar na musamman, don tun safe yake nuna min tsaf y shirya min, da yamma da ya fita ma haka ya kawo kayan lambu da duk wani abu na zabe fruit na hada mata hadi na musamman, da yake ya hana a kawo mana abinci da kaina nake girki, hidimar da nayi ranar y saka min gajiya haka ya sa ina gamawa na jera a table na wuce dakina nayi wanka da alwalan isha, bayan na yi sallah na fito parlourn don ina ta jin kamar maganar mutane. Abin ya bani mamaki taya ya dawo na san zai shigo. Haka na fito na samu yan matan family din ne a kan table sun saka abincin da nayi mishi suna ci, murmushi nayi na wuce kitchen na tsaya sai na ji raina yayi azabar ɓaci, koda na fito na samu ba iya cin abincin suka yi ba wulakanta abincin suka yi, kallona Badr tayi tana faɗin. ""Gidan dan uwanmu ne kuma mijina ni nan ni ce"
"kishiyarki da kika danne aurena ya auro ki."""
"""Sannu da kokari!"" Na ce mata sannan wuce dakina. ""Waye bai san labarinki ba? Sai dai shi wanda aka"
"yiwa asirin da yake ta rawan kai akanki!"" Juyowa nayi ka kalle ta nayi ƙoƙarin danne fushina da b'acin rai na ce mata. ""Sai me don kin san labarina? Tayu ki bada labarin da kika sani, amma ko gidan giya akwai babba."" Na juya zan wuce ta ce min.. ""Mahaukaciya wacce tayi jinyar hauka."" Ji nayi raina yana b'aci, ""kun ga ni ba ai na gaya muku tayi jinyar hauka yanzu ma Mentioned din sunan haukar yasa ta tsaya, yar"
"kwaya kawai."""
"Juyowa nayi a fusace amma kuma sai nayi ƙoƙarin gayyatar murmushi akan fuskana, na ce mata. ""Na"
"gode sosai, shima Arziki ne."" Na barsu nan suka yi ta zagina da fadar wasu abubuwan da ni dai nasan iya shi ya sani wannan abin ya b'ata min rai, kofa ya dawo bai zo da mota kofar gidan ba, da kafa ya dawo jin hayaniyarsu yasa shi ya tsaya sai da ya ji me suke cewa ya shiga tare da zuba musu idanu. ""Wai bana ce kada na ga kowacce mara kunya a gidana bane?"" Ta tambaye su, bayan ya rufe gidan ya saka key a aljuhunsa ya nufi daki hango table din kaca-kaca, ya shigo ya same ni kwance, kuka nake son yi amma na danne. Zama yayi yana faɗin."" Me ya kawo su gidan nan?"" ""Su da gidan dan uwansu, anan da kwanaki ita Badr ai amaryanka ce!"" "" Na sani amma me ya kawo su gidana?"" Nan ne bani da amsar bashi nayi shiru. Tashi yayi ya nufi dakinsa ya shiga ya sauya kaya yadda ake buga kofar gidan nayi mamaki ashe"
"tunda ya shigo suka ga ya shigo dakina ya zauna. Suka shiga kiran Iyayensu, ni dai ban ce kome iyayen"
"suka yi ta buga gidan, amma ya fusata da ya fito da bulala a hannunsu ya tambaye su waye ya basu izinin"
"zuwa gidansa? Suka nuna Badr, ya tambaye su waye ya basu izinin cin abincin da aka girka mishi, suka nuna ta. Murmushi yayi ya ce musu. ""Gobe idan ta janyo ku, kada ku mata musu ku zo ni kuma zan tabbatar muku da cewa nayi rayuwa da kowani dan bariki!"" Ya tara su wuri guda yayi ya zane su. Gajiya da ihun nayi na zo na fisge bulalar nayi na ce mishi. ""Wannan ba zai hana su fasa abinda suka yi niyya ba, sannan ni ban ga wani fa'idar zane su ba domin ni kake janyowa kiyayya, don Allah ka bar kome ya wuce babu amfanin tashin hankali don Allah!"" Na fada ina rike bulalar, sake min yayi ya nufi kofar ya bude yana faɗin. ""Ni ban haifa ba balle ku ce nawa ne, ku rike Yaranku idan suka cigaba da shiga rayuwata zan"
"gyara musu zama."""
"Haka yaran suka fita suna kuka, shi ko a jikinsa. Haka ya riko Badr yasa ta tattara abincin da suka bata"
"ya juye mata a jakarta, me shegen tsada. Aikuwa bayan ya gama da su, ya biyo ni kitchen, sauran abincin da ban ci ba na bari a kitchen na saka mana cokali muka shiga ci muna hira, wayarshi ce tayi haske ya dauka ok naji ya ce, sai da muka gama sannan ya riko hannuna muka shirya muka fita tare. Gidan kakanshi muka nufa. Gabana ne ya fadi nasan tunda suka yi haka sai a hankali. Sai da aka fara magana na ga ya d'ago zai magana na rike hannunsa, ina kallonshi. Murmushi nayi ina faɗin. ""Sanyi!"" Ba karamin al'amari ya faru amma haka suka nuna nice da laifi ai kiransa nayi, ce min yayi. ""Tashi Jasminah ta raka ki!"" Kallon nayi ya ce min. ""Jeki ba kome!"" Haka muka nufi gidan muka barshi, tass ya wanke su tare da cewa ya dake su ko za a rama musu ne,ya daka gobe ma ya ga wata ta zo mishi ai shi kan ma ya gama"
zaman gidan.
"Sun zata wasa ne, sai dasuka ga ya bar parlourn, duk yadda dattijan nan suka so ya zauna yayi tsalle"
"ya ce ba zai zauna ba, a ranar ya saka na hada wasu abubuwan muka bar gidan dama sanadi yake nima, sai kuma haka ya zo akan gabba, domin ba shi ya bar gidan da ra'ayinsa, mutanen gidan suka yi amfani da zuciyarshi domin ya bar gidan. Tabbas mun koma gidan mu a daren inda muka kwana a daki daya cike da damuwa shi fushi sosai yana faɗin me yasa naki gaya masa abinda ya faru, sai ya dauki fushi. Ni dai"
ban san yadda zanyi bayanin amarcin da na yi ba.
"Washi gari bayan ya fita, wurin karfe daya, aka ce ina da bako Adamu Jama'are. Cikin farin ciki, na ce a"
"bashi ya shigo Yayana ne. Tunda na ji haka na wuce kitchen na hado mishi abin motsa baki, sai dai ji nayi kamar nasan muryan wanda ya shigo domin kuwa. Bai kama da na Ya Ado ba. A hankali na fito daga kitchen din, idanuna ne ya ɗauka akan na Hafiz. Ji nayi gabana ya buga kamar wanda zai fito waje."
"Idanuna suka cika da kwallah.. ""Me kake nima a gidana!?"""
"Takowa yayi na sake tiren hannuna, wukar da yake kan fruit na dauka ina nuna mishi. ""Fita min a"
"gidana!"" Takowa yayi yana faɗin. ""Ba zaki iya kome