Advertisements
Chapter 46 Reading TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  Complete Novels

Chapter   46 / 61

135K to 138K   out of 180.5K words

na yi tare da kokarin mikewa don zuwa, yin abinda aka umurceni da yi,
Kitchen din nafara shiga na har,hada kayan yaji na zuba a wani roba na fara wanke wa san nan na zuba a cikin pot tare da dauko Lipton guda biyu na kada acikin ruwan,
Sosai na barshi yai ta dafuwa a saman wuta, don yayi masa dandano yadda yake so,,
Bayan na gama hada komai a flask na dauka zuwa falo dashi,
Sai dai babu kowa a falon abin yabani mamaki don da wuya irin wanan lokacin a samu Sallawatu bata falon,
Amma sai gashi yau bata falon hakan ya bani mamaki matuka,
Juyawa nayi da flask din na mayar kitchen na samu guri na boye ,
Dakina na koma na gabatar da Sallah sai kuma na dan kara gyara guri,
Yan mintoci da dama aka dauka kowa bai fito ba nan na gane a kwai matsala a gidan,
Anty Sadiya ce ta fara fitowa tana saye da rigan barcin ta fari na cotton, har kasa yake rigan,
Bata jima ba Sallawatu tafito itama cikin wasu kaya kaman na yan ghana, ita agañin ta wayewa ne,
Sai da na tabbatar da cewa nagama komai adakina nafito, wajen,
Kitchen nafara zuwa nadauko mashi dan wani flask karami baki da yake amfani da shi,
Tafe nake amma zaka ce ai rangwada na keyi a lokacin, don irin tafiyan nawa,
Cikin dogayen rigunan da Anty Amarya ta sayo min na saka guda,
Rigar irin in kana tafiya sai ya kama shocking yana wani dan fidda walkiya a jikin yadin,
Da yake darene sai ya kara ma rigan kyau da daukan ido,
Tun da na tunkaro hannu na yana dauke da flask din da cup duk hankalin su na a kaina,,
Nakarasa takowa a hankali gaban shi na durkusa tare da aje flask din ruwan a gaban shi,
Sai a lokacin ya dago kai yana cewa Ok har ya dafu ko ?
Na ansa da fadar eh yaya,
Kanshi yana duke ga system din shi yake cewa ki dauko min zuma a saman drawer a dakina please,
Ban dauka cewa dani yake ba don haka sai na samu gurin ina kokarin zama, a gefe,
Ya dan dago kanshi daga abinda yake yi yace bakiji bane wai ?
Sai na dan daburce nadan kalli Sallawatu wace ke da girki a ranan,
Yadda naga ta daure fuskanta tamau, ta wani hade rai, yasani mikewa,
Sai naji muryan shi yana cewa ki hado min da spoon please, na ce toh na juya zuwa inda ya aike ni,
Sallawatu wace ke kallon mu rai a bace tadan cije leben ta, tare da yin kwaffa,
Ban karasa hawa sama ba najiyo muryan ta tana cewa
Aiko baka nuna a fili ba kowa ya,san cewa, akan Meenatu zaka iya komai agidan nan ,
Yace au har kin manta da kince saboda tana yar uwana nake nuna mata hakan,
To ina son in gwada maki cewa,
Yar uwatace din ta kwarai don guri biyu take gare ni zuwa uku,
Kinga na farko yar uwar haihuwana ce,
Na biyu mata,ta,ce ta sunna,
Na uku yaruwata ce ga musulunci don haka babu ta inda ban hada da ita ba,
Don haka kalamin nan naki da kikafada shinake son gwada maki cewa, Meenatun zan iya sata zan iya hanata aduk sanda naso,
Tai wani har da ido tace ai sai ta haifa maka yara, mu gani ka cika gida dasu kuna cewa yan uwa kuke,
Sadiya wace tun fara zancen take sauraren su cikin bacin rai tace amma wanan abin naku bai kawo kallo ba, gaskiya
Tana kokarin mikewa tsaye take fadan haka gare su,
Ya nuna Sallawatu da yatsa adaidai lokacin da karaso dauke da kwalban zuma a hannuna yake cewa,
Wanan macuciyar mata ce so take ta cuce inzalumci rayuwana in kone,
Bazaki bani dokaba agidana don nina ajeki bakece kika ajeni ba,
Kuma kin san ai ina da mata ki ka aure ni hakana da su,
So sai ko kiyi hakkuri ki zauna kamar yadda kowa cen ku ke hakuri da dan uwa,
Nikan ina aje kwallba na juya na nufi part dina cikin bacin rai ,
Muryan Sallawatu naji tana cewa, ashe dama kai haka kake ban sani ba,
Ya Abubakar yace o da kinga yaro kin zo ki min wayyo ko,
Look Sallawa the door is open,
Yo can go and live us pls,
Bazan taba bari ki cutamin aka rayuwana ba in kwashi dukiyar mutane in dinga narka maki any how,

Dakina fada ina mai kiran innalillahi,wa,inna alai,him,raj,um,
May ke faruwa haka tsakanin yaya da matar shi gaskiya abin baiyi kyau ba,
Har zan rufe kofa sai na tuna da ban dauko goran ruwa sha ba,
Don haka nafito don in dauka naji yaya yana cewa , I can't stay, with you, being my wife like dis,
Abuse me like a ashawo woman in front of my family,
Jikina yana rawa da gurin da nake na hango idon shi sun kada sunyi jajir a lokacin,
Narasa may yai zafi har ya kawo wanan fadan tsakanin wa yan nan ma,auratan, haka ?
Da sauri na karasa ina cewa Yaya kayiwa Allah kadaina wanan halin ba alheri bane please na karasa kamar zanyi kuka,
Juyawa yayi ya dan kalle ni da rinanun Idanun shi da suka kada sukayi masa ja,,,,
Ko may ya tuna sai naga ya dauki system din da flask din ruwan da na kawo mashi ya haye sama,
Gurin Sallawatu na juya wace ke cike da masifa saidai kuma fuskan ta ya manne da nadama, sosai don irin yadda tabi bayan shi da kallo da yake hawa sama,
Na juya gurin tare da mata wani irin kallo nace haba haba please hakan bai yi kyau ba gaskiya,
Bai kamata ace kuna haka ba wanan ba alheri bane gaskiya hakan ba zai kawo alheri ba gaskiya,
A cikin mamaki kamar ba sallawatu ba naji tana cewa Meenatu,
Babu abinda zaki fada min tunda harda ke gurin son kuga bayana agidan nan,
Murmushi mai daci na hade ina cewa badamu tunda kinsan da haka amma yanzu sai kiyi hakkuri saboda dare muryan ki zai iya kaiwa ko ina,
Amma shawaran da zanbaki shine ke mace ce kiyi kokari ko sasanta da miji ki ina ga zaifi daga haka najuya abina wuce,

****** ********** ******
Washe gari tunda safe Sallawatu ce ta buga min kofa,
Ina bude kofa nagan ta tsaye cikin wani dan yalalon hijjab dagage tun a kofa tace min ina kwana Meenatu,
Hanya na kauce mata don na fahinci tana son shigowa dakin nawa,
Tana raraaba ido ko ina adakin tana kallon yadda dakin nawa yake da tsari da tsabta,
Bakin gado ta zauna yanayin idon ta y nuna cewa tayi kuka sosai da dare,
Itace ta katse shirun da cewa Meenatu nazo ne in maki godiya akan abinda ya faru daren jiya,
Nagode kwarai don kin bani shawaran da babu wanda yabani shi,
Sai kuma don Allah ina mai baki hakkuri ga yadda nasa ki a cikin rikinci mu bakiji ba baki gani ba,
Sai gashi kuma duk da ina maki kallon yarinya kinbani shawaran da yai min dadi,
Don Allah kuma ina rokon ki da kikara ba yayan ki hakkuri akan abinda ya faru please,
Nace a,a gaskiya tunda har kun sasanta a tsakanin ku komai ya wuce don Allah sai kuyi ta hakkuri please,
Tace sherin shedan ne kawai don ba wani babban magana bane haka dai Allah ya kawo
Na tare ta da cewa Allah ya kyauta ya tsare muna gaba don Allah muyi ta hakkuri da junan mu,
Tamike tana cewa nagode nagode Meenatu,

Tana fita nabi bayanta da kallo ina tuna maganan Anty Amarya da take cewa irin su Sallawatu baka gane kan su,
Sai ka natsu sosai don yan duniya ne na karhe,
Lalai Anty Amarya ta fadi gaskiya don dubi yadda wai yau Sallawatu ce kamar da gaske tazo min daki,,
Daren jiyane fa take ta zumduma min zagi harda gorin haihuwa,
Amma yau wai itace tazo take min dadin baki, kamar wata ta kawarai Allah ya sauka
Na kara da cewa Allah yai min katangar tsari ga duk wani sheri na ta,
Na nade sallaya na dama tasamay ni zaune ne ina karanta Hasbunallahu wani,iman wakeel kafa dari hudu da hamsi
Gyaran safe nai ma dakina na koma na kwanta batare da nafito waje gyara ba,
Barci nakara komawa batare da nasani ba har zuwa lokacin da Yaya Abubakar ya shigo dakin nawa,
Yau shigan kanan kaya yayi wanda ya kara fito maahi da kurciyan shi a fili,
Suman kanshi daya dan taru ya kwanta mai a kai bakikirin, yai lub
Hannu shi ya na saye da wani agogon White, silver, sai kafan shi da ya sa wasu takalmi buth na maza masu tsada,
Barci kikeyi ne Meenat ?
Ya tambaya alokacin da yake kokarin juyawa daniyar fita daga dakin nawa ?
A hankali na bude ido,na na kuma sauke su ga fadadar bayan ya Abubakar dake niyar juyawa,
Murya na ya tsinkayo ina cewa Yaya ina kwana,?
Juyowa yayi yana cewa kin tashi ne ? kwanta abinki ni zan fita ne,
Nace Allah, ya tsare hanya,,
Har zai fita na mike zaune daga kwance da nake,
Yaya ya zance ya Awal ne ?
Cikin mamaki yake kallo na yana cewa Awalu ?
Nace eh Yaya bai fada maka cewa matar shi ta haihu bane,
Cikin daure fuska yace ya fada min mana nai mashi barka,
Na kara gyarawa nace amma Yaya ai ya kamata ka bada gudun mawan ka,
Hannu ya daga min yana cewa look Meenat may kuma kike son in mashi, bayan barkan ?
Cikin dan tsuke fuska nace amma dai Yaya kasan fa haihuwa wani abune na farin cikin rayuwa da tarihi irin wanda mutum bazai taba mantawa ba,
Cikin dan hasala yace Meenat may kike son in mashi, ?
Kaina na dukar kasa bance komai ba sai dai na hade fuskana abinda ban taba mashi ba,
Sai ka dawo na fadi a hankali tare da kokarin juyawa ina lalaban filo na, da niyar kara kwantawa,,,
Bai juyo ba yasa kai yafita abinshi
Sam ban ji dadi yadda Yaya ya yi ba akan zancen haihuwan matar dan uwan mu,
Yin ranan a haka nayi a cikin bacin rai don gaskiya idan Yaya Abubakar zaici gaba da yi wa yan uwan mu irin wanan halin gaskiya ba,za,a samu cigaba da zumunci maidaurewa ba,
Don dai Babba shike hasa kan gida sanan na baya suji dadin biyo shi,

Kamar yadda na saba taya Anty Sadiya aiki yau ma banki yi ba don a tare mukayi abinda duk ya dace, sai dai jikina ba walwala a,tare dani,
Muna gama duk wanin abinda zamuyi sai da na tabbatar da cewa nayi,
Don haka na,shige daki abina na dan yi abubuwan da ya dace in yi,
Fattu na kira, muka gaisai mu kayi yaya kwana biyu, ?
Mun kai wani lokaci muna dan tataunawa akan zance Humaira,
Bayan kashe waya, ne ban kai ga ajewa ba sai na tuna cewa nace zan kira Yaya Awalu yau din,
Kira daya nabiyu na uku yadauka ya na cewa Meenatu yaya kuke ya Abuja,,
Nai dan murmushi na ce Yaya Awalu ya ruwan zafi ?
Kai haba Meenatu masu ruwan zafi suna gidan su inda suke,
Na ce a cikin mamaki, yaya gida ta haihune yace ,
Wallahi Meenatu daga asibiti suka wuce, da ita gidan su kinga yaya za,a yi, ba dole mu bar su ba,
Nace to Allah shi kyauta ya ce Ameen yanzu kinga ga suna sai kara matsuwa yake yi,
Gashi gwaunati batai albashi ba don banzaci haihuwan a yanzu ba,
Sai kawai kwatsan gashi yazo muna a bazata,
Nace akwai Allah yaya Allah zai rufa asiri insha Allah,,
Ya Awal ya amsa da cewa ameen Meenatu nace zakaji mu insha Allah kafin sunan yaya abin ne bai yi ready ba,
Mukayi sallama da Yayan nawa na kashe waya zancen shi suna damuna a rai na,
Daga daki ina jin karan TV da alaman yaya na kallon network News,,
Ban fita ba don tun gama girki mu naci shi a kitchen tsaye,
Duk zaman falon sai yaji ya ishe shi don rashin ganin na fito waje,
Sai dai yai kokarin danne damuwar tashi don gudun zargi daga sauran matan shi,
Sai dai bai san cewa Sallawatu duk ta fahinci halin da yake ciki ba,
Cikin dakewa yake cewa Sadiya Meenatu lafiya take bata fito ba,
Ina ga gajiyane kawai don tun da muka gama girki,tashige bata kara fitowa ba,
Ok kawai yace tare da ci gaba da abinda yakeyi a system din,
Barci, ne ya dauke ni sosai, don daga kallon sunna tv barci ya daukeni ban sani ba,
Kamar a mafarki naji maganan shi yana cewa barci baki kashe electronic, ba?
Nadan mike firgigit nace cikin idon barci zan kashe yanzu ai,
Tashi ki kashe ki rufe kofa, kafin barcin ya dauke ki,
Ban kara furta komai ba sai sai dan tashin da nayi don inyi abinda ya umurce ni dayi,
Maya hanaki fitowa falo yau,?
Dan marairai cewa nayi nace kawai dai banjin dadi ne sai na dan kwanta,
Batare da ya waiwayeni ba yace zancen Awalu kikewa fushi ko ?
Cikin wata irin murya kasa kasa nace ni ba fushi nakeyi ba ,
Akan may zanyi fushi tunda kaima ai dan uwanka ne,
Aini zan tura masu da abindake gate ni gobe insha Allah,
Kallon mamaki yai min yace ashe kudi gare ki haka?
Nace a,a kudin da kaba ni, in tafi,sallon ne mai sallon din ta raga nna ne zan hada da wanda ke gurina in aika mashi,
Hmm kawai ya iya ce min daga haka ya juya fita yana ce min sai da safe,
Yau ma kamar jiya na tashi fuskana a daure nafito daga wanka ina shafa mai ya shigo dakin cikin shirin tafiya office yau ya kasance juma,at,
Don hakani shaddane mai kalan milki sai shining yakeyi, da kyalli,
Ina kwana na,ce fuska ba yabo ba fallasa a cikin sa,
Ina kwana nai masa adan sake batare da na kalle shi ba ina shafa mai a cinyoyi na,
Ya saki ajiyan zuciya yana dubana cikin wani irin yanayi maradadi,
Yace ni zan fita babane za,a ba kudin ko Awalun ?
Nace cikin da murya karami da cewa karaba masu dai Yaya tunda kowa nada abin dai yi daga cikin su,
Ok zan turo maki Hamza ko Abdullahi sai ki mashi bayani yaje ya tura masu,
Ya dan duba agogon hannun sa yace ina ga bari a turawa shi Awalu da hamsin shi kuma baba talatin ko?
Nadan juyo ina duban shi nace dadai kabasu kowa hamsim din don lalura da yawa,
Ya amsa da cewa to shike nan zan ba shi ya tura masu sai kicewa Awalu ya turo da account
Nace cikin nuna farin ciki da Allah ya saka da alheri angode,
Yajuya yayin da nace Allah ya tsare cikin sakin fuska,



ZEEE MAKAWA YELWA

[8/18, 10:26] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
5⃣7⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL- WASIYU,,,,


Fatan Alheri gare ka da Zurian ka, Fatan gamawa da duniya Lafiya, Baba Alhaji Aliyu Harizami, Dan Amar Kano,,,, Gaba dai Gaba dai Baba Aliyu Dan Amar Kano,,,,,,,,


Zaune, Baba Musa yake Yaya Awal ya shigo gidan cikin farin ciki da jin dadi yana cewa,
Baba kaga ikon Allah ko ?
Wallahi, Mai sunan malam na ya aiko muna da alheri,
Masha Allahu, kai madallah aiko mun godema Allah,
Allah abin godiya inji mama matar Baba Musa mahaifiyar su yaya Awal,
Allahu Akbar inji Baba Musa lokacin da ya gama kidaya, kudin
Ya ce ance gari da yawa maye baicin kan shi, Allah ya rufa,muna,wagga asiri,
Wasu kudin yaya, Awal ya mikowa Baba yana cewa ga wanga,
Baba ya ce kuma ? Wai an mari kumama,
Yace Meenatu ta ce asai ma mai jego turmin zani wanga kuma naka na Baba,,,
Masha Allah inji baba ya karbi kudin ya nata sa muna albarka dubu goma ya ce cif,,
Allah kai ma wa yan ga diya albarka, Allah ka azurta, su zuri,a masu albarka,
Yaya Awal da Mama su ka karba da fadin Ameen ya Allah,
Kudin Baba Musa ya kaiwa malam tsoho ya nuna mashi tare da yi mashi bayanin komai,
Murmushi malam tsoho yayi tare da dan kad kanshi yana mai lumshe ido ya ce
Madallah madallah Allah mun gode maka da ka ba mu wannan yaro mai albarka acikin zuri,an mu,
Allah nagode ma da ka bu ikon hada auren wanan yaron da wanan yarinyar, mai albarka da sanin ya kamata,
Wana addu,an na karshe shi yasa Baba Musa saurin dago kai ya dubi malam,
Malam tsoho ya gane

46 / 61