Advertisements
Chapter 302 Reading ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu

Author :  Mai Dambu Category :  Complete Novels

Chapter   302 / 321

903K to 906K   out of 962.4K words

nufi a cikin"
lamarin ko zaman da yaudara. Amma ina gayawa Aunty Nuratu Kafaya ta ce nayi shawara zata nima min
aiki a wani makaranta. Ai kuwa ban gayawa Ya Ado nace mata xan tafi sai CEO din mu ya dawo.
"Ban san cewa haka yake da fushi ba sai da na ce mishi ya jira na dauko mishi takardan barin aikin, na"
"zo wucewa ta gabanshi, ya fisgo ni gabanshi. ""Kul ki hada ni da wani ko kishiya zaki min dole sai bayan idanuna, wallahi sai na shayar dake mamaki!"" Kura mishi idanun nayi kafin na ce mishi.""Ni dai na gaji ka gaya min me kake so na biya ka abinda ka min oho dama ance muna zaman dadiro ko? To gaya min inda"
zan zo na baka jikina idan zai wanke maka zuciya da asarar da
"..."" Tass naji ya kwashe ni da mari, wallhi sai da na nime jina da ganina na rasa. Na kura mishi idanun"
"cikin wani irin kaduwa da tsoro nayi baya. ""Ni zaki nunawa jikinki don ina bin ki?"" Murmushi yayi ya ce min,"" kin yi kuskure amma zan bi yadda kike so amma ba ta wannan hanyar ba, ina da kudin da zan saye ki na gaya miki ni sayanki zan yi siyanki xan yi kuma ki saka idanun! """
"""So what? Don ka saye ni ina ba kai ka halicce ni ba? Kuma marina da kai yi ban yafe ba, don bani da"
"karfin da zan rama, da kake cewa zaka saye ni ba iska na kuma ba zaka tab'a samun nasara a kaina ba, Iyayena ba kwadayayyu ba ne, idan don kuɗinka da ka ke ganin ka saka yasa kake tunanin zaka saye ni kayi kuskure. Da shiga cikin wannan Masifaffen zuriarku gara na koma gidan tsohon Mijina duk lalacewar masa tafi kashin shanu, ka je can ku kashe kanku mutane da basu da imani. Idan don raina ne ba zan tab'a zama cikin azzalumai irinku ba, kai ma bibiyar rayuwraka ake."" Cikin fushi ya bar gidan. Na fashe da kuka a wurin wallahi ba zan taɓa shiga rayuwarshi ba, ba zan shiga ba gara ma da Allah yasa na koma"
gidan Ya Hafiz.
"Cikin wani irin gudu yake bai kallon gabansa,a garin shan wata kwana ya daki babbar mota, tuni motar"
"shi tayi wani irin tsalle, ta fada can yayi wani irin juyi motar tayi sai da ta fadi sau uku kafin ta dungura da"
"kanta, haka yasa mutane suka taru a kan motar aka fara ƙoƙarin ceto rayuwarshi..........."
(Hegiya mai kan doya ta kahe shi)
"[12/12/2025, 7:52 PM] Maman Walid: 11"
"Dakyar aka fitar da shi a motar aka wuce da shi asibiti, bayan na dauki wayarshi aka kira Auta, aka gaya"
"mishi halin da ake ciki. Ai kuwa hankalinshi ya tashi. Ya gayawa Ubaid kafin wani lokaci sun isa asibitin. Hankalin sun a tashe, duk wanda yake makusancin Turaki ya zo asibitin. ""Yaushe ya dawo da yayi hatsarin?"" Babu wnada ya iya bawa Uncle Auta amsa domin hatsarin ya zo musu bazata, sai bayan awa biyu aka fito da shi, yana barci ba wani ciwo ya ji ba buguwa, anan suka wuni zubur har dare koda ya"
"farka sallah yayi, anyi tambayar duniyar nan akan ya fadi dalilin hatsarin yayi shiru bai gaya musu ba,"
"amma kuma buguwar da yayi a kanshi sai da dare yayi jini ya balle mishi ta hanci da kunne, sai a lokacin"
"aka san ya ji babban rauni a kanshi, abin tausayi Daddah cewa take. ""Zaki tafi kamar Babanki ko? Zaki tafi kamar Aisha da ya bar ni da kai, kada ki don Allah."" Haka aka sauya mishi asibiti a daren zuwa babban asibitin Lagos ana isa suka shirya mishi aikin gaggawa domin idan jini ya taɓa kai zai iya samun matsala,"
"basu fito ba sai karfe shida na safe, aka fito da shi kanshi ya kumbura."
***
"Wurin karfe tara na safe, ina kwance tun jiya da ya tafi nake jin tashin hankali, ban kyauta ba sam ina jin"
"haka a raina amma ina tsoron kiranshi kada ya gaya min magana ina tsoron kada ya ce na gama gaya mishi magana zan kira shi na ce mishi me? Wayata ce tayi ƙara na ɗauka a hankali na saka a kunnena. Idanuna a lumshe. ""Lubnah baki da labarin abinda ya faru ne?"" Jim nayi na san cewa zai bani labarin an kore ni ne don haka na ce mishi."" Allah yasa haka shine mafi alkhairi, na gode da haduwa da kai, ka taimaka min sosai shima Ceo ba zan manta alkhairin da ya min ba, yanzu ya ake ciki yaushe samu yi maganar kudin da yake bin family kana tare da shi ne?"" Cike da mamaki ya ke kara cewa. ""Da alamu baki san abinda ya faru ba kenan? Mr Turaki yayi hatsari har an yi mishi aiki da safe nan!"" Wani irin tsoro ne ya kama ni na dafe kirjina kamar zai dirko na ce mishi. ""Da yaushe?"" Na samu bakina ya furta haka, ""Da rana wurin karfe daya zuwa biyu!"" Ji nayi kamar zuciyata zata faso fashewa da kuka nayi na ce mishi. ""Na shiga uku!"" Na fada da karfi ina me kashe wayar domin nasan na ce ni ce sanadin shigar Mr Turaki wannan halin Family dinsa sai sun daure ni, Allah yasa Ya Ado yana gida na fita da gudu zuwa kasa na cigaba da kuka. Allah sarki shi a tunaninsa ma ya zata an gaya min wani abu ne ya faru da Abba, ai kuwa ya riko hannuna da ƙarfi yana faɗin. ""Lafiya meye?"" ""Na kashe shi?!"" Na furta tare da rike bakina da karfi, na fashe da wani irin kuka. Na zube a kasa na cigaba da cewa. ""Na kashe shi Ya Ado ni ce nayi mishi magana, ni ce na gaya mishi magana, ni ce nayi sanadin hatsatinsa. Wallahi bani da yadda na iya ne, na gaji ne family dinsa ba zasu iya dakatar da shi ba, amma ni sun san dole na nisanta kaina da shi, idan"
"suka san ni ce zasu zo kaina!"" Murmushi yayi ya ce min. ""Kina sonshi ko?"" Cak na ji kukan ya tsaya na kalle shi, ""me yasa ka min wannan tambayar?"" ""Ok shi kenan gara ya mutu kowa ya huta!"" Rufe bakina nayi na shiga girgiza mishi kai. ""Eh kai meye amfanin saninki da yayi a rayuwarshi tunda bakya sonshi?"" Anan yayi ta zazzaga min magana da fada wanda ya sa naji kaina kamar zai fashe na ce mishi da karfi. ""Waye ya ce maka bana sonshi?"" Sai kuma nayi shiru, na kifa kaina a tsakanin cinyoyina, na cigaba da kuka. ""Kina sonshi?"" Gyada mishi kai nayi ina kuka. ""Da gaske kina sonshi ba wahala zaki bashi ba ne?"" Cikin shashekar kuka na ce mishi."" Ina tsoron kada ya min rayuwar Ya Hafiz ne amma wallahi ina sonshi"
"don Allah Ya Ado kada ya mutu!"" "" Shi kenan daina kuka in sha Allah ba zai mutu ba!"""
"Haka yayi ta rarrashina don nayi shiru ya kira Uncle Auta, ya tambaye shi ya gaya mishi. "" Ok zamu zo"
"asibitin ni da Lubnah."" Yana gama wayar ya ce min. "" Je ki shirya amma ki sani kasa ki sake ki yi wani magana idan muka je."" Gyada kai nayi haka na haura sama, na shirya sannan na sauko, muka tafi asibitin hankalina a mugun tashe, a lokacin da muka isa iya mazan familyn ne a bakin kofar sai kakanshi. Wani"
"irin kuka ne ya zo min, haka na isa na gaishe su kafin na isa bakin kofar da kana iya hango shi kwance."
"Komawa daya daga cikin kujeran wajen nayi na zauna tare da fashewa da kuka, Kakanshi kallona yake"
"yana murmushi ya ga yadda na daura hannu na kaina ina kuka, Ya Ado ya ce min. ""Tashi ki koma gida, tunda bakya jin magana!"" Hadiye kukan nayi hawaye na zuba, ""kina tsoron kada ya mutu ko?"" Kallon kakanshi nayi da yayi maganar. ""Me yasa kika zo bayan kin ce bakya sonshi?"" Wani irin bugawa zuciyata tayi, ""sun miki barazanar zasu miki wani abu ne ko?"" Hawaye ne ya shiga zuba min. ""Lubabatu Bilal yana sonki tun baki zama mutum ba, yana sonki tun da ranar da ya daura idanun akanki, Bilal kowa shakkarsa yake amma ke din kece rauninsa. Yana iya yiwa kowa tawaye har da ni kaina amma ke ya kasa sarrafa kanshi akanki, gani yake idan ya fito ta kowani fuska ya ce yana bukatarki zaku iya zarginsa da cewa ba don Allah yake sonki ba, Lubabatu Bilal ba kashin yadawa bane, yana da kudin da zai aure ki da karfin tsiya amma yana son ya ji da bakinki kina bukatar shi a rayuwarsa. Idan wani ya kara kiranki ya miki barazana akan Bilal ki gaya min kotu ce zata raba mu, amma ke idan kika cutar da Bilal Allah ne kaɗai zai mana hisabi, yana sonki yana kaunarki, yana tausayinki yana jin ciwon halin da kike ciki, yasan idan ya takura dayawa zaki fama ciwonki yasa yake nan a tare da ke, baki yi mamaki yadda kome naki yake tsaye a cikinsa ba, ga Bilal nan a karo na biyu idan ya mutu mun yi asara amma samun namijin da zai tsaya miki a matsayin namiji kuma bango ni dai nasan me na haifa, mahaifinsa kuma yasan me ya bar min, Ubansa a tsaye yake akan kome haka shima yake, shi din zagi ne a waje amma gabanki kamar dan tsako ne, ki"
"yiwa zuciyarki adalci tana buƙatarshi amma tsoronki zai kai ki ya baro. Ki yiwa kanki adalci yana bukatarki, mu kuma muna bukatarshi."" Yadda dattijon yake min magana da adalci yasa zuciyata ta bude hankalina ya koma bakiɗaya kanshi. A hankali na mike zuwa kofar dakin, ina kallonshi yadda yake barci a wahale ni ce ma jefa shi cikin wannan yanayin? Ni ce na saka shi a wannan halin? Yanzu nice na saka shi a wannan halin? Ni ce sanadi kenan.Durkusawa nayi kasa ma fashe da kuka, na rasa me yake mun dad'i.."" kai ta gida kada itama ta samu wani ciwon?"" Haka Ya Ado ya d'aga ni, ya kai ni mota sannan ya koma ban san"
"me ya faru ba, sai dai na ga kyakkyawa farin ciki a tare da shi. Ai kuwa zazzaɓi ya rufe ni."
"Yadda nake kukan ya matukar d'aga mishi hankali, har muka isa nasiha yake min, sai da Aunty"
"Zakiyah ta bani magani na samu kaina, zuwa dare kome ya dawo min. Tsoro da kunyar Kakanshi ya hana ni komawa asibitin har sai da ya cika kwana biyar, a lokacin Ya Ado yayi tafiya, lokacin da na je ni da Yaran Ya Ado suka raka ni. Ubaid na samu sai wata yar uwar Babanshi, shi ya tsayar da ni tare da nuna min shi ana wanke mishi ciwon da yake kafad'arshi, mutumin nan akwai taurin rai. Domin ko gizau kai yadda yake latsa laptop zaka tabbatar da cewa shi fa bai san ana yi ba, a hankali na kai hannuna kan kofar, d'ago kai yayi idanunmu ya hadu da juna. Wani haɗe rai yayi kamar bai taɓa dariya ba, kasa da kaina nayi ina jin wani irin kunya. Har matar ta gama dress din ta duba kanshi sannan ta fito daga dakin. Bude kofar Ubaid ya min muka shiga har da ɗan abin tab'awa nayi. Yaran suka isa gare shi ni ina tsaye rike da basket din na kasa motsi haka ya kula yaran har da ciro musu apple da banana, amma ni ko inda nake bai kalla ba, kasa motsi nayi ina kallon kasa. Wani irin tsoro yana kama ni, Yaran yayi ta tambayarsu. Ina tsaye a wurin aka. turo kofar dakin, Yan matan family ɗinsu ne, sai da suka kalle ni kafin suka nufe shi. ""Hamma ya jikinka?"" Murmushi yayi ya ce musu. ""Da sauki sosai?"" Badr da ta koma gefenshi kamar zata shige mishi, tayi ya iyayi har da kukanta, ni dai kaina a sunkuye sai wani abin isgilanci suke suna dariya, ina rike da basket din. ""Badr hada min ruwan zafi."" Da sauri na kalle shi, bai kalli inda nake na, na"
"sunkuyar da kai, haka ta shiga hada mishi sannan ta fito cikin kulawa take gaya mishi ta haɗa,kwalla da"
"haushi ya cika ni, amma wannan ba matsala ba ce da xan nuna akan idanunsu. ""Ku bani wuri na shiga"
"wanka."" Kafin su fita na riga su fita, koda Yaran suka fito na mikawa Ubaid basket na ce mishi. ""Allah ya bashi lafiya zamu tafi!"" ""Ki tsaya ya fito mana!"" Murmushi nayi na girgiza miishi kai na ce. ""Ai mun sallama da shi!"" Na kama hannun Yaran ina jin wata cikin yan matan tana jefa min magana amma ban kula da batunsu ba, muka bar asibitin. Gobe ma zan dawo jibi ma xan dawo ga ta ma zan dawo sai ya"
gaya min har sai ya gaya min baya buƙatar ganina a rayuwarsa zan tafi zan koma inda na fito.
"Haka da na saka a raina, har muka isa gida."
---
"Bayan tafiyarsu ya fito idanunsa yana kan kofa, amma kasancewar ya iya takunsa ko irin a fuska ya nuna"
"yana son ganinta bai yi ba, ya cigaba da abinda yake ta yi. Ganin yadda ya masu a gabanta basu san yayi amfani da su bane don ya cusa mata b'acin rai kuma yayi nasara, shigo da basket din, Ubaid yayi yana faɗin. ""Ga abinda aka kawo maka."" Kallonshi yayi da harshen larabci ya ce mishi. ""Ina take?"" ""Ba kunyi sallama ba?"" Murmushi yayi yana daga cikin abinda yake karawa zuciyarshi kaunarta tasan kanta, ""zuba min abincin?!"" Haka ya shiga zuba mishi abincin, masa ce da miyar koda. A hankali yake ciki da dumi kuwa. ""Ka mata bakin hali ko?"" Ubaid ya tambaye shi, banza yayi mishi ya cigaba da cin abincin. Yasan idan Ubaid ya san me tayi mishi da kanshi zai ce ya hakura da ita. Amma ya kalli kwanon yadda yake cikin abincin. ""Hamma ka hana bazawarar ce zuwa mana? Babu amfanin zuwanta wurin ka."" ""Wurinki take zuwa? Idan da ke ce kika samu irin darajar da take da shi ai da kin hauka ce."" Inji Ubaid, "" kallonsu yayi da kyau ya ce mata. ""Na san dukkanku nan babu wacce bata taɓa kwanan a waje ba?"" Tsuru-tsuru suka yi suna kallonshi. "" Ita kuwa saboda tarbiyyar da aka mata, ko hannunta wani namijin bai rike ba sai wancan Tsinannen yaron da ya aure ta. Ina sonta ne don ita din ta cancanci zama uwar Yarana."" Murmushi yayi ya ce musu. "" Kuna son aure na ne don abinda nake da shi ita kuma tana gudu na ne saboda abinda nake da shi, kada wata rana na kalle ta nace ta aure ni saboda abin duniya da nake da shi"
ne........
"[12/12/2025, 7:52 PM] Maman Walid: 12"
""" Ku kanku baku da qualified na matan da nake son aura, baku cancanci na aure ku ba. Ita din rabi da"
"kwatan rayuwata ce, duk abinda xan yi mata ina yi ne don ta san ko babu ita xan rayu kuma zan iya rayuwa da wata mace bayan ita, ina son ta san da cewa akwai mata dayawa da suke bina ina gudunsu ba irinku da basu da aikin yi ba. Sai harin abinda ba nasu, kada na kara jin wani ya zage ta ban hana ku zuwa amma wata tayi mata kallon banza zata gamu da ni."" Daga haka ya cigaba da abinda yake yi."
Domin yayi imani a ransa zata dawo.
***
Tunda na isa gida na ji a raina kamar kada na kara dawowa amma kuma sai na ji ina son na kara komawa
"domin na ji yadda yake ji, haka na kwana susuku. Washi gari kuwa bayan Aunty Zakiyah ta tafi aiki"
kasancewar Yara suna hutu na kara shiryawa muka tafi asibitin da safe. Lokacin da naje na samu har su
"Uncle Auta, gaishe su nayi suka ce na shiga ana mishi dress juyowa nayi zan fita ya cewa Yaran. "" Adil! "" Kallonshi yayi a tsorace ganin yadda ake wanke mishi gefen cikinsa yana murmushi. Juyowa nayi na kalle shi, shima ni ya kalla ganin yadda na zare idanu ana wanke ciwon, wani irin kallon banza ya min ya mikawa Adil hannu. Ya zo ya rike shi ban san me suke fada ba, amma yaron ya daura kanshi a kafad'arshi, shi kuma yana shafa bayan Adil kama sauran yaran nayi muka fita wani irin tsoro yana kama ni. Zama nayi kamar zan yi kuka, na ce. ""Haka ake mishi wankin ashe jiya ban ga kome ba?"" Na fada ina shashekar kuka, dariya Uncle Auta yayi yana faɗin. ""Kin ga shi da yake haka yake bai san wani emotional ba, shi"
"yasa kika ga idanunsa babu tsoro ko karaya. Kece rauninsa idan da zaki shiga damuwa sai yafi ki shiga damuwa."" Murmushi yayi yana kallon yadda nake rike basket din Abincin, hawaye ya shiga zuba min kamar zan cire ciwon a jikinsa na dawo da shi. A hankali na tashi lokacin yana bawa Adil ayaba yana ci tare da nuna mishi dantsen shi. Ina shiga Adil ya fito daga dakin. Kallonshi nayi a hankali na taka zuwa gabanshi jikina a mace, wayarshi ya dauka yana dannawa. Yadda na zauna na ce mishi. ""Am sorry!"" Mutumin banza yayi kamar baya dakin, nayi ta bashi hakuri, ina kuka amma bai ce min ci kanki bai ce min ba, tashi yayi ya bar ni a dakin na sha kukana sannan na mike tare da barin dakin, kafin ya fito mun"
bar asibitin.
"Haka nayi ta jera zuwa asibitin amma babu abinda yake hada mu, baya ce min uffan. Ranar da na je"
"na karshe aka ce min an sallame shi, sannan aka bani basket din Abincin da nake kaiwa. A kasar basket faɗin takarda ce da dan girma na bude kudi ne dubu dari. Sai yar shot not."
"*Kada ki nime ni, ki koma wurin Ex dinki! Na yanke alakata da ke har abada* sai na ji abin kamar a"
"mafarki gashi bai ambaci sunan Hafiz balle na ce kishi ne, tow bai ambata ba, sai nayi ji kamar zuciyata ce ta bar gangan jikina, haka na durkusa a wurin, wani azazzaben tsoro ya shige ni mai cike da

302 / 321

Chapters