Advertisements
Chapter 15 Reading TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  Complete Novels

Chapter   15 / 61

42K to 45K   out of 180.5K words

Sosai suka nutsa a cikin hiran da sukeyi don Abdulhamed yana ta kokarin kara, kafa,wa kan shi tubali, a zuciyar Meenatu,
Ali, Abba's ne ya fito daga cikin gidan uncle yana kokarin gyara kwalar rigar sa,
Caraf idon shi ya sauka akan Meenat da Abdull din wa yan da suka yi nisa a cikin soyayya,
Gaba daya hankalin sa ya koma akan su kallon Abdul yake yi a zuciyar shi ya, ce wanan guy din shine ashe Yarinyar nan ke, kin sauraron kowa,
Wani irin kishi ne wanda bai taba jin kwatankwacin irin sa ba arayuwar shi,
Wani gumi mai zafi ne yaji ya keto mai a goshi alokaci guda,
Don haka da sauri ya kau da kansa gefe guda inda yataka da karfi zuwa gurin da ya aje motar shi,
Zuciyar shi sai faman tukuki yake yi bai san may yasa ba yau ,yau da ganin yarinya har ya fara jin feeling a kan ta,
Duk wana abin da yakeyi Abdullahameed wanda ke zaune saman motar shi yana dan kada kafar shi a hankali,
Meena waye kuma wanan bakon da nagani agidan ku,
Gurin da Ali, Abba's yake yana kokarin ta da mota Meena ta dan kalla
Juyawa tayi gurin Abdull tace mai nima ban san shi ba yanzu nagan shi da zan fito,
Amma ina ga dangin matan uncle ne tunda har ya shiga cikin gida,,,,,



ZEEE MAKAWA YELWA
[7/13, 07:21] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
1⃣9⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL-A'ZEEZ,,,


Tun zuwan Abubakar sai washegari musalin karfe goma na safe suka dan samu kebewa da kakan nashi malam tsoho,
Malam tsoho yana saman shifidar shi na gadon kara da ke kofan gidan shi,
Inda Abubakar din ke saman tabarman roba a kusa dashi zaune,
Daganin su kasan cewa ganawa sukeyi na musan man,
Don irin yadda suke zaune mutum zai iya gane hakan tun daga nesa,
Yan maganganu suka fara yi akan irin al,amuran da ke gudana acikin gidan su,
Sai kuma zancen gurin aiki, shi da suka saba yi da malam din a,duk lokacin da yazo garin,
Daga karshe ne shi Abubakar din ya jefo zancen son ya kara aure saboda wasu dalilai da bai fadi ba,
Malam tsoho wanda ke daga kishingide ya dan murmusa don dama yasan da cewa komai dadin dadewa irin wanan ranan zai zo,
Shiru yayi bayan ya gabatar da bukatan shi ga malam din don jin mai zai ce a lokacin,
Malam tsoho yadan gyara murya a hankali cikin natsuwa ya kai duban shi gare shi yace madalla maisuna nayi murna kwarai da jin wanan zancen daga bakin ka,
Ina mai adduan kulun kafin in kwanta dama in ga zurian ka a duniya,
Murmushi Abubakar yayi don dai shi a gaskiya irin wanan zancen ba wai ya damay shi ba ne a rayuwan shi,
Abubakar ya cigaba da cewa don haka akwai wata wace muka shirya da ita acan Abuja,
Dama ita ce nake son ko za a shirya sai su Baba su samu lokaci su tafi ayi duk wani abinda ya dace ayi ?
Jin malam tsoho yai shiru yasa shi dago kai ya dan dube shi don jin abinda zai ce,
Ganin yanayin fuskan tsohon kawai yasa shi gane cewa baiyi na,am da zancen ba,
A hankali Malam ya kira sunan Abubakar din sai yai shiru na dan wani lokaci,
Can yace mai zai hana ka duba nan gida ko a,cikin dangi kasamu wacce tai ma ku shirya,
Ina ga hakan zaifi ma don kaga mu a nan din ai muna da kyawawan yan mata irin yadda zaka so,,
Abubakar ya dubi kakan shi cikin yar natsuwa da kuma mamakin maganar shi ya ce,
Malam nifa bazan iya aure daga nan gida ba don ban son fitina da kuma raini,
Katse shi malam din yayi da cewa ai ba dole a nan gida zaka zaba ba ka zagaya acikin dangi ka duba ko, don akwai kyawawa nasani,
Malam inji Abubakar banda ra,ayin auren mace don kyaun ta ko wani abu,
Ni kwanciyar hankali kawai nake bukata, arayuwa na ,
Malam ya girgiza kai kawai don jin may Abubakar din yace a lokacin cikin takaici,
Shike nan Jeka mai suna zan zauna uban nen naka muga yaya za,ayi su samu lokacin zuwa kan zancen,
Godiya sosai Abubakar din yai mashi saboda yasan cewa tunda ya samu kan malam tsoho ya gama da kowa agidan ke nan ,,,,,
Daga haka ya bar gurin malam din zuwa gidan sarakuwar shi hajja,

****** ******* ******
Baba Buharine zaune tare da mahaifin shi suna magana akan zancen da Abubakar din ya zo dashi na son karin aure a can birni,,
Sai da Baba buhari yagama sauraren zancen da mahaifin shi ke koro mai a kan dan shi Abubakar,
A jiyan zuciya yayi inda ya dago kai a fusace yace wa mahaifin shi,
Amma malam wana shawaran na a,yar darwa yaron nan sam bai yi ba saboda babu alheri ko kadan ga auren bariki,
Murmushin jin dadi Malam Manya ya sauke saboda fahintar shi da danshi Buhari ya yi ,,
Amma a fili cewa yayi wa Baba Buhari abi shi a sannu don kaga ai auren shi na fari yai muna biyayya ko,
Baba Buhari ya ce amma malam sai naga bai fi yaran gidan da wani kama ba ko,
Malam ya ce ai shi ya ce ba ra,ayin shi bane auren mace kyakyawa don haka kaga yana da nashi irin zabin ke nan,
Don haka sai kuje ku fara shirin zuwa nema mashi aure kamar yadda ya bukata,
Baba Buhari ya dago kai kamar wanda zai yi magana, a lokacin sai kuma ya maida kan shi kasa yai shiru don biyayya saboda yaga ba wasa ga zancen tsohon,
Kusan duk iyayyen su Abubakar sun yi rashin aman na da wanan auren da zaiyi a birni ba acikin gida ba,
Amma yadda zasu yi don dole suka ja bankin su sukai shiru,
Baba Hamza da Baba samaila da Baba yahayya sune zasu tafi sai wani makwabcin su wanda shima anan cikin unguwar shiyar sarakuna yake da zama akusan shakuwar gidajen biyu ya koma zumunta, sosa,,,,

****** ******** ******
Tun da safe take kokarin kiran layin wayan shi amma not reachable ake ce mata,
Har zuwa yanzu da wayan mobile din ta ya nuna mata karfe biyar da rabi na marance,
Don haka ta sake kiran layin shi din don taji ko zai shiga,
A cikin sa,a ta ji layin yana ringing alamar kiran na shiga,
Allah Allah salawatu takeyi ya dauki wayan amna sai ba,a dauka ba,
Wanan abin ne ya tayar mata da hankali sosai har ya sa ta shiga wani dan hali,
Azaton Salawatu ko a gida iyayyen Abubakar sun yi rejected din zancen ta da shi ne,
Dole badon taso ba ta dai,na kiran shi acikin damuwa take sosai ,
Sai musalin karfe takwas na dare ne taji call a wayan ta tana dubawa taga ashe Abubakar ne a layin
Cikin zumudi ta dauki wayan tana mai kashe murya, ta,
Da sallama yafara zance kamar kullun don hakan akidar shi ce shi,
Ina,shiga gari da,zun naga kiran wayan ki a lokacin a kwai go slow sosai a hanya,
Ya hanya Sir ya mutanen gida,?
Ya kabar su mama da sauran jama,a,
Sosai yaji dadin wanan maganar da takeyi mai don ta nuna mai kulawar ta akan yan uwan shi,
Shiru ne yadan biyo bayan hirar nasu sai ita salawa din ce ta kau da shirun tana tambayan aka maganar da ta kai shi gida,
Dariya yai mata inda yaje cewa ai nasan cewa shine dalilin kiranki haka tunda,zun,
Cikin jin kunya tace No sir ba hakana bane ,
Saidai dama don ina son inji ko zasu yarda dani ne in zama surukar su ko
Nan dai ya ce mata gajar ce ki zauna ashiri don anytime zamu iya ganin parents di na agarin nan akan issue din mu,,
Wani irin dadi ne ya ziyarci zuciyar salawatu a lokacin,
Inda harda dan ihun ta don jin dadi wanda har ta kasa boyewa,
Murmushi Abubakar yayi a bangaren shi don dai shi dariya ta bashi sosai,

****** ******** ******
Saye take a cikkn rigar barcin ta wani mai ruwan ja, jajir,
Kanta yana daure da ribon wanda ta kama kan tun daren jiya da zata kwanta,
Kitchen din ta shiga don ta kama ma mummy girkin safe kasan cewar itace da girki yau kuma tana dakin maigidan
Idan abin ta mummy bazata fito ba sai rana ya haska sosai,
Wayan ta dake gefe guda gurin da take tsaye tana fere dankalin turawa,
Idanun ta kawai ta dora akan screen din wayan ba tare da ta dauka ba,
Dan uwa tagani a rubuce, kan screen din wayan nata,
Wani lalausar murmushi ta sake, a lokaci guda tare da saurin kokarin aje yukan da ke a hannun ta na firar dankalin da takeyi
Bayan ta ta jingina da abin zinc din dake cikin kitchen din,
Fuskanta dauke da murmushi tace Assalamu Alaikum
Tankar Abdulhamed din ya na gurin a lokacin
Meenat wacs haduwar ta da Abdul ya kawo mata wasu sauyin ra,ayi da dama, yanzu,,,
A cikin wanan zazzakar muryan nata tai masa sallama tare da lumshe ido,
Abdull wanda a lokacin yana tsaye da yar three quarter wando yana kallon Birch daga masaukin su,
Bayan sun gaisa ne take cewa cikin muryan nata mai sanyi,
Ya hanya dan uwa da fatan ka isa lafiya dai ko ya gajiya da jama,a
Gajiya Alhamdullah sai dai ta kasa samun sukuni saboda ke Meena,
Kai dan uwa saboda ni fa kace. ?
Murmshi ta sake mai tare da cewa kai dan uwa fadi dai gaskiya ko dai gajiyar wanan dogon hanya da ka sha,
Au to baka yarda ba to bari ki ji da kunnuwar ki ko zaki gaskan ta,
No barshi kawai ai na yarda don nasan baka fada min karya
Murmushi yai mata don yardan da tayi a lokacin guda
Tabbas yasan cewa meena tana son shi sosai kamar yadda shima yake sonta,,
Hira sosai sukayi na ina kwana ya gajiya ya kewan dan uwa ?
Daga karshe take fada mai cewa tana kitchen zata hada break fast ne, don haka ya kyale ta badon yaso ba,

****** ******** ******

Dukkan su hudu a vikin shigar manyar riguna suke, don girmamawa,
Sun isa garin lafiya cikin gajiya, don haka masaukin da Abubakar yai masu a wani hotel da aida nisa da uguwar dasuke,
Sai dai su basu so hakan ba tun ma dai da aka ce wai har abinci duk na hotel zasuci,
Baba hamza ne yafara magana yana cewa gaskiya Abubakar ka tona muna asiri
yanzu a ce abinci da kafirai sunka dafa shina zamu,
Baba Samaila wanda yake kokarin nade hannun rigar shi yace cikin shirin daura alwala,
Don yin sallolin dake gaban su tun rana,.suke saman hanya,
Washe gari ne da safe suka je yin abinda ya kawo su watsu ne man aure,
Tun kafin su shiga suka fara ganin abin assha aciki don yawanci a cikin shi
Duk jikin su ba sitirun karai ga kuma gidan da kazanta,
Sai kuma babu wani babba mai tsayayye a gurin du taron yara ne,
Duk a matse suke da su bargida don basuga wani sbin kwarai ba da har dan su zai so hada zuria da irin wa yan nsn mutane ,
Daidai da zasu wuce shi baba hamza ke tambayar wacece sarakuwar tashi,
Wata babban mace da ke saye da dogon rigar atamfa ya dan dane mata jiki wai itace dan nasu ke so hada zuria da ita ,
Tun a hanyar su ta dawowa masauki suke suka fara sauke numfashi an rasa wanda zai fara magana daga cikin su,,,,
Shiko Abubakar din sai jin dadi yakeyi Salawatu ta kusa dawowa hannun shi,
Zai zama tankar kamar kowani magidanci shima yayi yadda masu aure keyi,
Sam idon shi ya rufe bai hango abinda iyayyen shi suka hango mai ba,
Baba yahaya yace ko shi dai da yake uba ga Abzai kwashi wanan tsohuwar mace ba wai mata,
Baba Samaila ne yai masu magana akan su daina don komai ra,ayine,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[7/14, 07:07] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
2⃣0⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH AL-JABBAAR

Duk kan su hudu ne zaune cikin ladabi a gaban malam,
Dawowar su ke nan ko gida basu shigaba a lokacin ,
Sun tsaya don su sanar wa da malam sakon gabacin da aka,aike su yi, a can
Baba Sanaila ne yai saurin tare yan uwan nashi don gudun kada su aiban ta zancen a gaban malam mahaifin su kamar yadda su ksi tayi a can,
Dafarko ya fara cewa malam Allah ya dawo damu lafiya,
Abubakar da iyalinshi su na gashe ka kwarai da gaske,
Ya ce muyi masa godiya sosai a gurin ka kafin yazo,
Can kuma gidan ita matar muntafi gaskiya sun karbe mu hannu bibiyu sun kuma yi munar sosai, don haka muma muka gabatar da komai kamar yadda ya kamata ayi,
Baba Hamza' cikin wani irin kallo da yakewa dan uwan shi ya kasa hakkuri yace,
Haba samaila may zai sa ka boyewa malam gaskiyan zancen,
Tunda tura mu yayi don mu wakilci gidan mu, mun kuma je munga akasi a gara mu fada mai don ya san yadda za,a bullowa abin ko ?
Haba yaya Hamza' haka bai dace a gare mu a matsayin mu na iyayye ga Abubakar ,
Ganin yadda suka fara kaulewa da gardama yasa malam tsoho dakatar da su a cikin daga hannu irin na manya,
Inda ya ce haba ba aiken ku nayi ba,aigara ku tsaya ku fada min gaskiya don kar sai abu ya baci adawo kuma ana da,an sani,,,
Gaskiya kan inji wanan dattijon guda da suka tafi tarr da shi Abuja, watau makwabcin su,
Yanzu kai malam sani fada min duk yadda akai don Allah saboda hakan ne ai na hada ka da su,
Gyara murya malam sani yayi yafara da cewa to a gaskiya malam ba irin arziki za a dauko a gidan ka ba,
Darajan gidan ka da mutuncin gidan ka bai,dace a ce yaron irin wanan zirian ya auro mace irin wancan matar da muka gani don sam babu tarbiya,
Baba yahaya ne yajefa baki da cewa ga shi kuma ta girmi shi Abubakar din,
SUBBAHANALLAH inji malam tsoho shi Abubakar din ke kuma son ta a hakan ?
Kwarai kuwa don da muka tafi ya nuna muna jin dadin shi kwarai da gaske a lokacin,
Shiru malam tsoho yayi batare da ya iya cewa ufan ba saboda atake zuciyar shi ta baci
Baba Buhari wanda tun,fara magana bai iya cewa komai ba sai kai yake kadawa kawai a lokacin
Can ya ce watau shi mai sunan malam sabon al,amari yake son kawo muna kuma ke nan?
Gaskiya hakan ba zai yuyu ba sam dole ne idan har aure yake son karawa ya dawo gida ya zaba a cikin dangi ko yan wanan yankin,
Ido kawai malam tsoho ya kura masu baki dayan su yana nazarin abubawa daga zancen kowan su,
Baba Hamza yace aiko a nan gida muna da yara sai ya zaba daga sashen shaibu ko yahaya da hamza,
Sam bai kawo sunan Baba Samaila ba wanda ke da yar matashiyar diya guda acikin su,,
Shima din sam bai damu ba don dama ba wai wanan karon bane suka fara numai haka ba,
Komai a yasu,yasun su suke abin su sai, dai su ware shi shi kadai koda yar uwar shi
Mikewa yayi don jin inda zancen ya juta akala yana mai ce masu to jama,a mukwana lafiya fa,
Dag haka ya shige abin shi cikin gida zuwa gurin iyalin shi,
Ido malam tsoho wanda ke daga kishigide yabi dan nashi dashi kawai don yasan halun samaila sai shi,
Samaila mutum ne mai murdaden halin wanda ba ruwan shi da shiga shirgin wani arayuwan shi,,,

****** ******** ******
Tafiya take yi a hankali kasancewa rana yau yai zafi,
Wanda hakan yasa masu abin hawa sukai karanci a saman titin a lokacin,
Tafe take da irin takon ta tankar tana tausayin kasa, ne
Wata bakar mota lafiyyaya ta zo ta harba a saman titin,
Can kuma Meena ta hango motar na yowa baya baya
Har zuwa daidai inda take batare da ta waiga ba

15 / 61