Author : Mai Dambu Category : Complete Novels
tashin hankali, sai naji kamar bani da amfani akan kome. Na ji kome na duniyar ya tsaya min cak, tausayin kaina da rayuwata. Haka na kwashe minti goma har aka fara min magana na tashi da kyar na dauki jakata da"
"basket din da wanda na kawo abincin, na tsare abin hawa ina kuka yau."
"A can nesa da inda take durkushe Ubaid ya ce mishi. ""Wallahi ta tuba kada ka mata haka, hukuncin yayi"
"zafi ka saurare ta."" Sunglasses dinsa ya saka ya ce mishi. ""Matsalata ce ba taka ba, muje gida."" ""Gaskiya you too heartless, haba ka ga yadda take tafiya har."" ""Uncle Auta matata ce kake fasala tafiyarta wallahi"
"zamu samu matsala da kai!"" ""Allah ya baka lafiya!"" Daga haka suka bar asibitin."
"Akwai karamin hauka da wanda ya dara soyayya yake, wnada na fahimci cewa ina cikin waɗanda suka"
haukace ko suka zauce a kan sha'anin zuciya. Bakiɗaya na ji kome ya tsaya min cak. Tunda na dawo gida
"na gane bani da hankali, sai na ga ashe da ban yi kome ba, domin a daddafe na yi kwana biyu me kyau na"
"uku kuwa sako nayi ta tura mishi both what'sp da Text message, amma babu reply sannan uwa Uba ko zan kare ranar ina kiranshi wayarshi baya shiga, kaina ya kunce bana son fita koda waje, ina nan zaune na rasa meke min dad'i. Haka na kira Mama ina kuka na kasa magana. "" Ba kin ce gidan Hafiz zaki koma ba? Tow wata sati na ce Yayanki ya dawo dake gida sai ki ji dadinki. Tunda gidansa kika zab'a amma ki sani ko namarki Hafiz yake yanka yana gasawa wallahi ba abinda ya dame wawuyar banza shi kuma Turaki Allah ya bashi budurwa ba ma ke da wani ya gama da ke ba, ba wani baki da lafiya. Lafiyarki lau"
"iskancin ne kawai da renin hankali mara kunya wacce bata da godiyar Allah."" Tayi ya fada kafin ta ce min."
"""Ki sani tunda Hafiz kika zab'a bani ba ke, ki je kada ki sake ki shiga inda nake na gaya miki."""
Zan iya cewa ko abinda nayi Mama da Yayuna basu dauki zafi kamar yadda suka dauka don sai na ji
"ina tsoron kiran kowa bayan Ya Ado. Shi ɗaya yake saurare na. Bayan ya dawo ya sake min fada da nasiha. ""Ya Ado ka ba Mama hakuri tayi hakuri, wallahi ba zan kara ba."" ""Ya isa haka in sha Allah babu abinda zai faru."""
"Fushi Yayuna mata suka dauka, kusan na rasa inda xan saka raina. Karshe Taj na kira na tambaye shi"
"ko Oga yana gani ya ce min eh yana nan."" Don Allah ka zo ka kai ni na gaishe shi."""
"Shiru yayi kafin ya ce min. "" Ok zan zo yanzu!"" Wata Turkish gown ma saka, sai mayafi da na lallube"
"jikina da nayi da shi, na fita tare da yiwa Yaran sallama na fita bayan na turawa Ya Ado sakon zan fita. Taj ya zo ya dauke ni na ce mishi. "" Na gode amma ka taimaka min mu saya mishi fruit! "" Tunda na shiga ya ce min."" Amma wani ya taba gaya miki kina da kyau? Gaskiya kin haɗu. "" Haɗe rai nayi ban kuma magana ba, har muka isa inda na saya mishi fruit, muka nufi gidanshi. Sai magana yake min amma naki amsa mishi. Har muka isa gidan, yana tsayar da motar na saka kai xan fita rike hannuna. "" Meye haka ina miki magana kin share ni?"" Juyawa nayi na kalle shi, kafin na kalli hannuna. Yadda na mishi wta irin kallo sai da ya ji tsoron sake ni yana cewa."" Sorry na jima ina son na gaya miki gaskiya ina sonki!"" Murmushi nayi mishi sannan na ce mishi. ""You too late, domin ni da CEO muna son juna!"" Da wani irin sauri ya cire hannunsa a kan nawa yana faɗin. ""Don Allah kada ki bari ya san da wannan zancen wallahi zai iya korana."" ""Ni ba haka nake ba, amma ka kula sosai kowacce kwarya da abokin burminta."" Daga haka na fita a motar, haka na fito dauke da abinda na sayo mishi na nufi cikin gidan. Da sallama yana tsaye jikin window, yana juyowa muka yi ido hudu da shi. Sunkuyar da kai nayi ina wasa da jakan hannuna. Takowa"
"yayi ya wuce ni zuwa upstairs, wani irin abu na ji, ina tsaye sa ga"
Airah tana saukowa a hankali. Wani irin rufewa idanuna yayi na sunkuyar da kai ina ambaton Allah.
"Bayan ta fito ta wuce kitchen. Bai sau ko ba ita kuma bata ce min na zauna ba. Haka na cigaba da tsayuwa har zuwa wani lokaci. Ya sauko daga sama sanye da wasu kananan kaya a jikinsa. Idanuna yana kanshi. Na ce mishi. ""Ya jikinka?"" Kamar bai ji ni ba, ya wuce na ajiye mishi kayan a sama inda yake na ce mishi.."" nazo na kara baka hakuri ne!"" Sosa kunnensa yayi yana latsa wayarshi, da na cigaba da magana tashi yayi ya riko hannuna ya janyo ni ya kai ni bakin kofar ya ce min.. ""kada ki kara zuwa inda nake!"" Ya"
"bude min kofar, zuba mishi idanun nayi na ce mishi. ""Ba zaka kyale ni haka, ka gaya min ba bukata na ne"
"a rayuwarka ne? Idan ka fada min haka wallahi zan tafi na rantse da Allah zan tafi, ba zan kara zuwa gare"
"ka ba amma idan ka ci-gaba da tureni zan cigaba da zuwa har sai ka gaya min abinda yake ranka."""
"""Zan rufe gidana kin ga yarinyar da zan aura tayi shiru kada ta ji babu dad'i."" Haka ya saka na fito, na"
"tsaya a kofar shiga gidan, ina tsaye har danginsa suka zo, babu wnada ya ce min ke uwaki. Ko sun yi maganar ne sai ga Uncle Auta, ya shigo bai shiga ba ya ce min. ""Zo muje!"" Girgiza kai nayi na ce mishi. ""A'a ba zan tafi ba sai ya gaya min me yasa yake ture ni.""yayi juyin duniyar nan amma naki binsa Sai da ya shiga sai gashi ya fito. Amsar key yayi ya wuce ni, na tashi na bi bayanshi. Tunda na shiga motar yake waya da harshen Russian, bai fada wayar ba har muka isa gidan, dab zamu shiga kwanar ya mai da wayar video call. Wata har dattijuwar baturiya ce ta ce min. "" Labobu;"" kallonshi nayi fuskarshi a haɗe, gaishe ta nayi da harshen turanci ta amsa mun jima muna magana tana min tambayoyi ina amsa mata, kafin ta juya cikin taushin murya take rarrashinsa, ban san me take ce mishi ba, naga ya sake mata"
murmushi. Nima sai na tsinci kaina da murmushi.
"Bayan sun gama ya karasa da ni gida. Sai da na zo fita ya ce min. ""Ki daina zubar min da mutunci, idan"
"zaki yi haukarki ya tsaya ina nan, kada ki kara zuwa kada ki kara kusantar inda nake idan ba haka ba, zan miki wulakancin da kare ba zai ci ba, wai ke an taɓa yin wa mutum dole ne? Bakida zuciya ne? Kada na kara ganinki a gidana. Idan na kara ganinki nasan me kike nufi da haka!"" Ya fara min wani irin kallo irin"
"na yan iska, da sauri na kare kirjina tare da yin baya, ban san lokacin da hawaye ya zubo min. Na ce mishi. ""Hakuri nake baka, ni ba yar iska ba ce amma tunda kallon da kake min in sha Allah ba zan kara zuwa ba, idan na kara zuwa ko na kulaka suna na ba Lubabatu ba ce!"" Na fita daga motar na barshi a wurin ina"
kuka domin na fahimci wani irin kallo yake min.
"Jan motarshi yana faɗin ""Good gurl kada ki kara zuwa ni kika sayawa mutunci. Da gudun tsiya ya bar"
"unguwar ko tunawa da ya yi hatsari baya yi. Lokacin da ya isa gidan damuwarsa biyu ya tirke Taj domin ya ga abinda yayi mata daga window yana daga cikin dalilan da yasa ya mata haka, na biyu abinda ta kawo mishi. Lokacin da ya isa kai tsaye inda ta ajiye mishi leda bag din ya nufa, yadda ya je ya ga babu shi babu dalilinsa ya kwalawa Airah kira tare da tambayarta. Da sauri ta ce mishi.."" yanzu Badr ta wurga a wancan gwandon sharan. "" Wani irin zare idanu yayi kafin ya ce mata. "" Ko Ubanta da Uwarta basu isa na ajiye abu su sauya min wuri ba, ke ubanki ne ya ce ki sauya mishi zama daga inda yake? "" Da sauri ta nufi inda ta jefa ta ciro tana faɗin."" Kayi hakuri hamma."" Kamar zata yi kuka ya ce mata. ""Oya je ki wanke ki kawo min, abin Lubnah ko a kashi aka saka zan wanke na ci!"" Mahaifiyar Badr ta ce masa. ""Allah yasa na asiri ake baka ba."" ""Ni nake bata kudin da zata kaiwa bokonta domin wallahi ya iya aiki. Domin ta"
"mallake ni."""
"""Allah yasa ba wani abu take wankewa take baka ba ."" ""Ai yanzu nake son gaya miki ko shi ta bani nake"
"sha, ba matsalar babban matsalata shine yadda ba ayi mana aure nayi da kaina naji abinda masu mata suke ji, idan suna....."
(Dan iska )
"[12/13/2025, 7:26 PM] Maman Walid: 13"
"Watsa mishi ruwa Ubaid yayi domin kaf a duniya babu kunya cikin lamarinsa, ya kauce ruwan ya watsu a"
"gefenshi. ""Kai wani irin mutum ne da bai san ido ba?"" Ubaid ya tambaye shi, ""ido? Sun aka ace maka sun san idon ne? Matar da nake so zasu gayawa Magana sai nayi shiru saboda ina son su so ta? Kai ji idan suka ce basu sonta ni ina sonta. Zan iya rayuwa da iya ita ba tare da nayi nadama ba, zan kuma iya datse alaka da kowa domin ita, gaya min wani abu nake bukata? Yau suna tare da ni ne domin abinda nake da shi ita kuma tana guduna ne saboda su. Idan da yau babu su babu abinda nake da shi tabbas rayuwata"
"sai tafi haka citta."""
"""Me yasa kake karawa matsalar nan fetur ne?"" ""Saboda na gaya maka su din basu gaba, idan babu su iya"
"Mujitafa gare ni su basu da abinda zasu ba ni, idan aka ce iya kai ne babu abinda zai saka na kalle su. Su gode ma da nake kula su oya su bar min gida!"""
"""Amma kasan dole matarka ta shiga cikinsu?"" Ya fada yana kallon shi ya kara da cewa. "" Dole Matarka"
"tasan su din naka ne? "" ""I fuck su nawa ne, kai dalla su fita min ina da kake magana anan basu ne suka turawa Matarka hotonka da Lunah ba? Ko an gaya maka basu ne suka tura min hotonka da Lunah ba, kai ma kana manta da bala'in mutanen nan su fita kafin na kira Dattijo ya min waje da su."" Jin haka yasa bakiɗaya suka mike tare da barin parlourn musamman yadda ya kara da cewa."" Damuwarku na auri Yaranku idan suka samu ciki da ni na zama next victim to ba da ni ba! Da naci guba a hannunku gara na"
"mutu a tsaye. Sai kace an taɓa soyayya ko auren dole kun bi kun dame ni. """
"Suna fita Ubaid ya mishi magana ya d'aga mishi hannu yayi ya ce mishi."" Tsaf kafi kowa sanin waye ni"
"Please je ka wurin matarka kada ka dame ni! "" Shima ya samu nashi kason, ba musu ya bar gidan, ya kara wanke fruit din da kanshi sannan ya zauna ya fara ci kusan abinda ya ci kenan, fitowar Airah da take jin kome ya watsa mata harara ya ce mata."" Ki tattara abinda kika dafa ki je na gode."" A rud'e ta ce mishi."" Sir me na aikata? "" Wani haɗe rai yayi sosai ya ce mata. "" Taya xan yi bakuwa tazo gidan nan amma ki ganta ki basar da ita kin san how she meant to me? Da zaki ganta ki share ta don ni na share ta? Daga yau kada ki kara zuwa gidan nan, wannan shine zuwanki na karshe sannan ji gayawa mutanen da suka turo ki ita din rayuwata ce. "" Yadda ya mata tas ya kore ta, abin ya bata mamaki domin kuwa yanzu ta fahimci dalilin da yasa yake bala'in ashe basu shiri Yes tasan basu shiri amma kuma meye na jin haushin"
kowa?
"Labarin nan har kunnen Alhaji ELYakub, murmushi yayi yana faɗin. ""Shi kuma irin nashi borin kenan, a"
"kyale shi yayi yadda yake so ai matarsa ce idan ya gama fushi da kishin zai sauko a saka ranar da ya dace."" ""Baffa me kake nufi?"" ""Eh abinda nake nufi kenan;"" ya tashi ya bar parlourn."
*
"Karfe tara na dare Taj ya shigo gidan, yana parlourn abinda Uncle Auta da Nurse tana wanke ciwon,"
"kallon Taj yayi ya dauke kai kamar bai ganshi. ""Good evening Sir?"" Banza yayiwa Taj Uncle Auta ya amsa"
"mishi, tsayawa yayi a can gefe nurse din ta gama ya sauke rigarshi ya kishingida yana jin zafi da shigar"
"maganin. ""Sir!"" Bai iya karasawa ba saboda yadda ya buɗe ido akanshi. Zubewa a kasa Taj yayi ya dawo gabansa. ""Kayi hakuri wallahi kuskure ne, wallahi ban san cewa ita din taka ce ba."" "" Wai mai ya faru ne?"" Murmushi yayi ya ce mishi.""Tashi ka tafi!"" Ya cigaba da kallon tv, Uncle Auta ya kara mishi tambayar me ya faru, amma yayi shiru can ya kara cewa."" Wai kai meye matsalarka ne da kowa kake son samun matsala ne?"" Ɓare ayaba yayi ya gutsara yana kallon tv, "" naji irin rashin kunyar da kayiwa su"
"Khaulatu."""
""" Taya zan yi kunya arba'in da wani abu idan na ji kunya kai zaka bani auren Dadah karama? Kai ko kai"
"ka min rashin mutunci zan rama daidai gwargwado, kowa ya ji yadda ake ji."" Daga haka ya cigaba da cinye abin da ta kawo mishi. ""Tow shi Taj fa?"" ""Kama shi nayi yana rike hannun Matar Turaki!"" Daga haka na cigaba da abinda yake sai kuma Uncle Auta yayi shiru wato maganar gaskiya shine zai matuƙar wahala"
"zaka samu sune suka mishi laifi, shi kuma kamar mace wurin gasa bakar magana."
"""Dazun mun yi magana akan lamarin, ina ga kamar su a bangarensu akwai babban challenge da dole"
"ta bangarenka ne za a samu masalaha. ""Shiru yayi kafin ya ce mishi. ""Gaskiya bana ganin akwai wata mafita, zan duba in sha Allah."""
***
"A few weeks later na ji gara na koma Bauchi na gaji da lagos, har saka wayata nake a gaba ko zai kira ni,"
"amma mutumin nan na rasa inda ya saka ni, abin da nayi nasan nayi kuskure amma taya zai manta da ni bayan nasan cewa mutumin nan yana kokari tow ya zanyi da danginsa? Sune. Daukar wayar nayi ina kallon sunansa wato Masifaffen da na saka sunanshi. Wani bude kofar dakina aka yi da wani karfi ban san lokacin da na danna kiran ba. Wayar na cillar tare da kallon kofar dakin. ""Kika ce zaki koma Bauchi?"" Bakina yana rawa na ce mishi. ""Eh Ya."" ""Aikin fa?"" ""Yace kada ka kara zuwa!"" ""Ke wacce irin mutum ce bai shegen taurin kai?"" ""Ya Ado ba fa!"" ""Amma kece kika ce zaki ajiye aikin? Ya Ado ya kake so nayi?"
"Bakiɗaya an hade min kai a office din kamar wacce nayi wata zunubi, wacce take kula ni itama ta daina kula ni. Ya Ado ina son aikina ina son na, amma kullum turo min sakon barazana ake akanshi. Na rasa yadda zan hatta wurin aikin ina ganin yadda ake bina idan ban ajiye aikin ba ya zan yi? Ni kaina bana son nayi haka don za'a ce saboda abinda ya mana zan yi butulci amma ka fahimci wani abu bana son saboda"
"ni ya samu matsala da kowa zan koma Bauchi."""
"""Hafiz ya can yana jiranki amma kin sani ko? Kuma Baban Jama'are yana bibiyar Abba akan ki koma"
"gidan Hafiz, ki sani ba zan shawarar gidan Hafiz ba, amma ki bude baki ki cewa CEO ya turo domin shine irin mijin da kike bukata. "" "" A ce na aure shi saboda abin duniyarsa ka fahimta mana! Allah yanzu"" "" wannan yarinyar Allah ya san dalilin da yayo ki a yanzu baki shiga cikin arnan farko ba, wurin taurin kai. Da ba karamin wahala za'a sha dake ba, shi Mr Bilal din ya ce ba zai iya kare ki ba ne?"" Tura baki nayi na ce mishi."" Ya ce maka yana sona ne? Ina korata yake a jikinshi gara na koma Bauchi na huta! Ko ban"
"koma gidan Hafiz ba aure zan yi."" Na manta da wani zancen wayar ya Ado ya zuba min idanu ya ce min."""
"Yanzu kina nufin zaki koma gidan Hafiz kenan?"". "" Ya Ado mugun da ka sani."" Tass naji saukar hannunsa"
"a fuskana, ban san yadda akayi ya tawo gabana jikinshi yana rawa ya ce min. "" Har fata kike ki koma wancan kazamin rayuwar? Burinki shine ki wulakanta Mama da ta gama kunce zaninta a kasuwa ko mr Turaki bai ce yana sonki ba, wallahi kin ji na rantse da Allah na bashi ke, idan kin so ki shiga bariki aure babu fashi domin ba ma zaki koma Bauchi satin nan zan daura auren na ga uban da ya isa dakatar da ni, bari ki ji sadaka zan bashi ke. Yar iska mara kunya!"" Cin mutuncina Ya Ado yayi min, kiranshi yayi a waya ya ce ya shirya nan da sati biyu. Ai kuwa na fashe da kuka har da ihu, na kira Mama ko zata goya min baya amma ta ci mutuncina tare da cewa, idan da na san wutar da ake hurawa a Bauchi da ba zan fara"
"kiranta ba, tayi ta sakawa Ya Ado albarka."
"Ai ban san lokacin da na fara rashin lafiyar karya ba, Ya Ado ya ce ko mutuwa nayi sai an daura auren"
"naje gidan shi ayi min jana'iza. Kwana biyu da faruwan lamarin ba sai ga Uncle Auta da sadaki ba, shi kuma Ya Ado yace a kai Bauchi, lokacin da suka isa Bauchi Ya Umar da Ya Tahir suka amsa, tare da Alhaji Sa'idu. Domin har da baki daga Gombe babban hidima aka yi, lokacin da labarin ya isa Jama'are an kawo sadakina, sai hankalin kowa ya tashi. Immediately sai ga Ya Hafiz a lagos, duk