Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : Complete Novels
zama yan uwana yanzu,
Sai tai shiru taji yaya zaiyi re,action,
Duk lafiya suke suna gasheki sun kuma yaba da sakon ki sosai,
Kai, Sir har fa naji dadin wanan zancen da na ji
ZEEE MAKAWA YELWA,,,,
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
1⃣4⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA,
ALLAH_AL-MALIK,,,,
BANZAN MANTA DA KAUNAR KU GARENI BA,,,
SAFIYA ABDULLAHI HUGUMA
MARIYA SB
HAFSAT YUSUF
NAFISAT HARZAMI,
MAMAN FARIDA
SAFENAT MAHMUD MAIDUGURI (ABUJA)
PRECIOUS HINDU KB
MAIJIDDA HARZAMI,
FATIMA YAHAYA NASAWA,
FATIMA GARBA LUV,
MAMA WALID DA WALIDA,,,
DAMA DUK WANCE BANKAI GURIN SUNAN TA BA, NAGODE MAKU KWARAI DA GASKE GA TAIMAKON DA KUKE BANI A KULLUN,,,,
Duk yadda suka so tafiya a karshen mako hakan bai samu ba don ciwon da Sadiya take fama dashi,
Dole tafiyan nasu ya dage zuwa wani lokaci don tana jin jiki,
Ga Samira fafir taki zama agurin su itama tashirya dawowa gida, gurin yan uwan ta,
Gado a,kabawa Sadiya don haka su Aisha da murja da suke manyan su,
Su ke zauna da ita a sibiti
Ganin irin yadda take wahala yasa yaran hankalin su tashi, sosai,
Suna tsaye a kanta har zuwa lokacin da abin yadan lafa mata,
Yayan su ya umurce su da su zauna da ita i je yadauko masu abin bukata a gida,
Barci Sadiyan takeyi i,yanzu don haka suma suka samu kujera su ka dan za,zauna a gefen ta,
A gida su Samira ne ke faman kokatin girka abinci kafin su dawo asibiti,
Kwatsan sai ga yayan su yashigo yanayin ba dadin gani don fuskan shi babu annuri ko kadan,
Hakan ya tayarwa yaran da hankali do sun matsu suji wani irin hali matar yayan nasu take cikine ?
Ba wani sakin fuska kamar kulkun fuskan shi a,daure, tam,
Kai tsaye yace masu ku sa min ruwan zafi a flasks, da kuma yan kayan da ake bukata a,asibiti,
Wanan dalilin yasa su gane cewa, an kwantar da ita a,asibitin ke nan,
Daga haka ya wuce, direct zuwa dakin kwanan shi,
Ido suka bishi dashi cikin jin takaicin irin halin yayan nasu,
Meenat dake daga cikin kitchen tana jin duk yadda suka yi tare da yan uwan ta,
Sai ga Samira tafado kitchen din tana cewa Meena kinji wanan matar wai gado aka bata, ashe,?
Ni wanan abin wallahi haushi yake bani,sai da mutane suka shirya zuwa gida, sanan zata wani kakalo ciwo ta narke a gado,,,
Sai ta karasa da jan guntun tsuki tana kokarin duba flask din dake gefe a jiye,
*** *** ***
Duk wani abinda ya umurce su da su hada mai don tafiya asibitin da su,
Sun hada mai a cikin wani basket da ke cikin kitchen din,
Yadda ya shiga fuska babu walwala hakan ya fito masu,
Yana kokarin sa bottom din hannun rigar shi fuskan shi a kan kayan da suka hada,
Inda Samira take zaune ya dan kalla yana cewa naga kayan da yawa mana , yaya haka, ?
Cikin dan girmamawa tace dama har da abincine muka hadawa su, Aisha,
Bai tankawa kowa ba sai kokarin da yakeyi na daukan basket din,
Samirace tace yaya dama wai muna son mu, bi ka zuwa asibitin ne,
Kamar bai ji may take fada ba ya sakai fuuu ya wuce abinshi,
Samira wace ta kai iyakan sai cewa tayi a fili, mugunta, har kan shi ya ke yi wa,,,
Nafisa wace ke zaune a cikin shirin bin yayan nasu zuwa asibitin da suka sa rai tace,
Ni tun farko ban so kisa musa ran mu ga zuwa ba wallahi don na san yaya bazai ko saurare mu ba, don dai kawai ina son ganin gari ne,
Hon din motar shi ne suke ji daga waje cikin karfi ya ke masu,
Samira wace ta san halin shi da sauri tace ashe, miskilin bai wuce ba mu yake jira a waje fa,
Meenat wace tana zaune har yanzu batai wani alamar motsawa ba yasa Samira cikin sauri tace mata taso mana Meena don kin san fa ba jiran mu zaiyi ba yana iya wucewa,
Kai ta gyada mata tare da kokarin shafa addu,a a fuskan ta sanan tace,
Anty Samira idan nace in biku wa zai zauna gida yayi muna girkin dare,
Baki Samira ta tabe gami da fisgan gyalen ta da sauri taja hannun Nafisa suka fita,
Su biyu Abubakar ya hango tun,daga nesa sun tunkaro gurin da yake,
Mamaki yayi na rashin ganin diyar Baba Samaila a tare da su,
Kamar zai masu maganar ta sai dai kuma ya share su kawai suka bude mota suka tafi,
***** ****** *****
Fitan su babu dadewa Meenat tafito tsakar falon gidan da nan tafara inda ta gyara shi tas takawo kamshi ta fesa,
Girkn dare ta dora sai kuma ta fara gyaran dakun gidan tun daga nasu har zuwa na matar gidan da na yayan su Abubakar din,
Ba, ita tasamu kanta ba sai zuwa gab da magrib a lokacin duk ta hada komai,
Kiran sallahbda akeyi a ko ina ina ya sanar da ita cewa,lokacin sallah yayi ,
Don haka babu bata lokaci Meena ta fada dakin su ta dauro alwala don tai sallah,
Falon gidan ta dawo can wani dan angul ta tsaya don,tai sallah, saboda yau gidan yai mata girma,
A gurin da take zaune ne taji sallaman shi yadawo,
Tun daga kofa Abubakar ya gane cewa gidan yasha gyara yau,
Kamshi biyu ne suka daki hanncin shi, a lokaci guda, gana air fresh ga na girki,
Ganin tana sallah yasa shi shigewa dakin shi direct,
Tsowon lokaci ya dauka da shigan shi dakin nashi,
Don ganin irin yadda dan lokaci guda dakin shi ya sauya kama, dakin ya bi da kallo ko ina tsab,
Ko bai tambaya ba yasan cewa meena ce tai wanan aikin haka,
Ita ko Meena tana zaune tana karatun Alkur,ani maigirma izu, biyu,
Jin muryan shi tayi kamar daga sama yana cewa ina, ina abincin da za,a kai asibintin, ?
Da sauri Meena ta dago daga duken da take tana karatu, don ta bashi ansa,
Voil ce a jikin shi mai ruwan madara, ya,na ta kyalli,
Mamakin wanan irin kwalliyan da ya sauya takeyi,
Don dai ita, tun zuwan su gidan shi, bata ga yana sa manyan kaya irin haka ba,
Kan ta, ta marya kasa da sauri cike da kunya da ladibi,
Sai kuma nauyin da ta dan jin don wani daure fuska da yayi da yaga irin kallon da taimai,
Don shi azaton shi yarinyar miskilace ta karshe ,
Mikewa ta yi inda kai tsaye ta wuce gurin da basket din abincin yake,
Cikin mamaki yake kallon irin yadda yar yarinya kamar meena ta iya wanan aikin haka, ?
Unlike matar shi Sadiya wace ko wankin toilet aikine a gurin ta balle daki,
Ya dauka har ya kai kofa ba tare da ya juyo ba yake cewa i hope baki sa masu plates da yawa ba don akwai na dazun a can,
Kan ta dake kasa ta girgiza alamar a,a tare da dn cewa a,a a asanyaye,
Daga haka yabar falo ya na dauke da basket din abincin,
Inda dama Meena a matse take don gani take duk a takure take dan tsayin da yayi a gaban ta,
***** ****** *****
Shiga na gani na fada, tayi cikin wasu tsaddadun material masu daukan ido,
Dinkin dogon riga ne sai shara, sharan hannun da akai, ma,su,, sai kuma saukan da rigan yi har kasa,
Ga jakar su, da takalman shigen kalar kayan, da ta sa, sai kayan su kai mata wani irin kyau, ajikin ta,
Ita da kawarta aminiyar ta watau lubuna, suke tafe don zuwa duba mara lafiyan,
Kayan fruits ne,suka tsaya a hanya suka siya don kaiwa mara lafiyan,
Basu wani sha, wuya ba sosai gurin gane dakin da Sadiyan take kwance aciki,
Saboda tambayan noban dakin da ta,ke kwance aciki,
Gaba daya yan mata suna cikin dakin sun barbaje sai kwasan girkin da kaunar su ta tsaya gida ta girko ma su,su keyi abin su da kuma shan "ya"yan fruits , wanda yayan su, ya siyo wa mara lafiya,
Tun kafin su shigo dakin kamshin turaren su ya sanarwa duk wanda ke a cikin dakin a lokacin zuwan su gurin,
Gaba daya hankalin na cikin dakin ya koma gurin masu shigowan dakin a lokacin,
Saboda kamshi da kuma sautin, takon takalman su,,
Da sallama suka shigo dakin a lokacin, Sadiya wace ke kwance tana facing din kofan dakin,
Mata ne yan gayu, su biyu da ganin su gogagun Abuja ne basai an fada maka ba,
Sun yi wankan mai sunyi wani irin fari wanda har ya fara canza masu kalar fatan jikin su,
Aisha ce tafa yi masu sannun da zuwa inda murja tafara mikewa saman kujeran da take zaune akai, ta basu,
Samira ce saman dayan kujeran, don haka ta tsaya wani dan shan kamshi kafin ta tashi sama, ta mika masu,,,
Fuskan su gurin Sadiya wace ke kwance saman gado wani kimdin da ita kanta wanda ba kitso ba kuma gyara yai wani chushewa guri guda,
Ya ya jiki ?
Inji Salawatu wace ke wani kallon mutane uku saura,
Da sauki inji Sadiya inda ta juya kan,ta don bazata jure irin kallon da suke mata ba na kurullah,
Dakin yai wani tsit a lokacin kamar ba kowa acikin shi,
Ko wacen su da abinda take, sakawa a zuciyar ta don zaman kallon kallon akeyi,
Yaya Abubakar nr ya shigo dakin a lokacin shima sai kamshi ke tashi a jikin shi,
Hannun shi dauke da ledan maganin da ganin shi kasan daga gurin sayo magani yake,
Abin mamaki sai ga yaya Abubakar yana yar murmusawa don ganin wa yan nan matan, da yayi,
Cikin mamaki sisters din nashi suke mai wani irin satan kallo,
Muryan shi sukaji yana cewa sannu ku da zuwa ashe har kun kara so, ne, ?
Da hausan su na yan Abuja suke cewa eh amma dai bamu wani dade da zuwa ba ai,
Ashe yan hutu basu samu tafiya ba ?
Eh ciwon madam ne,ya hana su tafiya wallahi,amma yan,zu ta samu sauki zuwa wanan lokacin, sosai,
Allah ya sauwaka suka ce tare da kokarin mikewa inda Lubuna take kokarin tura ledan da suka shigo dashi a gaban su,
Salawatu wace tasa hannu a cikin jakarta ta debo kudi yan dubu guda guda,,
Samira wace ke kusa da ita tsaye tun bayan mika mata kujeran da tayi ta miko ma kudin,
Karba tayi cikin rashin wani nuna zumudi kamar yadda Salawatu ke tsan manin zasu nuna kwadayin kudi a fili,
Tacewa Samira ga wanan ku kara a tsaraba ko ?
Murja ne ta ansa da cewa mun gode ,
Cikin wani kashe murya daidai lokacin da suke mikewa tsaye
Salawatu ta ce, Sir zamu koma ke nan Allah ya sauwaka,
Abubakar ya gyara tsayuwan shi da cewa barin sauke ku mana,
Koda mota ku,kazo abinda yasa har su sisters din nashi suka dago kai don su kara kallon matan,
No Sir motar tana wurin service wallahi kuma munga idan mun tsaya dare zai yi ,
Amma ka barshi kawai zamu dauki drop ai ba wani matsala,
No mu je kawai na sauke ku sai in dawo in kai, wa yan nan gida su ma,
Ba wani musu suka mike suna mai cewa Allah kara sauki,
Su kuma wasu daga cikin yan matan suna cewa mun gode Allah kai lafiya,
Da haka suka bar dakin cikin karairaiyan kwankwaso da kafadan su,
***** ******* *****
Leda ne rike a hannun shi babu komai a ciki sai kayan cefane irin su alaifo, tumatir, albasa, da tatasai,
Daidai lokacin da zai shiga cikin kofan shiga babban gidan nasu
A,daidai wanan lokacin mama Ladi ta ke kokarin fitowa cikin wani katon hijab, baki,
Kamar kada ta gaida shi da dawo wa amma sai ta dake tace,
"Illah ho,,
Ingwaiyyah,inji baba samaila, ya ansa mata gaisuwan da ta ansa mai,
Fuskan shi a daure kamarkullun idan sun hadu don haduwar su bai faye dadi ba,,
Yadan zarta ta kadan da niyyan shiga ciki sai yaji muryan mama Ladi tana cewa,
Shin yaushe yaran nan da kuka tura can gurin yaron nan zasu dawo ne wai,
Kaga gaskiya an takurawa wanan yaron da yawa don dai ace rai har biyar a lokaci guda,
Ai sai su ja mashi matsala, ga matar shi ko ga inda yake samu,
Inba hali irin na son kai ba da ganin iyaka wanan ai son ganin karshen mutum ne kawai ,
Cikin wani tsawa Baba Samaila yace mata ke dakata Ladi,
Wawiyar banza mala hankali da tunane, ke in har kina da kunya har zaki iya tarona ki ce wai bamu da hankali mun tura wa Dan ko yara,
Baki ta rike cikin shirin bada ansa sai muryan mijin ta baba buhari ta ji daga bayan ta,
Yana cewa ke kan Ladi tir da halinki mara hankali da wayo ,
Shin wai Ladi yau in tambaye ki Dan ga ke kadai adda shi ko kuwa,?,,,
Muryan ta na rawa tace don dai, na tambaya shine zakuyi min taron dangi,
Hakan ya jawo hankalin wasu daga cikin mutanen gidan,
Ganin an fara taruwa masu yasa ta wucewa inda ta nufa simi simi, da
Da wanan bacin ran Baba Samaila ya karasa shiga ashen shi cikin fada da mamakinnirin wanan karfin hali na mama Ladi,
Mama Saratu ce tai kokarin kwanatar mai da hankali da cewa
Malam ai wanan zancen bada kai ta ke yi ba don ba kai ka tura su zuwa inda yake ba,
Da malam take son tai jayayya kawai shi da ya tura su zuwa can,
Huci yayi tare da yin kwaffa mai karfi yace ai kyale ta kawai
Bari kawai yace ladi zata gane kuren ta,
Don duniya ka shirin bashe ta,
***** ****** *****
Zaune suke adakin su sunyi dadaya sai iran mamaki sukeyi irin yadda suka gani a gurin yayan nasu yau a asibiti,
Gulma yakai gulma don har gwada yadda kowa daga cikin su yayi sukeyi suna ta kwasan dariya,
Inda kuma suka juya suna sifanta irin yadda Salawatu take yi da taga Abubakar,
Muryan shine su,kaji a falo yana kiran samira acikin natsuwa, yake magana,
Abinci yake da bukatan ta hado mai don bai iya cin abinci a asibiti, shi,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
1⃣5⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH AL-QUDDUS,,,,
KAUNA TA A GAREKU DAGA ALLAH NE,,,,,,,,,
BABY ISAH
SAFIYA HUGUMA
FIDDAUSI SODANG
BABY, DEEN
MAMAN FARIDA
NAFISA HARZAMI
Ya kai wani lokaci zaune a falon batare da sanin su ba,
Duk zancen da sukeyi a lokacin yayan nasu Abubakar yana sauraron ,su,
Bawani zance bane sai zancen wa yan nan bakin matan da suka kawo wa sadiya ziyaran dubiya a asibiti dazun da yamma,
A daidai lokacin da yake shirin magana ne yaji muryan da tun fara zancen bata ce komai ba tana cewa,
To ke anty Samira may ye abin kushewa a wanan zancen ?
Ina dai wa yan nan matan da kike zance akai da sanin yayan mu sukazo, gurin ko
Kuma ai yayan mu idan kin kula yai farin cikin zuwan nasu,
Don haka kama yayi mu ma muyi farin ciki ga duk wani abinda da dan uwan mu ke son don taya shi, jin dadin abin,
Amma ni sai banga wani abin kushewa ba sam ga re su, tunda don dan uwan mu suka zo gurin,
Bafa ke ce zaki zauna mai da su ba shike ra,ayin abin shi don haka namu addu,a kawai idan da alheri a ciki, Allah ya,,,,,,
Da sauri Aisha ta dakawa Meena tsawa tace Alheri a cikin may fa ?
Amma ko dai ke Meena ke bani mamaki kwarai da gaske,
Wa yan,ga yan barikin zakiwa yaya Abubakar kwadayin su,
Kallon mamaki Meena taiwa yar uwar nata kamar za tai magana sai kuma
Mike don kokarin barin dakin don zuwa bayi, ta watsa ruwa har takai kofa sai ta dan juyo tace
Ai da ku san cewa ba,kwa son su sai ku,ki karban kudin su da su ka baku,
Daga haka tabar dakin zuwa abinda take kokarin yi kai tsaye,
Daga gurin da Abubakar yake zaune yana jiyo hiran yan uwan nashi cikin fahintar ko wacen su,,,
Huci yayi tare da furzar da iskan dake a