Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : Complete Novels
don in ta da Sallah,
Alokacin ne naji muryan Yaya Abubakar yana cewa may yasa baki jirani mun shiga tare ba,?
Murmushi mai sauti kawai nai masa batare da nai magana ba na tayar da Sallana kawai,
Har zuwa lokacin da na kusa sallamay wa na,ga ya mike zuwa wanka,
Bayan ya gama muna Odan abincin da zamuci daren da muka iso,,,
Bayan na idar da sallah ne na mike tare da dan, gyara muna kayan mu, inda na zuba su cikin,
Wardrobe din da nagani a dakin na nufa na sa kayan mu a ciki,
Sai na fitarwa yaya Abubakar, wasu simply kaya don ya saka ajikin shi idan ya fito,
Rigace mai yar guntun hannu da wando tree quarter, na samu acikin kayan na shi
Suna fitar mai don ya saka idan ya fito daga wanka,na kuma feshe mashi su da turare,
Dago kan da zanyi ashe Yaya ya fito, yana zaune a bakin gado daure da towel, sai wani dan karami, da yake ta gugan sumar kan shi da shi,
Idon shi na akaina duk lokacin,,
Kayan da na fitar mai su ya saka ajikin shi bai wani bata lokaci ba ya ta da sallah,
Nagama gyara jikina tsaba yadda ya kama ta batare da na bari ya gane may nakeyi ba, ba,
Daga gurin da yake zaune yana addu,a yadan waigo yana ce min, ki saka hijjab dinki don ga wani nan zai shigo ya kawo muna abinci,
Bamusu da sauri na saka hijab dina akaina, na koma can bayan gefen gado nadan zauna,
Wani buzu ne ya shigo bakin shi dauke da sallama,
A binci ya kawo muna wanda ke dauke da abinsha mai sanyi,
Abincin ba laifi don tankarka kalan namu na Nigeria,
ZEEE MAKAWA YELWA,,,,
[8/11, 05:43] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
5⃣0⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH- AL-HAFEEZ,,,
Jumma,at Mubarak,,,
Shafin yau na kine ke ka dai kuma bada kowa ba
SADIYA SIDI MARUBCIYAR, SIDIYA,
Nagode da irin kaunar da kike gwada min,,,,,
Bayan mun karasa, cin abinci ni da kaina na gyara gurin na kawar da kayan abincin a can gefe,
Hand bag dina na bude na ciro daya daga cikin Sweet's din da Anty ta sayo min masu kamshi, nasaka ga baki na,
Wayan Yaya Abubakar yai kar da alamar daga cikin abokan tafiyan shine suke waya,
Nikan sai da na kara kakabe gadon sanan nazauna ina gabatar da addu,oina kamar yadda na saba yi,
A hankali na kai kafada na saman katifa saboda gajiya, na dan lumshe idona tankar mai barci,
Tunanen matan Yaya Abubakar ne yazo min a rai yadda akayi baizo da dayan su ba mussanman ma amaryan sa,
Nai zurfi ga tunane ban san cewa Yaya ya gama wayan shiba,
Yana zaune a gefena ya kura min kyawawan idanun shi,
Duk duniya ya fahinci ba macen da zai gani yaji sha,awan ta ya motsa mashi, kamar wanan yarinyar,
Sai yanzu ya gane cewa komai na Meenatu daban yake da na sauran matan shi, kai dan das da shi gwanin sha,awa,
Muryan shi kawai naji gab da kune na yana ce min,
Meenat, nayi rashinki da yawa atare da ni,
Firgigit na bude idona adan tsorace,
Ashe gab yake dani kwance, idon shi sun canza kala zuwa wata irin muguwar sha,awa,
A hankali na dan motsa dan in gyara kwanciya na alokacin,
A hankali, naji hannun shi kuma a jikina yana wasu maganganu da zan iya cewa bai san may yake cewa ba ma,
Wani irin mahaukacin soyayya ya gwada min ranan,
Don duk yadda nake tsan manin cewa, yai amarya bazan samu wani doki ba sai gashi ya ma fi kullun, nuna min, duki,
Don irin yadda Yaya ya gwada min ban san da cewa ana iya yiwa mace shi ba, balle ma shi da nake ganin bai dauki mace a wani matsayi ba,
Sai kusan asuba nasamu Yaya ya sarara min nai barci,
Daga ni har shi sai da muka makara ga sallah asuba ranan,
Sai dai shi ya rigani tashi don haka sai da ya tabbatar da cewa na tashi sanan ya kyale ni,
Sai da na idar da sallah na mike zuwa gaban mirror dake dakin ina gyara jikina,
Zuciya ta fam da tunanen iri, irin, yadda Yaya ya canza min sallon soyayya,
Shin kodai harda shawaran da Anty Amarya taba ni da cewa ni ma in gwada mai nawa, sallon,
Murmushi nayi tare da dan rintse ido na ahankali ina anyana cewa mutum mai mata biyu, zaiyi wanan irin abu haka,
Muryan Yaya Abubakar ne naji daidai satin kunnuwa na yana cewa my queen,
Ya gajiyan hanya da na Yayan ki ?
Murmushi kawai na sake mai tare da cewa sai hamdala, duk ka biyun,
A can cikin kunni na ya rada min a hankali,
Anty ce ta kara gyara,min ke ko Meenat ?
Dif na dakatar da murza turaren da na keyi a jikina tare da dan sake murmushi, kadan,
Mikewa yayi tsaye daga dan rankwafo min dayayi a kafada na,
Jin ya mike a bayana yasani sauke dan ajiyan zuciya tare da dan lumshe ido na,
Azuciya na nace No Wander, nasha wuya jiya hannun Yaya,
Ashe yaji abin da yaji ne ajikin nawa,
Idona na lumshe a hankali ina cewa a raina watau wanan gyaran da su, anty ke tamin da gaske yana da amfani ke nan,
Mikewa nayi na shirya tsab cikin wasu, tsaddadun material dinkin riga, da skirt, a kai masu ya dan matse ni das don mazauna na sun fito tsab daga cikin shi,
Dan kwalin su na daura a kaina sai dan kitson kaina da yadan fito da ribon din kai na, waje kadan daga baya,
Wasu plat shoe's Anty ta sayo min don in hada su da kayan,
Dan karamin gyale na, yafa a kaina , tare da kara shafa kamshi a jikina
Saboda naji har malaman addini na cewa kamshi yana kara kauna tsakanin mata da mijin ta sai dai ban shafawa, a gurin da nasan cewa zai min illa kama saman nono, karkanshin nono da saman gashin kaina, saboda gudun cancer,
Zaune Yaya Abubakar yake a bakin gado ya gama waya da masu kula da abincin mu,
A hankali nake takowa har zuwa inda yake zaune ya tsura min ido, har na karaso gare shi,
Gefen shi dan tsuguna har kara tare da dan dafa gadon da yake zaune akai, nace,
Ina kwana Yaya ?
Murshi yayi tare da dan kamo hannu na namike tsaye zuwa jikin shi ya zaunar dani a saman cinyar shi,
A hankali yace Meenat ki karya ki kwanta ki huta kinji nasan cewa daren jiya ban kyauta maki ba don kina tare da gajiya kuma ban sarara maki ba,,
Murmushi nadan sake ina mai dan dukar da kaina nace,
Yaya nifa matar kace dole ne inyi hidimar ka duk sanda ka bukaci hakan daga gare ni,
Murmushi yayi tare da dan rausaya kan shi azuciyar sa yace lalai meenat ta,sake ga yadda ya san ta,
A hankali ya kai min kiss a goshina yana mai cewa Meenat ina mai alfahari dake, Meenatu,
Nasan cewa iyayyen mu sun, muna hadin mafi, alheri a rayuwar mu,
Fatana mu zauna lafiya, a tare dan, su kara alfahari da mu arayuwan su,
A, hankali na ansa da Ameen ya Allah,
Ranan kafin su fara fita abinda yakawo su haka na zama mai shagwaba, da wani irn langabewa,
Take yaya duk ya wani bi ya susuce ya koma tankar karamin yaro,,,,
****** ********* ******
Rayuwa ke nan a yayin da muke kasar Niger Republic da Yaya Abubakar muna jin dadin rayuwan mu,
Sai dai kuma iyayyen mu suna can a cikin halin, haula,i
Don abin duniya ya kai ko ina Saboda rashin wadda ta da talkawan kasa ke a ciki,
Don a bangaren mahaifina yar akwalar motar da mahaifina ke neman kudi dashi ya ja ya tsaya saboda tsufa,
Sai malam tsoho ya taimakawa iyayyena da dan abin sayen abinci,
Wani lokaci kuma sai Yaya Ibrahim ya dan je ya samu yunwar haya ta yar vespa, ya dan yo cefane,
Shikuma Baba yakan tafi ya samo aikin karfi ya samu kudi,
A cikin haka kuma yake tallafawa Baba Buhari don sai yake ganin ya fishi dan hanyar samu,wadata,
Sam.iyayyen saboda irin tarbiyan da suka samu daga mahaifin su malam tsoho basu taba damuwa da cewa Dan su yana acikin waddata yaki ya taimaka masu,
Sam basu sa rai ga dukiyan dan su ba balke ni mace wace auren shi kawai nake yi,
Mutane ne kawai yan gani da dauka kan,ce Mama Ladi ta hana dan ta ya taimakawa mahaifin shi dan uwan shi,
Wasu kuma sai suce daga dai Yaya Abubakar din ne baida halin kyauta don rayuwan turawa gare shi,
Ance gidan shi ma wai idan ba notice ka tafi baza, a baka abinci ba,
Kuma ba,a bari ma ka shiga cikin gidan sai dai wai mutum ya koma,
Wasu kuma su ce wai baidai da halin yin alheri ne , ko kuma su ce bai samu matan kwarai wace zata dinga bashi hawara ba, shi yasa bai damu da gida da dangin shi ba, sam,
****** ********** ******
Izuwa yanzun mun kusa kai sati biyu a Niger, don aiki sosai su Yaya ke yi acan din aiki na tsakanin kasa da kasa,
Yau ma kamar kullun ya,dawo da wuri daga gurin aikin saboda yana son mudan shiga garin muyi tsaraba kamar yadda na ce mai,
Don ni yanzu na fara fahintar shi Yaya Abubakar mutum ne mai I don't care attitudes, ko a kansa balle wanin shi,
Don haka nakan yawan jin yana waya da amaryan shi wace ina zaton bata san cewa tare muke da yaya ba kasan Niger din
Takan yawan ce masa ya sayo masu tsaraban Niger,
Ganin bai damu ba yasani cewa, idan zamu wuce zan shiga garin mu sayi tsaraba,
Shaddodi masu kyau da tsada muka saye na mata da nashi sai kuma dinkankun kaya wanda suke har kasa sun sha design masu kyau wasu kuma zani da rigane hade,
Wasi shago naga kayan suna da sauki don haka dan tsaya ina son inji saukin price din su,
Daidai bayana Yaya Abubakar yadan dawo yana cewa har yanzu shadda basu isheni bane,
Kai na langabe ina cewa wanan dinkin yaimin kyau a fuska ina son a sai wa malam tsoho ne yasamu na zuwa jumma,a,
Murmushi Yaya yai min tare da cewa ai sai ki zaba mai ko?
Kai na kara langabewa nace to Yaya idan da hali ai da ka sayawa su Baba don da wuya asamu irinsu acan da saukin kudi haka,
Ba musu Yaya, yace idan zan iya daukan kaya ai Bissimillah ko ?
Kaloli masu kyau na zabawa duk iyayyen mu maza gar Baba wadda,
Azato Yaya zaice min kayan sunyi mashi kudi da yawa sai kawai naga ya biyya batare da wani gardama ba,
Mamaki ne fal a zuciyana ina tunanen nafara sanin wasu daga cikin bahagon halaiyar shi da mutane basu gane, ba,
Don tun ina karama nakan ji malam tsoho yana cewa Abubakar ai bahagon mutum ne, mai murdaden hali ,,,,
A kasuwan na ga nonon rakumi na sayo su da yawa na kuma sayo chikwi da dabino da sauran kalar abinda bamu dashi a kasar mu,
Ranan a gajiye muka dawo daga kasuwan sai korafi yayake min wai duk nice nasa shi yin wahala,
Murmushi kawai nayi nace yaya aikin lada ne fa mukatsaya yi sai yakan ce min sai kuma akace a,wahala ko ?
Ni kadai ce adakin don Yaya Abubakar yana gurin da suke zaman karshe,
Yau sun,fi kullun dadewa don haka har zuwa lokacin barci don haka na tashi, nashirya cikin wasu jajjayen kayan barci iyakar tsayin su gwiwana,
Na daure kaina, da wani ribon baki, sai, na koma bakin mirror na fara shafa turare ta ko ina ajikina,,
A gajiye Yaya Abubakar ya shigo dakin yana rataye da couth din shi ga kafadan shi,
Kokarin cire takalman shi yakeyi a lokacin nakaraso gurin shi cikin wani irin tako, rigar jikina yana shaking,
Hannayen shi ya ware na shige ya mayar ya rufe hannayen dani a ciki,
Ajiyan zuciyan zuciya muka sauke kusan atare, tankar mundade bamu ga junan mu ba,
Bayan yai wanka yai sallah shafa,i da wutir, sai nagabatar mai da abinci
Zaune nake a gaban shi na tsurawa abincin ido na kasa cin komai, sai faman tunane nakeyi
Hannu shi na hagu yai amfani dashi gurin kada min hannu,
Abinda yadawo dani daga duniyan tunanen da na shiga ke nan,
May kike tunane haka bayan ga yayan ki a gaban ki kuma ?
Murmushi nayi nace a hankalo ba komai yaya ina dai tunanen cewa gamu anan muna cin abinci mai kyau da lafiya amma ,
Har mu rage afita dashi batare da mun iya cinyewa ba,
Amma gida suna can yanzu nasan a wanan irin lokacin na damana da abu kan yiwa mutane tsaye suna nema,
Murmushi kawai Yaya Abubakar yai min tare da kokarin tsiyaya ruwa a cup ya sha
Da sauri na karbi goran ruwan ina tsiyaya masa a cikin cup na mika mai,
Sai da ya kora ruwan sanan ya dan kalle ni yace,
Kina nufin cewa yanzu gida a matse suke cikin irin wanan lokacin ?
Cikin yar murya irin ta mai shagwaba nace Yaya kasan fa ba wai suna wani aiki bane,
Sai fa abinda Allah ya basu zasuyi amfani dashi,
Ajiyan zuviya naji yayi a lokacin tare da sauke numfashi a hankali,
Har ya gama cin abinci bai kara cewa komai ba na mika mashi tissue ya goge hannu da bakin shi,
A irin yanayin da naga Yaya Abubakar tun zancen mu na abinci sai na dan shiga damuwa batare da na bari yagane ba,
Don inaga baiji dadin zancen da nai masa ba a take nace wa kai na sannu dai Meena uwar rigima,
Daga gani saki sai in kama talala,
Daga gurin da nake a kwance ina kallon Yaya Abubakar tsaye a gaban mirror ya na shafa roll on a hammatar shi tare da dan, jefa mintin a bakin shi dan na zube muna saman mirror ne, idan zamu kwanta sai kowan mu ya dauki yar kallan da yake son tsotso, yasa abaki don sanya dan kamshi baki,
Ina jin lokacin da ya hawo gadon tare sa rungumoni daga baya inda ya fara sunsunar wuyana har zuwa sumar kaina,
Sai naji ya kira sunana acikin wani irin murya mai rauni,
A hankali na amsa mashi da na,am Yaya,saboda na fuskanci magana ce ta muhinmin zai fada min,
Tambaya naji ya jefo min da cewa shekaranki nawa yanzu ?
Gaba yaba da dam don nasan dama na taba yan mazan yau ,,
A hankali nace ina cikin na sha tara Yaya
Hmmm naji ya ce tare da matseni yaci gaba da addu,oin kwanci,
Barci ya fara dauka don nasan yau ba kan,ta don ran yan maza da alamar a jagule yake,
Muryan shi naji yana cewa Meenatu banda abinda zance sai dai in kara godewa Allah ubangiji subbahanahu,wata,ala da ya bani ke amatsayin abokiyar rayuwa,,
Meenat wanan zancen da kikai min a gamay da gidan mu ya kamata ace hankali na yakai can da dewa,
Amma sai kawai shedan yasa na shagaltu da zance saboda aiyukan da sukai min yawa mutane kuma suna shakkan fada min gaskiya saboda su na ganin cewa wai ina dashi nafi karfin su yanzu,
Wani irin ajiyan zuciya na sauke tare da dan kokarin juyowa na dan fuskance shi,
Ai tuni idona ya ciko da kwalla, hankalin Yaya, Abubakar yadan kara tashi jindayayi ina hawaye,
Janyoni yayi zuwa, jikin shi ya kara matse gam yana cewa,
Kada kiyi hawaye Meenat, nasan cewa kece kwanciyar hankalina iyanzu,
Saboda nadade ina neman mutumin da zai dunga sani a hanyoyin alheri arayuwana,
Nasa gefen hannuna na share hà waye da ke zubo min a hankali ,
Nace Yaya nadade ina shawaran yadda zan sanar da kai irin bukatar da mahaifan mu ke çiki a gida,
Musanman ma Baba Buhari wanda mutane ke maka kallon baka kula dashi don tun ina karama nake ji a na fadar haka,
Subbahanallah naji yace haka mutane ke kallo na Meenat nagyada kaina nace kwarai ma yaya don gashi ko dan abin hawa
Kakasa saiya mashi don komai nisan guri akassa zakaga Baba yanatafiya zuwa,
Innalillahi naji yaya yana ta maimaitawa don da alamar maganar ta daki zuciyar shi sosai har cikin rashi,
Abin mamaki sai gani kawai nayi mutum kamar Yaya Abubakar yana hawaye,
Yace Meenat, wallahi ban fara hawa abin hawa ba sai da na sayawa Baba mashin amma mama tace yace baison abin hawa indai bashi kudin shi,
Kinji dalilin da yasa ban sha,awan saya masu abu sai in bashi kudin
Innalillahi nace a raina don nasan sherin Mama Ladi haka,