Advertisements
Chapter 47 Reading TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  Complete Novels

Chapter   47 / 61

138K to 141K   out of 180.5K words

nufin shi, don haka ya dagawa Baba Musa kai tare da,sauran iyayyen mu da ke gurin,
Ya ce zaman Meenatu tare da mai suna,na wani babban TARKO ne na haka muna wanda gaba dayan ku baza ku gane hakan ba yanzu,,
Gaskiyane inji Baba Buhari wanda ke sauraren zancen su,
Yadan murmusa tare da fuskantar mahaifin su ya ce,
Ai malam iyanzu na fara fahintar, gaskiyan zancen ka sosai,
Don sanin halin yaran nan da,nayi gaba dayan su
Don ka ga shi mai sunan malam zuciya da saurin fushi,
Ita ko Meenatu uwayen hakkuri da sanin ya kamata,
Malam yace to kun ji dalilin hada tarko nan da nayi ke nan badon komai sai hankalin wanan yaron ya dawo gida gare mu,
Wanda idan kun kula ku kan ku za kusan cewa da, da, da yanzu nan ban daya ba ne,,
Don da farko sam maisuna badamu da damuwar mu ba ko kadan,
Yanzu kuma idan har kunyi la,akari sai kuga cewa, ai ba, duk wani harka yana dubuwa,
Gaba dayan su sukace haka ne malam maganan ka gaskiya ne ,
Baba musa ya ce, ai watau, malam wanan mahaukaciyar uwar tashi ita ce duk ta kawo wanan matsalan wallahi,,
Malam ya ce kusa ido kuyi kallo in akwai rayuwa ko bani da rai zaku ce na fada maku,
Don Ladi na kallon bai boyewa zai dinga yiwa yan uwa da abokan arziki alheri babu yadda zata yi,
Kuma shi kan shi duk wanan miskilancin nasa zai daina ya rabu da su a hankali, kudai sa ido a hankali zaku gane amfanin wanan hadin nawa,
Malam Bashir makwabcin mu yace lalai malam kayi babban hikima guri wanan hadin ba karamin TARKO ka haka ba,
Malam tsoho yace ai duk zage zagen da ake yi lokacin da nai wanan hadin auren ina ji ba wai ban ji bane,
Su wa yan nan yaran da kuke ganin cewa ai sun girmi ita Aminatu,
Su ya kama ta a hada da mai sunana, na ba gaskiya bane,
Don da sune aka hada dashi da zuwa yanzu anfara kai ruwa rana ko
Saboda ba zasu iya ratuwan mai sunana ba san nan ita Ladi irin wanan mugun fitinan da take yiwa Saratu da,shi kan shi samaila yana iya kawo karewan auren,
Gaba daya sukace wanan gaskiya ne malam don dai duk matan mu in ba Saratu ba babu mai iya hade fitinar Ladi,
Don,ko shi Samaila idan ya yunkura nasan cewa matar sa ke taushe shi yayi hakkuri,
Kowa yace gaskiyane malam gaskiya abin yayi kyau sosai,
Yace kun ga yanzu muna sani halinda suke ciki kamar yadda su ma suke sanin labarin gida a kai akai har yake taimaka mu na irin hakan,
Ko wa ya karba da cewa, gaskiyane malam abin yayi kyau kwarai da gaske,
Malam ya kare da cewa Allah ya kyauta Allah kuma ya raya muna su yasa albarka

Daga, haka a ka fara zancen abinda ya kamata su yi tunda kudi sun samu yanzu,
Baba Musa bai boye ba ya dinga fadin alherin da, Yaya Abubakar da Meenatu, suka turo masu,
Mutane sai albarka akesawa yaya Abubakar din tare da fatan alheri ga rayuwa,
Zance na yawo ya kewayawa har caraf a kunen Mama Ladi,
Mariya ce ta jiyo zancen ta zo tana shedawa mama cewa ashe , Abubakar ya aiko masu da kudin hidima,?
Mama Ladi tace bari zancen nan Mariya, akwaodai inda suka ranto (aro su) su ,
Walleh Mama shina ya aiko ma su da shiya kuma ance kudi na masu yawa ya aiko masu ,
Wai harda Meenatu sai da taturo da nata taimakon ita ma,
A take rayuwan Mama Ladi ya baci may mutanen gidan nan ke nufi da har zasu rufe min alherin da dan cikina ya aiko da shiya,
Mikewa tayi Anty Mariya tana dakar da ita amma ina wucewa tayi zuwa cikin gida,
Bata tsaya ba sai, sashen Baba Musa tashiga surfa jidalin cewa an maishe ta batasan komai ba kenan
Baba musa na jin ta yai wuf ya fito daga dakin shi, shi ya na cewa ke Ladi walle in kina cin kasa ki kiyayi na shurem,,,
Don tafi karfin taunar ki saboda dankon ta, kedai san ni bani dauka shedanar ki,
Don haka duk abinda kin ka jiya ba karyana ba gaskiya ta,
Sai ki tai ki hana gobe shi basuwa, ki gani inzai hannu maki,,,

****** ********** ******
Tsafi gaskiyan mai shi don Hajja tun daga Birni Kebbi ta tashi har bargu tai tafitan yini don kwana bai yi gare ta,
Ta samu bokan ta tai mashi bayanin irin rayuwan da take ciki yanzu inda take she da mashi duk irin abinda yanzu dodo ke ciki,
Shiru boka yayi kamar mai nazari can ya nisa yace ,
Abinda kike mashi da farko shine, yanzi baya samu daga gare ki,
Anyi alkawari dake kin amince yanzu kuma sai baya samun hakan,
Tace to amma ai naga dai ta nawa bangaren babu matsala,,
Don duk abinda, ya ke bukata na tsare mashi ina kokarin yi,
Boka yace dole a kwai matsala, don haka kawai ba zai daina abinda yai ke yi ba,
Muddin yana,samun biyan bukatun shi to shi kuma ba fashi ga abinda zai gudanar gare ki,,
Hajja cikin magiya take cewa bokan ta don Allah dai ya taimaka mata akan dodo ya dawo kamar farko,
Yan abubuwan surkulle boka, yai ma Hajja tare da mata albashir din komai zai dawo, daidai,
Ta bashi abinda ya kamata,ta bashi tare da mashi godiya sosai,
Ranan ta, juyo, daga can ta biyo ta garin illo don yafi mata saukin tafiya,
Sai zuwa yamma sosai ta iso gida da kunshin abubuwan da bokan ta ya ba ta tayi,,

Bata tsaya wani hutawa ba ta shiga aiwatar da abinda, boka ya bata tayin,
Wani hayaki da ta turara har makwabta sai da suka shiga damuwa saboda mugun karfin shi,
Amma sanin halin Hajja yasa kowa ya kama bakin shi da ita, don ba zasu iya jidali ba,
Sai da ta tabbatar da cewa ta gama hada komai san nan hankalin ta ya kwanta,
Ta ne mi abincin da zataci ta dan samu guri ta kwanta jiran tsan,mani,,,,

****** ********** ******
Kitchen na ke ina,aiki yau ni ce, ke da girki sai dai Anty Sadiya tace min bata jin dadin jikin ta, a yadda take fada min wai jikin tane ya mutu mata kai yai mata sanyi,
Bayan na idar da sallah la,asar, na fito falo ina kara gyara yan wguraren da ya dace in kara gyarawa,
Karan tafiyan takalmin naji shigowa gidan har mai shi ya kawo tsakiyan falo babu sallama,
Sau guda na daga kaina na dan kalli, gurin da naji motsin mutun shigowa,
Sallawatu ce wace tun safe tafita gidan sai yanzu tashigo,
Ko da zata fita ma batai muna magana zata fita ba don haka ni ma, na maida kai na ga abinda na keyi, batare da nai mata magana ba,
Don banga dalilin da zan mata sannu da zuwa ba bayan ba tai min sallama ba, da zata fita,
Daga gurin da take tsaye ta ke cewa abincin rana fa Meena,
Aikina naci gaba dayi batare da na nuna mata cewa najita ba,
Sai ji nayi tace, ke Meenat dake fa nake magana, zaki wani share ni,
Batare da na juya inda take tsaye da tana jiran abinci bayan yunwan da ta kwaso daga gurin gantalin ta,
Ji min rainin hankali ga wanan yarinyar abincin ma kuma shi bakin cikin bani kikeyi,
Nace sai kin dawo gurin koyon Sallama zan baki ansa ai,
Wani irin takaici da mamaki ne suka rufe ta a lokaci guda,
Karamar yarinya kamar Meenat, in badon rayuwan aure ba ina ita, ina yarinya kamar meenat,
A fusace Salawatu ta juya zuwa, part din ta tana kokarin aje kayan da ke a hannun ta,
Ta dan jima don lokacin har na karasa abinda na keyi ina kokarin shigewa,
Ta dawo cikin wani irin yanayi wanan karon fuskan ta babu dafin kallo,
Tace sai naga raini ya shiga tsakani na dake sosai don kina ganin cewa wai abu gudane ya aje mu agidan dake,
Nadago fuska na nace au da make baki sani bane sai yan zun nan,?
Cikin wani irin mamaki take kallon ta ce laila ma yarinyar na kin samu guri wallahi,
To bari kiji yau babu kowa a gidan nan idan ki kai min tsiya wallahi kafin wani ya shigo sai na nada maki dukan tsiya tukun,
Cikin wani irin rashin tsoro da karfin zuciya na ce Bissimillah uwata ,,,
Aiko ban yi aune ba naji tayo kaina gadan gadan, da nufin duka,
Ai take na Fulani ya ziyarce ni wani irin zuciya ya rufe min ido a lokaci guda,
Wani irin zazzafan mari takawo min na kauce nikuma Allah yaban sa,an ta nadago ta tun daga kasa na makata a tsakiyan falo,,
Zan kara yowa kanta naji an rike ni ta baya ban tasya ba nai cikin su ita da wanda ya rike ni ta baya,
Gam naji an kara rikeni sai wani irin tsimi jikina keyi a lokaci guda ,
Najuyo cikin masifa sai naga Yaya Abubakar ne a tsaye bayana rike dani sai kuma Anty, Sadiya, wace ke daga gefe acikin tashin hankali, ita ma,
A zuciye nake cewa a sakeni, dan Allah kafin wanan, mara mutuncin ta taso,
Cikin wani irin tsawa yaya Abubakar ya ke ce,wa, Meenatu kina da hankali kuwa,
Haushine da kishi ya kama Salawatu, dake kokarin mikewa ga kasan da nakai ta,
Ita a ganin ta irin yadda yaya Abubakar yayi yana magana kamar bai son yi yaudarane yana son ya goyi bayana ne,
Don haka take cewa Meenatu nice ki,kaiwa wanan abin haka?
Abubakar kana ganin yadda tai min ko ?
Yaya Abubakar cikin wata irin murya yace shout, up, my friend, ya ce cikin wani irin muryan daka tsawa,
Tayo cikina da wani irin karfi har saboda wani irin kishi da ya turnike ta a lokaci guda,
Ban hango alaman imani ba ko kadan ga fuskanta a lokacin, don haka,
Ta na kawowa na daga kafa na kai mata shuri aiko takara yowa cikina haikan,
Wani irin wawan mari Yaya Abubakar ya sake min tare da daka min tsawa,
Dole na shiga hankalina, Anty Sadiya ce naji daga bayana ta riko ni tana cewa kadai so dukan tane
Amma ai meenatu bata da laifi a wanan zancen don daga maganar fatan baki takai mata duka fa,
A take anty Sadiya tashiga fada mashi abinda ya faru, tiryan tiryan,
Daga gurin da Salawatu take kai yamutse tankar mahaukaciya take cewa,
Aike dama Sadiya munafuka ce don na fahinci duk munafuncin ki ba yau ba,
Anty Sadiya acikin muryan nan nata, tace ba komai amma ki sani babu wace nake tsoro daga cikin ku ,
Enough Yaya Abubakar yace ciki wani irin tsawa yana wani irin hucin bacin rai,
Ya juya gurin Salawatu dake rera kuka acikin kissa yace stop dat please ?
I don't want to hear your silly voice,,
Ta wani langabe kai tankar yarinya tana cewa dama nasan sun hada min kai basu kaunan zamana a gidan nan don ina bare acikin ku,,
Kallon ta mu kayi gaba dayan mu don saboda Sallawatu ta cika makiran mace, domin abinda tace,
Maganan da tayi na cewa mun hada mata kkai mun maida ita bare yasa shi yasa shi wucewa batare da yai muna magana ba,

Juyawa mukayi ni da Anty Sadiya muna kallon juna a cikin mamaki saboda duk inda makiran mace takai Salawatu ta wuce gurin,
Ba wanda yaiwa juna magana daga cikin mu kowa ta nufi part din ta mu kabar muna fuka nan tana share hawayen munafunci,,

Kamar kada in shiga dakina sai kawai naji wani irin kuka mai karfi yazo min a lokaci guda,
Tausayin kaina ya kamani take tunanen iyayyena yazo min a rai,
Nace ashe wanan shine manya kecewa aure sha kan yaro,
Yau ni kadai ke cikin tashin hankali kuma babu mai bani hakkuri,
Kuka nai tayi inda acikin kukan tunane yazo min da cewa,
Sallawatu ni kadai takewa wanan halin don na fahinci duk ransn girki na sai ta kawo matsalan da zai sa duk zukatan mu ya baci a gidan,
A hankali naci gaba da rera kukana batare da nasamu mai rarashina ba
Anty Amarya ce ta fado min a rai don itace zata iya warware min wanan matsalan a ruwan sanyi,
Wayana jawo daga inda nake na fara neman nomban Anty amaryan
Ta dauki wayan cikin cewa babban diyar ya kuke ya gida,
Inadai lafiya kika kirani cikin wanan daren, don ba halin ki bane,
Kuka taji inayi tace subbahanallahi Meenatu,
Watta ba ki shin?
Missa may ki,?
Wai may ankayi ne shin?
Ban iya cewa komai ba sai kukan da naci gaba dayi kawai,
Cikin dan rudewa tace shin ko in kaiwa uncle din ki na ?
Nace a,a anty cikin dasasshen murya na fara labarta mata halin da muke ciki da Sallawatu tun zuwa na

Shegiyar tsohuwa annaminiya,
May ya kaiki Meenat ai hada jiki da kishi da sunan fada tsiya yake sawa wallahi,
Daga yau ka da ki kara hada jiki da kowan su don walle baida kyau so sai
Kuma tsiyata maigida shikayi irin hakan din gaskiya ba a son fitani na agida tsiyata gida shikai,
Idan tayi ki dai rabu da ita don duk sherina hakan,
Wai ita makira da gangan taka haka don dai ta bata maku tsarin dare ke da shiya,
Nace nima Anty abinda na fahinta ke nan yanzu don ni kadai takewa hakan,
Anty tace share hawayen ki ke jiya tashi ki kimtsa jikin ki ,(gyara jiki) kitai zuwa gurin mijin ki,
Kuma ki sa ido ki kallo in Allah yayi duniya don manzon Allah sai Allah ya saka maki Meena am,
Yanzu bari har gobe don kega dare yayi amma gobe in Allah ya kai mu zan kiraki mu kara tataunawa akai keji,
Na,amsa cikiciki da cewa insha Allahu Anty, tace Allahi shi haushe ki kan su gaba daya nace Ameen Anty,
Tace don walle babu kishiyar da kason kishi shiya saidai mutum kawai ya boye kishine shine saukin,

Wanka na shiga inda na dan dauki lokaci gurin gyara jikina yau ban ko tsaya sa rigan barci ba saboda duk zuciya na a cakushe take min,
Daurin kirji kawai nayi da zani na nakawo katon hijab dina na aza sama,
Na jawo kofan dakina a hankali nasa key na rufe nakama hanyan hawa sama,
Ashe Sallawatu taji motsin rufe kofana don haka ta tashi da sauri tana dan lekawa tagani ko kulle kofa nayi daga ciki,
Sai ganina kawai tayi na gilmata kamshin turaren da na fesa duk ya rufe mata hanci,
Wani irin kishi da takaici ya ziyarci zuciyan ta don bata zaci hakan ba yau, daga gare ni,
Don dai tasan cewa ta rshe wanan plan din yau ke nan,,
Zagi ta jefo da cewa yar iskan yarinya ta rushe min plan dina, ke nan,
Amma ai dani kike zancen zaki gane ni ce,muje zuwa dai,
Natura dakin a hankali batare da nai sallama ba inda na hango yaya Abubakar kwance saman gadon shi yadafe goshin shi da hannayen shi idon shi a lumshe,
Idan baka sani ba sai kace barci yakeyi a lokacin amma ni tun shigowana nafahinci idon shi biyu,
Don haka na koma daga can karshen gado na kwanta a hankali,, batare da nai wani kwakwaran motsi ba,
Shima dai yau din yaya banji ya mirgino ya rike ni ba yadda ya saba yi min,
Wani irin tunane nakeyi wanda hakan ya haddasa min ciwon kai a take, lokaci guda,
A haka na samu barci ya saukeni ba tare da na sani ba,
A cikin batci naji wani irin murdawan mara ya zo min lokaci guda na farka na bude idona,
Murda sosai maran ke min a hankali na bude iddona yaya Abubakar yana daga kwance ya barcin shi hankali kwance,,
Tunda nake ban taba irin wanan ciwon maran ba don duk yada naso in daure sai na kasa saboda wani irin yanka da marana keyi a lokacin,
Kasan gadon na sauka ka ko zanji ya fada min kaina na daga saman gadon amma kamar karamin zugin sa akeyi a lokacin,
Wani murda min da yayi da gurin da nake duke kaina saman katifa nace,wayyoni Allah na
Nishi na ke yi da karfi abinda ya farkarda Yaya daga barcin ke nan,
A hankali ya fara saurarawa sai yaje jin nice ke wanan irin nishi,
Zubur ya mike zaune yana cewa ke lafiya haka may ya faru da ke ne wai,
Nace Yaya marana ne kaman zai balle min wani irin murdan mara,naji nakara,sa kaina saman katifan gadon ina cewa wayyo Allah na zan mutu,
Subbahanallahi ya,ce a,cikin kaduwa yai kaina yana ce sannu, sannu da,sauri ya jawo rigan sa ya zura ya kashi key din mota ,
In tafiya kafana ya ja ya rike guri guda ban iya daga kafa,ko kadan,
Ai

47 / 61