Advertisements
Chapter 297 Reading ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu

Author :  Mai Dambu Category :  Complete Novels

Chapter   297 / 321

888K to 891K   out of 962.4K words

ƙara ganin fuskarka."" Wai ance rashin sani yafi dare duhu, ashe shi Abu ya gani a sama ta inda nake, ban gama masifar ba na yi abu ya fisge dan kwalina kasancewar ko ina haske ne amma ban san meye a saman ba, fisgo dan kwalin yayi birin ya fado, nima tsalle nayi tare da komawa bayanshi, abinda ya faru kenan har inda Ya Umar yake ya kawo ni, kallonshi nayi ta yi amma bai kalli inda"
nake ba.
---
Washi gari.
"Lokacin da na fito wurin karfe daya, na sami yan uwana bakiɗaya suka ta hiran abinda ya musu na"
"alkhairi. Basu gaya min ya tafi ba sai da na zauna ina karyawa. ""Ke kan tun jiya kuka yi sallama ko?"" ""Waye kenan?"" Na tambaye Aunty Hindatu da take cin meatpie, ""Mr Turaki!"" Kwarewa nayi, abinda ya faru a hanyar dawowa dakin ya fado min, shiru nayi bayan na gama tarin, tabbas nayi rashin hankali. Da nasan cewa jiya biri ne a saman bishiyar da nake tafiya a wurin da ban gaya mishi magana, har bayan la'asar da muka gama yawo a yankari muka dauka hanyar Jos domin mun tattara kome na mu, haka muka samu rakiyar Yayuna har Jos da dare muka isa gidan Aunty Raliya mu kwana saboda gidanta Babba ne, tunda na shiga ban dAki nake kallon wayar hannuna, can na yi shahadar kuda na kira shi. Ringing daya yayi ya dauka. ""Assalamualaikum Sir Turaki am sorry."" Cike da mamaki wani ne ya dauki wayar a"
"hankali na fahimci kamar wannan Ubaid din ne, ""sorry for yourself, kada ki kara kiransa!"""
"Kashe wayar nayi ina jin wani irin tsoro, haka na fito, na ga sai kallona yayuna suke tare da kashe tv"
"parlourn, nima jikina a mace na zauna na ci abinci. Abinci kai ban wani ci ba, sallah ma da yake mun isha"
"a hanya, sai naji na tsinka haka kawai. Karshe na shige daki na kwanta. Har wurin karfe biyu na dare"
"idanuna biyu, kamar na fita waje yadda nake jin tsinkewar zuciya. Haka na tashi nayi sallah nafilla sannan na kwanta addu'a nake domin na kasa barci. Bayan sallah asuba na samu barci. Kafin wani lokaci har na"
samu nutsuwa.
"Karfe goma na safe muka bar Jos, wurin karfe sha biyu muka isa Ya Ado ya zo tay dauke mu, ba karamin"
"gajiya nayi ba. Tunda muka yi sallah, na kwanta ashe bani daya ba ne har Aunty Zakiyah haka muka fito wurin karfe hudu muka gyara kitchen aka daura abinci. Sannan na taɓa kaɗan bayan isha na kwanta da wuri domin ina son gobe na koma aiki, na ga sakon da Taj ya turo min ta Email. Don ban tafi da laptop din ba. Bayan na gama rabin aikin na kwanta. Cikin dare haka na sake farkawa nayi sallah dare na gayawa Allah kuka na, washi gari da wuri na shirya na fita don Ya Ado ya ce ba zai fita da wuri ba, lokacin da na isa office sai naga kamar ana kus-kus, a hankali na wuce jikina a mace, na rasa meke min dad'i. Ina haurawa na samu an cire karamin office din a wajen an mai da shi ɗaya dakin da yake gefen na shi, kofar shi kuwa an mai da shi na glass yadda duk wnada zai wuce sai ya ganshi, inda aka mai da ni. Ina iya hango shi a cikin office din domin window dinsa yana cikin office ɗin, shima glass aka saka, an gyara kome gwanin ban sha'awa, fitowa nayi na shiga office ɗinsa na gyara kome tare da tattara kayan da suke watse na kai kan table ɗinsa, a hankali idanuna ya sauka a wani hoton da yake tables dinsa me dan fadi shi da family dinsa ne, yana cike da maraici. Turo kofar office din aka yi garin ajiye hoton ya fadi. Da sauri na durkusa, wato kofar na ciki zai ga na waje amma na waje na dai taɓa ganin na ciki ba, shi yasa ba a san ina cikin office ba, jin kamar ana waya da cewa. ""Eh gani nan a office ɗinsa."" Na kara shiga kasar table din nayi shiru, har wanda ya bude wani drower yayi ta bincike. Ban san me aka dauka ba, can na ji an fita amma tabbas namiji ne kuma abu ya dauka. Haka na fito na gyara wurin sannan na fita. Zuwa office dina, wunin ranar ban sauko kasa ba, sai da aka tashi a hankali na fito ina tafiya a bakin gate na hadu da Khamis, dariya yayi yana kallona. ""Zo na rage miki hanya!"" Banza nayi mishi na cigaba da tafiyata har inda zan hau motar gida, kusan tun Monday babu wnada ya bani labarin wani abu. Sai a ranar juma'a ina aiki da yaki karewa kusan ni daya nake ta aikin ina tara mishi a office din, sai ga Ubaid. Har office dina ya shigo ya samu ina aiki.. ""Uban waye ya baki izinin zuwa kamfanin nan?"" Kasa magana nayi ina kallonshi. ""Ba magana nake da ke ba."" Banza na bawa ajiyar shi. Na cigaba da aikin da nake, cikin fushi ya nufo ni, da wani irin fushi, Hafix ne ya fado min da karfi ya nufo ni, na dafe kaina tare da rintsa idanuna. ""Kul Ubaidullah, kul Ubaid kada ka saka mu kashe juna. Lunah tafi ƙarfin kallon banza balle har ka d'aga hannu a kanta."" Ajiyar zuciya na sauke na ga kanshi ya sha dauri sai sanda da yake rike da shi."
"Na rufe bakina da hannuna biyu na tashi da sauri zuwa gabanshi. ""Sir yaushe haka ya faru?"" Wani irin bugu nake jin zuciyata tana yi na fashe da kuka tare da zubewa akan gwiwata, na shiga rera kuka. Jan kujera ya ajiye sandar yana faɗin. ""Ai na zo lagos lafiya kafin na isa gida nayi hatsarin!"" Ya shiga rarrashina yana faɗin. ""Ba kome ba gashi na warke ba!"" D'ago kai nayi ina faɗin. ""Me yasa baka min sallama ba? Ai ko Addu'a na maka Allah zai kare maka hanya."" ""Gaskiya nayi laifi tow gani nan ai na ji sauki taso muje! "" Na mike da sauri na dauki sandar na mika mishi. Muna fito ashe a motar asibiti aka kawo shi, koda muka fito wani haɗe rai yayi yana faɗin..""Rigunan nan dole sai anyi musu shap ne?"" Haka muka shiga motar asibitin ya kwanta.."" Bilal Haris Kumo, ka rabu da yarinyar nan bata dace da kai ba,"
"yarinyar."" "" Idan ka sake kayi wani magana akan rayuwata sai na kashe ka!"" Ya nuna mishi sandar"
"hannunsa, kwace sandar nayi ina faɗin.."" ba kyau cewa da a kashe Muslimi idan ya zo da karar kwana ai"
"sai ka kwan ciki;"""
"Asibitin da yake muka je, tunda muka shiga bawan Allah ba sai ya narke ba kamar an jika takarda."
"Bakiɗaya kakaninsa suka kara shiga damuwa. ""Wannan taurin kan naki Turaki ita kaɗai ma zata kashe ki, ina ke ina tafiya kamfani don kin ji Ubaid ta samu Yaron nan Lubnah! Sannu ina bata yi mishi kome ba?"" "" Daddah gata nazo da ita."" "" Allah sarki sannu Lubnah Allah yasa Ubaid bata maka kome ba!, murmushi nayi domin na fahimci ni ce take nufin girgiza mata kai nayi, haka tayi ta jana da hira har nurse ta shigo tare da Alhaji ELYakub Kumo, kallona cikin fara'a yayi ya ce min.. ""kin dawo daga Bauchi lafiya?"" Gyada kai nayi, ya kalli Mr Turaki da yake nishin kafad'arshi tana ciwo. ""Ai ya auna arziki, shi ya ce kada a gaya miki don ko jiya Adamu yana nan!"" Kallonshi nayi cike da mamaki. To akan me zai ce kada a gaya"
min........
"[12/8/2025, 11:21 AM] Maman Walid: 4"
"Ban me yake kokarin boye min ba, amma ni har ga Allah bana nufin kome da shi, kallo daya nayi mishi"
"ban kara kallonshi ba, ba mamaki abinda ya faru a Bauchi. Na ji a raina ya kullace ni, don haka nayi ta"
"kallon kasa, a haka suka tafi sallah juma'a amma, Kakarshi mace ta haɗa mishi ruwan zafi, ya shiga yayi wanka ajiye mishi kayan tayi muka fito waje. ""Kana da kyau!"""
"Ta fada min murmushi nayi ban iya bata ba amsa ba. ""Turaki tana da kirki, kuma yana da mutunci ita ba"
"mutumin banza ba ne, amma haka suka yi mata sharri wai tana bin maza."" Sai naji maganar tayi min wani irin girma, lokacin da ya fito sanye da Jallabiya ta maza, tayi mishi kyau. ""Mamanta baturiya ce babanta Yarona na farko, tana da shekaru kusan arba'in amma taki aure, idan kin samu wani me hankali ki mata hanya tayi aure na san da iyayenta tana raye ba zasu barta tana gantali ba. "" "" Daddah don Allah ki bar tona min asiri"" ya fada yana satar kallona, nima kallonshi nake, saboda yadda yake shafa mai a jikinshi turare a jikinshi ina ga ko mai dai ban ga ya shafa ba, sai body spray da asalin oil perfume, abin"
har mamaki yake bani daga can ya dauko blue seal ya shafa tare da taje kasumbarshi.
"Wannan mutumin anya ba dan daudu ba ne, mutum ya bata lokaci yana kashewa jikinsa kudi"
"kamar mace, kamar yasan me nake fada ya ce min."" Kina da matsala ne da ni?"" Ya fadi haka daidai Daddah ta shiga cikin dakin. Zama yayi a kujeran da yake kusa da ni. "" Kina ta kallona!"" Ya ajiye comb din Yana gyara link din hannun rigarshi. "" Bar kallona!"" Dauke idanuna nayi kamar nayi kuka na tura baki nan, ji nayi ya saka comb din ya zungure bakina. "" Kada ki kara tura min wannan bakin domin ina iya hakuri da tuzarancina, amma ba zan iya hakuri da tsokanata da ake yi ba."" Kamar mai kunnen maciji a hankali ya mike ya koma can tare da tura min table tap ya ce. "" Oya fara aiki!"" Ba musu na fara aiki har Alhaji Mudansir tare da Alhaji Abbas kumo suka shigo dakin ina aiki tare da gaya mishi abinda yake a ciki, mikewa nayi na gaishe su, a wulakance suka amsa, na koma na cigaba da aiki. Magana suke mishi amma yadda yake latsa wayarshi kamar bai san suna wurin ba ya ce min. ""Bani hot tea!"" ""Ok sir!"" Na mike na"
"shiga haɗa mishi, Daddah ta fito daga ban daki, cikin harshen fulatanci Alhaji Mudansir ya fara faɗa."
"Zuwa tayi ta shafa kanshi Daddah tayi cikin kulawa ta ce mishi. ""Turaki wai baki amsawa kawunanki ba?"""
"Sai da ya gama shan kamshi kamar ba zai magana ba, kafin ya ce mata. ""Ni yaushe suka min magana?"" Yadda yayi maganar sai da nayi kamar an goge min zero plus, sake bude baki nayi ina kallon shi bakina cike da mamaki. ""Lubnah kin ji sun gaishe ni da jiki?"" Kasa magana nayi sai na kalle su, sai kuma na kalle shi, me yasa yake son involved dina cikin maganarsu? Jin nayi shiru Daddah kuwa ta rufe su da fada, yadda take shiga ba nan take fita ba, wani magana da ya fada na ga bakiɗayansu sun razana. Ban san me ya fada musu ba. Amma bakiɗayansu har Ita Daddah sai da na ga ta nime wuri ta zauna tare da fashewa da kuka. Bakiɗaya suka yi ta rantse rantse, ni kaina sai nayi na tsargu balle su. Shigowar Alhaji ELYakub da Uncle Auta, suka samu rigimar Daddah ya gaya musu dalilin kukanta, fulatanci suka juya Uncle Auta ya ce min. ""Taso muje na kai ki gida."" ""A'a ka bari zan kaita da kaina."" Cikin fada Uncle Auta ya ce mishi. ""Idan baka da hankali ne ya kamata ka nima, domin wannan haukar da kake ba shi dai sauya kome ba, ka zauna nan kada ka sake ka yi wani shirme da zai cutar da rayuwarta!"" Duk da ba da hausa yayi maganar ba, amma na fahimci kusan a kaina ake wannan maganar. "" Muje Lubabatu!"" Mikewa nayi na bishi. ""Lunah!"" Ya kira sunan da yake kira da shi. Juyawa nayi. "" Ki kula da kanki kin ji, idan wani ya miki kallon"
"banza ki gaya min."" Gyada kai nayi na fita."
Turaki
"Cire duk wani daurin da aka mishi yayi ya watsar ya zuba musu idanu. ""Alhaji Mudansir ka kira karen"
"farautarka, yanzu ko kuma wallahi birnin lagos ya mana kaɗan."" ""Hauka kake ne?"" Inji Alhaji Abbas. "" Daga turu nake karewar hauka. "" Yadda ya yi ta masifa da jidali zaka rantse da Allah akan wani abu ne can ko kan hatsarin da yayi ne amma ina tsabar masifa ba kan shi ba ne, kawai akan abinda Ubaid yayi ne, sai da Alhaji ELYakub ya kira Ubaid, kai an ga tashin hankali domin kuwa Turaki ya rantse idan Ubaid ya kara shiga harkan Lubnah sai an ya batar da shi. Shi kuwa Ubaid da ya ji maganar Turakin da kuma yadda ya rantse da Allah. Ya ce mishi. ""Akan mace zaka rabu da ni?"" Wani kallon banza yayi mishi bai"
"kara bashi amsa ba, abin har mamaki yake basu domin yadda ya nuna zai aikata kome tabbas."
"""Son yarinyar kake yi ne? Ka dai san sakatariyarka ce?"" ""Eh sanin haka yasa nace ya fita harkanta,"
"saboda sakatariya ta ce."""
"Jin haka yasa kowa ya sha jinin jikinsa, ya kara da cewa. "" Ko Taj ban yarda ka shiga harkansa ba. """
"Yadda ya haɗa da Lubnah da Taj wuri guda yasa suka fara tunanin cewa ai ba mamaki kawai don suna aiki ne da shi, amma Ubaid da Alhaji ELYakub ya mishi fada ya kuma juya kan Turanci ya mishi tasss domin fadar Turakin yafi ba Ubaid din. Haka suka tafi Alhaji ELYakub ya ce mishi. ""Ka fita hanyar mutanen nan, sannan ka daina saka Lubnah a cikin maganarmu, ina tsoron kada su cutar da ita ne, na"
"san kafin su san matsayinta abubuwa sun yi nisa."""
"Shiru yayi yana jin hakan ya ja wayarshi ya turawa Uncle Auta, sakon Ubaid domin ya jima da goge"
"number shi tin ranar da ya ce yana zarginsa, ai kuwa kamar bayan minti ashirin, sai ga sakon Ubaid yana faɗin. *Wato saboda Lubnah shine ba zaka gaya min da bakinka ba, sai dai ka turo a gaya min ka dai kula da kyau, domin mai son abinka yafi ka dabara* bai kula maganar ba. Bayan ya gama nan ma suka sake dasa wata drama shi da Alhaji ELYakub Kumo, yana tuhumar dattijon da boye mishi mutuwar auren Lubnah, wannan masifa na Turaki sai gyaran Allah, bakiɗaya dattijon ya rasa yadda zai yi da shi, ga rikon da yake da shi na cewa ai da gyara yaki gaya mishi mutuwar iyayensa yanzu ma ya kara laifi akan wani laifi wallahi idan ya kara boye mishi wani abu ba zai kara zuwa inda yake ba har abada. Tunda duk abinda yake yi baya gani. Rasa yadda zai yi da Turaki yayi ya zuba mishi idanun yadda yake rigima kamar wani"
Yaro karami.
***
"Tunda Uncle Auta ya dauko ni, yake kallon titi yana murmushi ya ce min. ""Ita rayuwa da kika ganta, tana"
"da sauki amma kuma saukin bai kai yadda kowa yake gani ba. Turaki ya takurawa mutane dayawa musamman da yake zargin da saka hannun wasu a mutuwar iyayensa."" Shiru yayi ya cigaba da tukin da yake yi har ya kusan isa gidan Ya Ado. "" Ba ina gaya miki haka ba ne, sai dai zuwa ranar Monday zai dawo aiki akwai abu guda biyu a gabanki, ki yi kokarin ganin sun daidaita da abokinsa na yarinta, na biyu ki yi kokarin ganin ya fasa koran ma'aikata domin kuwa akwai abinda yake yawo ina ga ya ci a ce kin fahimci haka."" Gyada kai nayi ya ce min. "" Lubnah Turaki ya ce kina mishi kallon mutumin banza, wallahi ba mutumin banza ba ne shi, na gaya miki gaskiya shi ba mutumin banza ba ne koda wani zai miki wata magana na cewa wani abu ya faru a past dinsa, mutumin kirki ne da ni har mamaki bane yadda aka yi bai ajiye wata mace ba, Turaki nagartaccen mutum ne da Allah ya sani har cikin raina nake jin shi domin kuwa shekaru goma na bashi, amma ina jin shi kamar dan cikina. Kin san irin halinsa kuwa? Ko yana son abu bana tab'a fitowa ya ce yana son wannan abin amma kuma zai tsaya akan abinda yake so da haka muke gane girma da kaunar da yake yiwa abinda yake so, bana son na cika magana amma na san tunda Turaki ya shigo rayuwarki zai matuƙar wahala wani ya miki kallon banxa, na ina gaya miki haka ba ne don na tilastaki kula shi amma kece mutum ba farko da yake iya bata lokaci yana magana da ke, ko yayi fada akanki. Kace mutum na farko da ya tafi har inda kike, a idanun duniya ke sakatariyarsa ce amma a maganar gaskiya ke kin wuce yadda ake tunanina, baki ga office din an sauya fasalinsa shirinsa ce, yana son ya nisanta ki da kowa ya zama ke daya ce a gefensa. Idan har haka ne gare ki, wani aiki ne domin shi dai bakiɗaya rayuwarsa da ayyukansa kaɗan ce ta yan arewa sauran dabi'unsa na turawa ce, amma ba ina gaya miki haka don bai da ilimin addini ba, hmmm kada ki latsa shi domin zai iya goge miki lissafinki. Ki nuna mishi girma da ƙaddara domin ta haka ne zai fahimci ba dukkan mutanen duniya ba ne azzalumai."" Kaina ne ya cika da magana na rasa ina zan fara shi kuma tashi matsalar kenan, bakiɗaya sai nake jin kamar anya ban so kaina ba? A hankali na d'ago kai tare da cewa.."" Me yasa sai ni?"" "" Ce miki aka yi daukarki aiki yayi? Tun ranar da ya ganki a cikin masu niman aikin, ya yanke a ransa ko kina da aure ko baki da aure zai ajiye ki a gefensa. Sanin cewa zai iya hana ki sakat idan ya gano baki da aure kuma haka zai iya shafar aikinsa yasa muka ji gaya masa cewa ai baki da aure muka ko nuna masa Kumo tana da alaƙa da Yayanki. A yanzu da ya mai da kanshi dan gidanku ya samo labarin rashin aurenki. Yana"
da kyau ki kara

297 / 321

Chapters