Advertisements
Chapter 59 Reading TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  Complete Novels

Chapter   59 / 61

174K to 177K   out of 180.5K words

yamiko min nakarba tare da fadar nagode yaya,
Godiyan yai masa dadi sosai irin yadda naga ya lumshe idanuwan shi, yana murmushi,
Abinda rai ke so a take na fara shan Ice, cream din kamar mayunwaciya,
Irin yadda nake sha babu kakautawa yasa shi kura min ido acikin mamaki,
Muryan Yaya Abubakar da samun Ice cream yasa na manta cewa yana dakin tsaye ya harde hannayen shi, guri guda ya kuramin ido yana gani irin yadda nake haukan sha,
Yace haba Meenat yanzu kina son wanan abin haka kika kasa fada min, indinga sayo maki,
Ya kamata ace kin saki jiki dani zuwa yanzu ace nasan bukatar ki,
Don kada ki dinga sa ina zaluntar ki haka dubi yadda kike shan abu tankar mayunwaciya,
Cikin shagwaba nace ni yaya ban san yadda zance a dinga sayo min abuba haka ni kadai,
Sai inga cewa baka sayo wa sauran yan uwa na ba ai, gara sai a,sayo muna gaba dayan mu,
Yai murmushi yace aikuwa kowace da abinda takance azo mata dashi, wanan ai abin ra,ayi ne ,
Don kinga ita Salawa ai abinda tace tana bukatar a sayo mata ko ?
Yafara tafiya yake cewa ashe shiyasa kika kasa tuna min da zancen lefen ki da na manta banyi maki ba ko ?
Murmushi nayi tare da dukar da kaina ina man cigaba da shan Ice cream dina sai dai wanan karon a hankali na fara sha,
Yana mai dafa kofan gita dakina yake cewa kiyi hakkuri please wallah mantawa na shap da zance,
Amma yanzu na bada sako a kasar Dubai za a hado maki duk abinda ya kamata,
Kuma nasan cewa Anty Amarya zasu ga cewa kawai dai banda niyar maki ne shiyasa na share zancen,,
Nace cikin kada kai gaskiya wallahi Yaya banta ba jin wanda yai wanan zancen ba,
Yace ok hakan yayi yanzu dai ai zasu ga kayan ya riske su girshi ko ?
Bugon kofan da Salawa takeyi tare da kwada Sallama da karfi yasa shi yin shiru,
A zuciye yace, wai waye wai ta karba daga kofa da cewa Nice,
Bai fita daga dakin ba sai daga labulr da yayi ta yadda zata iya hangoni, daga inda nake zaune, ina shan Ice cream di na,
Yana bude labulen na hango Salawatu a tsaye cikin masifa,
Ta zuba mai wani irin uban harara, tare da jefan sa da wani irin mugun kallo
Mai cike da zargi akan yadda ta han goni daga bakin gado a zaune ,
Yaya Abubakar ya hade, ran shi yana mata wani irin duba yace Lafiya haka,?
Ta wani ya mutsa fuska tace naga dawo wanka tun dazu kuma banga sakon nawa har yanzu,,
Ya kara daure fuska yace tun da ni yaron aiken ki ne shine kika kasa hakkuri har izo in samay ki,
Salawatu ta fahinci yanayin da Yaya Abubakar ya nuna mata na bacin ran shi,
Watau ma yana nufin cewa tazo tana damuwar shi ke nan ko ?
Saboda iya mu,amulan salawatu da maza zata iya gane k irin halin da namiji ke ciki tundai mashi da take mutuwar so,
Wani irin kishine da bakin ciki suka ziyarci zuciyan ta
Idanun ta suka canza launi a lokaci guda tare jin wani irin haushi da takaici,
Ta tabe baki tace, duk dai abinda, mutum yayi ai Allah yana ganin sa,
Yaya Abubakar, yasaki wani murmushin takaici yace,
Idan zaki iya jiran inzo sai ki jirani idan bazaki iyaba kuma sai ki shigo ko ?
Ta tabaki ta juya acikin bacin rai zuwa tsakiyan falo zuciyan ta tankar ya buga, saboda wani irin bakin kishi da ke cin ta,,
Bayan ta ya bi da kallo a hasale yana maigirgiza kan sa a cikin takaici tare da yin tsuki,
Ya juyo yana fuskanta ta na dukar da kaina da sauri naci gaba da shan Ice dina,
Sai da ya dan dauki dan lokaci kadan a dakin nawa duk da ba komai yake yi ba inba wayan shi da yake ta faman dakila ba, sanan ya fito, yana mai min sai da safe,

Yana hawa sama yafara
Kokarin cire rigar jikin shi don yai shirin barci,
Tashigo dakin a cikin dan daure fuska yai tankar bai ga shigowar ta ba,
Tace wai ya zancen sakon nawa ne Sweet Oga ?
Yaya Abubakar yayi saurin dakatar da ita acikin daga hannayen shi yana cewa,
Wait Salawa ban son surutu da yawa, so please live me alone,?
Salawa ta zubawa Yaya Abubakar ido kamar mai son ganin wani abu,
Yayin da zuciyar ta ke tafarfasa tana anyana cewa lalai Yaya Abubakar zuciyar ta na gurin wanan munafukan yar karamar yarinya,
Lai la ba shakka Oga hankalin shi yana a gurin matar shi yar uwar shi tabbas,
Itace fa ta aika sako amma sai gashi ya sayowa wata ita ko zancen nata,
Yazu Oga nice fa na baka sako amma baka sayo min ba ka sayowa wace bata ce tana so ba da farko,
Yace look Salawa ban son yawa fitina na fada maki ,
A kinsan cewa kece kika bada sako nafita don may bazaki iya jirana har in dawo ba in baki naki tunsa aguri guda zamu kwana dake,
To amma ai ba wai lalaine ace sai ka shiga dakin ta ba ko ?
Ya Abubakar ya juyo a hasale yana cewa, Salawa please will you live me alone ?
Ta zauna cikin bacin rai a bakin gado tana mai tsura mashi idanu, ta bayan shi yayin da yake kokarin daura towel a jikin shi don shiga wanka,
Tace yanzun dai ina sakon nawa yake yace cikin hasala da fadan babu shi,
Baki fada ba in time, don haka ban samu sai dai nabar kudi gobe zan karbo maki,
Tace amma kasan cewa, yanzu ne cinsa ya zo min arai ko, don may zaka ce sai gobe kuma,
Yace to ban sayo ba sai kifita kije ki sayo da kanki ko. ?
Cikin mamaki take kallon shi tace Oh, haka kace ko ,?
To, Babu inda zan tafi tunda ai bani kadace da wahalan cikin ba harda kai ma,
Ya ce a yar hasale to ban siyo ba saiki kyaleni hakana please,

Fanin fruit din sunada yawa sai na raba biyu na nufi dakin Anty Sadiya dashi don in basu su sha, in suna da bukata,
Na samu Ramatu a zaune tana jan tasbaha anty tana daga kwance tana kallon TV,
Nai masu Sallama ina mai mika ma Ramatu ledan Fruit din ,
Nace ga Fresh Fruit da aka siyo yanzu nace barin debo maku ko ?
Daga gurin da Anty Sadiya take tace da watermelons a ciki ?
Nace eh da akwai shi ta mike zaune Ramatu tajawo plate tafara zubawa a ciki,
Nai masu sai da safe nadawo dakina, nai addua na rufe kofana,
Ban wani dade a farke, bayan na gama yin addu,oi na da na saba yi kafin in kwanta barci,
Duk da ina yi amma kuma tun ranan da matsala ya faru da anty Anty Sadiya ban yarda in yi barci banyi addu,oi na ba

****** ********** ******
Washe gari ban fito ba sai da nai wanka na gyara jikina tsaba acikin wani purple material, mai adon flowers ash,
A Niger na sayo su da muka tafi shida kan shi Yaya Abubakar ya zaban min shi,
Nasa su ne don nasan yana sha,awansu tunda har ya zaban min su,
Ashe kenan zai ji dadin ganin nasaka su ajiki na da ina boyon su ne saboda banda kaya da yawa amma yanzu da naji cewa zai sayo min sutiru sai kawai nace barin saka abina ajiki inja aji,
Suna zaune a dining don cin breakfast, din su wanda yanzu da karfi da yaji Salawatu ta hana aci a tare,
Daidai lokacin da nake kokarin fitowa cikin tako irin nawa ,
Salawa ta zubu min ido, tana mai min wani irin kallon kamar manya,
Nasan ba komai take kare min kallo akai ba sai wanan tufafin da na saka ajikina, masu daukan ido,
Kamar yadda na hango ta ta ashe ni da ido nima din haka nai mata don wani irin kallo na watsa mata tare da harara,
Daga gurin da Yaya Abubakar yake zaune ya tsuro min ido tare da sake min wani mayaudarin murmushi,
Ya tataro dukkan hankalin sa gareni, yana ma sakemurmushin gani na,
Nima dai muna hada ido murmushin nasakar mashi, mai narka zuciya don nima kaina ban san da cewa na iya irn sa ba,
Tuni Salawatu ta tsura mashi ido acikin mamaki tana mamakin yadda yanzu bai ko iya boye feeling din shi kan wanan yarinyar,
Wani harara ta wurga mashi tare da jan tsuki, batare da tace uffan ba taci gaba da kokarinkai cibi a bakin ta,
Na karaso har gaban table din yayin da kamshin jikina dana tufafina ya daki hancin salawatu,
Wani mugun haushi da takaicin wanan yariyanr ya ziyarci zuviyar ta
Yaya ina kwana nace mashi yayin da nakai gwiwowi na kasa gab da kujeran da yake a zaune,
Sai da ya dan hade abincin da ya deba ya kai a bakin shi,
Yace lafiya kalau Meenat yaya dare ya karfin jikin ?
Da sauri ta dago kai tana kallon inda nake a tsugune cikin harara,
Sai kuma taci gaba da cin abincin ta tana wani murde fuska
Yace kizo ki zauna muci abinci ko ko kuwa kin karyane ko ?
Nadan dubi abinci nagan shi wani fari fate da shi da gani baiji wani ingredients ba,
Sai naji kamar amai zai kamani a lokacin da sauri na kauda kaina daga kallon abincin ina cewa ba yanzu zan karya ba yaya,
Ya ce O right amma dakin karya ki karasa shan maganin ki please ?
Nace insha Allah a lokacin da nake mikewa tsayd da ga tsugunen da nake,
Na wurga mata harara kamar yadda take wurgo min daga inda take zaune,
Kitchen na shiga don hada abinda zanci don gaskiya bazan iya cin wanan abinda nagani ba wai jeloup din taliya,
Ina kokarin Fere Irish yaya yaleko daga kofan kitchen din yana mi sai yadawo inajin wucewar shi dakin Sadiya,,
Naci gaba da aiyukana kawai ban tsaya wani rakiyar shi ba don ina sauri in fara aikin na saboda yunwan da cikina yafara yi,
Banyi aune ba sai muryan mutum kawai naji abayana cikin fada tana cewa,
Ke Meenat gurinki nazo wallahi barin fada maki gaskiya ki fita a idona wallahi,
Idan ba haka ba har kika bari muka sa kafan wado guda dake, agidanan wallahi zaki gane kuren ki sosai,
Ke in ma badon hadin iyayye ba ma may zai yi dake yar kauye kawai kamar ki,
Murmushi nayi kawai don sanin halinda nake ciki don ba zan bari ta kara cutana ba,
Taji haushin murmushin da na keyi batare da na kula ta ba,
Tace a hasale ai dole ki mayar dani mahaukaciya yar iska kawai macuciya azzauluma waike kina takama ke tar uwar shi ce, dake da munafukin tsohon kakan ku kukayi kutun kutun kuka aure shi don kada ya aureni,
Cikin wani iriin tsawa nace mata ke yar iskan tsohuwa gantalala,
Duk kika sake zagan min iyaye wallahi sai yau kingane koni wacece,
Tana kokarin ta yo cikina Ramatu tazo da sauri ta shiga tsakanin mu,,


ZEEE MAKAWA YELWA
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
6⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH - AL -QAWI,,,,


Ganin irin yadda yanayi Salawatu ya nuna min nasan cewa zata iya yin duk wani abinda ta furta a kai na alokacin
Shigowan Ramatu a gare mu yasa Salawatu ta juya da fadan a gurin ta,.
Ban san may Yaya Abubakar ya manta yadawo dauka ba don tun daga kofa yake jiyo muryan Salawatu tana cewa,
Munafukin tsohon da ya hana aure ne don a aure ki wai ya yi maku hadin gida,
In har shi yace ki takamu yadda ranki ke so to ki fada mashi aikin shi bai ci ba don ni Salawatu naci dubu sai ceto,
Bata karasa abinda ta bude baki tafadi ba kamshi da takon Yaya Abubakar ya baiyyana a kitchen din namu,
Maganan da ya makale a bakin Salawatu ke nan bata karasa ba,
Ramatu ce tace to Alhamdullahi tunda Allah yadawo dakai Alhaji,
Wallahi fitina baida kyau baida faida maida gida baya yake yi,
Idan badon nima Allah ya kawoni ba aida ba asan yadda abin zai tsaya ba irin yadda ta taso ma,
Ga kuma zagin iyayye wanda bai dace tunda iyayyen yarinyar nan ai sai nake gani kamar duk naku ne da dake tunda dan su kike aure ko ?
Fuskan Yaya Abubakar wanda zakace bai ta yin dariya ba dashi ya hade guri guda,
Salawata matso kusa dashi tana ceea yawa Oga gara da Allah ya dawo da kai,
Kafadawa wanan fitsararan yarinyar tafita hatka wallahi don ni ba sa,ar ta bace,
A zuciye ya juyo gare ta ya daka mata wani irin tsawa yana cewa,
Shut up my friend I don't want to hear from you,
Maza zoki fice min daga gida please,?
Salawa ta juyo tana duban shi a cikin mamaki tace Oga ni kake kora daga cikin gidan ka don muna fada da wanan yarinyar,
May wanan yarinyar zata gwada min ne wai da har kake kokarin ko yaushe kare ta,
Ran Yaya Abubakar ya kara baci yace, a fusace tare da mata wani kallon rainin hankali,
Wanan yarinyar ai kema kin san cewa tafi ki komai ko,
Tunda har kika tsaya duk yawan shekarun ki a kanta wai kina fitina da ita,
Tunda idon ka a rufe yake a kanta ai bazaka ga lafin ta ba ita,
Yaya Abubakar ya watsa mata harara yace ni mata na sun fiki komai Salawatu tundaga mutunci, dakuma kamun kai, don babu wace ke jamin fitina da bacin rai a gida da waje sai ke,
Wani irin mugun bacin rsi Salawatu taji a wanan kalaman nashi ,
Take taji gidan tankar yana juya mata, yau ita Salawatu ce ake fadawa haka cewa,
Muryan shi taji yana ceea Get,out in my house please ,
Fuskan shi ta duba wanda babu alamar wasa a zancen shi dole fita zatayi
Lailai ma watau namiji baida tabbas yau ita da tske ganin cewa duk ta dara sauran matan Abubakar a komai ,
Wai ta ce akewa wanan cin fuska a gaban kishiya da ar aiki,
Hawaye ne na takaici ya zubo mata a fuska yanzu bata da wata magana tunda har ya kwnce mata zanin a gaban kowa don har Sadiya dake daki saida wanan hayaniyar ya fito da ita,
Takasa koda motsawa agurin muryan shi stil yana cewa kuma ina mai tabbatar maki wanan tsohon da kika zaga har sai kin nemi gafaran shi ke da gidan nan,
Don shine sillar zuwa na duniya har kika gani kika lake min,
Da sauri ta daga kai ta kalli Abubakar wanda yau ya koma mata tankar zaki agabanta,
Yace idan na kyale ki agidan nan wata rana zan dawo na samu kin min kissan kai a gidan nan tunda ke dabi,un ki na yan jagaliya ne ,
A hankali naga Salawatu ta juyo ta kali gurin da nake tsaye da yukan da nake fere dan kali,
Sai kuma ta juya ranta abace tafice da ga kofan kitchen din hawaye na zuba mata a idon ta,
Bayan ta Yaya Abubakar yabi a fusace ya cewa Iam tied with dis in my house please live us alone,
Daga dakin ta yana tsaye daga kofa ya ke fadar hakan ta girgiza kai azuciyar ta tace tab dijam yau kan angama sance mata a kasuwa daga wani irin kallo za,a dinga yi mata agidan kuma,

****** ********** ******
Tafiyan salawatu bai min dadi ba a rai don ba dadi irin haka , duk da dai mahaifana ta zaga da kakana,
Amma bai,kamata ace har ta bar gida akan hakan ba don saboda yaya Abubakar tsaye yai mata har sai da ta gita gidan,
Shima ya fita, duk Anty Sadiya ta nuna cewa hakan shine daidai ni dai a gaskiya har cikin raina banji dadi ba,
Maganar Ramatu ne ya dan hankaltan da ni inda take cewa to ke uwar daki na. Idan har Alhaji bai dauki mataki a kanta ba watarana babban magana zata jawo mai a gida,
Sai a lokacin nagane cewa warning din ta yake son yayi don haka nace Allah ya kyauta kawai,
Ganin da nayi cewa yanzu Anty Sadiya taji sauki sosai yasani cewa ta karbi girkin ta a ranan idan don cooking ne ni zan dinga yi gaba daya,
Batayi musu ba ta karbi girkin ta tare da yi min godiya gurin Yaya Abubakar ne dai muka samu matsala,
Don daya dawo yagane cewa Sadiya zata koma girki yai ta masifa yana cewa kamar abin gudu bazata bari taji sauki ba sossi , zata soma girki a yanzu,
Amna sai na bashi hakkuri ina sheda mashi cewa nice zan diga cooking din gidan gaba day,
. kuma indai yai haka Sadiya zata zaci ko wani abu yake

59 / 61