Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : Complete Novels
zan fita waje,
Anty Safiyace ke tambayana ina zan tafi,? nace mata sallah zanyi don ba muyi sallah ba, daman,,,,
Ita ce da kan ta ta taso tabani buta da sallaya sai kuma ta rakani tana nuna min inda zanyi tsarki,
Gurin da na idar da Sallah muke zaune da Anty, Safiya da Samira, muna kara zance akan ciwon Mama,
Samira ce ta kara jefo min tambaya cewa har yanzu ina Abuja ne ko na dawo sokoto,
Nace mata ina Sokoto ai tun sati kusan uku, da suka shude,
Sai naji ta nisa tana kallon yar uwar ta can dai tace,
Gaskiya Anty Safiya idan har Meenatu bata Abuja za,a samu matsala sosai idan ance Mama zata can jinya,,,
Anty Safita tana kallon yar uwar ta tace, matsalar may,
Ai baza a samu matsalar komai ba kin manta cewa Sadiya diyar Mama ce,
Ni Samira ta kalla amma sai nai kamar ban fahinci may take nufi ba don haka sai mukabar zancen kowa yai shiru a cikin mu, duk kan mu uku kowa da abinda yake kiyastawa a zuciyar shi,
Daga inda muke zaune muka hango yaya Abubakar shi da Aliyu tare da wani doctor, sun nufi dakin da mama take kwance a ciki,,
Ba,a dauki lokaci ba sauran yan uwan mu dake cikin dakin har mama Sa,a su ka fito waje daga dakin,
Gurin da muke zaune, su ka dawo suna cewa likita zai duba Mama, ne,
Nan kuma gurin aka sake hada wani sabon daban hira sai kace ba jinya a,kazoyi asibiti ba,,,
Sun dauki lokaci adakin tare da likita ciki zuwa can likitan yafito yabar su yaya da Baba acikin dakin,,
Sun dauki lokaci a ciki saiga su sun fito har Baba Buhari,,
Gurin da muke a zaune,da yan uwa nan suka nufo mu gaba dayan su,
Yan bayanai yaya ya kewa su Anty Mariya da cewa zasu bari zuwa gobe sugani idan mama ta dan kara samun sauki,sai su wuce Abuja da ita,,
Ina daga can zaune tsakiyan anty,Safiya da Anty Samira,
Yaya Abubakar ke cewa kizo muje ko zan samu indan huta, hakanan,
Wani irin nauyi ne da kunya suka rufeni a lokacin don duk wanda ke gurin ya girmay ni don nice karaman su,
Anty Safiya ce da Mama Sa,a suke cewa alokaci guda,
Meenatu tashi kuje kinji yace duk ya gaji don Abuja ba kusa bane,
A hankali na mike tsaye daga inda nike zaune saman sallaya,
Barin raka matar yayana inji anty Safiya, anty Samira kuma cewa tayi barin bisu su sauke ni gida nikan ,,
Bayan shigar mu motane, naga zamu tafi yqyq bai bar masu komai, ba,
Daga can bayan motan nake cewa yaya ya kamata fa kabar masu dan wani abun kashewa,
Bai yi musu ba ya ciro kudi daga aljihun shi yace wa Anty Safiya da batai nisa da motar mu ba tazo takarban masu,
Anty Samira wace ke tare dani a bayan mota tace wa dan uwanta,
Yaya shima Baba fa da mashin suka zo shi da mama Sa,a,,,
O,o Allah na nace, daga gefen da nake zaune, nace Allah ya yaye muna wanan halin da muke ciki
Anty Samirace takarba da fadin Ameen ke dai Meena,
ZEEE MAKAWA YELWA,,,
[8/4, 21:38] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
4⃣4⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH- AL-HALEEM,,,,
Wanka na fito ina daure da tawul, fari na hotel din a jikina,
Yaya Abubakar yana daga bakin gado zaune cikin wani dan wandon boxes na maza,
Kokari nakeyi in daure kaina da ribon fin da na dauko daga cikin jakata,
Muryan shi da abin da yake fadi yana kawowa daga gurin da nake a tsaye bakin mirror,
Hakan ne yasani gane cewa da mace yake magana kuma ba Anty Sadiya bace,
Saboda irin yadda naji yana bada amsa cikin shauki da so,,
Wani irin abune naji yai min tsaye a zuciya ta,har naji kamar idona yana rufewa,
Amma abinda yafado min arai shine zancen Anty, Amarya, alokacin da nai mata hira lokacin da Salawatu tazo gidan mu a Abuja,
Anty Amarya tace min,Meenatu koda mata biyu yayan ki zai auro yanzu a lokaci guda babu ruwan ki don ba yadda zakiyi,,
Don auren ki dashi aure ne na mutu ka raba ban ga dalilin da zai sa ki tayar da hankalinki ba,.
Abu gudane yanzu agaban kishine kisan yadda zaki tafiyar da rayuwar ki dana Mijin ki ta yadda duk wace ma zai auro bazata iya dake ba sai dai ta barki, da shi,,,
Ajiyan zuciya na sauke tare da dan kirkiro farin cikina a fili,
Ban san zuwan yaya Abubakar kusa da ni ba sai dai jin hannun shi nayi a baya na,
Daga haka muka dan yi tafiyan hazo a tare ba tare da na kara, tunazancen wata Salawatu can ba,
****** ********* ******
Karfe takwas na safe muna a haraban gidan mu kofan gidan malam tsoho dake uguwar shiyan Sarakuna cikin garin, Birnin Kebbi,,
Idan na tsaya baiyyana irin farin cikin dake dauke a fuskan kakan mu malam tsoho da wasu daga cikin iyayyen mu dake gurin,
Babu wanda yakai mahaifina farin cikin ganin mu a lokacin don dagani har yaya Abubakar ban san wanda yafi jin daddin gani ba a tsakanin mu,
Nafito daga bayan mota tare da ni da yaya Abubakar cikin murna yau gani a gida, bayan dan dadewan da nayi batare da na shigo ba,
Yaya Abubakar yana gaba ina biye dashi kamar yadda yake a gidan mu,
Don kusan doka ne hakan don duk wani dan gidan idan har yai tafiya yadawo dole ne sai ya fara zuwa rufar malam tsoho ya kai gaisuwa da neman albarka,
Sosai malam ya kasa boye irin farin cikin da yake ciki yau don ganin yadda TARKO shi yai kamu,
Mun gaisa da shi cikin wasan jika da kaka inda yake cewa watau Abubakar wayau da kai min ke nan, ?
Ka karbe min mata katafi da ita birni, kuka barni nan a cikin rumfa ko,
Dariya sukayi atare inda yaya Abubakar yana zama yace mai, ai, kai ba jarumi bane sunan kawai muka ara maka,
Don haka kaga da ni jarumin maza tadace shiya sa ka,sadaukar kabar min kawai,
Atare suka kara sa dariya malam na cewa to haka zaka ce min yanzu ko,
Tun da nai maka wanan, halarcin kake ganin kamar ban kai jarumi ba ko,
A hankali yaya Abubakar ya dan sasauta muryan shi kasa kasa yace bance ba tuba nake, malam tsoho mai ran karfe,
Nan nabarsu zaune a tare da malam din suna kara tataunawa a tsakanin su,
Direct sashen mahaifana na wuce kai tsaye,,
Na samu Mamana tana kokarin hada muna breakfast,,
Da dan gudu na nakarasa gurin ta na rugumay ta, ta baya, nadade rungumay da mama ina jin dumin jikin mahaifiyata,
Sai kuma ga hawaye sun zubo min shar ga ido na subbanallahi
Yar Baba may ye haka kuma farin kisa wata tashigo taganki kina kuka ace ai, wani abin ne ya faru, dake kuma,
Cikin muryan kuka nace mama naji marmarinku ne wallahi,
Tace to yanzu ba gaki ga muba sai ki cinye mu tunda kinji marmarin mu,
Kaina nakara nutsarwa a jikin ta nace, mama idan na cinye ku ingawa kuma,
Muryan mahaifina ne mukaji daga bayan mu yana shigowa gidan, yana cewa,
To ke Saratu tunda sun zo ai sai abarshi su karya anan ko?
Anan kuma malam mama ta tambaya cikin mamaki, da fargaba,
Nan muka zauna gaba dayan mu a yar barandar tsakar gidan mu ana hiran yaushe rabo,,
Babana yakalleni yai murmushin jindadi yace, to ya wajen kawun naki, ina fatan duk suna lafiya ko,?
Na ba Baba ansa da cewa duk lafiya suke suna gaisheku,
Baba yace , Nafi,u dan rigima,saiga shimkafa da su mai, ya turo min dasu wai, muyi anfani da su,
Shigowan yaya Abubakar a sashen mu yasa ma sauri dauko hijabin ta tasa,
Wai kada suriki ya ga jikinta,surukin da tun ba mu zo duniya ba yake ganin ta a hakana,
Shima afaninyaya Abubakar din yau sai yake jin wani irin nauyin Mama da Baba,
Don haka sai ya kasa sake jikin shi kamar yadda ya saba,
Baba ne yai mai umurni da ya zauna su karya a tare dashi,
Bai fi minti biyar da zaunawa zai yi breakfast ba sai ga Baba Wadda yana sheda mashi cewa, wai ana sallama dashi a waje,
Har zai mike sai baba yace dakata ka tsaya kaci abincin ka kafin ka fita,
Don yanzu haka da ka tashi bazaka kara dawowa ka zauna ci ba,
Masa ne da miya, sai, kunu koko, da kosai, da sugar,
Sosai yaya yaci masa da miyan da aka siyo muna gudan mai yawa, sosai,
Kafin ya kai karshe,sai ga yaya Aliyu ya shigo yana ce mai wasu daga cikin abokan su ne su kazo mashi murnan samun girman da yayi,,,
Daga wanan fitan ban kara ganin yaya Abubakar ba har zuwa, wani lokaci,
Nikuma ganin haka yasa nasamu sakewa da mahaifiyana da yan uwana munata hirar mu gwanin ban sha,awa,,
A dakin mamana in kwance saman gadon ta mana tana zaune saman kujera,
Mamana tace yar Baba naji dadin ganin kuna zaman lafiya da maigidan ki fiye da yadda muke tsanmani,
Da farko zancen auren ku hankalina ya tashi sosai wallahi sai nake gani kamar zai wullakanta min ke,
Amma tunda mahaifin ku ya ce min mubar wa Allah al,amarin sai kawai naji hankalina ya kwanta sosai
Don haka nashiga rokan Allah da ya kara sanya alheri fa wanan al,amarin,
Yakawar da duk wani sheri ko kulli dake tattare da wanan auren naku,
Tambaya najefo mata da cewa amma Mama Ladi ta daina wanan irin zagin da take muna ko,
Murmushi Mama tayi wanda ya nuna min cewa bata daina ba, har yanzu tana yi,
Sai Mama tace inma har bata daina ba ai sai tayi da wanda ya kulata,
Yanzu ai wanan ciwon kawai ya isheta ishara in tana da hankali,
Haka mukai ta hira da mahaifiyata mu na yi muna girkin abincin rana, tare,
Sai bayan Sallah azahar yaya Abubakar yabugo min waya yana cewa daga gida suka wuce, gaida mama sai kuma wani abokin su da gidan shi ya kone suka tafi mai jaje,
Akarshe yake tambayana da cewa ba dai matsala ko ?
Murmushi nasake ina cewa saidai na rashin ganin yayana a kusa dani, ba,
Yaji dadin may na,ce haka yasa shi dan murmushi jindadi,
Yace ai, gani zuwa don nasan mama tai min abinci rana, yanzu haka ko ,
Nace kaman kasani yaya amma dai tuwon shimkafa nace tai maka shine ta hada ma harda dan wake wai tasan kana son cin danwake da,
Murna sosai naji yanayi yace wa kifara min godiya kafin in zo, don ban san yaushe, rabona da cin dan wake ba,
Kafin yazo na dan tashi na shiga wasu sassan gidan mu ina gaida su,,
Sai zuwa dare na samu shiga asibiti,gurin gaida mama,
Gaskiya yau jikin ya dan yi dama sau don da alamar taji sauki,
Tun shiga na mama wace ke zaune tana shan kunu acikin cup,
Mu kayi arba da ita, sai naga ta kauda kai gefe guda, kaman bata kaunan gani na,
Har gaban ta na karasa ina gaishe ta da jiki,
Kamar bata son ansawa ta nsa min tare da kauda kanta gefe guda,,
Nagane may take nufi amma sai naki gushewa daga gaban ta naja na tsaya, mata,
Da ta gaji da aje kanta a gefe guda sai takai kwance ,
Anty, Safiya ce ke min magana daga bayana, tana cewa,
Matar yayana jiyafa munga sako, daga yayan mun gode,,
Da mamaki na juyo ina kallon Anty Safiya ina murmushi nace nikan anty ai wanan zancen kune ba nawa bane,,
Sai da dare yaya zo dakin inda yake tambayan yan uwan haihuwan shi, koda wace cikin su za,ai tafiyan,
Inajin yadda suke muhawara a tsakanin su, don anty ,Samira ce tafara magana tana cewa nidai kar ku sani don kun ga halin da nake ciki,
Haka dai sukai ta cecekuce, inda anty mariya tadage akan cewa itace zata,
Dole kowa ya kyale ta, ta tafi din su zasu zo daga baya suga jikin mama din insha Allah,,
Motar asibiti ce yaya yai haya zata kai, Mama Ladi har Abuja, tare da baba Wadda da Anty mariya,
Washe gari badon naso ba mukayi sallama da iyayyena da yan uwa da abokan arziki,
Mun kusa shiga sokoto,ne na dan matsa kusa da yaya Abubakar,nadan kwantar da kaina ga kafadar shi,
A hankali naji yana sauke ajiyan zuciya mai yar nauyi,
A hankali nace mashi yaya Allah yaba wa mama, lafiya
Ya ansa min da amin a hankali,,
Inda naji ya dankara matse ni zuwa jikin shi yana cewa, kici gabada kula da kanki pls,
Kudi ya mikomin don zasu kai kamar dubu hamsin, zanyi magana ya kada min kai dole nayi shiru bance komai ba sai dai ina rike a jikin shi,,,
A sokoto yaya Abubakar suka saukeni a gida tare da tsarabar da nazo ma su da shi,
Mun rabuzukatan mu babu dadi acikin ta don ga zancen ciwon mama ga kuma kewan rabuwa da junar mu da zamu kara yi,
****** ********* ******
Masu tafiya sun isa Abuja lafiya inda ba bata lokaci ya kai,ta Turkish hospital,
Inda kwararu likitoci suka diba mashi ita, Baba Wadda tare dashi aketa faman wanan zirgazirgan asibitin,
Salawatu tare da abokan ta sun zo gaida mama da abin arzikin su fam a leda,
Sun dan zauna jim kadan sanan su kace zasu tafi,
Kufi lubuna ta mikowa, Anty Mariya, tana cewa su zasu tafi Allah ya sauwaka,
Anty Mariya tabi bayan su don yi masu rakiya, suna cewa ta tsaya amma saida ta bi su har bakin motan su,
Sai da zasu tafine Anty mariya ke tambayar wace amaryan tasu ne daga cikin su,
Lubuna ta nuna mata Salawatu, wace take kokarin shiga mota, daga dayan bangaren,
Addu,an, Allah ya nuna masu anyi wanan abin arzikkin suke fata, kamar yadda tace,
Ai mu mun fi son ki shigo ko gidan dan uwan mu zai gyaru,
Bayan ta koma daki ta zaina kirga kudin da Lubuna ta miko mata dubu ashirin ne cif,
Tace cafdi mace ke kyautar kudi haka masu yawa, don aso ta kawai,,
ta maida kudin acikin aljihun bujen ta taja zip, ta rufe,
Sun kwana sun wuni Sadiya bata lekasu ba, tun zuwan da tayi da dare ranan da akabawa mama gado,
Tun abin bai damun Mama wace tafar murmurewa zuwa yanzu,
Har takai ga cewa su Anty Mariya, da Baba Wadda,
Shin Sadiya ko tazo ne tana barci?
Anty Mariya tace tun ranan da mu kazo tun ranan tazo dubaki tare da yaya,
Kagin su tafi duk ta ishe mu da tsaki tana tacewa yaya wai a kai,ta gida, ina jin sai da yai mata dan fada ta daina damun shi
Mama tace ke Mariya, badai, Sadiya ba sai dai in akwai wani matsala da ya hanata zuwa kawai,
Shiru Anty Mariya tayi don tasan cewa mama bazata taba yarda ai maganar Sadiya ba agaban ta,
Don ita Sadiya bata laifi agurin ta, sai dai yaya Abubakar yayi laifi,,
Sai bayan kwana biyu anty Sadiya tazo duba Mama yadda take wani ya tsune fuska tankar mai jin, warin su,
Shigowan yaya Abubakar dakin ya sa hankalin su dawowa gareshi,
Dauke yake da ledojin take away, din da ya sayo masu abinci,
Daga gurin da mama take kwance ya karasa yana cewa mama tashi kidan ci abinci ko sai kisha maganin ki ki kwanta,,
Mama ta ya mutsa fuska tana cewa, nagaji wanan shimkafa shimkafan maisunan malam, kace ma matarka tai muna tuwo mana haka,
Gurin da Sadiya take yadan kalla yana mata wani kallon ke kin ji ko ?
Ita ko Sadiya ko a jikinta don bata damu ba sam, don ba matsalar ta bane,
Yan office, din su yaya Abubakar da kuma abokan arzikin shi haka suke zuwa, gaida Mama, Ladi tare da mata abin arziki,
Wanda ganin haka yasa Mama Ladi kara mikewa saman gadon asibiti,
Don ita bata da niyar tashi, zuwa gida sam, ranan da yaya Abubakar yazo fada mata cewa za,a sallamay ta sai cewa tayi,,
Kada akawo mata bakin ciki a filin Allah don anga ta na samun abin arzikigurin mutanen arziki za aimata bakin ciki haka,?
Sai da lalashi da ban baki aka samu mama tayarda zata koma gida,
****** ********* ******
Yaya Abubakar bai samu kwaso su, ba da kan shi zuwa gida,
Don haka ya tura malam Mudi da driver don su kwaso su mama zuwa gidan shi bayan an sallamay su daga asibitin,
A falo su ka yada zango don basu san inda zasu shiga