Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : Complete Novels
hanya,
Bayan ta koma gida ne duk abin duniya ya damay ta don tunawa da kalamin, Hajja na karshe da tayi,
Alwala tayi inda ta shiga daki don gabatar da sallah azuhur saboda lokaci ya gabato,
Bayan ta idar ne ta zauna ta dinga jero irin addu,oin tsari da tayi dama wanda ba na tsari ba,
Hakan ne yasa taji wanan kwallan ya rage kukan da ya ke yi ,
Saidai duk da haka hankali mama bai kwanta ba sam,
Yau, ce rana na farko da tai nadaman kulla kawance da Hajja a rayuwan ta,
Mai gidan ta ya hane ta da hurda da hajja amma duk taki haka ma malam manya da kan shi yasha fada mata cewa ta rage zurewa Hajja amma sai taga kaman suna mata kyashine da hassada,
Don sun gan ta tare da wace zata mai hanya ci gaba,,,
Yadda taga dare haka taga rana, don ta kasa runtsawa, kuma ta hana kowa ranan kwana dakin ta,
Dama malam Buhari ba a dark n ta yake ba, a ranan,
Tun da asuba bayan idar da sallah kwalla ya fara maimata kukan shi irin na jiya sosai ,
Don na yau babu kakautawa, don kuka yakeyi bilhakki,
Mama Ladi hankalinta ya kara tashi sosai gata duk ta zabge a lokaci guda ta,wani ramay wa,
Bayan an idar da sallah baba buhari ya,gama ganawa da mahaifin shi,
Direct sashen mama Ladi ya nufa don su, gaisa don haka dabi an shi yake dama,
Zaune take a kofan dakin ta a cikin tashin hankali tayi tagumi da hannu guda,
Tun daga nesa baba Buhari ya gane cewa babu lafiya,
Ladi lahiya dai ko?
Baba Buhari ke tambayar ta cikin sanyin murya irin nashi,
Maimakon ta bashi ansa sai ta kasa daurewa ta sa kuka , hankalin Baba Buhari ya kara tashi inda yace,
Subbahanallahi, halan mi,ya faru, ?
Wa mutun shin ?
Ta,na yi tana dan leken kofan sashen kishiyan ta tace cikin marairai,cewa,
Walleh malam magana na ni, dauko maka, shina ka damun,
Halan mi ankayi ?
Sai kuma tasake sa kuka,
Nan hankalin Baba Buhari ya kara tashin don yasan kukan ladi ba na wasa bane,
Yau ko gata tana yi ido biyu,
Hwada min mana mi,nana shin ?
Malam am, mutai ciki ka jiya,
Dakin suka shiga tare, da shi inda sai raraba ido ya keyi ko zaiga yaran dakin amma baiga kowa ba,
Shin ina yaran sun ka tai,?
Suna can inda Bagudo na tura su,
Mama ladi ta bashi ansa da hakan,
Mi kawo kaza har kuryan daki shin?
Walle malam Ba kazata ba,
Kaza ta ke bakijin kukan ta na,,
Walleh malam nice maka ba kazata ba,
"Sihiri" ta,
Murmushi yayi yace wane irin sihiri shin ga kaza ina jin ta haihu tana kuka,
Ko ni an malam nice ma sihiri na wallah,
Sororo Baba Buhari ya tsaya tsaye yana kallon ta cikin mamaki,
Wane irin sihira na haka, ?
Bata boye mai komai ba ta fara fada mai ,
Dakatar da ita yayi don bai iya sauraren ta shi daya,
Saboda mamakin abin da yaji ta fara fada mai da farko,
Shin Ladi mi, kin ka rasa a rayuwan ki da har kin ka tai zuwa yin wagga harkan,
Sai kuma maganar ta makale mai saboda takaicin da ya rufe shi,,,,
Cikin bakin ciki da kunar zuciya ya zubawa mama Ladi ido, kuri,
Sai kuma tunane ya zo mashi yanzu shi wa zai tun kara da wanga zancen abin kunya da mama Ladi ta jawo mai,
Baba Samaila kanin shi wanda basu hada uwa guda ba dashi ya fado mai arai,
Wanda yasan cewa bazai taba jin wanga zancen ba in har yayi shi da shi a gurin wani,
Don haka Baba Buhari ya juya batare da kara magana ba,
Yayi sa,a ranan Baba Sama,ila yana gari bai kwana daji ba,,
Da sallama ya shiga har cikin Sashen Baba samailan,
Da mamaki ya fito yana wa dan uwan shi kallon mamaki,
Yau may ya kawo shi har cikin sashen shi abinda bai taba ga nin Baba Buhari yayi ba kenan zuwa sashen kannen shi,
Don haka zuciyar shi ta ba shi cewa da magana ke nan yau,,,
Yaya lahiya ko?
Samaila, babu lahiya yau kan don dai walle matan ka Ladi ta dauko magana,,
Nan yadan fara ba Baba Samaila labari kamar yadda ta fada mai da farko,
Shiru yayi yana sauraron dan uwan nashi cikin na tsuwa,
Sai da ya gama fada mai yace ,
Wanga zance shina Gaba kura baya Karen Daji,,
Wa ka fadawa bayan ni ?,
Baba Buhari ya ce cikin wata irin murya mai bantausayi,
Wani ka hwada ma bayan kai,
Da can wurin ta niyo nan,
Inda kake, don babu wanda nika iya fadawa wagga magana,
Ajiyan zuciya Baba Samaila ya yi tausayin dan uwan nashi ya kama ahi don yasan gaskiyan zancen ke nan ya fadi,
Ina zuwa yace cikin sauri ya shiga dakin su bai jima ba ya hito saye da wata yar karamar riga ajikin shi,
Mutai, yaya yace cikin karaji da sauri, inda dan uwan nashi yabi bayan hima da sauri,
Mama ladi wace take a tsayen tun fitan Baba Buhari,
Don a zaton ta Baba Buhari zai tara mata mutane ne a shiyan ta ya tina mata asiri,,,
Sai ganin su tare, da Baba Samaila tayi girshi a Sashen ta,
Cikin sauri Baba Samaila batare da ya tsaya dogon magana ba ya ce,
Ina kwalla, yake, ?
Kamar mai tsoro mama Ladi tadan nuna mai karkashin gadon ta da yatsa a hankali,,,
Ba bata lokaci Baba,Samaila, ya duka karkashin gadon bakin shi dauke da addua,
Ya sukuci, kwallah ba bata lokaci yai hanyar fita wajen gidan inda baba Buhari, shima yabi bayan shi da sauri suka bar gidan,,,,
Da, sauri su duka biyun suka fada yar akwalan motar pekof din Baba samaila dake, can gefe guda ajiye,
A bayan motan suka dire kwallah sai gudu baba Samaila, ya ke yi,,,
Tunda ya dawo daga office ranshi yake a bace don baisan ko, wace irin mutum bace Sadiya,
Ya za,ace mutum ya sauka agidan ka amma baka gan shi ba kuma baka tambaye shi,
Da farko ya na ganin shine wanda bai da mu da hurda da mutane ba ko a gida,
Amma sai yaga yanzu garama dashi bisa ga Sadiya wace bai taba jin ko tai hiran yan uwan ta ba ,
Daga inda yake zaune saman kujeran dake facing din nata,
Ya ja wani rin tsaki mai tsananin karfi da kara, sannan ya ce,
Wanan hali naki bai yi ba Sadiya idan zaki canza ki canza tun baki makara ba,,,
Kallon shi Sadiya ke yi a cikin mamaki, don bata san ko fadan may yake mata ba haka,
Yace ace mutum yai Bako bai gan shi ba kuma bai tambaya ba,
Wanan wani irin rayuwane haka pls,?
Mutumin nan fa kin sani sani kanin mahaifina ne,bawai wani bare ba,
Amma kika nuna ko in kula a kan zuwan shi kika barni da dawai niya dashi,
Maimakon tai magana sai kawai ta sake wani irin kuka mai karfi mai tsuma zuciya,,,
Mamaki ta bashi saboda baiga abin kukaba acikin wanan zancen da yake mata ba a halin ywnzu,,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA,,
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
6⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
MALIKI, YUMEEDEEN
Tafiya kawai sukeyi batare da wani yai wa dan uwa magana ba,
Kowa da irin abin da ke a bakin shi, adduan sukeyi ta neman tsari daga shedanu ko wani iri mutum ko dabba ko Aljan,
Hanyar JEGA, ya dauka don fita gari amma suna kai wa KALGO, sai ya dauki hanyar BUNZA,,
Tafiya mai tsawo su kayi daga titi zuwa cikin wani daji,
Sanan ya samu wani guru ya Parker motar suka fita ba tare da wani yai,wa dan uwa magana ba,
Fatanyar dake a baya da shebur yadauka sai ya nufi wani kwazazaben rami inda ruwa ne acikin sa,daga gefe,
Kuma a ko da yaushe ruwa zai iya cika gurin don damana ce,
Rami mai zurfi ya haka agurin inda ya duka yai ta addua, a cikin ramin,
Wasu irin manyan duwatsu da ke gefe ya kwasa,
Shi dai Baba Buhari sai kallon ikon Allah ya ke yi a cikin mamaki,
Mota Baba Samaila ya koma ya dauko wanan kwallah,
Da farko a bakin ramin ya aje kwallah dake ta faman ihu da kuma kukan kaza,
Cikin dakiyar zuciya Baba Samaila yace kai shedani daga yau babu mu babu kai, har abada,
Idan kaga dama ka koma can gurin wanda ya kawo ka anna mu babu mu babukai babu iyalin mu,
Kamar ana jira ya kare zancen shi sai sukaji wani irin tsaki mai karfi daga cikin kwallan a lokaci guda, ance,
Matsiyata kawai a haka zaku kare ai ,
Arziki na binku kuna ki,
Baba Buhari sai ya fara ja da baya don tsoro,
Shiko Baba Samaila sai kawai ya duka ya sukkuci kwallah bai tsaya jiran komai ba sai ya juye wanan halittan a cikin wanan katon ramin da ya haka,
Wani irin kuka wanan halittan ya kara sakewa kamar mutum a lokacin,
Yace don Allah kada ka kashe ni zan bauta maku zan baku ko nawa kuke so,
Zan dinga yo maku farautan duk abinda kuke so a duniya kada ku kasheni ,
Ina son in zauna a duniya nima kamar yan uwa na,
Dutsen dake a gefen shi yadauka bakin shi na dauke da sunan Allah ya sake dutsen a cikin ramin da karfi,,
Wayyo karku kasheni malam San,inna ne ya aiko ni gurin ta don in bata kudi,
Wani dutsen Baba Samaila ya kara azama mai sama,
Wani kara ya sake gami da yin tsuki ya ce wawaye kawai da kun barni da kun sha kudi da shanaye da hatsi,,,,,,,
Kasa Baba samaila, ya mayar saman dutse tare da kara dora wasu irin manyan duwatsu akai yakara dabe gurin,
Kana ya tofe gurin da addu,oi masu karfi sanann yadaga hannayen shi sama yai addu,a,
Daga haka suka bargurin da sauri cikin tashin hankali,
Sai a lokacin Baba Buhari ya samu bakin magana,,,
Sai sharan gumi sukeyi suna ajiyan zuciya, ba tare da wani ya iya yiwa dan uwa magana ba,,,,,
Da kyat Baba Samaila ya iya jawo mota, suka iso cikin gari,
Saboda wani irin mugun zazzabi da ya rufe shi a lokaci guda,,,,,,
Tun isan su ya shiga gida ido rufe ya cewa matar shi ta rufe shi sanyi yake ji,,,,
Yai Barci yafi a kirga acikin motan kafin su iso Birnin Kebbi,
Tun ganin sun fara jin kamshin gida sai barci ya fita daga idon shi,
Babu abinda yake yi sai sakawa da warwalewa, na abinda zai cewa mahaifan shi a gida idan ya isa,
Yace ba don sakon mutane da Abubakar ya bashi da bazai fadawa kowa cewa ya tafi har Lagos din ba,
Shigan su garin Birnin kebbi da misalin magriba mota bata tsaya da shi ko ina ba sai uguwar su watau, shiyan Sarakuna,,,,
Mutane suna alwalan sallah magrib suka ga tsayawar mota a sheke da kaya cikin ta,,
Kowa idon shi na kai har malam wanda bai san ko wani bako ne ba a wanan lokacin, na huturo,,,
Wada ya bude mota tare da ahi da driver suka fito a lokaci guda,
Daga shi har driver haraman alwala suka fara yi duk da dinbin gajiyan dake a tare da su,,,
Sai da ya karanto, yan addu,oin da ya iya wai kada malam yai mashi fada, a kan tafiyan shi,
San,nan, ya tunkari gurin da malam yake a zaune ya jan casbi,
Ganin yana lazimi yasa shi komawa baya a lokacin har driver ya fara sauke kanyan motan,
Nan Wada ya kira yaran dake gurin don su kwashi kayan zuwa cikin gida,
Mahaifiyae shi da tun isowar shi yara suka sheka suka fada mata tana cen cikin farin cikin ganin dan ta ya, dawo gida lafiya,
Ganin irin kayan da ake ta faman shigowa da shi wai duk tsaraban Baba Wada,
Shi yasa har matan wani lungu zuwa ganin gulma da sunan sun,zo taron Wada ne,
Abin "da mahaifi, har mahaifiyar shi ta gabatar mai da abinci da su ruwan sha a daki,
Sai daukan abincin yayi yace bari ya kai, waje su ci da driver,
Sai a lokacin mahaifiyar shi wace jin dadi ya hana ta tun farko tambayan Dan, nata inda ya tafi,
Kai tsaye batare da wani shakkunta ba ya ce mata, Lagos gurin Abubakar,
Lagos Wada ?
Da kai dawa shi katafi ?
Ni kadai ya bata ansa a takaice,batare da jin wani darr, ba,
Kafin tai wani magana ya sukkuci kolan abincin nashi zuwa waje gurin driver da ya ce,
Ya samu har yana niyar tafiya alokacin amma sai wada ya tsaida shi da magiya don ya tsaya suci abinci,
Da kyat driver ya tsaya inda sukaci abinci da abokin tafiyan shi na wanan ranan,,
Wada ne a gaban malam kai a sunkuye, cikin tsananin tsoro malam karo na farko a rayuwan shi,
Don haka ya yanke wa kan shi shawaran fadawa malam cewa Abubakar ne ya bukaci ya zo inda yake,
Wanan zancen ya batawa malam rai inda yace a harzuke yaushe har ka ga Abubakar din yace kazo,
Kai a sunkuye Wada ya ce tun lokacin da zai koma da yazo ,
Wanan zancen kawai ne inji malam watau kai ka girma har ka kai lokacin da zakai bugun gaban kan ka, ka ai,watar da abin da kaga dama,?
Wada yai maza ya kara sunkuyar da kan shi a kasa,,
Don jin may mahaifin shi yace, da kyat ya iya cewa ayi hakkuri malam,
Malam yasan idan yace zaiyi magana rayuwan shi zai ci gaba da baci sai kawai yaja bakin shi yai shiru,,,
Tsawon wani lokaci Wada ya na duke a wurin, malam bai ce komai ba sai can yaji muryan malam ya na cewa akira ma shi Samaila,
Hakan ya sa wada gane cewa ba zancen shi malam ke yi ba,a yanzu, kuma, bai da halin yin maganar,
Don haka ya mike a hankali zuwa dakin mahaifiyar shi,cikin sanyin jiki,, duk sai bai ji dadin abinda ya aikat ba,
Dan sako yadawo yana sheda,wa Malam cewa Baba Samaila wai tun safe bai da lafiya,
Cikin murya mai kama da fada Malam Manya yace,,
Samaila yaro na ? da zai zauna da ciwo daki bai fadawa kowa ba,
Baba Buhari malam yasa a kira mashi don ya je ya dubu Baba Samaila, ya ga ya jikin na shi, ya ke,?
Sosai Baba Buhari hankalin shi ya tashi don dama duk yinin yau baida kwanciyar hankali,
Rayuwan shi yau a,bace yake don bai ko son yaga mama ladi a fuskan shi yake ji,,,,
Yadda Baba Buhari ya samu Baba Samaila yasa hankalin shi tashi a lokaci guda,
Don a rufe yake tun daga kan shi harzuwa kafan shi cikin wani katon bargo,
Take abinda yafaru da safe dasu ya fado mai a rayuwan shi,
Cikin wani irin tausayi da kuma tsoron halin da dan uwan shi ya ke a ciki,,,
Cikin sauri ya juya zuwa gurin Malam Manya mahaifin su don ya sanar da,shi abinda ke faruwa,
Tsugune Baba Buhari ya ke agaban mahaifin su yana sheda mashi abinda yafaru dashi,
Subbahanallahi inji Malam yace ya akayi baku sanar da ni ba tun farkon faruwan abin,
Daga haka ya mike shima yau da kan shi har cikin Sashen Baba Samaila,
Kamar yadda Baba Buhari yabar shi tun farko hakan suka samay shi,
Kira biyu zuwa uku Baba Buhari yai ma Baba Samaila amma bai iya ansawa, ba,
Hakan ya kara tayar masu da hankali sosai don haka ba bata lokaci malam ya,juya,zuwa Shiyan shi,
Bayan wasu lokota,sai ga malam ya,dawo dauke da wani roba mai, ruwa aciki, shi,,
Malam, yasa Baba Buhari ya kware mai bargon da ya ke a ciki,
Kwance yake idon shi a kafe sai, rawan dari da yake yi,
Daidai gurin kan shi malam ya nufa inda ya dafe goshin Baba,Samaila, a hankali,
Adduoi, yafara jefo mai ya na tofa mai a goshi, sai kuma, ruwan da yake yayafa mai a duk kan sassan jikin shi a hankali,
Ba,a gushe ana mai haka ba ya sake wani irin ajiyan zuciya mai karfi, tare da kokarin dagowa,
Cikin sauri Baba Buhari ya dan danne shi ta mai da shi saman gadon,
A hankali ya ke bude idon shi acikin wani yanayi na rashin fahinta, inda yake sosai yake kallon su,
Ganin haka hankalin