Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : Complete Novels
kawar Antyn saloon zaune suna kallo a dakina,
Nace don Allah kuyi hakkuri na samu yana bayi ne shi yasa,
Tai murmushi tace, haba ai ba komai tunda har munriga da munzo ko, ai,
Ba ai wani daukan lokaci ba ya shigo dakin da sallaman shi ,
Suka gaisai faram faram tare da kara mashi ya mai jiki ?
Fuska a daure yake cewa Alhamdullahi da sauki sosai,
Tace ga matar da nake magana zata iya aikin tazo,
Sai lokacin ya dubi matar ba wata tsohuwa ce ba sosai haka,
Kara gaishe shi Ramatu tayi tana çewa barka da rana yallabai,
Yace ina fatan zaki tsaya kiyi abinda ya kawo ki kamar yadda kikai alkawari,
Don kinga aiki nan sai an,daure, ansa hakkuri a cikin sa sosai,
Agina, kawar Antyn Saloon tace duk nai mata bayani sir,
Yaya Abubakar yace, OK nawa ne kuka shirya da ita, ?
Aginatu, tace gaskiya bamuyi wanan zancen ba tun farko iyaka dai makwabciya tace ita maigidan ta ya dade da rasuwa ,
Naga wahala yai mata yawa shine nace barin mata hanya tunda naga kamar yar shiyan state din kuce ita,,
Yace, yanzu ke nawa ki ke ganin cewa zan baki ya fadi a kage don duk ya matsu yabar mu, kamar mai tsoron mata,
Ramatu tace Alhaji duk abinda ka bani nagode Allah yasa masu albarka,
Yace OK zan ganta sai muyi magana akai yana nufin wai zai gan ni sai muyi magana dashi,
Daga haka yasa kai daniyar barin dakin har ya kai kofan fita sai ya dakata,
Batare da ya juyo ba yace kisan cewa a tsakiyan mata uku zaki zauna sai ki kiyayye please ?
Tace insha Allah zan kiyayye Alhaji nan inda aka daukeni zan tsaya da kafana,
Bayan fitan yaya Abubakar ne muka kwasa zuwa dakin sadiya gaba dayan mu mu uku,
Barci takeyi tun dazu nan nafara yiwa bakuwar mu Ramatu bayani abinda zata dinga yi,
Muryan mu da Sadiya taji yasa ta bude idon ta, a hankali tana kallon mu,
A kusan tare mu kai mata yaya jiki tace da sauki a hankali,
Tana kokarin mikewa ne nasa filo nadan gyara mata a bayan ta,
Kara gaisawa sukayi nan nake ce mata ai an kawo wace zata zauna da itane saboda Maman biu bazata iya ba,
Sun gaisa da Ramatu tana cewa, ok zaki ko iya yi yar uwa don kinga da wahala abin,
Ramatu cikin sakin fuska tace babu damuwa yar uwa zan iya insha Allahu Allah dai ya baki lafiya,
Muka karba gaba dayan mu da Ameen Ameen,
Munyi Sallama da Aginatu mata mai mutunci da tausayi,
Inda na karbi nomban ta da cewa duk abinda ake ciki zan kirata in sheda mata,
Duk abinda mukeyi madam din gidan mu tana kallon mu sai dai bata sa baki
Kamar yadda ta nuna ciwon Sadiya bai damay ta ba kuma baya gaban ta ma sam,
Sai wani nan nan yanzu naga Yaya Abubakar yana yi da ita wanda hankalina baigano ko may ye dalilin hakan ba,
Gashi duk dare sai naga ya shigo mata da ledan kayan fruit masu kyau,
Ina so amma dayake ita yake kawai ko a kitchen nagan su cikin fridge duk son da na ke masu ban sha,
Sam iyanzu babu wani shiri a tsakanina da Salawatu don duk ta dauki tsanar duniya ta samin,
Idan da farko tana boyewa yanzu sam bata iya boye don ko a hanya muka hadu cikin biyu sai na samu daya,
Harara ko tsuki daga gare ta, abin dariya yake bani don nasan babu yadda zatayi dani dai,
Kuma ganin irin rawan kafan da yaya keyi yasani kawo ido in sa masu,
Dole aiyukan gida duk da bawai naji saukin jikina bane nice dai maiyin su,
Sallah na idar ina zaune gurin ban kai ga dagawa ba naji waya ta tana kara,
Yaya Abubakar ne yakirani daga office murya kasa kasa yake cewa,
Meenat ina fatan yau zaki karbi girkin ki tunda kinji sauki ko ?
A cikin marairai cewa nace don Allah yaya kayi hakkuri bazan iya ba ,
Don har yanzu nakanji marana yana min ciwo time to time,
Yadan tausa muryan shi yace please Meenat for Allah sake ya kuke son inyi ne please ?
Nace cikin murya kamar zanyi kuka wallahi yaya bawai naji sauki bane kawai dai karfin hali nakeyi don kada a zauna da yunwa a gidan,
Yace look Meena bawai shawaran ki nake nema ba command ne na baki
Naji fit ya kashe wayan inda nabi wayan da kallo tankar shi nake kallo,
Wahalan da nasha aranan nan ne ya fado min a rai lokaci guda,
Inda na rutse idona, cikin wani irin jin zafi azuciya nasan cewa tunda har yaya ya ce hakana to ya zama wajibi in kai masa kaina daren yau in har ina son kaina da lafiya,
A haka naci gabada aiyukana batare da hankalina ya kwantaba saboda ina tunane yadda zanyi da Yaya Abubakar a daren yau,
Don nasan cewa maganar gaskiya ke nan ya furta har cikin rashi,
Dole nadan fara yin an abuwan shirin kwana dakin maigida kamar yadda mata keyi inda kanada kishiya ko kishiyoyi, agida,
Kamar daga fara gyara dakin maigida yin yan gyare gyaren gida, sai kuma girki tare da tsala kwalliyan daren don taron maigida,
Saidai duk ni yau acikin fargaba nakeyin nawa saboda yadda yanayin jikina yake,
Duk abinda nakeyi yar sa idon gidan mu tana biye dani don ganin shirina,
Na,gane may takeyi amma sai nai tankar ban fahince ta ba,
Daga inda nake ina gyara kaya a dining table na hangota tafito a lokacin yayi daidai da time din dawowan Yaya Abubakar gida yayi,
Har gaban table din da nake tafito tana wani taunan chewing gun irin na yan duniya ,
ZEEE MAKAWA YELWA🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
6⃣2⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH- ASH -SHAHEED
Daga kwance nake rigingine fuskana yana kallon Ac din dakin da ke sako min ni ima wanda ke sani cikin wani yanayi mai dadi, ga kamshi dake tashi na turaren humra, daki,
Duk da Motsin da naji na shigowa dakina a lokacin, bai,sani juyawa don ganin kowaye ba,
Ya iso gab da gurin da na ke, zaune a bakin gado,,, yana min wani kallo acikin mamaki,
Muryan shi naji yana cewa lafiya kike kuwa yau, ?
Batare da na kalle shi ba nake cewa, lafiy kalau nake,
Hmmm naji yace,
Kamar zai juya amma sai naji muryan shi yana cewa,
Breakfast din Baba Wadda fa,?
Banyi ba na bashi ansa a takaice,
Saboda may ? ya tambaya cikin mamaki
Nace don banice da alhakin badawa ba nagani , yau din,
May kike nufi da hakan ne,?
Ai bani kadai bace da alhakin wanan laluran ko
Wani irin tsawa ya daka min tare da cewa
Ke ni zaki gaya wa magana haka kai tsaye kina rainawa hankali ina fadi ki na fadi ke ma,
Ban yi magana ba sai hawayen da idona ke fitar wa shar a lokaci guda,
Ki tashi ki fita ki girka mai abinda zai karya idan ya dawo,
Daga haka yasakai ya fita dakin a fusace cikin bacin rai,
Ban ce komai ba sai kokarin mikewa da na keyi don zuwa kitchen din,
Na jawo dan karamin gyale na na rufawa kaina tare da gyara daura zani na,
Abinci lafiyayye na hada mashi tare da ni da su Anty sadiya,
Nasa saura a kula don nasan cewa zuwa anjima kadan yunwa zai iya zo min,
Nakai abina daki na gyara gurin da nai aikin a lokacin na juya daki na shiga wanka,
Bayan na fito ina zaune a bakin mirror ina shafa mai don yanzu ba zama yin kwaliya na keyi ba,
Ina kokarin zura wani dogon rigan pepper lace da akaiwa combination,da shi,
Yaya Abubakar ne ya shigo dakin yana min wani kallo amma fuskan shi acikin daurewa yake,
Tambaya na abincin sa saboda yana son fita, ban kai ga bashi ansa ba idon shi ya kai, ga abincin da na zuba a plate saman mirror don yasha min isaka kafin in zauna ci,,
A tsatsaye yafara kai spoon abakin sa,yakai kusan sau biyar da yaci a tsatsaye don da alama sauri yakeyi a lokacin,
Bayan ya aje spoon din,Ya dan juyo gurin da nake tsaye ina gyara dankwalina yana cewa,
Shi zai fita amma da Baba Wadda zasu fita don akwai inda zasu tare,
Murya ciki, ciki nace Yaya lokacin komawa na sokoto fa yayi,
Wani kallo naga yai min na yarinyarga fa kin rainani naci gaba da cewa,
Don da mun koma zamu tafi final teaching practices din mu, inha Allah,
Tankar baiji may nace ba don bai ma nuna yaji din ba sai sa kai yayi yabar dakin,, abin shi
Ganin uana fita baice min komai ba nabi bayan shi da kallo,
Yana fita daga dakin gaba daya nasa wani irin kuka mai tsuma zuciyan mai sauraro ta,
Ina cikin kukan da babu mai rarashi na sai Allah naji anshigo dakin,
Yaya Abubakar ne ya dawo dakin yana cewa inzo mu gaisa da Baba wadda kafin su fita,
Ganin da yai min na kifa ciki ina kuka cikin filo ya sashi tsayawa yana kallo na acikin mamaki yana cewa,
May ke faruwa ne wai Meenatu ?
Banyi magana ba ya kara jefo min tambaya da cewa,
An maki wani abune wai don tun jiya nake ganin damuwa a fuskan ki,
Nadan tsakaita kukana ina cewa ni gida kawai nake son komawa yanzu,
Murmushin takaici yayi tare da cewa bazaki ba idan kuma kika matsa min karatun ma gaba daya sai ince a fasa yin sa,
Don dama banga amfanin shi ba don ba dai aiki zakiyi ba balle, jin haka yasa na,
Kara gumzan kukana nayi yadda zai tayar mai da hankali,
Da sauri ya juya ya bar dakin hankalin shi a tashe bai iya cewa Baba Wadda komai ba sai kawai ya nufi hanyar fita waje,
Shima Baba Wadda yana ganin haka ya tashi ya mara mai baya suka fita tare,,,
****** ********** ******
Labarin ciwon Anty Sadiya ya iso Birnin Kebbi ko
A, take zance ya fara yawo cikin gari kala,kala, don kowa da abinda yake fadi,
Wasu suce ai kishiyoyine sukai mata su suce ai sherin uwar ta ce,
Ranan da mama Ladi ta samu labari hankalin ta ya tashi sosai, don kada iyayyen Sadiya suji suce ba,a dauki mataki akan ta ba,
Don haka bata tsaya bata lokaci ko ina ba sai gidan Aminiyar ta Hajja,
Don kada taji labarin ga mutane tace ai ba,a fada mata ba,
Amma bayan zuwan ta sai tai mamaki da taji Hajja na cewa ai mai sunan malam ya bugo mata waya
Amma ta fada, ma shi cewa, ai basai ta tura,kowa daga nan ba,
Don a can ai,basu rasa mutane ko amma haka dai zai sa in tura mashi mutun daga nan,
Wama yasan ko may ke damun ta balle adawo nan ana yadda zance kan karya,
Abinda mutum baiji ba bai gani ba ya taho yace shi ya gano acan,
Don haka ni banga abinda za,a ce sai an tura wata ko wani daga nan ba,
Hakane inji Mama Ladi tace amma dai duk da haka da daga cikin yan uwan ta a samu wata a turata, mata can ina ga haka zai fi,
Don fa ranan wuya sai naka ,
Hajja ta tabe baki tana cewa, haka ne amma gaskiya ni babu wanda zan tura daga nan don
Ai fanin, ku, da kuma mijin ta baku rage ta da komai don haka abar zancen tura wani, saboda tana samun kula daga mijin ta ai,
Tun da Mama Ladi ta gane cewa Hajja bata kaunar zancen kwata kwata yasa ta kyale wa,,
Sai suka fara hiran wani abu can daba don sam bata kaunar wanan zancen,
Don zancen yana tayar mata da hankali saboda bata san may zatayi ba i yanzu akai,,
Haka mama ladi tai sallama da ita batare da ta gane komai ba gare ta,
Ga warin hamman Dodo da ya isheta tun zaman ta,
Amma anan cikin gidan mu gidan malam tsoho sai zance ya canza da cewa,
Ai sherin Hajja ce duk yadda akayi ke bibiyan don tunda har malam ya saka bakin shi ciki, zance,
Zance yazowa Mama Ladi cewa ai nayi barin ciki, a kwanakin nan,,
Anan Mama ta fara fitina tana zage,zage tana masifa,
Ita Allah ya tsare ta, da ta hada zuri,a da zuri,an irin Baba samaila,
Da kuma mahaifiyana ita dole Maisunan malam ya sako Meenatu, tun bata kara yin wani ciki ba,
Yanzu shi mai suban malam har may yagani ajikin Meenatu da ya,rude shi har ya afka mata wai harda samun ciki,
Aiko amanan ta ya ishi cikin ya zube don dai Allah yagani ita bazata hada da irin mu ba,
Kuma wanan sherin na malan tsohone shi da yai uwa yai makarbiya harda hada aure tsakanin jikokin shi,
Yakuma rasa wanda zai hada wai sai yar Samaila da na ta,
Dan dama, dama dama ace a cikin diyan wa yanda suka fito ciki guda da Baba Buhari ne zata dan yarda,
Dole sai Yaya Abubakar ya turoni gida kwanan nan inba haka ba zai hadu da fushin ta,
****** ********** ******
Tafiya ya keyi zuwa gida malam saboda karbo wa Sadiya magani shi da Baba Wadda,
Wayan ce tai kara yaga ashe Mama Ladi ce ke kiran layin nashi,
Sai da ya bari kiran ya tsaya kamar yadda yake mata kulun sai ya kara kiran ta,
Mama bata bari sun gaisa ba tafara cewa Kai mai sunan malam shin batun ga da najiya da gaskiya na ?
Yace cikin tambaya mama wane batu ke nan kika jiya ?
Tace wai Aminati tasamu tagon kaya ?
Kwanan nan shin ?
Yace cikin dakewa hakane Mama gaskiya na yayi barin kwanan nan,
Salati ya Abubakar yaji Mama ta sake a lokaci guda,
Tana ewa da ka tona min asiri maisunan malam ace duk cikin zuka zukan matan ka ka rasa wace zakaiwa ciki sai waga yar ficikan yarinya,
Me kagani gare ta shin ?
Me zaka ganewa gurin wagga dagin bararo,
Nace maza ka dawo da yarinyar nan gida kafin wani sati ya zagayo,
Kajiya ko ?
Shiru yayi Mama takara cewa shin kaji abinda na fada maka ko ?
Najiya Mama ya bata ansa da fadar hakana, a takaice,
To kadai jita nan zuwa wani sati ka turo masu ita gida su san wadda zasuyi da ita,
Ya kara ansawa da fadin to Mama zanturo ta kafin lokacin,
Su na kashe waya ya furzar da iska daga bakin shi yana mai dafe gefen kan shi da hannun shi guda da bai tuki dashi,,
Ya ce kai, Mama ho, ba dai fitina ba Mama, don kawai ata da sabon fitina a gida, ta dawo da wanan zancen,,
Baba Wadda wanda ke zaune daga gefe yace to wai ita, Maman Mariya dake cewa haka shin, may ye hujjan ta,
Babu inji yaya Abubakar ya bashi ansa da cewa, kawai dai akidace ta su irin na mata,
Wayan shi dake a gefe ya laluba ya na neman nomba Uncle, dina,
Ya ce hello Uncle su ka gaisa a cikin mutunci da girmamawa,,
Yace Uncle dama ina son don Allah a taimaka min a school din su Meenat don a bata excuse saboda tace zasu fara exam gashi kuma tana nan on medication,
Uncle ya ke ce mai zai tafi school din na mu ya bin cika ya gani, inda yadda za,ayi,,
Sukayi sallama acikin mutunci tare da yiwa juna fatan alheri,
Baba Wadda wanda ke daga gefe ya dan murmusa ya ce kai o,o yanzu, ita maijiran dawowan Meenatu fa can gida, murmshi kawai yayi,
Sun karbo maganin kamar yadda kullun ake zuwa karba ,
Ya tafi Baba Wadda ne don yaga wuri saboda ya dinga zuwa karba don shi baida enough time,
Baba Wadda ne ke tunasar dashi zancen sadakan da malam tsoho ya cd su yi,
Baba Wadda yace ina fa yin sa a wanan kauyen zaifi don ka ga acan cikin gari babu yaran da zaka bawa,
Yays Abubakar yace gaskiyane Baba barin wa malam magana sai a sayo min,
Shawaran Baba Wadda yai amfani sosai gurin, don yara har sunfito fiye da tsanmani saboda sun saba karban sadaka a gurin malam sun san da yana sada shiyasa da anfara cewa Ana Sadaka,,, zasu fito dayawa karba,
****** ********** ******
Sallaman Fattu naji a daidai lokacin da nike daga baya ina shanya kayan dana wanke muna,
Dan saukin da na samu ita Sadiya bata amfani da kaya sosai,
Sai godiya take min a lokacin da nashiga kwasan kayan wankin nata a dakin