Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : Complete Novels
nufi na daban,
Dole ba don yaso ba ya hakkura ya barta taci gaba da yi duty din ta,,
Bayan na kare aikin komai dake gabana sai na shige dakina don in huta,
Ban kai minti biyu da kwantawa ba Anty Amarya tabugo min waya ,
Na dauka da sallama abakina ina mata gaisuwa tare da tambayan ta kan,nena,
Nakuma tambaye ta lafiyan uncle dina tare da na su mummy,
Anty ke ce min kwana biyu banji ta ba tana can gidan hajiya suna jin yarta kamfanta ke ciwo har sai da ta kwanta asibiti,
Na tausayawa tsohuwan tare da yi mata sheri irin na jika da kaka,
Nan Anty take ce min ai Abokin Uncle dina Nasir ya samu matsala da matar shi, don tana ganin kamar har sun rabo
Nai Innalillahi tare da tambayan yaushe ?
Anty Amarya take cewa ai ankwana biyu da yin case din yanzu haka tana gidan su kano,
Yara kuma suna nan an dawo dasu sokoto gidan iyayyen shi,
Allah sarki amma gaskiya banji dadin wanan labarin ba anty
Tace ai kowa ma meenatu don kin san halin mu mata bamu tsaya muyi bincike ko muyi tunanen mafita ga al,amari.
Sai dai kawai mu kama hauka akan dan abinda baikai ya kawo ba,
Waifa wayan mijin ta ne taga photo wata mace a ciki ga kuma kafan wani namiji kwance, sai dai ba a dauki photo namijin full ba half body ne kawai, ya fito,
Shine ta ce duk yadda akayi mijin tane a kwance ba kowa bane wai Nasir ne,,
A take zuviyan ta ya hau ya na shigowa take tambayar shi ko wacece a picture yace mata ina ruwan ta da tambaya,
Kinji abinda ya hada su fada ke nan Meenat, niko anty amma dai mata Uncle Nasir tai sakaci sosai wallahi ,
Mumata idan abu yazo sai bamu kwantar da hankali mu yi nazari sai kawai muce zamu yanke danyen hukunci,
Yanzu Anty musalima ace full picture din shi ta gane ai sai tayi kokari na farko ta rufa mai asiri,
Na biyu ta zauna tayi nazari may yakai shi gurin waccan matar da har ya ita tsalake ta,
Kyawo ko dressing ko marking love, da sauran su,
Amma wai sai ki ga mace tana ta hauka kamar ba diyar musulmai ba wace tun tana karama tana jin yadda, akecewa mata hudu Allah ya umarci maza da yi,
Matsala dai da abin tsoro shine baka san ko wace ce za,a kawo maka ba,
Wanan kuma ai sai naga mutun ya dukufa ga rokon Allah kawai don samun mafita,,
Hakane inji Anty Amarya tace ai idan ido ya rufe komai, mace mai kishi tana iyayi,
Yanzu da tai hakkuri ta tsaya tayi na zarin wa yan nan abubuwan da kika lissafa ai da baikaisu ga haka ba,
Ni wallahi Meena da ni ita ce zan fara yiwa Uncle din ki duk wani abinda nasan najan ra,ayin maza ne,
Don yanzu idan kin bibiya ma bata ko kama kafan matar Nasir din ba ita ta cikin photo,
Nace ni yanzu anty bagashi ba kaman kin sani kikace in fita zancen Salawatu ,
Ba sai gashi ba kawai ta tunkare ni jiya, wai zata dake ni kuma again,
Ina kitchen ina aiki sai da mai aikin mu ta ta shiga tsakanin mu da ita ,
Ta dinga surfa min zagi ta uwa ta uba har da dan bawan Allah tsohon mu malam tsoho jiya yasha surfa,
Wanan mata dai anyi yar iskan banza wallahi mace kamar iblishiya haka,
Nace Allah yasa ashe mai gidan da take tunanen ko ya fita bai kai ga wucewa ba yai mantuwa ya dawo, duk abinda takeyi a kan idon shi ne,
Masha Allah inji Anty takara da cewa da kya wallahi ai gwamma da yaji ta da kunnuwan shi,
To yaya akayi nan na kwashe duk yadda akayi na fada mata da cewan da yayi sai ta ta roki malam tsoho gafara sanan zata dawo gidan shi
Kai amma ko dai Abubakar ya burgeni sosai wallahi yana son ya gwada mata cewa yasan darajan iyayyen shi sosai,
Anty ta ce to in dai har haka gaskiya Meenatu aiki ja yasamay ki sosai wallahi,
Don yanzu tunda ba imani ne da ita ba zata ce duk yadda zatayi taga cewa yai maki wulakanci zata yi,
Don haka sai ki kara dagewa gurin addu,oin dakuma sadaka akan duk abinda ta dauko ya koma mata,
Yanzu dai kinga kina da ciki babu zance amfani da kayan mata,
Musaman na cusawa duk da nasan baki yin amfani dana cushe cushe dama,
To amma shi wanan hayakin kanunfari ki dakartar da yin shi don Wallahi idan har mace nada ciki tai hayaki a gaban ta zubewa yakeyi tayi bari,
Don haka kada ki fara kice zakiyi yi shi yanzu babban abinda zakiyi tunda kina a haka shine ki yawaita shan kayan sa ni ima, kawai,
Da kuma dabarun gado sai ki sanyadda zaki kama mijin ko a wanan fannin,
Don zata tafi ta kara jin huduban shedan gurin aminan ta na banza fiye da da,
Don haka wallahi duk mace keda kishiya irin haka ko da tafiya tayi sai kiyi kokari kafin ta dawo kema ki kara naki fannin,
Nace Anty aikuwa na gode wallahi tace maza ki maida kaimi gurin kara jawo mijinki a jikin ki,
Nace insha Allahu Anty zan gyara don a gaskiya banyi dabaran yin haka ban sam,
Tace aiko zaki kirani da kanki kisheda min idan har ta dawo, din,
Tace na fada maki harda kwalliya yana sa namiji kara susucewa don wallahi mazan wanan zamanin sun banbanta da mazan da can
Don mazan yanzu zakiga ko mata biyu gare su idan guda bata da karfin yar uwa sai kiga hankalin su ya koma ga wace keda shi,
Mai kaya tab ga daki da kuma kayan sawa itace tauraruwan gida agare su,,
Nace wallahi anty wanan maganan naki haka yake ba wai ba, don tun ina gida nake ganin haka ga mazajen garin mu,,,
Munyi sallama ba don munso ba saboda Uncle danaji muryan shi ya shigo wurin anty
****** ********** ******
Ido a rufe Salawatu ta isa gidan Lubuna, wace ke kokarin shirin fita gurin aiki,
Da mamaki tabi salawatu wace ta wuce direct saman kujera ta zaune rai a bace ,
Tsaya tayi tana kallon aminiyar nata duk da tasancewa ba lafiya ya fito da ita gida ba da wanan safe haka,
Kuka Salawatu keyi riris kamar karamar yarinya, kamar ranta zaifita,
A hankali Lubuna ta taka zuwa gare ta ta dafa ta cikin tausayawa tace,
Wai may ke faruwa ne haka Salawa ni baki fada min abinda ya faru ba kin barni a duhu haka
Cikin dan tsagaita kuka tace Lubuna Oga ya wulakantani ya cuceni don ya ci min mutunci agaban kowa nagidan
Wani irin takaici Lubuna taji tai tsaye tana ma Salawa wani irin kallo,
Tace gaskiya Salawa ban san irin ki ba wallahi shin Oga Abubakar ne namiji kadai a duniyan nan, ?
Karki manta ko yau ya sake ki zaki samu masoya da yawa to may zai saki dinga wahalas da rayuwan ki akan shi haka wai,
Bafa kwantai kikayi ba Salawa, kece dai da irin nacin ki kika lake masa,
Har yana jin dadin wulakan ta ki yadda ran shi ya so a gaban kowa,
Auren sa fa ba dole bane idan zaki rufawa kan ki asiri ki rabu dashi kirufawa kanki,
Ki gwada mashi cewa kema fa din mace ce mai aji sosai,
Kai ta daga tare da kallon Lubuna tace, ke ma kin san cewa ina son Oga ba zan iya ba sam, don shine kadai zai iya hakkuri dani yadda nake so,
Lubuna ta tsuwa Salawa idanu tana kallon ta acikin takaici,
Can tace saboda wana yarinyan ce again ko yai maki wani abu,
Tace wallahi kanan kin sani fa don tane yai min cin fuska tun a daren jiya yafara,
Don nace masa ina son cin shawarma, nako wani irin piza ne sai ita ma tace wai ya sayo mata Ice cream da fresh Fruit's ,
Bayan yadawo naga bai sayo min ba maimakon nida ce mai ina so ya fara zuwa guri na kuma fa nice da duty a ranan sai kawai ya nufi gurin ta dakin ra ya kai mata nata sakon,
Da naji shiru shine na bishi tundaga can muka fara fada dashi wai don maye bazan jira shi har yazo ba,,
Cikin takaici Lubuna tace you see akan karamar yarinya kina ganin wulakanci, haka,
Yanzu dai tunda har ya kai ga haka ai sai ki kara zage damtsen ki,
Don dama matan hausawa dinan kina ganin su haka wallahi is not easy kafi karfin su ,
Mistake dina shine da ban bari sai jima da fitaba sai kawai na samay ta kitchen daniyar inci mata mutunci sosai ashe yana gida bai fita ba,
Yaji irin yadda na dinga zagin iyayyen su da kakan su wanda ya bashi auren yar iskan yarinyar,
Yanzu dai dakata kiji inji Lubuna wace ke kokarin kawai, zaune gefen hannun kujeran da take a zaune,
Tace yanzu fa dole ne sai mun mike tsaye so that we should rideout that foolish girl away,
Salawatu ta ce hmm kin dai sai koda yaushe ko nawa nake kashewa akan irin hakan amma abin yaki,
Murmushi Lubuna tati tace Salawatu ke nan ai yanzu tunda har kina son shi haka dole ne sai mun dage sosai don mu kwata maki shi,
So kada ki damu ki dan bani time kadan please akwai inda zan tafi maki,
Sai dai yanzu dole ne mu samu mu dan lalabashi ki koma dakin ki,
Salawatace bakiji may yace bane cewa fa yayi sai natafi har garin su naba wanan witch din tsohon hakkuri,
Da wani irin karfi Lubuna tace WHAT ?
May yake nufi da hakan impossible, hakan ma ba zai yuyuba gaskiya,,
Tace dole ne mu samu mutane anan wa yanda yake tare da su , subashi hakkuri gaskiya amma idan yace wai sai kin tafi can ai bai kyauta muna ba,
Kuma wallahi yan uwan shi zasuyi hating naki ne sosai har ma yaran ki idan kin aihu dashi,
Wani irin ajiyan zuciya ne Salawatu tayi tare da ce o,o wallahi Lubuna nayi hating din wanan yariyan sosai ,,,
****** ********* ******
Tun lokacin da wanan abin yafaru yaya Abubakar yake jin wani irin zafin Salawatu a ran shi har yake ji gara kawai ya sallamay ta tafita daga rayuwan shi don shi gaskiya bazai iya zama da macen da ke zagin iyayyen shi ba haka,
Yayi nadama sosai ga hanashi da malam tsoho yayi amma ya dage akan sai yayi,
Yanzu gashi baida kwanciyan hankali ko kadan da ga gare ta, duk ta hana gidan shi shakat,
Yasan cewa babu wanda zai tunkara da wanan zancen , dole ya daukan wakanshi mataki akan fitinar ta,
Driving yakeyi amma hankalin shi tankar baya a jikin shi a lokacin,
Wayan shi tai kara sai dai bakuwar noba ce ya gani don haka ya dauka da sallama,
Saidai murya mace ce yaji bayan sun gaisa tafara bashi hakkuri a kan case din su da Salawatu,
Dif ya katse layin tare da sake guntun tsuki, yana cewa a fili rubbish ,
Yashigo gida a gajiye ya nayin tafiyan shi mutum zai gani ya fahinci hakan,
Muna zaune gaba dayan mu a falo muna kallon wani season film na hausa,
Jin shigowan shi yasa gaba dayan mu muka,waiga don ganin mai shigowa,
A irin yadda ya samay mu zaune a falon har Ramatu mai aiki yasa shi jin dadi,
Duk da dai ba wai fira mukeyi ba amma yanayin zaman mu ya nuna kwanciyan hankali,
Mikewa nayi daga inda nake zaune, don zuwa gurin shi in karbi case din shi,
Ya zuba min ido daga inda yake a tsaye har lokacin da na iso gare shi,
Sannu da zuwa nai masa tare da dan rusunnawa kadan,
Murmushi yasaki tare da sauke a jiyan zuciya yace Ya gida Meenatu,
Alhamdullahi,
Daga gurin da Anty Sadiya take a zaune ta mashi sannu da zuwa,
A daya daga cikin kujerun falon ya zauna yana mai cewa wassh Allah na duk na gaji wallahi,
Ina saukowa da part din shi nahango shi zaune afalo tare dasu Anty don haka na shiga kitchen, na dauko mashi ruwa, a gora tare da dora cup a ture din,
Ina tafe cikin bakar jallabiya mai fitar da sharp, din mace
Zakace ko wata yar larabawa ce, rigan yasa ina tafiya kamar da gaiyya nake rausaya ,
A gaban shi na aje ruwa a saman stol din dake gefen shi,
Zan dauki ruwan da nufin in tsiyaya mashi a cup yace No barshi kawai kawo goran,
Nayi saurin dago kaina na kalle shi da mamaki nace abar cup din kuma,
Ya daga min kai kawai alamar eh,
Daga haka ya dauka ya kafa goran a bakinshi bai cire ba saida ya kwankwade, shi gaba daya san nan ya aje goran a saman tire din yace min ya gode tare da dan lumshe idon shi ya koma saman kujeran ya zauna,,
Nadauki turen da cup na mayar kitchen na wurga gora a dustbin,
Ramatu tamike a hankali don tabar falon saboda ganin yaya Abubakar azaune,
Yace No dawo kawai ki zauna abinki zau hau samane ni,
Daga gurin da Sadiya take a zaune take cewa, maganin ta na sha ya kusa karewa fa,
Yace ok zan tura Baba Wadda da Hamza gobe insha Allahu su karbo maki,
Daga haka ya mike zuwa sama yana mai rike karfen da akai matagalin steps din dashi,
Bayan shi nabi inda muka hau steps din a tare dashi don a tare muka shiga dakin,
Daga gurin da Anty Sadiya take tabimu da kallon tare da sauke ido da sauri tana mai tabe baki,
Ramatu na gani haka tai saurin kawar da kanta daga kallon ta ta ci gaba da kallon tv abinta,
Amma can kasan zuciyar ta mamaki takeyi na yadda nake ma Anty halarci amma akwai burboshin kishina a zuciyar ta,
Muna shiga daki na riko Yaya Abubakar tabayan shi na rungumo shi, tare da sauke ajiyan zuciya,
Naji ya sauke ajiyan zuciya again akarona barkatai kenan tun shigowar shi,,
Hankali cikin wani irin murya nace, Yaya Abubakar ka yi hakkuri damu please kasan mata sai hakkuri,
Yaya yadan yi wani jim kamar yana tunane, sai naji ya juyo dani ta yadda zamu fuskanci juna, da shi,
Kai minkiss yayi a goshi yana cewa Meenatu bana son fitina arayuwa na sam wallahi,
Nakara dan narkar da murya na nace yaya kayi hakkuri don Allah ka yafe muna please,
Yasa dan ya tsanshi a saman lebbana ya ce Shiiii alaman inyi shiru kawai,
Yace gaba dayan ku nasan halaiyan kowan ku don haka nasan abinda nakeyi,
Ina judge din kowa akan laifin shine, bazan yarda da yawan fitina ba agida na, sam,
Azuciya na ce ashe zancen Anty Amarya gaskiya da tace koda namiji baya gida ya kan fahinci halaiya iyalin sa daya bayan daya,
A hankali na ke kokarin zamay jikina daga rikon da yai min ina cewa barin hada maka ruwan wanka ,
Ya ce no ki barshi idan natashi zan hada da kaina,
Ya shiga shinshinan wuyana har zuwa wasu part na jikina yayin da na lumshe idon cikin wani irin tsiga, yarrrr da na ji,
Kokarin juyawa na keyi don barin dakin, naji ya riko min hannuwa ,
Najuyo muka hada ido naga idanuwan shi sun kade sunyi jawur,
Nai saurin kauda idona daga gareshi sai naji yana rada min a hankali haba, Meenat,
Ya kuma zaki wuce ki barni bayan nasan cewa kinzo ki ga farin ciki na,
Na dan sunkayar da kaina kasa cikin jin nauyin shi nace bazan tafi bane girkine sa ban sauke ba nake son zuwa na sauke kada ya kone,
Na san ba dai ya yarda bane, just kawai yabarni ne in fita kawai,
****** ********** ******
Salawatu da Lubuna agaban malamin su a zaune,
Lubuna ce bayan sun gaisa da malamin nata take cewa,
Boka ko malam mun zone gurin ka dama wanan kawar tawace ke da dan matsala da mijin ta shine nace muzo gurin ka, da ita ka duba mata,
Don Allah ina son ka taimaka muna ai mata aiki mai zafi wanda zai girgiza abokiyar zamab nata.
Boka ko malam yai murmushi yana mai gyara zaman shi tare da duban shi yana cewa,
Yanzu may kike so ai mata a rabata da gidan ko a haukatata ko a barta a dambalata kawai,
Salawtu tace ai matsalan shine, zuri,an su guda mana,ana gidan su guda don iyayyen su gudane,
Amma in akwai yadda zaa ayi na mallakeshi ni kadai zan so hakan gaskiya duk su sauran biyu ayi waje da su,
Murmushi Boka ko malam yayi yana cewa wanan ai ba wani babban aiki bane,
Nan yashiga yin irin abinsu na bokaye sai da yadauki dan lokaci mai tsawo zuwa can ya dan dago kai ya