Advertisements
Chapter 44 Reading TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  Complete Novels

Chapter   44 / 61

129K to 132K   out of 180.5K words

plat shoe's din mazane,
Direct part dina ya dosa a lokacin don ganin halin da nake ciki,
Wani kunci Salawa taji ya rufe ta tabi bayan shi da harara,
Komawa tayi saman kujera ta zube don takaici, da bacin rai

Ina zaune Tv na yana aiki na kai Africa TV 3, suna program na addu,oin marance,
Daga gurin da nake a zaune ina dan bin su a hankali, kamar yadda suke yi idona a lumshi,
Kamshin turaren Yaya Abubakar ne ya daki hanci abinda ya haddasa min bude idon nawa a hankali,
Cak muka hada ido dashi yana tsaye kallo guda nai mashi na gane cewa tun dazu ya shigo kena, don har yai shirin fita sallah magrib can kasan mu
Kokarin gyara zamana nayi ina cewa sannu da dawowa Yaya,
Ya an,sa da cewa,, lafiya kike daki bangan kin fito gaidani da dawowa ba ?
Lafiya lau Yaya na ba shi ansa da hakan ina cewa, wani program ne ya dauke min hankali ban san time yayi ba,
Ya maida kallon shi ga tv don yaga kowani tasha nake kallo,
Kan shi ya juya, yana cewa ai ina ce ko har yanzu jikin ne ?
In ce mu tafi asibiti hakana dai,
Na girgiza kaina da sauri ina cewa, ai naji sauki yaya don ko alaman fever na daina jin sa yanzu,
Ya ce ni zan fita zuwa massalaci saina dawo,
Allah ya tsare hanya nace tare da fatan adawo lafiya,
Har ya kai kofan daki na na manta Yaya mun fa gode Allah ya saka da alheri Allah ya umfana dukiya,
Murmushi yayi daga gurin da yake tsaye yace har ta sanar da ke, ke nan ko ?
Nace Yaya kasan abin dan uwa ai yadda yake ko ?
Daga haka ya sai kai ya fita dakin fuskan shi dauke da murmushi,

Sallawatu wace ke zaune ta hau tayi fan a motar kishi,
Sai faman jijiga kafa takeyi tana leken han fitowa daga part dina,
Hango shi da tayi tafe, yana dan murmusawa, yasa ta mikewa tsaye,
Kafin ya karaso gurin ta, ya kara daure fuskan shi tam, do ya gane nufin ta tun daga nesa,
Dan dabur cewa tayi tana ce har kafito ga time ma yana son ya kure maka,
Batare da yai magana ba ya sa kai yabar gida tare da turo kofan shiga falo,

****** ********** ******
A bangaren Mama Ladi Yaya Abubakar yakira ta sun gaisa yake tambayan ta akan zancen haihuwan Samira,
Sai cewa tayi dama tana son fada mashi cewa ya turo da abinda za,ai mata, hidima dashi,
Don dai yasan cewa yanzu ita bawai wani karfi ne da ita ba,
Kuma gashi haihuwan Samira na farko ke nan a gidan,
Don haka kaga ba karamin sha,ani za,a yi ba ke nan don haka katuro da abin kwarai,,
Yace to Mama zan turo ma Baba Wadda sai ya kawo maki,
Sai naga sakon ke nan ta fada kai tsaye kamar mai fada a lokacin,
Suna kashe wayan ya numfasa tare da lumshe idon shi, don lamarin Mama yana bashi, mamaki sosai,
Don ita ko diyan da ta haifa bata barsu ba sai tai mashi nasu kalan,
Sam ko yan uwan haihuwan shi,mama bata kauna yai masu wani alheri a tsakanin su,
Don sai dai sakon yafito ta hannun ta dole saboda tadan samu ta tsankwara,, daga ciki,,
Amma yanzu wanan shawaran da Meenatu ta bashi haka zai dinga yi a tsakanin su,,

Bayan ya dawo daga sallah ne, Salawatu wace ke zaune daga bakin gado,
Ogana ina son zamuyi magana da kaine please idan har ba damuwa,
Ba tare da ya kalle taba ya natsaye daga bakin wardrobe yana ciro kayan da zai saka a jikin shi,
Gaskiya Ogana ina son inyi request a wurin ka irin yadda kaduty kana shiga wani daki please,
Da sauri ya juyo yana mata wani irin kallon mamaki,
Yace are you out of your mind,,
Ta dan fadi a hassale, da cewa gaskiya mind dina is not styling idan kana haka,?
Ya ce so da wanan kika shigo min gida ?
To dakata kiji bazan yarda ki kawo min matsala acikin family na ba,
Ke da su wa ya fara shigowa gidan nan first ?
A hankali, tace sun rigani zuwa gidan, gaskiya,
Yace may yasa su basuyi bakin ciki dake ba sai ke ce zaki nuna bakin cikin ki a kan su,,
Shiru tayi tana cewa, gaskiya ni bana jin dadin hakan ?
Amma kin san cewa suna gidan ki shigo ko don haka sai kiyi hakkuri amma idan bazaki iya ba hanya a bude yake gaskiya,

Ni dai a ranan kaman nasan yadda sukayi da Yaya Abubakar,
Haka kawai naji ban son fita falon kamar yadda ya ya umurce mu dayin haka kullun,
Sai ma da na tabbatar da suna falon a lokacin na mike don in gabatar da Sallah da na idar kuma zan kwanta ne kawai abina,
Saboda irin yadda naga take taken ta tun da rana yasa nace barin kama kaina,
Ina kokarin shimfida sallaya Salawatun da kan ta tashigo dakin daga kofa tadan tsaya tana ce min Oga yana magana da ke a falo wai,
Nace mata cikin alaman nuna ina sallah da cewa uhum, uhum,
Ta juya batare da tace komai ba ta nufi fallon don ta sheda mashi cewa ina sallah,
Bayan na idar na kawo nafilfili na dora akai, dafa bisani kuma nazauna naci gaba da yin addu,oi na,,,
A takaice dai sai da na ga time ya kusa na barin falon yasani tashi don in tafi falon,
Idona ya fara kawai ga kayan dake saman table din a cikin ledoji guda uku duk da alama iri dayane,
Kamar kullun na nufi kasan carpet na zauna irin yadda na saba yi,
Sai da ya gama tura sakon nan shi a,system yadago kai ya dubi time yana cewa,
May kika tsaya yine haka baki fito ba yau da wuri haka ?
Nace, Sallah na gabatar Yaya sai kuma, na tsaya nadan watsa ma jikina ruwa,
Ok kawai ya furta, tare da kokarin jawo ledejon dake gaban shi,
Inda Anty Sadiya take yace kizo ki zabi guda daga ciki,
Anty Sadiya tamike tazo gaban table din ta mika hannu ta dauko wanda tagani can daga karshe,
Sai ya juyo gurin da nake zaune saman carpet ya ce oya zaki zaba ko ?
A lokacin ne naga Sallawa tana wani kada kafa, kamar yadda idan ran mutum ya baci yake yi,
A hankali na dan karasa bakin table din na dauki ledan dake gabana,
Tare da cewa cikin wata irin murya mun gode Yaya, Allah ya kara dukaka,
Naji lokacin da Yaya yai wani irin ajiyan zuciya tare da cewa hmmmmm,
Sai ya juyo gurin Sallawa wace ke ta wani irin taunan baki tagefe tana karkada kafa,
Ta mike, jiki ba kwari zuwa gaban table ta dauki ledan karshe din ,
Nikan ina zaune na jingina bayana ga kujeran da nake zaune a kusa da shi,
Kafana yana daga mike ina karkadawa a hankali batare da ma na kalli ledan ba,
Hankalina yana gurin TV da,nda suke wasan tseren ruwa,
Karan bude ledojin da ke gefen su nake jiin suna tayi,
Nidai ban bude ba sai ma mikewan da nayi a hankali ina cewa zan kwanta sai da safen ku,
Na mike tare da daukan leda na wanda Sallawatu ta kura,wa ido kamar tana son ta kwankwance abinda ke cikin Ledan nawa,
Nikan ina shiga daki, na aje Ledan saman mirror dina na rufo kofana na kwanta kawai,
Sai da na jero addu,oina na shafe ko ina na jiki na sanan na jabargo na kwanta,

Barci na soma yi amma sai nake jin kamar hayaniya daga cikin gida,
Tun ina daurewa har yakai na bude idona inajin muryan su su uku ana ta masifa a tsakani,
Saida yaya ya daka masu wani irin tsawa su kayi tsit gaba dayan su,,,
Magan ganun da nake ji jefi,jefi a kan ledan kayan da yaya ya siyo muna ne sukeyi,fada,
Don naji anty Sadiya wace bata magana ma ko banza tana cewa daga kawai,
Nshiga kitchen dauko ruwa zaki canza min leda an fada maki cewa ban gane kallah roban man dake ciki bane,
Tsuki nayi kawai tare da gyara kwanciya na ina mai jin haushin su a zuciya na,



Afuwan yau ba yawa sosai please,,,,,,,,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA,,
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈTARKOπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
5⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL-RAQEEB,,,,

Alheri, Rahama Ni,ima, Gafara, Daukaka, Daraja, Baiwa Dake a cikin wanan Watan mai albarka ya Allah muna rokon ka , ka sada mu da shi gaba dayan shi,,,,πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘


Yau Anty Sadiya ce da girki, don, haka na tashi tun da safe na fara gyara gida,
Kagin kowa ya tashi ko ina na gidan mu sai kamshi ya keyi,,
Ko da Sallawatu tafito don ta sa girkin breakfast ta samu kitchen din mu na wani irin kyali saboda yasha gyara don har store din kitchen sai da na sharo,
Gaba dayan su duk wanda ya fito sai ya ja ya tsaya don mamaki, saboda gyara shine gida,
Dining table din mu har kafafuwan shi sai da nagoge su tas, don tun daga nesa zaka gane hakan,
Wai duk wanan aikin da sha babu ko mutum daya da ya fito daga cikin gidan a lokacin,
Na kare na koma dakina don in yi wanka indan sarara,
Na dade zaune a gaban mirro ina gyara jikkina tare da yan shafe ,shafe,
Sai a lokacin na hango ledan kayan da Yaya Abubakar ya bamu adaren jiya,,
A hankali da gurin da nake na mika hannu na bude ledan don inga abinda ke ciki,
Sabulai ne na wanka da man shafi,masu kamshi maclean, su tissue, cotton bund, da sauran su,
Sai wani material mai kyau da dauka ido kalan nawa, light pink,
Kalan yai min kyau sosai a idona don nakai wani lokaci ina ta shafan material din,,
Namayar da kayan a leda na dauka na sa cikin wardrobe, dina,,

Dogon riga na yan kasan Niger da na sayo ya ji aiki a gaban shi nasa,,,
Nayi wanan kwalliyan ne don kin san idan kina da kishiya, bawai sai ranan da zaki karbi girki bane zakiyi kwalliya a,a
Next day to kiyi girki zaki gyara jikin ki ta yadda mijin zai rude yaji kamar ace ke ce zakiyi, girki a ranan,
Jin banji motsin kowa a waje ba yasa na koma saman gado na na haye,,,
Gadon da yasha gyara cikin wani zani gado ja mai zanen flowers farare,,,
Dakin yaji room fresh tunga labulen dakin zanin gado da bathroom don sune ake sawa room fresh, sai daki ya dade yana kamshi,
Dan kwantawan da nayi ashe barci ya fara kwasa na saboda gajiya,
Sai muryan Anty Sadiya naji kaman a mafarki, tana cewa
Au, Meenatu kin kwanta ne,?
A hankali na bude idona ina kokarin tashi daga zaune, ina kuma, cewa, yanzu fa na kwanta ashe barci ya dauke ni, ko
Idon Γ€nty na saman rigan da nasa alokacin, yana daukan ido, ,
Anty ina kwana ?
Tace Alhamdullahi Meenatu,
Ya gajiyan aiki,?
Na tashi naga ko ina gidan yau sai kyalli ya keyi murmushi nayi nace naga idan anyi tun da safe yafi sauki ne shi yasa nayi,
Ta ce to nagode, murmushi nayi yayin da naga ta juya zata bar dakin don fita,
Ni kuma sai na koma saman pillow da nake kwance da farko,
Amma sai kuma Anty ta tsaya tare da juyo wa tana fuskan ta ta,
Tace Meenatu dama yau, tuwon alkama naso in muna kuma sai dai nasan idan nayi zai sake ne, nace to babu matsala Allah ya kaimu anjima lafiya ,
Sai dai ina son idan anbarni zan tafi gurin wanke kai anytime na dawo sai muyi,
Na karashe zancen cikin murmushi ,
Tace ai badamuwa ko sai kin dawo, ke nan don ni zan shige ciki,
Komawa nayi na kwanta sai dai kuma barcin baizo ba again, don haka sai na lumshe ido,na,,,
Tausayin irin rayuwan, Anty Sadiya nake,yi mutum ba ruwan shi da komai shi,
Idan ba ka zauna da ita sosai ba sai ka dauka bata son mutane ne ita,
Kamar tana kyaman zama da mutane don yawan, daure fuskan ta,
Amma daga yau tunda har na fahince ta insha Allah a tare zamu dinga aiyukan mu na gida,
Na nisa nace, aiko banza ita matar yayana ce kuma kaman yan uwa muke don zama gari guda, da muke,
Idona yana daga lumshen da yake ina ta tunanen duniya,
Alaman mutum ya na tsaye a kaina naji sai kuma kanshin turaren da hanci na ya shako, min, na dan baiwa, watau Yaya Abubakar, ke nan,
Hakan yasa ni bude yan daradaran idona sai cikin na Yaya Abubakar wanda ke tsaye, a gaba na, fuska ba yabo ba fallasa, ya kura min idanun nan nashi masu firgita mata,,
Kokarin mikewa nayi zaune ina mashi wani irin murmushin jan ra,ayi,
Kafin in ka daga zaune sai naji muryan shi

Tambaya ya jefo min Barci kike ne ko kuwa hutu ?
Nace, kawai dai ina dan hutawa ne kawai, kafin in fita,
Ina kwana Yaya ?
Lafiya kalau ya kika tashi ,?
Ko da yake naga ai lafiya kike tunda har kin yi wanan irin aikin haka ?
Murmushi nayi nace gidan ne yai min ba dadin gani shi yasa na kamawa Anty gyaran shi,
Kin kyauta yace tare da dan murmusawa, ya ce zai tafi shi sai ya dawo,
Ban san lokacin da na jefo mashi tambaya ba da cewa kayi break fast ne ko Yaya ?
Sai naga ya dan bata rai yana dan jiji ga kai yace yau bazan tsaya break ba agida kifita ku karya,
Na ansa mashi da fadin to Yaya,
Zai fara tafiya nace
Don Allah Yaya ina son yau in tafi saloon gurin gyaran kai ?
Cak ya tsaya yadan yi shiru zuwa can ya nisa yace,
Ok ki dauki ki nan a saman drawer a dakina Hamza ya kai,ku, amma dan Allah ku kula kada yai tukin ganganci da ke ,
Nace tare da Fattu zamu tafi insha Allah zamu kulla,,
Ya ciro kudi daga cikin ajihun wandon shi ya miko min,, yana cewa,
Ba matsala yace yasa kai ya fita abin shi,
Godiya nai masa, tare da fatan a dawo lafiya,,,
Na nisa bayan fitan shi tare da komawa na kwanta,

****** ********** ******
Mun samu mata da yawa a cikin saloon din, don haka muma muka bi layin zama,,
Matar mai shago tafito a take ta shedani, don bata manta da ni ba,
Da murna tare da sakin fuska, ta, tare mu ta na jin dadi,
Ta umurta da a kawo muna ruwan, sha duk yadda naso, kada ta wahal da kan ta gare mu amma sai taki,
Bamu kadai ba ranan harda sauran mutanen da ke shagon ta saya muna ruwa masu sanyi,,
Mata sai hiran duniya akeyi ana ta yan dararaku kowa da abinda ake mata,
Wata daga cikin matan ta dan dubeni take cewa da za a wanke maki kafa, ai maki ado zai yi kyau,
Murmushi nayi ina cewa ai naga kamar da layi da yawa yau, akwai jama,a agurin,
Anty mai shagon tace barin maki da kaina kaunata,
Ba bata lokaci a ka kawo roba a gaba aka fara gyara min kafa,
Matar da tabani shawara a fara gyara min kafa wayan ta yai kara ta dauka suna magana, sai dai a cikin zafin rai take zancen ta,
Bayan taga tafara fada ita kadai tana cewa ita za,a kawo iskan ci ?
Sai Anty mai shago tace to ai shi wanda kike fadan dashi yanzu baya kusa,
Matar tadan ja tsuki gefe tana mai kauda kan ta ,tace,,,
Bari kawai Anty wata shegirya matace ke son shiga gona ta,
Wata mace ce gurin aikin su guda da maigidana shine take ta kokarin shige masa,
Yanzu wai kirana yayi yana ce min wai an kawo lace masu kyau a shagon su amma, Aliya ta zaba muna,
Ina ruwan ta da ni da har zata zaba min a binda zan sa tasan colour din da nake so ne,?
Anty mai Shago ta nisa tace aiko naki ya samay ki wallahi,
Don kin san irin matan nan idan sun lakewa mijin ka sai Allah,
Fattu daga gefena tace, irin amaryan gidan ku ke nan Meenatu,
Nai murmushi kawai batare da nace komai ba don dariya abin ya bani,
Anty mai shago tace, ke kardai ki ce min an ma kauna ta kishiya kuma,
Da ba kun ce su biyu bane,?
Fattu tace wallahi Anty, wata irin garmakekiyar mata na nan a cikin su wai itace amaryan su,
Duk ta girmay masu har maigidan nasu, sai kishin bala,i,,

44 / 61