Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : Complete Novels
don ganin gurin da motar take
Sai ji tayi mai motar na dan dana mata hon din motar,
A hankali ya sauke glass din motan inda yake cewa, Beauty daga ina kike haka a cikin wanan ranan ?
Sai a lokacin Meena tajuyo don ta ga waye ke mata magana,
Ta tsura masa manyan idanuwan nan na ta , wanda ke rikita duk mai kallon ta,
Ali,Abbas ne taga yana sakar mata irin shu,umin murmushin nan nashi,na ranan,
Bakin shi na yar kyarma cikin rawan murya da ganin fuskan ta ya ce kizo in rage maki hanya pls,
Ranan nan yai yawa kada ya illanta mun ke pls,
Meenatu wace ta kada idon ta wai ita harara ta dan rausaya kanta gefe guda cikin yar yatsune fuska, tace,
Kayi hakkuri malam don ni bana shiga mota da namiji dagani sai shi,,
Daga haka ta juya abinta taci gaba da tafiyan ta,.
Murmushi Ali, Abbas yayi, don yasan abinda ta fadi har cikin ranta haka zancen yake,
Don haka sai bai matsa mata ba yasa kai abin shi zuwa gurin da ya nufa,
Meena wacce tasha tafiya donbdaga karshe hakkura tayi da ta sara da kafa kawai tun da har takawo nan babu yar vespa,
Da kyat taga gida don haka ido rufe ta iso, sai dai gidan na tsit a lokacin,
Batai mamaki ba don tasan yaran gidan suna makarantan islamiya a wanan lokacin ,
Gurin Fridge ta nufa don ta sha ruwa ta duka ta dauko goran ruwa masu sanyi ta kafa kai da niyar sha,
Har tasha takai rabin yar, goran, sai taji an rungumo ta ta baya,
Wa, iyazu billah,,,
Cikin sauri Meena ta furzar da ruwan da ke a bakin ta lokacin,
Ta juyo a fusace, don ganin ko waye mai wanan dabiar banzan
Ali,Abba's ne ya na sakar mata wani irin shu,umin murmushi a fuskan shi,
Idon ta dan rutse inda tadaga hannu da niyar kai mashi mari,
Cikin sauri ya gwauce, sai bata samay shi ba ta samu iska,
A lokacin wasu irin hawaye masu zafi suka ziyar ci fuskan Meena,
A cikin masifa ta nunashi da dan yatsan ta tace,
Cikin daga murya tace daga yau daga rana mai kamar ta yau kada ka kara shiga tsabagata ko ka nuna ka san ni
Kasa ni cewa ni ba yar iska bace irin ka wanda ya tashi cikin rashin tarbiya,
Kuma ina neman tsarin Allah daga duk wani sheri daga ire, iren ku shedanun mutane,
Daga haka taja wani irin dogon tsaki gami da hararan shi ta watsar gefe guda,
Sai a lokacin hawayen idon ta suka fara yawa a fuskan ta,
Wani kallo ta watsa mai , mai tatare da tsana da kiyayya,
Baki bude Ali,Abbas, ya tsaya yana kallon yadda yar yarinya, karama ke gaya mashi, magana son ranta,
A fusace Meenatu tabi ta gaban shi ta wuce zuwa cikin gida, rai bace,
Direct dakin Anty amarya ta nufa da shiga ta zauna a,bakin gado idon ta na mai zubar da hawaye kawai,
Anty tana fitowa daga bathroom taga Meena acikin wanan halin,
Take hankalin ta ya tashi da sauri ta karaso gurin da Meenat take zaune ta na tambayar ta cikin tashin hankali,
Amma Meenat ta kasa bude baki tayi magana don bakin ciki, da ya mamaye mata rai,
Da tambayar yai mata yawa ne ta kwanta ga kafadar uwar dakin nata cikin kuka take fada mata abinda ya faru,
Rayuwan amarya ya baci sosai nan ta shiga bawa Meena hakkuri har ta samu ta dan sasauta kukan nata,
Shiko Ali,Abbas shigar Meenat ciki yasa shi sauke yar ajiyan zuciya cikin takaici,
A lokacin ne yasan cewa ya tabka babban kuskure don nan kasar hausane ba wai turai ba,
Gashi kuma ko banza Meenat still karamar yarinya ce tukun ba wani girma tayi ba
Gashi Allah yasa mai son wanan yarinyar a rayuwan shitun ranan da ya ganta,
Sam ba zai iya jure rashin taba a halin yanzu don haka dole ne ya jure duk wani cin fuska da zai gani a gurin ta,
Cikin yanayi na rashin kuzari da kyat ya ja kafan shi da yaje jin sunyi masa nauyi,
Tankar bazasu dauke shi ba, ya nufi hanyar fita wajen gidan ran shi a bace,,,,,
****** ******** ******
A cikin gidan malam tsoho ko wani sashe sai kokarin ganin ance yar su za ai wa Abubakar kamay,
Daga sashen Baba Hamza' da Baba Shaibu har da Baba yahaya,
Sai kuma bangaren gidajen gwagwan,nin su suma suna son wanan hadin,
Duk wanan wainar yan gidan Baba Samaila basu da labari sam,
Ko ma suna da a yanzu yar shi bata cikin jerin manyan yan matan gidan, tukun na don duk sun girmay mata sosai,
Malam tsoho wanda yau da kan shi yasa aka kira mai wayan jikan shi na fari Abubakar,
Bayan sallama da gaisawa ne, malam tsoho ke cewa jikan nashi
Kana magana ne da Abubakar manya mai almajirai,
Murmushi Abubakar yayi a bangaren shi sai da malam din yaji tankar yana agaban shi ne,
Abubakar magana nake son yi ta fahinta da kai don mu fahinci junar mu,
Abubakar wanda a lokacin yana zaune yana cin abincin dare, ne ,
Yadan dago kai ya kalli gurin da Sadiya take zaune tana kallon wani shiri a African, magic,
Malam din ya soma da cewa akan zancen auren da kake da burin karawa ne mai suna,
Banji dadin yadda iyayen ka suka dawo suna fada min irin zurian da kake son mu hada iri da su,
Shin mai suna ina tarbiyan ka da sanin ya kamatan ka suka shige da har zaka kwaso wa kan ka irin wanan macen,
Tun a wanan ookacin rayuwar Abubakar ta baci yaji wani iri a zuciyar shi,
Muryan malam din ce ya dan dakatar dashi daga tunanen shi,
Malam yace kazo gida cikin dangin ka da yan uwa kaduba iri mai kyau kaza ba
Don dai a gaskiya ba zan yarda tun ina da rayuwa ba, ace wai jikana ne ya auro irin wanan zurian agidan mu,,,
Abubakar wanda tun fara maganar kakan nashi yake sauraren shi ya ce malam
A gaskiya na fada maka akwai kalar matar da nake bukatar in aura tun farko,
Don haka yanzu kuma naga wacce nake so don Allah kubar ni inyi abin da rayuwana ke muradi,
Malam ya ce badai ita wanan din ba sai dai ka dawo nan gida kebbi ka duba kalar ta,,,
Daga haka tsohon ya kashe wayar shi batare da yajira yaji mai jikan nashi zaice ba,
Innalillahi kawai Abubakar ya iya nanatawa a lokacin don tun daga kafan shi har kai wani irin abu yake ji tankar ya fadi,
May zai sa suyi mashi hakane bayan tun yana yaro baida zabin kanshi komai akan umurni yake tafiyar da shi,
Rai bace ya lalabo noban Baba Samaila duk da dai ai har da shi a cikin masu zuwa su fadawa malam mumunar labari akan salawatu,
Bayan sun gaisa ne sai zancen da yasa ya bugo mai waya yafara da cewa,
Baba a gaskiya ban ji dadin abinda aka fadawa malam ba a kan wanan yarinyar da na tura ku nemar min,
Baba Samaila wanda a lokacin shima ya na zaune ya fara cin abinci a take yaji abinci ya fita ran shi,
Baba Samaila ya ce haba mai sunan malam ka kwantar da hankalin ka mana ka fahinci komai, yadda yake,
Koda zamu bata zancen ka ne ai kasan bakamar yadda kake nufi ba ko ?
Kaifa ba jahili bane ya kamata ace kasan yadda zancen yake,
To baba in banda abin malam auren zumunci auren sunna ne ?
Manzon Allah S A W babu yar uwar sa acikin matan shi ko da akwai ma bai tilasta yin hakan ba ko da acikin sunna
Kuma ai matan sa bawai duk yan kabilar sa bane,
Don haka ita dai wanan din itace zabina ita nake so in aura koma yaya take,
Kana ko cikin hankalinka mai sunan malam ?
Kada zancen mace ya sa ka koma mara biyayya ga iyayyen ka ?
To bara kaji wanan karon babazan goyi bayanvka muddin kace zaka bijerwa mahaifan ka,
Kabari abi abin asannu don a samu a rabu lafiya ai naga ko anan gida birnin kebbi akwai yan mata kyawawa da zaka so,
Baba har yanzu baku fahince ni sosai ba, ni fa ba wai al,adace a gaba na ba
Addini nake son koyi akai nasan cewa yaran mu suna da kyau da asali da tarbiya irin wanda yan birni basu da shi,
To amma ko wani namiji da akwai abinda ya ke so ga mace ,,,
To ka bari abi abin a sannu ko ina ga zaifi sauki sosai,,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA,,,
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
2⃣1⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH-AL-MUTAKABBIR
Sheshekan kukan da Meenatu ke yi yatayar wa amarya da hankali sosai cikin fada take cewa kiyi shiru Meenatu an,
In uncle din ki ya dawo zan fada mai yai masa iya ka dake,
Don su ba kunya bane garesu, ya dauka cewa ke irin dabi,un yaran gidan su ke gare ki,
Dabiar da za aita rugumar juna da dan uwa wai dabiun wayewa wanan ai lalacewa ne da watse,
Wanan maganar ya sa Meenatu dan dakata wa don ta saurari zancen amarya,
Anan ta shiga bata labarin rayuwar turawan da sukeyi a gidan su,,
Sai a lokacin meena cikin murya mai kuka tace to ni iyayye na ba yan aron al,adun wasu bane su yarda koyarwan iyayye da kakan,ni,
Mu gidan mu muna koyi da sunanan maikin Allah ne mazon rahama,
To kin ga ai hakan da kikai masa gobe bazai kara ba don ya san tarbiya ba daya,,,
A haka ta samu har meenat din tai shiru daga kuka da bacin ran da take ciki,
Sosai rayuwan uncle Nafi,u ya baci don jin abinda ya faru tsakanin Meenatu da kanin matar shi,
Duk irin mutuncin da ke a tsakanin Nafi,u da Ali,Abbas sai da wanan zancen yaso ya hada su fada sosai,
Amma da yake mazane sai suka kai rayukan su nisa suka sasanta da junan su,
Inda shi Ali, Abbas ya kwantar da kai gurin Nafi,u yana cewa shi wallahi auren Meena yake son yi ba wai yai mata haka da wani manufa bane,,,,,
Daga karshe dai uncle Nafi,u ya ce ya bari abi abin a sannu don har yanzu Meenat yarinya ce,,,,,,,,,
****** ******** ******
Abubakar yayi shiru yaji duk jikin shi yai sanyi lankwas,
Wanan sabon al,amarin da ya bolle mai maigirma ne sosai,
Don haka maganar Baba Samaila kuma gaskiya ne,
A hankali dole zai bi da malam tsoho ya samu ya lalaba shi akan zancen,
Shi in fa badon mahaifan shi ba bai ga dalilin da zai sa malam tsoho ya dinga taka mai burki ga al,amarin shi ba,
Duk yan kwanakin nan duk wanda yasan Abubakar yasan da cewa ya canza sosai,,
Ga kuma aiyuka da suka taso mai daga gurin aikin su,
A bangare Salawatu kuma duk da ba wani abinda tagani na canji daga Abubakar amma jikin ta ya bata cewa tun zuwan iyayyen shi Abuja akwai matsala sosai,
Don a irin yadda da farko yake nuna mata cewa bada dadewa ba zasu yi aure sam yanzu ya daina hakan,
Kwatakwata ma bai zancen auren su a yanzu din sai dai yana yawan nuna mata kulawa da kuma kashe mata kudi,,,
Abubakar yana sane da cewa hankalin salawatu a zuwa yanzu ya tashi matuka don dai bata ga fuska yadda zatai mai korafi bane,
Tun bayan wani rana da ta faraxmai magana suna acikin mota a hanyar su ta dawowa daga gurin aiki,
Tsawa ya daka mata tare da mata kashedin yi mai katsalandar ga harkan shi,
Yace bani nace maki naji zanyi ba koke ce kika sani ,
Salawa sai hakkuri kawai take ba shi a lokacin don ganin irin yadda idon shi ya rine a lokaci guda yai wani ja kamar garwashin wuta,
Mtsss ya ja wani dogon tsaki tare da rike kanshi da yake ji a lokacin tankar zai tsage,
Hannayen shi guda biyu da suje a cure guri guda yake dan dukka kadan kadan,
A wanan yanayin, shi kadai yasan,irin abinda yake ji a zuciyar shi
Zaune yake a office din shi saman kujerar shi duk da tolin aikin dake gaban shi ya kasa aiwatar da komai akai,
Mtsew ya sake jan wani sabon tsaki, tare da furzar da iska daga cikin bakin shi a lokacin,,,,,
Yasan duk inda wanan sherin yafito daga bakin kannen mahaifin shi ne,,,
Baba yahaya ko baba hamza don koda rantsuwa yayi bazaiyi kaffara ba ,
Baba samaila bazai taba yi mai wanan gamin ba a surin tsoho,,,
Ajiyan zuciya ya sauke a lokaci guda don tunawa da shawaran da Baba Samaila ya bashi yasan cewa shima Baba samailan zai yi wani abu akai ke nan,,,,
****** ******** ******
Tun faruwan wanan zance Meena bata wani sake jiki a gidan ba,
Kwatakwata ma hankalinta ya koma gida birnin kebbi ba abinda take so kamar taje taga kakan ta malam tsoho, mai bata sudin kwanon fura da waina,,da, baban ta da maman su da yan uwanta,,
Kasan cewar zasu kwana biyu ba su da lacca,
Musalin karfe goma na safe sai kawai ta yanke shawaran ta wuce birnin kebbi kawai ta gano gida,
Gurin anty amarya ta wuce ta sheda mata cewa zata je birnin kebbi yau,
Da mamaki uwar dakin nata ke kallon ta, tana tunanen kodai Meenatu nason zuwa gida tafadi abinda ya faru da ita ne,
Ido ta dan tsurawa meenatu din sannan ta kira sunan ta ,
"Meeena,
Meeenat wacce ta dan dago kai ta kalle ta a hankali,
Anty, tace kardai ince abinda yafaru tsakanin ki da Ali Abbas zai saki tafiyagida ?
Kai meenat ta kada a hankali alamar a,a badon shi ba zata tafi,,,
Murmushi anty ta, sake a lokaci guda tace, don Allah meenatu kada ki fadawa iyayyen ki don rayuwan su zai baci suga kamar ba,a ai maki rikon kwarai a nan,,,
Meena ta dubi anty amarya tace insha Allah anty ba zan taba fada masu wanan zancen ba,
Karfe daya saura Meenatu ta na cikin garin birnin kebbi, a cikin shiga ta mutunci,
Kallo guda zakai mata ka ga canji sosai daga gare ta saboda yanauin canjin gurin zama,
Mai mashin na sauketa a kofan gida da yar jakar ta da tasa kayan ta aciki sai kuma wani jakar vaco da ta saka tsaraban da su Anty amarya da mummy suka bayar ta kawo wa mahaifiyar ta da kannen ta,,
Tun daga nesa malam tsoho ya hango ta yaga irin yadda yarinyar ta canza a lokaci guda,
Su baba Buhari da ta sama a kofan gida su ta fara gayar wa dacewa
Baba ina wunin ku ?
Meeenatu ke, ta tahe yanzu,
"Ni ta Baba'
Ina wajen su kawun naki duk suna lahiya ko ?
Walleh duk lahiya muke Baba,,
To, a gaishe ki, ke ji
Da murmushi a fuskan ta, ta karasa gurin malam din ta na cewa malam ina fatan akwai sudin fura mai sanyi,
Ho yar nema kina son sudin fura kika tafi kika bar ni da fura na,
Meeena tai murmushi tace to ai gani naji kewar ka na dawo don in gan ka insha kuma fura,,,
Ke ta att ta he yau, ?
Ya ya gurin kawon naki da sauran jama,an ku,,
Lahiya lau muke malam tsoho,
Wani kamshi ne mai ma,ana yaji yana tashi a jikin jikar tashi,
Wanda hakan ya nuna mai cewa yanzu akwai canji mai yawa daga jikan tashi, sosai,
Mikewa tayi cikin fara,an ta zuwa cikin gida rataye da yar jakar ta a kafadar ta,
Da murnan ta tashiga ciki tana cewa Salamu,Alaikum,
A,a a maraba da mutan sakoto kece a tafe yau Meenatu, ?
Mutanen da ta ke cin karo da su a hanyar ta ta shiga cikin sashen su ke nan,
Murna sosai na jin dadi meena keyi don wani irin yanayi sa ta tsunci kanta aciki,
Matar baba yahaya, tace a a maraba da Meenatu, wallahibdazun nagama zancen ki,
Murmushi Meenatayi don tasan gaskiya ce saboda suna dasawa da ita sosai,
Daga haka Meenat ta wuce zuwa cikin shiyar su,
A bakin murhu ta samu mama,Saratu tana kokarin raba abincin rana,
A,a ke ta tahe yanzu ?
Darabon yau muci abincin rana da ke ?
Murmushi tayi kawai tana kokarin aje jakar hannun ta a cikin rumfar dake tsakar gidan ku,,
Ya wajen su kawun na ku da