Advertisements
Chapter 52 Reading TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  Complete Novels

Chapter   52 / 61

153K to 156K   out of 180.5K words

dani ba don zan iya mata sheri,
Muryan Maman Biu naji tana cewa ni dai wanan matar batai min ba gaskiya bata dace da maigidan ku ba,
Ai duk matar da bata son kwanciyan hankalin mijin ta bata san may ta keyi ba ke nan,
Sadiya tace ba kowa ke harin rayuwa na ba sai wanan makiran don nasan cewa kowa rantsuwa nayi ban kaffara,
Mamakin ta daine ya kara kamani don jin ko may tace akan Sallawatu,,

****** ********** ******
Da yamman ranan suka koma gurin maimagani harda Sadiya, sai dai mama bata samu zuwa ba tace kan ta na ciwo,
Sun samu malamin a gida sabanin dazun da safe da suka zo,,
Amma yace ace da safe yamna su dawo su samay shi,
Bayan yadan dade yana wasu yan abubuwa irin nasu na malamai, ya dago kai yana kallon su,
Yace gaskiya Alhaji a kwai matsala sosai a gidan ka,
Saboda idan har ba a fitar da wanan fitinar ba a gidan to irin haka zaku dinga gani,
Wani irin nisawa Yaya Abubakar ya sauke don jin may malam yace,
Don haka ya tambaya da cewa malam ai sai in sake gida ko,
Don ina ganin cewa hakan zaifi man sauki don ba musan ina wana mugun abin yake aje ba,
Malam wanda yai shiru yana kallon wani tasbaha dake hannun shi,
Can ya nisa ya na cewa ai ba a ainifin gidan akasa wanan kullin ba,
Asalima ba a wanan gatin da kuke yake ba, don haka kaga ba zanven gida bane,
Yace tun can garin ku kazo da abinka, don haka sai katashi tsaye sosai don neman mafita,
Saboda ai ba wanan ne karo na farko da hakan yafaru ba,
Sai dai ku baku iya gane hakan kuma du inda kuka tafi wanan abin yana bibiyan ku,
Yanzu duk yadda akayi akwai akasin da akasamu da har kuka gan shi da idon ku,
Malamin yace barin fada maka gaskiya Alhaji idan har a gidan ka za ai ciki to ba zai taba samuwa ba ga matan ka,
Sai dai idan har babu wanan kullin akusa za,a iya samun ciki bance maka a,a ba,
Wani irin firgicin rayuwa suka shiga gabadayan su sai Lawal ne ya ke kara tambayan malamin da cewa,
Yanzu malam baka fada muna yadda al,amarin yake ba sai magana kake muna adunkule
Murmushi malam yayi yana cewa bazan ce komai ba amma bada dadewa ba komai zai walwale insha Allah,,,
Kuje kuci gabada yin abinda na baku mu gani har Allah ya bata lafiya,

Baba Wadda ya iso garin alokacin su yaya basu gida sun tafi gurin katban magani,
Don haka ni kadaice agida saboda Salawa tafita ita ma alokacin,
Nan Baba Wadda ya fitar da sakon da malam ya bayar akawo min harda zuma mai yawa acikin sakon nakarba tarr da godiya nakai dakina na boye, inda babu maigani,
Abincin da na girka na debowa Baba Wadda, tare da bashi abin sanyi don jika makoshin sa,

A hanya su Yaya Abubakar suna dawo wa daga suleja sai zufa yake faman sharewa,
Don maganganun malamin yana mashi yawo a rai,
Kenan ita Meenatu da ta samu ciki ba,a nan ta samay shi ba ke nan ko?
Sai ya tuna cewa ai, duk yadda akayi kenan tafiyan mu kasar Niger Republic nasamu cikin da ya zube kenan,
Bai san lokacin da ya furta Innalilahi, Wa,inna,Alaihim Raj,un
Yanzu yaya zaiyi ke nan ana nufin crwa idan har zaiyi ciki da wata mace sai bai kusa dawa ke nan,
Bayani dai ya nuna cewa, Meenatu dai bata aciki ke nan tunda har ta samu ciki,
Innalillahi ya kara furtawa a filli, tare da goge gumin da ya karyo mai agoshi,
Watau rashin haihuwa agidan shi yana da wani nasaba kenan da wanan abin sihirin da ya gani,
Ashe zama bai gan shi ba ke nan don dole ne ya mike,
on neman mafita akan al,amarin kafin yai yawa don gaskiya iyanzu yafara son haihuwa, a rayuwan shi,,,


ZEEE MAKAWA YELWA,,
[8/24, 05:58] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
6⃣1⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL-BAAITH

SAKON GAISUWA DA BARKA DA SALLAH GARE KU MASOYA ZAINAB MAKAWA,
FATAN ALHERI ZUWA GARE KU KAMAR YADDA KU KE MIN,
IDAN NACE ZAN TSAYA ZANA SUNAYEN KU BAZAMU SAMU ZANA LABARIN BA YAU,
AMMA DUK MAI KAUNATA DAKU MA YAN UWA MUSULMAI NA DUNIYA
ZAINAB NA MAKU BARKA DA SALLAH ALLAH YA MAIMAITA MUNA,,,,,,

Tashin hankali wanda yafi karfin furta zance shi Yaya Abubakar ya shiga ciki,
Don sai gumi ke feso mashi da kafafen jikin saboda irin yadda ya ke ji, a lokacin,
Allah kawai ya tsare su don tuki kawai yakeyi batare da yasan may yakeyi ba,
Tunane kala kala sun zo mai a lokaci guda batare da yasan yana yi ba,
Sun iso gida sun samu Baba Wadda ya iso a lokacin don har yaci abinci yai sallah ko,
Nan suka zauna da Baba Wadda a falon gaba dayan su a na gaisawa,
Ina kitchen ina yan aiyu kana tare da kara rusa abincin a cikina,
Jin shigowan su yasa na fito don in masu barka da dawowa,
Kallo guda naiwa yanayin Yaya Abubakar nagane cewa yana cikin tashin hankali,
A take naji banji dadi ba don gabadaya a rude yake sai faman mazurai da idanu yakeyi yana kallon ko wani sashe nagidan kamar mai nemqn wani abu,
A lokacin da naji Baba Wadda zai fara mashi bayanin akan Sakon da yazo dashi sai na bargurin zuwa part dina,
Ganin irin halin da Sadiya take ciki ne Baba Wadda wanda yaro ne sosai amma ya kawo shawaran cewa ya kamata fa asanar da yan uwan Sadiya don a samu wanda zaizo jinyar ta,
Cikin murya mai nuna damuwa da kasala Yaya Abubakar kecewa saida nai tunanen hakan nima,
Don kaga wanan tsohuwa dai tai muna mutunci sosai gaskiya,
Ba kuma zatai ta zama a nan haka ba, don ita ma tana da nata laluran ai,
Matsala guda yanzu shine ai kasan halin irin na Sadiya, ba kirki ne gare ta ba,
Ba ruwan ta da yan uwanta bakajin tana zancen kowa daga cikin yan uwan ta,
Ba ta damu sam da yan uwan ta ba balle wani daga cikin su yaji dadin zuwa gurin ta,
Ai akwai wata wace ta taba zuwa lokacin da nafita karatun wata shidda amma kafin in dawo matar ta wuce saboda irin zaman da su kayi,
Baba Wadda yace amma dai duk da haka ni sai nake gani da dai a sanar dasu zai fi,
Don kada daga baya su zo su ce ai ba,a fada masu ba,
Gaskiya ne kuma inji Yaya Abubakar wanda ya fada cikin bata rai,
Yana cewa zan kirasu in sanar da su idan sun zo to idan babu wanda yazo kuma shi ke nan,

A lokacin Salawatu ta shigo gidan saye da wani dogon riga sai dan wani yalalon gyale daidai wuyan ta,
Gaba dayan su kallon ta sukeyi kowa da irin kallon mamakin da yake mata,
Duk da ta sheda Baba Wadda amma sai batai masa sannu da zuwa ba tasa kai zata shige,
Cikin wani murya Yaya Abubakar yace, Salawatu da karfi abinda yasa ta juyowa tare da dawowa baya,
A cikin bacin rai yace baki ga Baba bane zaune ko baki san shi bane ?
Kunya taji amma sai ta dake tana cewa, gaskitan kula dashi ba don ban kalle gurin ba,
Sannu da zuwa ya hanya tace tare da wuce wa çiki,
Yaya Abubakar ya dan rintse idon shi don shima halin shi kaman namune don bamu kaunan a taba yan uwan mu,
Baba Wadda bayan shigewan wata ya dubi Yaya Abubakar yace
Maisunan malam wanan matar taka ai ba sa,an yin ka bace, don da alama zatai wuyan saitituwa, kamar sauran mata,
Murmushin yake kawai Yaya Abubakar yayiwa Baba Wadda don jin abinda yace,
Ya san halin Baba Wadda shi bai boye zancen zuciyar shi sam
Wayan shi ya jawo daga aljihun shi inda yafara neman layin wayan mahaifiyan Sadiya,,
Kamar bazata daga wayan ba amma sai yaji muryan ta tana cewa Salamu Alaikum,
Sun gaisa acikin mutunci sai dan shiru ya biyo baya,
Can Yaya Abubakar yace Mama dama Sadiya ce ba lafiya yau kwana biyu ke nan,
Gaban Hajja ne ya fadi don itama kwana biyu kenan da take fama da Dodon ta wan da ya dawo duk jikin shi ya salle saboda tabin da Sadiya tai masa,
Amma karfin hali irin na Hajja sai cewa tayi yanzu may zan yi mata nida ke nan, ku kuna can,
Allah dai ya bata lafiya
Daga haka ta kashe wayan ta tabar gurin cikin kunan rai don a lokacin taji hamman Dodon ta wanda idan yai hamman zakaji wani irin wari, mai doyi, yana tashi, a guri,
Wani irin mamakine ya kama Yaya Abubakar a lokaci guda,
Yadade da sanin cewa,Sadiya halaiyan uwar ta ke gare ta, na rashin mutunci,
Bai kara gaskan tawa ba sai yau din ya tabbatar da hakan ,
Ace yar ki ga halin rayuwan da take ciki amma sai ki cewai, ke ya zakiyi babu Allah ya sauwa sai kawai ki kashe waya don rashin imani,,
Baba Wadda wanda ke daga gefe yana nazarin yadda suke waya da Hajja yace,
Ya ce tayi ma halin nata ko ?
Murmushi mai kama da yake Yaya yayi kawai tare da hade wasu miyau masu zafi,
Daga gurin da yaya Abubakar yake zaune, kasan carpet, ya jingina bayan shi ga kujera,
Ya sanya hannayen shi guda biyu ya dafe goshin sa da su,
Zuciyar shi sai wani harbawa takeyi tana masa ciwo, da radadin saboda duk, abin duniya yai masa yawa,
Falon na shigo da sallamana, ganin yanayin sa yasa na gaishe shi a sanyaye,
Cikin dauriya Ya Abubakar ya cire hannu daga goshin shi ya,dago idon shi da,suka rine sukayi ja,
Yake ce min a hankali Meenat kina kuwa shan maganin ki ?
Na ansa ma shi da cewa ina sha yaya har sun kusa karewa ai,
Baba Wadda wanda ke gefe sai cewa yayi Meenatu malam na cen duk ya tayarwa mutane da hankali yana cewa wai kina garin mutane babu mai kula da ke,
Daga gurin da nake na sake wani irin murmushi ya subuce min, har ina yar darawa, nace malam ho,
Ya Abubakar ya ce, daga gurin da yake zaune ai kasan malam baida kamar meenatu duk gidan nan,
Ina fada mashi cewa ta yi bari ya na batun fasa min dodon kunena da wani irin salati,
Wani irin duban wasa na sakewa yaya Abubakar ina cewa amma dai kowa yasan cewa kaine dan gaban goshin sa bani ba,
Ni da watarana muke fada har ya hana min fura, ko zuman cin masa,
Abin mamaki sai kiran malam din ya shigo a wayan yaya Abubakar, a lokacin,
Cikin dan ya mutse fuska yaya Abubakar yace ga dan rigiman nan ya bugo ai,
Nace, Allah sarki malam yana dai ji da kai Baba nasan ya bugone yaji ko ka iso,
Bayan sun gaisa ne yake tambayan ma su jiki yaya Abubakar ke masa da,sauki,
Sai kuma yafara mashi bayanin yadda zai da maganin da aka kawo mashi,
Sai yake cewa yaya Abubakar ya tabbatar da cewa yai sadaka da masa mai zuma ranan jumma,
Sai kuma gyadaw wanda akasoya, suya ruwa wanda zai ba wa yara kanana sadaka,,
Sai sugar na kwali cubes yaraba yara kana shima yace duk wani abu wanda zakaba yaro yasha har yaji dadi dashi zaka hada ka basu sadaka,
Amma ka tabbatar da duk yadda nai bayani kayi da wa yan nan sakon kayi
Godiya sosai ya Abubakar yayiwa malam tsoho tare da fara mashi bayanin abinda malam dake kauyen da suka tafi yace masu,
Malam tsoho ya kira sunan yaya na kwarai da cewa,
ABUBAKAR, yaya ya amsa mashi da cewa na,am malam,
Malam yace ba sai ka fada min ba don ni nasan komai ko,
Don tun bayau ba nake hasashen wasu abubuwa da dama a gidan ka,
Yanzu ne zargina ya tabbata cewa aike ne ake maka daga nesa,
Don ni tun auren ku da Aminatu nagane cewa akwai wani bakon al,amari a tare da kai,
Amma mutun karya yayi saidai Allah badai mutum ba wallahi,
Tun lokacin da suka fara zancen abinda malam ya fada masu hankalina yai mugun tashi,
Muryan Baba wada ne suka ji daga inda yake zaune yana cewa cikin dan kwantar da murya,
Ai wanan mace muguwa ce yanzu mutane ko da kudi basu bi hanyan gidan ta,
Yaya Abubakar ya ke tambaya da crwa wake nan ?
Ba wani shakka ko tsoro a fuskan shi ya Hajja mana,
Da sauri naga yaya Abubakar ya dan juta gurin da nake yana kallo na,
Baba Wadda wanda bai san may ba sai ci gaba yayi da fadin
Ai tun ranan da ta shigo gida da nufin gaida Maman mariya (Mama Ladi)
Iskokin mata yai ta tashi harda mariya wace mun koma daga nan ba,a wani dade ba
Mariya nada iskane ?
Yaya Abubakar ya tambaya cikin jin haushin hiran shirmay da Baba Wadda keyi,
Nan Baba Wadda yashiga zaiyana muna tiryan tiryan yadda al,amarin ya faru a ranan,
Dagani har yaya Abubakar shiru mukayi tankar ruwa cimu muna sauraren abin al,ajabi,
Idan hankalina ya kai dubu babu wanda bai tashi ba a ranan don tsoro, da fargaba,
Don tun ina karama nake tsoron Hajja muna ji a,na cewa muguwa ce,
Wanan labarin yasa na shiga wani irin hali wanda har na kasa boye,
Ya Abubakar wanda sai Innalillahi yake maimaitawa, don mamaki,
Duk da ba wai yarda da zancen yaya Abubakar yayi ba amma sai zance ya sosa mashi zuciyan shi sosai,
Shigowa Sallawatu cikin wasu matsatsun kaya tana taunan chewing gun, da wani irin kara, wanda ya dawo masu da hankalin su gare ta,,
Cikin wani irin murya take cewa Yaya Abubakar sweet Oga, na son,ganin ka ne fa ,
A hankali ya dan dago kai ya dubeta sai yake ce mata, naji ina zuwa,
Bai wani dauki lokaci mai tsawo ba ya mike tare da dan tsuki, ya bi bayan shu,uman,,,

Wani irin ajiyan zuciya na sauke, tare da kallon gurin dashupba Wadda yake zaune, a cikin mamaki,
Nan nake tambayan shi zancen al,amarin Hajja ya ke bani labarin irin muggancin ta da takeyi,,
Tsoro ya kara kamani sai naji ba ma zaman gidan ba duk garin gaba daya ya fita raina,,,
Nace gaskiya Baba ni zan koma sokoto ne don duk garin nan ya isheni wallahi
Baba Wadda yace Meenatu in sha Allahu babu abinda zai samay ki,
Don Allah ya natare da bayin shi , ke dai kawai ki rike ibada da addu,oin neman tsari daga sherin mutun ko dabba ko, aljan ko kwaro,
Nace ina yi duk wanda malam tsoho ya umurce ni da yin tun da farko,
Yace Allah ya tsare ni kin ga wanan matar ta mai sunan malam batai min ba sam,
Don duk take taken ta na ya zauna da ita ce ita kadai don wanan bata kaunar ta bude ido ta ganshi da wat mace daga cikin ku,
Baba Wadda yace tun dai ke Meema don baki gari a lokacin zuwan ta gidan nan ida ta dage adole sai dakin ki, zata zauna wai yafi kyau da girma,
Sai da,na nuna,mata ni da Hamza cewa mun fisu iya,iskanci, sannan aka zauna daidai...
Nace Baba har yanzu bawai tabar ni bane ji take kamar ta daina ganina agidan nan kwata kwata wallahi,
A hasale Baba Wadda yace sai dai tabar maki gida wallahi don babu inda zaki,
Auren ki da mai sunan malam mutu ka raba bana rabuwane in ta sawa ran ta sauki ta,
Nace cikin yar tausa murya wallahi Baba ka daina zancen ta don zaku iya batawa da Yaya a kan ta wallahi,
Ai shi yasan cewa bani kaunar wanan matan a rayuwa na wallahi don ni sam batai min ba,,
Saboda kallon yan Togo nike mata, knga waya dai ta taho tai mashi,
Dariya sosai Baba Wadda ya bani nace cikin dariya Baba So ne fa haka na, son ta ya ke yi shinasa,,
Baba Wadda yace kai wani irin So Meena son yaudara ko ?
Yanzu fa debo tahowa dai tayi ta ce mai ya taso yatashi ya bita kamar Rakumi,
Yanzu ke kina iya cewa Taso kazo ya taso zuwa inda kike haka kai tsaye,
Sod di ya,i gwalmad,diya,i,,,,
Dariya yasani shigewa dakina don Baba Wadda a cikin serious yake zancen shi,
Na shiga don gabatar da Sallah nakai wani lokaci kamar kullun ina kai kukana ga Allah,
Daga inda nake zaune zancen labarin Hajja da Baba Wadda ya bamu yazo min a rai,
Nan gaba na ya shiga faduwa don nasan cewa tunda malam tsoho da kan shi har ya furta cewa da matsala a

52 / 61