Advertisements
Chapter 312 Reading ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALAƘAR ZUCI BOOK 1& 2 by Mai Dambu

Author :  Mai Dambu Category :  Complete Novels

Chapter   312 / 321

933K to 936K   out of 962.4K words

da Turaki ya mishi shegen duka, ya bar Lagos ya dawo ya shirya da kyau, sai dai Me yana isowa"
"Jama'are, ya samu labarin Karima ta zo ta kwashe Yaranta, wani abin tashin hankalin Yaran da yake ta"
"zargin na shine ta ce a gaya masa Yaran ba nashi ba ne, Yaran da ta haifa na tsohon saurayin ta ne,"
"sannan kada ya ce zai nime ta domin ba zai same ta ba. Kusan hauka ne Hafiz ne bai yi ba domin sai da aka daura shi a gadon asibiti, daga karshe aka tura su asibitin Bauchi domin abin kamar zai saka shi hauka, kafin aka shawo kan matsalar, tun da ya dawo hayacinsa ya tuna ya kashewa Lubnah bata mahaifarta bayan shine baya haihuwa, ya wulakanta Lubnah akan Yaran kai duk abinda yayi na mugunta sai gashi yana dawo mishi, haka zai zauna yayi ta kuka. Domin yasan yanzu kan Lubnah ta mishi nisa,Ita kanta Jalilah da ta fahimci Hafiz din da ta sani ba shi ne yanzu, sai ta fara niman hanyar da zata rabu da shi, ranar wata Alhamis bayan isha yana zaune ya zubawa tv idanu. Ta zo ta zauna da takarda da biro ta mika mishi. ""Ina son ka sake ni, domin kaima kasan naka haihu ana aure don a hayayyafa ne kai kuwa baka da wannan damar."" Murmushi yayi sannan ya ce mata.""lokacin da nake tare da Lubnah kina daga cikin mutanen da suka yi ta zuga ni na rabu da ita? Na kara mata kishiya, nayi yadda nake so amma yau an wayi gari don bana haihuwa ki ce zaki rabu da ni? Ina soyayyar da kike min Wanda yasa kika gagara zama da mazankina baya? Yanzu bani da amfani zaki guje ni. Ai ba zan iya rabuwa da ke ba domin sai na"
"fanshe sadakina sai na rabu da ke."""
"""A'a Hafiz ni bance ka rabu da Lubnah ba!"" Murmushi yayi ya bai kara magana ba, yana kallonta tare"
"da nazarin abinda zai mata yadda zasu yi balance. Haka ta bar parlourn yayi ta nazarin, ya rasa Lubnah har abada, ya sani kashedin da Mijinta ya mata kaɗai ya razana shi amma ya zai yi? Yana son Lubnah ko wani hali yana son ya rabata da kwanciyar hankalin gidanta. Yana son ta fuskanci halin da yake ciki, amma yasan ko me zai yi ba zata tab'a dawowa gare shi ba. Amma kuma yana da hanyar da zai dawo da"
ita gare shi ko bata dawo ba itama ta fuskanci yadda yake ji.
"(Labarin Hafiz ko ba zance muku kai tsaye gaskiya ba ne, amma kuma akwai maza ire-irensu da suke"
"ganin idan basu sami yadda suke so ba, gara ayi ragas kowa ya rasa, sannan idan suka ga mace ta samu"
"nasara a Rayuwarta bayan rabuwa da su, sai su fara jin ciwo da bakin ciki burinsu su ga ta wulakanta. Allah yasa mu dace!) Amma kafin ya zo ga Lubnah sai ya fara ta kan Jalilah."
**
Allah ya gani ta kowani fuska Ni da mijina muna samun zaman lafiya. Sai dai kuma yadda wasu
"abubuwan suke faruwa da barazanar da nake fuskanta yasa na gayawa Mama, murmushi tayi tana faɗin. ""Ai ko na kwantar da hankalina, miji mata hudu ne shi, ba xai yiwu ki ce ba zai kara aure ba, idan kika ga haka shine maslaha ki kwantar da hankalinki, idan kuma kika fara fuskantar matsala ki min magana nazo na dauke ki."" Sai na samu nutsuwa ko ba kome Mahaifyata tana tare da ni, ko sun yi magana da ita ne naga ya dan damu da zuba mishi idanu da nayi, har ya kai ni gidan Ya Ado na wuni sannan ya dawo da ni"
gida.
"Sannan wani abu da na kara fahimta, mutum ne da ba zai yiwu ya boye maka kome ba, amma dan"
"zaman da nayi da shi sai na hango mutane biyu da suke tare da shi, kusan kamar shine yake kulawa da su."
"Akwai wani abu da na kara yarda cewa mutum ne shi mai matuƙar kishi, hana Ubaidullah shigowa"
"gidansa. Haka idan ka ga Uncle Auta a cikin gidan nan, tow abu me muhimmanci ne ko tare suke,"
"tsakaninsa da Ubaidullah parlourn baki ni kuwa bana tab'a shiga domin kai tsaye ya gaya min, Ubaid da Uncle Auta, suna da tsalle shi kuma yana da kishi, idan ya wuce gaisuwa don Allah bai yarda na sake da su ba. Sannan idan baya gari duk abinda zasu kawo min iya waje zasu tsaya su bada a kawo min cikin"
gidan. Wannan yasa ko gidajensu ban cika zuwa mazan nan ba.
"A watan da muka cika wata uku da aure ne, wata makociyar mu ta haihu. Suka gaya min da yake yar"
"arewa ce. Matar Uncle Auta ta gaya min ta waya, yana dawowa daga Office bayan ya ci abinci na gaya mishi. Murmushi yayi ya ce min. ""Ok sai kin dawo!"" ""Na gode sosai! Ai sai gobe zamu shiga gidan!"" ""Tow Allah ya kai mu!"" ""Amin Ya Allah!"" Bayan ya gama cin abinci muka dawo parlourn ina jikinshi aka buga kofar gidan, kallon juna muka yi ya mike ya fita can sai gashi da Matar Ubaid, Maman Nihla. Zama tayi na tashi na kawo mata ruwa na ajiye mata. Sannan na koma dakina. Ban san me ya faru ba amma yadda take kuka da mishi bayani da fulatancin yasa na fahimci rigima ce. Kwanciya nayi na cigaba da abinda nake yi da nake da Aunty Hindatu. Muryan Ubaid na ji sama-sama, fada kamar zasu daku. Har sai da na fita don na ji maganar da hausa Mr Turaki yana faɗin. ""Ai gaskiya ne akan me xan barka ka shigo min gida, bayan nasan waye kai, na san halinka matarka baka tsaya a kanta ba, baka Musulmi baka Kirista, me kake son cimma? Idan ba rashin mutunci da rashin arziki ba."" Fitowa nayi suka juyawa zuwa gare ni. Allah yasa da hijab har kasa, ""Me kika fito yi?"" Ya daka min tsawa, juyawa nayi na koma dakin. ""Ai na gaya maka ni matata sirrina ce, har abada ba zaka tab'a samun damar kare mata kallo na, kayi focus din matsalarka. Idan ka rungume matarka zaka fahimci nimar da Allah ya maka, ita Lubnah da kake cewa matarka tayi koyi da ita ka manta yadda muka yi da kai ne? Don Allah kada ka lalata min aurena domin ni"
"ban shiga rayuwar gidajenku ba."""
"Da haka na fahimci idan matar shi tayi mishi wani abu yake huce haushinsa akanta bata iya kome ba,"
"ga Lubnah nan tana yin abinda ya dace a gidanta, dama ba shiri muke da ita ba, ashe Mijinta ya kara a abubuwan da zai kara dagula lissafin kome. Kawai sai naji zuciyata bata min dad'i ba......"
"[12/23/2025, 12:47 PM] Maman Walid: 25"
"Don haka suka gama rigimarsu, ya shigo zai min masifa na saka mishi kuka. Ganin yadda nake kukan da"
"gaske sai ya rungume ni yana shafa baya har nayi shiru. ""Dayawan mutanen da suke kusa da ni idanunsu akanki yake ni kuma kishi ne da ni kamar na cire zuciyata na fitar da shi waje. Ina sonki dayawa don da na kasa boye shi, sorry idan nayi kuskure ki yi hakuri kin ji!"" A hankali na janye kaina daga jikinshi, zuwa"
"yanzu na fara jin tausayinsa be mess with everyone domin ni. ""Kin yi shiru?"""
"""Tsoro nake ji, tsoron kada kishi ya cigaba da ruguza zamanmu!"" Na faɗa ina shashekar kuka."
"Murmusa min yayi tare da rike hannuna, ya ce min. ""Tabbas ina kishinki, ina kishin wasu mazan su kalle ki. Ina kishin idan na tuna duk tarin ni'imar da Allah ya miki kafin ni wani ya fara ɗanɗanawa ina ji kamar na mutu, a duk lokacin da na tuna Hafiz ya fara samun kusanci da ke kafin ni sai na ji ban cancanci haka daga kowacce fuska. Look ina da zafin kishi wallahi ina ji kamar ni ɗaya Allah ya halitta da kishinki."" Ya d'ago kai yana kallona idanunsa sun jajjur murmushin karfin hali yayi kafin ya ce min. ""Ina da kishi"
"sosai!."""
"A hankali na janye a jikinshi, na cigaba da kuka, zama yayi a kusa da ni yana faɗin. ""Amma ba ina bin"
"abinda zuciyata, ta saka ni ba ne,. Kawai abu daya na san ina yi shi ne kaurace miki, dole na ke saka kaina"
"a tare da ke, nayi ƙoƙarin danne haka amma ina."""
"Aure wata uku zuwa hudu yau Turaki yake gaya min yana kishina, kishin da yake yasa shi kaurace"
"min? Kallon kasa nayi ta yi ina jin kamar zuciyata zata buga. A hankali na matsa daga kusa da shi na koma can gefe. Nayi shiru na rasa me zan yi na huce idan nace ya sake ni ma ba zai sake ni ba. Don haka nayi shiru ban kara magana ba, sai dai shi a lissafinshi ai ya fada min abinda yake ranshi ne, don na daina jin zafinsa, ni kuwa sai nake ganin gara mu rabu kowa ya kama gabanshi. Idan ba haka ba, a banza zan ta"
cuta da sunan kishin da yake ji da shi.
"Duk yadda yaso ya rarrashe ni, zan ture hannunsa ina murmushi. "" Na fahimce ka ai! "" Daga haka na"
"datse duk wani abin da yake tsakaninmu, daren ranar ban shiga dakinshi ba da ya zo yana tambayar ko abinda ya fada ne ya saka ni ware kaina daga gare shi na girgixa kai nace mishi, ga ""period nake bana son Magana!"" Kuma nayi dace period din ya zo, don na samu sauki na bar shi, haka yayi hakuri ya koma dakinsa, na kyale shi ya zauna shi ɗaya. Washi gari, ban tashi nayi abin karyawa da wuri ba, ina tashi na hada mishi tea da bread da egg, na koma na kwanta. Lokacin da ya shigo dakin ina juyin ciwon ciki, ""ko za mu tafi asibiti ne?"" Girgiza mishi nayi tare da cewa. ""Ba damuwa ka je ai ba kome."" Haka ya bar gidan da kyar shima sai da ya makara. Wurin karfe biyu na gama abincin dare da na rana, don ya ce zai zo duba ni. Haka na gama kome nayi wanka, da ya tashi zuwa sai gashi tare da Airah. Yadda take wasu abubuwan yasa na kai zuciya nesa. Murmusa mata kawai nake, har ya ci abincin ya kalle ni cikin kulawa ya ce min.. ""Ya jikin naki?"" Murmushi nayi kawai na cigaba da cin apple. ""Da sauki ko?"" Lumshe idanuna nayi ina gyad'a mishi kai. ""Allah ya baki lafiya."" Tura mishi sako aka yi ta wayar ya duba, tare yanayinsa ya sauya. Ya kalle ni da kyau sai ya cire hannunsa a cikin abincin yana faɗin. ""Na koshi!"" Ya fada yana ture plat din, murmushi nayi na tashi na hada juye wanda ya ci na gyara wurin, ya ce min.""mu koma!"" ""Allah ya kiyayye hanya!"" Na shige kitchen a bisa ka'ida raka shi nake, amma na barshi ya fita shi kanshi sai da ya juyo ya kalle ni, sannan ya bar gidan. Sai da na shiga kitchen hawaye yayi ta zubo min. Haka na sha kuka"
"na ban gayawa kowa ba, shima kuma ban san dalilinsa nayi haka ba,"
"Wurin karfe hudu da rabi, na fita gidan Uncle Auta, muka tafi gidan barka a can muka hadu da Matar"
"Ubaid, kamar yadda ta yi kamar bata ganni ba, haka nayi kamar ban santa ba, na cigaba da danna wayar ita kanta mai jegon da yake kawarta ce da kyar ta amsa min, ban yi karambanin a bani yaro ba, daga kan cinyar Matar Uncle Auta na kalle shi, daga nan na cigaba da uzurina. Ba zaka fahimci yadda abin yake ba, kusan kowa a gidan sai na fahimci kamar baya maraba da ni, har muka fita daga cikin gida, bayan mun dauko hanya ne matar Uncle Auta take tambayata. ""Wani abu ya haɗa ki da Maman Nihla ce?"" Girgiza kai nayi ina kallon kasa. Na d'ago na ce mata. ""A'a."" ""Tow shi kenan!"" Daga haka muka isa gidanta na zauna kadan sannan na wuce gida, ina shiga na same shi yana aiki, ""sannu da dawowa!"" Ya ce min, murmushi nayi na yi nace mishi. ""Yawwa!"" Na wuce dakina na barshi a parlourn yana aiki, kiran sallah"
"Magariba yasa shi lekowa ya samu ina tattara wasu takardun, zuba min idanu yayi kafin ya ce min. ""Me"
"zaki yi da su?"" Murmushi nayi mishi, na ce mishi. ""Ina shiri ne in case."" Daga haka na cigaba da aikina. Kai"
"wasa wasa sai da muka shafe sati uku zuwa wata guda hala har ya manta ya gaya min bakar magana, tafiya ta kama shi Russia, mutumin nan na zata zai ce min na shirya mu tafi amma ya wani hada kayansa yayi gaba, ni kuwa na hada nawa kayan na wuce Bauchi don tsabar masifa mota na bi, balle har ya bincika ya ji labarin inda naje, zuwa yanzu watanmu hudu da sati biyu, a cikin watannin nan bai wuce a"
"kirga hada shimfidar da muka yi, haka na shanye duk wani b'acin rai."
"Kwana biyu me kyau muka yi a hanya, muka iso Bauchi kafafuna sun kumbura. Sai da na wuta"
"sannan na dauki keke napap, zuwa gidana da yake G. R. A. Ya samu me kula da gidan yana waje, na isa cikin farin ciki ya amshi jakata yana tambayar ya hanya? Na ce Alhamdulillahi, na shiga bayan ya bude min, sannan na shiga cikin gidan. Kasancewar isowar safiya ce mika mishi atm nayi na ce mishi. ""Don Allah ayi min cefane, sannan ka haɗa min da dankalin turawa, kome dai ka kawo min and ina niman"
"alfarma kada wani ya tambaye ka, nazo kace na zo don Allah!"" ""In sha Allah Hajiya."""
"Daga haka na wuce cikin gidan na shiga aiki, nayi wanka na gabatar da Sallah da ban samu ba asuba,"
"kwanciya nayi wurin minti arba'in ya dawo da kayan abinci, na amsa na kai kitchen ya ce min. ""Hajiya nayi karambanin saya miki nama gasu nan!"" Na ce mishi. ""Na gode sosai!"" Daga haka na y fita na duba kayan na kai kitchen na duba kudin da ya cire na ciro 5k na kira shi na bashi, sannan na koma na kwanta, wani sabon aiki na ga ba gas haka na kira shi ya fita ya sayo min gas sannan na yi abinci na saka mishi, da"
"daren na kwanta nayi barcin gajiya, wayata a kashe babu yadda zaa same ni."
Lagos.
"Kwana biyu me kyau Mai kula da gidan yayi ya ga bana ko fitowa, haka yasa shi zuwa gidan Ubaid don ya"
"ga fitar Uncle Auta, da yake ya san gidan ya shiga ya samu yana shirin tafiya aiki. Bayan ya gaishe shi ya ce mishi. ""Oga Iyawo yau kwana biyu bana jin motsinta, ban san me ya faru ba, ko zaka zo la ga jiran ne?"" ""Kuma lafiya?"" ""Ni dai kwana biyu kenan bana jin motsin ko karatun da take sakawa bana ji."" Gyada kai yayi kafin ya ce mishi. ""Jeka ina zuwa!"" Ya koma cikin gidan, ya samu Matarshi tana bawa Nihla abinci.. ""kin san inda Matar Turaki ta tafi ne?"" Wani shewa ta saka tana faɗin. ""Ni kuma zaka tambaya? Waye ya san inda take bayan kai tunda abokiyar harkallanka ce."" Bai kulata ba, ya fita zuwa gidan Uncle Auta, ya tambayi Matarshi, ta ce mishi. ""A'a bata zo!"" Kanshi ya shiga duhu sosai. Don haka ya zo gidan ya duba bana nan babu alamar inda nake, kasan kiran Turaki yayi ya kira Uncle Auta suka shiga tattaunawa. "" Haka kawai Lubnah ba zata tafi haka ba, akwai abinda shegen ya mata wallahi ba zata tafi"
"ba. """
"Haka suka yi ta jajjantawa, kai karshe Uncle Auta ya kira Alhaji ELYakub ya gaya mishi amma ya ce"
"kada ya gayawa Turaki. Haka dattijon yaji abin kamar saukar aradu, kwanakin da suka biyo baya. Abin ba dad'i Uncle Auta ya je gidan Ya Ado ya tambaye shi ko na zo ya ce mishi a'a. Bai yi saurin fitar da maganar ba, zuwa gida abu daya Ya Ado ya gaya masa.."" Lubnah ba yarinyar ba ce, sannan tunda ta bar"
"gidan Turaki da kafarta imma tayi haka don ta fahimtar damu cewa tana zaune amma bata jin dadi, ko"
"kuma an je har gida anyi mata abu ta ji haushi ta fita. Idan baka manta ba, da aka bashi ita mun gaya"
"masa idan ba zai iya ba ya dawo mana da ita, idan har gazawar tashi ce tow tabbas Turaki yayi abinda ba xamu iya yafe masa ba, idan kuma ita tayi kuskuren zamu hukutatta daidai da laifinta."""
"Uncle Auta ya shiga tashin hankali, domin zarginsa akan family ɗinsu ne, don haka yasa hukuma cikin"
"lamarin, a wannan lokacin zuriar KUMO suka fahimci girma da darajar Turaki baya nan amma yadda Mahaifinsu yake barazanar tsine musu albarka. Suka yi ta rantse rantse. Al'amarin da ya janyo suka ji a ransu lokaci yayi da zasu bar Turaki tunda na da zinari aka halicce shi ba, gwanin har kwashe sati daya ba labari kawai aka kira shi aka gaya mishi. Duk abinda yake ya dawo gida fa, lubnah ba a san inda take ba,"
wani abin yafi kome tsaya mishi a raina.
"Cikin abinda bai wuce 10hrs ba, sai ga Turaki a lagos, kamar wani zarrare. Haka ya zauce aka yi ta"
"nimana, Ya Ado ya hura mishi wuta ya nimo ni, shi kuwa ya rasa inda zai saka kanshi. Haka ya je Airport ds taimakon shugaban airport ɗin ba a samu wani labari ba. The next abinda yayi shi ne fara binciken ta ina zai samo ni. Ya kira Mama yayi shiru kafin ya gaya mata gaskiyar abinda ya faru, shi a tunaninsa ya fadi haka ne don ya rage wani wage da yake tsakiyarmu, amma ina abinda ya fada a wannan lokacin Mama ta ce mishi. ""Idan ka samo min ita ka haɗa da takardar shaidar saki ka kawo min, na zata kai me"
"hankali ne ashe sakarai ne, ok idan ka samo ta ka dawo min da ita don ta gama aure da kai."""
"A lokacin da ya tafi gidan Kakanshi ya gaya mishi, abinda ya faru. Kifa mishi mari yayi har sau biyu."
"""Mutumin banza kawai gata hauka ne, a shekarunka idan baka yi hankali ba yaushe zaka yi hankali ga matar Kanin Ubanka, matar Ubanka ya aura har da

312 / 321

Chapters