Advertisements
Chapter 10 Reading TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  Complete Novels

Chapter   10 / 61

27K to 30K   out of 180.5K words

simi simi da ita kamar wace za,a kama,

Yana cikin falon still saidai wanan karon a tsaye yake yana waya, ba kamar yadda ta barshi dazun ba,
Daga kuma wanda yake wayan dashi yana da mutunci matuka agare shi,
Saboda irin yadda yake magana cikin girmamawa tankar a gaban mai shi yake,
Ta gefen shi sukabi suka wuce batare da sun gaishe shi ba,

Ba,a dauki wasu lokutaba suka hado mai zobon mai sanyi yaji kayan hadi kamar yadda tasaba yi a gida don sana,ar mama Saratu ne kayan sanyi,,,
Sunan Samira yakira inda ya dakatar da ita, sai dai ita Meenat kan har ta shige abinta,
Tambayar ta yayi da cewa,
Wai cikin yaran nan wace ce diyar Baba Samaila,?
Tace yaya Meenat ce ai diyar shi,
Wacece Meenat din daga cikin su,?
Itace mana wqnan da muka hadama zobon da ita ai,
Cikin mamaki ya ce itace wana yarinyar dake bin babban dan shi ko, ?
Ita ce kuwa inji Samira ta bashi ansa,
Wani irin faduwar gabane ya ji tamkar zuciyan shi zai yi rawa,
Yace yanzu dama da diyar Baba na Samaila a cikin ku shine ban sani ba,
Samira ta dan mai,da hankalin ta gare shi da kyau tace eh yaya,
Subbahanallah inji yayan nasu ya fadi cikin kidimaywa,
Ita kan Samira tai shigewanta tabar shi nan gurin da yake zaune,
Kusa da Meenat ta zauna tana cewa ke Meenat wai fa tayan mu bai san dake acikin mu ba,
Sai yanzu yake tambayana wai wacece diyar Baba samaila daga cikin mu,
Meenat cikin zuciyan ta, ta ce mugu kawai ai,gara da bai,sani ba tun da farko,,
Washe garine suna falo sai gashi ya fito acikin shigar shi ta zuwa office,
Gaba dayan su su ke rige rigen ce masa ina kwana yaya,
Cikin daga hannu ya ansa masu gaisuwa tare da cewa a takaice, lafiya,
A gurguje ya dan kurba tea din da ya hada wanda ga mamakin shi ya sha kayan kamshi kamar yadda iyayyen su ke yi,
Har ya fara tafiya sai yake cewa batare da ya kalle su ba,
Malam tsoho ya bugo waya jiya yace a tura ku ku koma gida don hutun wasun ku ya kare wai,
Daga haka kawai yasa kai ya wuce inda suke ta ce mai adawo lafiya yaya,
Fitan shi yai daidai da juyowan Samira gurin Meenat tace inaga saboda kene aka bugo mai waya,,,,,

***** ****** *****

Zaune take tana kokarin jawo wani file dake karkashin takardun dake saman tebur din ta,,
Wayan tane yai kara alamar kira ya shigo mata alokacin
Kamar kada ta duba amma sai wata zuciya tace mata ta duba mana taga ko waye ke damun ta haka,
Da yar tsukin ta ta jawo wayan don ganin ko waye ke damunta tana tsakan aikin ta haka,
Cikin wani irin mamaki takai zaune saman kujeranta don ganin noban dake kiran ta,
Cikin rawan hannu ta dauki wayan don karba kiran na bazata da yai mata a yau,,
Wani irin kashe murya tai sallama dashi tare da kara gigita mashi zuciya,
Salawatu indan antashi daga aiki zakki rakani wurin shopping akwai wasu yaran da sukazo hutu gurina ina son in masu sayayan komawa gida,
Cikin sauri sauri tace ok sir insha Allah zan shirya da wuri mutafi,,,,,



ZEEE MAKAWA YELWA,,,
[7/2, 13:11] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
1⃣3⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,


ALLAH_ AR-RAHEEM,,,,


Wani irin uban tsale Salawatu, ta daka tare da mikewa da sauri ta suri jakar ta,
Gida ta koma inda ta kara yin shiga ta alfarma ta gyara duk sassan jikin ta tsab,
Ta dawo, office duk wanda yaga ta canza shiga daga cikin abokan ta sai sun tsaya mamakin ya haka kuma ?
Sai tai masu far da ido tace abin ai sirine kawai basu gane ba yanzu,,
Har kusan zuwa tashi office, sanan ta dauko jakar hannunta takara dauko madubi ta gyara duk inda ya dace,
Wani turare ta shafa a jikin ta mai wani irin mugun kamshi,
Sai kuma daurin dan kwalin ta da ta gyara da kyau, tare da sabale gyalen nata,
Wayan ta ta aje gefe guda tana jiran kiran shi kawai,
Shiko dama dan over time ne yana can yana over din shi,
Har ya manta da zancen zasu fita da ita, sai aikin gaban shi ne yake kokarin yi kawai,
Malam Abdullahi masinja ne ya hango ta a tsaye bakin motar shi tana ta kallon agogon wayan ta cikin bacin rai,,,
Shigan malam Abdullahi office din yasa shi dago kan shi a cikin sauri
Da mamaki ya ce malam baka tafi gida bane har yanzu,
A haba dai yallabai ai jira nake har ka rarage sai in kulle ko ina ,
Allah sarki hakene fa malam Abdu don Allah kayi hakkuri, dani shap na manta da ka na jirana ne, wallahi,
Ba matsala ai,na san baka gama bane yanzun ma nazo ne in sheda maka cewa kamar naga ana jiran ka a waje ko ?
Cikin mamaki Abubakar ya ce ni ta alamar nuna hannun shi a jikin shi,
Saida Abdullahi yadan yi shiru tukun sai yace kuma yarinyar nan mai yawan tsayawa dajai nan ma,aikatar,
Cikin wani iri Abubakar ya ce Subbahanallah wallahi ni nace ta tsaya min zata rakani in saiwa yaran nan da su kazo hutu wurina tsaraba,
Daga haka ya mike tsaye yabar gurin cikin daukan yar briefcase din shi,

***** ****** *****
Daga gurin da take kwance tai mafarki kamar yadda ta saba yi a,duk tsakiyan wata,,
Ciwon maran da tasaba yi shine har zuwa yau ma ya tayar da ita daga barcin da takeyi, a dakin ta,
Nishi takeyi sama, sama ta murdewa guri guda kamar macijiya ,,
Sai kuma wani irin kugi da takeyi ga jikin ta na wani irin rawa,
A daidai bayan dakin da suke suna hiran su da kuma wanki, murja ta fara jiwo wanan kugin har sai,da tace wa yan uwa suyi shiru su saurara,
Daga dakin kwanan Sadiya ne wanan sautin ke fitowa,
Kallon juna sukayi a lokaci guda inda kuma suka kwasa gaba dayan su zuwa cikin gida,
Samira ce suka kai karo da ita zata fito gurin da da suke hannun ta dauke da sabulun wanki,
Murja ke sheda mata abinda suka ji daga dakin Sadiya,
Tsuki tayi cikin rashin nuna tausayi tace ai aikin ta ke nan duk lokacin da zatai period ko ta kare,
Acikin mamaki duk suke kallon ta inda take kokarin wucewa abinta zuwa waje batare da ta damu ba,
Meenat ce ta sa kai zuwa cikin gidan inda sauran suka mara mata baya,
Irin yanayin da take ciki yasa su gaba dayan su rudewa sai kiran sunan ta suke,yi,,,
Da sauri Aisha ta koma falo inda ta dauko goran ruwa da cup ta dawo dakin ,
Tsugunnawa tayi tafara karanto addu,oin da kakan su malam Manya ya koya masu,
Ganin haka yasa ita ma Meenat zuwa daidai inda Sadiyan take kwance cure guri guda, kamar wace zata mutu,
Addu,oi suka fara mata suna tofawa duk da dai a tsorace suke,
Aisha tace su taimaka su daga mata ita, su bata ruwan da tai addua,n aciki,
Komawa sukayi tsatsaye suna kallon ikon Allah kawai,
Can sai sukaji tayi wani irin getsawa da karfi sai ga zufa ya keto mata a goshin ta,
Daga haka tafara sakewa tankar mai shirin yin barci ko somaywa,
Sai faman sannu, Anty sannu Anty suke mata,
Ita ko kai, kawai take iya kada masu saboda azaba,

***** ****** *****
I am sorry pls abinda ya furta ke nan da isowar shi gurin da take a tsaye,
Batare da ya tsaya wani magana ba kawai ya bude motar nashi, suka shiga,
Tuki Abubakar keyi a hankali kamar wanda ke tausayin sitiyarin motar,
Wanan yanayin tukin nashi yasa Salawatu jin dadin yanayin da ta tsinci kan ta yau tare da Abubakar din,
A hankali ya mika hannun shi inda ya kara volume din redio motar kira,ar shuriem ne ke tashi a cikin suratul AN-NISAN,
A hankali Abubakar yake bin kira,an malamin cikin wata irin murya,
Salawatu wace batasan may zatayi ba awanan lokacin sai gyara zaman ta tayi a hankali tare da bin lafiyan kujeran mota,
Tafiya sukeyi batare da wani yaiwa dan uwa magana ba,
Shi Abubakar din ne yadan kau,da shirun ta hanyar juyowa gurin da take zaune yace,
Wani shagone zamu tafi, ?
Hakan yaiwa Salawatu dadi don haka bata lokaci tace mai mutafi sahad, aiko,
Tace hakane don tasan matatara ne wanan shago dole ne ma wani yaganta tare da Abubakar kafin su fito,
Daga haka bai kara magana ba inda ya juya kan motan shi zuwa sahad store din,
Shigan su shagon ne sai taga Abubakar yace mata bissimillah ko sai ki zaba masu,
Da farko English wear ta fara dauko masu, masu kyau, don taji yace kada ta damu da kudin kayan ta dai zaba masu,
Tambayar shi tayi da cewa ko su nawane yaran inda ya sheda mata cewa su biyar ne,
Kai ta kada cikin mamaki tace wani abu sai malam bahaushe,
Har mutum biyar za,a turo hutu a garin Abuja haka ?
Ganin bata zabi kayan da yasan yaran hausawa suna sawa ba yasa shi kiran sunan ta
Karo na farko kega tun lokacin da tafada mai sunan ta,,
Wani irin dadi salawa taji don aganin ta ko mahaifanta da suka rada mata suna basu kai shi iya kiran sunan ta, ba,,
Wasu dinkakkun kaya readymade, ya nuna mata dinkin shadda ne masu kyau zani da riga da dan kwali akwai kuma masu siket, da riga,
Sai kuma gurin turamayn zannuwa inda ya ce mata tazaba mashi masu kyau da kuma tsada,
Ganin tana ta dauka baice komai ba yasa ta dan juya tare da daga kai ta kalle shi,
Tambayan ta yayi da cewa sun ishe,su ko ?
Mamaki taji a zuciyan ta tace shi wanan wani irin so yakewa yan uwan shi haka,?
Da,bai jin zafin kashe masu kudi, ?
Lailai za,a rina awanan gurin, don haka dole ne tayi kokari ta kutsa kanta gareshi,
Daga karshe itama yace ta dauki duk abinda take so,
Ba karamin mamaki salawatu tayi ba don jin irin kudin da aka caje shi,
Amma ba bata rai yasa hannu ga Aljihu ya biya su atake,
Masu kwasan kayan store din suka kwasa zuwa inda suka Parker motar su,
Sun fara tafiya ba,a dadeba taji muryan shi yana cewa,
Sannu da kokari miss salawatu, na gajiyar dake da yawa ko ?
Nagode kwarai,
Cikn jin dadi da rausaya kai, tace ma shi,,
You are welcome,,
Murmushi yayi alamar maganar ta ya gamsheshi har zuciya,
Yace godiya nake,
Yar siririyar dariya ta sake tace Sir, kamar wanda nai wani abu wanan godiyan haka,?
Saida ya sake murmushi ya furzar da iskar bakin shi yace mata,
Lokacin ki fa kika bani salawati,
Aikin ga dole na gode maki ko ?
Da kwatance ya isa gidan su Salawa din inda ya fahinci bawasu masu karfi bane gidan su,
Rufin asirine kawai irin na Allah, ke tare da ita,
Kayan da ya siya mata ya bude but din motar takwashe ya kara mata godiya ya sa kai zuwa nashi gidan da kayan tsaraban yan hutu niki,niki,

***** ****** *****
Jin yau cikin ikon Allah, ciwon baiyi mata tsanani irin yadda ya saba yi mata ba,
Tadan rarafo zuwa falo inda ta samu dogon kujera ta kwanta,
Sai,dai daga kwanciyar zaka gane cewa tana cikin wani irin yanayi gaskiya,
Da sallama kamar kullun yadda ya saba shiga gidan nashi ya shigo,
Duk da yasan ba lalaine ya samu ansawan sallamar tashi ba,
Tun daga kofa ya hango ta daga yanayin kwanciyar ta yasa shi gane cewa ba lafiya,
Sai bai kula da yan kan,nenshi dake zaune falon ba cikin yanayin damuwa,
Da wata irin murya ya kira sunan ta cikin nuna kulawa,
Ba tare da ta dago ba ta, ansa mai kiran nashi da naam,
Tsungunawa yayi daidai kanta yana mata magana kasa kasa ta yadda ba dole ba ne wani yaji may yake cewa,,
Hannu ya kai daidai wuyan ta yana taba jikin nata don jin lafiyan ta,
Muryan Aisha ne ya katse mai tabe taben da yakeyi a jikin matar na shi,
Yaya dazun mun ji tsoro sosai irin halin da mukaga anty sadiya ta shiga ,
Sai da Allah ya bamu ikon yi mata addua, da kuma tofi irin yadda malam tsoho ya gwada muna akan ciwon mara,
Daidai lokacin da yake dagowa tsaye da ga duken da yake ne yace mata Ok,
Daga haka yasa kai abinshi ya wuce zuwa ciki,
Gaba dayan su kallon mamaki suka bishi dashi a lokacin irin yadda yai masu,
Kallon kallo suka bi junan su dashi don dai irin yadda ya basar da su,
Sosai abin ya bata masu rai saidai babu halin su nuna tunda yayan su ne,
Kuma kadan daga cikin irin rayuwan shi ke nan, don mai ba hagon hali suke jin iyayyen su na ce mai,
A dakin su inda suke zaune suna ta kus,kus, kowan su a gajiye yake da ya koma gida,
Tun dai manyan su irin su Aisha da murja masu samari
Gashi sun bar,su can ba hira,,nan kuma tunda su,kazo babu inda suka taba zuwa ,

***** ****** *****
Baba Buhari ne tafe cikin wanan ranan da aka famtsama yau, rigar shi uk ta jike da zufa da alamar da kàfa yai yawo cikin wanan ranan,
Daidai zai shigo sashen nashi ne yaji muryan mama Ladi tana cewa,
Su wa yan nan yan jakar uban basu da ranan dawo wa tunda sunji dadi sun samu gidan ci da sha, mai galmi,,
Kai Allah dai ya sau,waka da wanan irin rayuwan na rashin sanin ciwon kai,
Zagi haka har kowa naji suwa kika samu haka ne wai ladi?
Wa yan nan yan jakar uban yara mana da suka tafi gulma,
Wani irin mugun bacin rai Baba Buhari yaji alokacin
Don har sai da gaban shi ya fadi gudun kada iyayyen yaran su ji,
Wani irin kunya ya lulubeshi a lokacin da ya hango matar kanin shi gufa ta lungun su tana kada kai,
Mama taci gaba da cewa wanan yaron ai wahala ta samay shi tunda ya nuna yana dashi,
Haka kawai a dinga yiwa mutum iko inga tausayi ai bai kamata atura mai su dukkan, su ba
Ke Ladi cikin wani irin daka tsawa baba ya kira sunan ta yace ahir din ki wallahi,
Naga abin naki tabin hankaline,
Shin ke ka dai keda yaron gane wai shin?
To wallahi ki iya kan ki akan wanan zancen don zan bata maki rai fiye da tsanmanin ki,
Ganin irin yadda rayuwan shi ya baci yasa mama tai shiru don tasan irin zuciyan baba yanzu zai iya mata abinda yace din,

***** ****** *****
Dukkan sune a falon inda yasa Samira da Murja suka kasa kayan gida biyar,
Baki yabasu akan kowa ta zaba daga cikin, sanin cewa sune manya gare ta,
Tana zaune gurin da take har suka gama zaben su,
Komai itace ta karshen dauka daga cikin abinda aka saya masu din,
Sai murna da farin ciki sukeyi don ganin irin wanan tsaraban mai tarin yawa da tsada da akasaya masu,
Cak tamike har zuwa bakin hannun kujeran da yake zaune akai tadan dafa,
Cikin girmamawa tace yaya mungode Allah ya kara bude ya kara rufa asiri,
Kai ya kada mata alamar bakomai, dama tasan cewa ba lailaine ya ansa mata ba,
Ganin hakane ne suma tan uwan daga gurin da suke suke tacewa yaya mungode mungode,
Sauran kayan da zasu kaiwa sauran mutanen gidana kuma nan ya shiga dan yi masu bayani sama sama,
Kiran Salawatu ne ya shigo a lokacin don haka bai karasa zamcen shi ba yadauki wayan,
Cikin murmushi a fuskan shi yake magana da ita,
Rankashi dade ka isa gida lafiya ko ?
Ya madam ya bakin ka ko ince bakin mu,
Don nima ai sun

10 / 61