Advertisements
Chapter 53 Reading TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  Complete Novels

Chapter   53 / 61

156K to 159K   out of 180.5K words

gidan to da matsala ke nan,
Wani irin tsoro ne ya kara ziyara na yadda baba ya fada muna cewa wai mata nata ihu suna ce ga dodo da diyan shi na lasan mutane,
Tsab na mike nadauko wayana dake caji a gefe guda,
Noban malam tsoho na kira duk da nasan kila yana cikin masallaci yanzu suna wuridi,
Cikin ikon Allah sai naji ya dauki wayan yana cewa Aminatu ke ta,
Na ansa da wani irin murya na damuwa nace nita malam,
Mun wuni lafiya ya ansa da fadin wallahi lahiya lau Aminatu,
Ya jama,an wajen ku,?
Suna lafiya malam, sai kuma nai shiru ba tare da nace komai,
Aminatu Yaya ankayi na nace malam naga sako gurin Baba, Wadda nagode
Malam yace kai haba babu komai ki dai yi amfani da suwa kinjiya,
Nace to malam,
Amma malam, ni gaskiya hankali ya daga ga gidan nan yanzu sosai gaskiya malam bazan iya zama ba zan dawo gida ne ni,
Sai kawai kafin yai magana nasaka mashi kuka mai tsuma zuciya,
Subbahanallahi naji ya na fadi, yana cewa ashha Amina ,
Mi zai tayar maki da hankali haka nace maki ki kwantar da hankalinki don Allah,, babu abinda zai samay ki insha Allah,
Nace cikin kuka wallahi malam duk kwanakin nan bana barci a tsorace nake don da idona naga wanan abin sihirin da ya shigo dakin Sadiya lokacin da yake fita,
Abin mamaki maimakon malam tsoho ya nuna damuwan shi sai naji ya yi murmushin manya yana cewa
Amina kwantar da hankalin, ke jiya, insha Allah babu wani sihiri da zai yi tasiri akan ki,
Ke dai ki tsare adduan da ke gaban ki don babu abinda zasuyi da ke,
Wanan abin da kike gani ai bai isa yazo gare ki ba sai dai in Allah ya bashi iko hakan ?
Don ke ba jinin su bace sai dai yazo gurin wace adda alaka da shi,
Amma ke mi kin ka hada da suwa ?
A,buguda da yanzu ka damuna, shine mijin ki Abubakar ina tsoron kada su illanta shi a sanadin zaman da yake dasu, a gida,
Nace cikin muryan kuka kaman mai tausayi may ya faru da shi malam ?
Yace, babu komai Meenatu kwantar da hankalin ki
Zaman da yake yi da yar gidan Hajja na ke dan jiyewa don kin san mace shu,umace,,
Saboda haka ki kwantar da hankalinki kamar yadda na fada maki tun farko ki dinga karanta,
Lahaula wa,la,quwati, illa billahi aliyal,azeem kafa 41
Kafin ki fito waje, duk safe, sai hasbunalah shima 450,
Babban makami wanda zai sa har basu kaunar hada ido dake shine,
Kalman shahada,,,kamar yadda na fadi a baya,
Idan kuma kin fita anguwa ko kin dawo kafin ki shiga gida kikaranta, Alam tarakaifa, kafa uku ahannuwan ki, sai ki shafe jikin ki,
Naji yace hummm Amina bazasu iya komai da,ke ba wallahi, muddin kika tsare wanan abin ,
Ke wallahi ko shi Abubakar sai ya koma ya shakkan ki,
Daga gurin da kika idar da Sallah magrib ki karanta Basmsla kafa 21 a kulun,
Na ansa da cewa to malam nagode,
Yace kin san kanufari na amsa da eh malam ina dashi, ma, ai,
Ya ce masha Allah to wanan KANUN FARIN zaki kirga guda 41 sai ki nika su ya zama gari,
A kullun sai kina lasawa a hankali har ya kare ,
Insha Allahu zai maki amfani ta hanyoyi daban daban Amina,
Don tsarine mai amfani sosai don zai maki tarei dakuma gyaraki,
Watau Amina,abinda ku yaran yanzu baku sani ba shine,
Wa yan nan abubuwan da akai amfani dasu a da can baya sunfi aiki bisa ga wanda kuke yi yanzu,
Don da mace zata tare yin su wallahi zataga fa,idan su so,sai don haka ki yi hakuri ki zauna tare da dan uwan ki,,
Sauran bayani sai ki bari duk ranan da Allah ya kawo ki sai muyi shi a fayyace,
Yakare zancen da tambayan yadda na kara jin karfin jikina,
Na,ansa dafadan cewa Alhamdullahi malam naji sauki sosai,,,
Bayan mungama waya da malam na mike don zuwa gaida Anty Sadiya,
Na samay ta zaune tana hawaye ita kadai a daki, ta,na jin sallamana tai wani irin firgigit tana cewa Meenatu don Allah kizo ki taimakamin don tun dazu na ke son in kewaya babu wanda zai kaini,
Tausayi tabani sosai irin yadda na sa may da kuma yadda tai min magana,
Na kamata har zuwa bathroom na kuma samo leda nace ta da ita ta tura hanayen ta kadan daga cikin ledan ,
Sai dai ta kasa yin hakan sai da na kama hannun ta na saka a ledan da kaina,
Wanka nai mata don ta danji daman jikin ta, sai faman yi min godiya take yi idon ta na zubar da hawaye,
Na gyara mata inda zata kwanta, da kuma duk abinda ya dace da dakin nata,
Ina shafa mata mai Yaya Abubakar ya shigo dakin cikin mamaki yake kallon mu,
Tambayan Anty Sadiya ya jikin nata ya keyi sai take ce mai da sauki don yanzu ma Meenat tai min wanka,
Tare da Yaya Abubakar muka shafa mata magani a jikkin ta, muka bata na sha,
Ina kokarin yi masu saida safe ne Mama Bi,u ta shigo da sallamanta,
Na tsaya muka gaisa da ita sanan nai masu sai da safe,na juya zuwa daki na,
Ba Yaya Abubakar ba har Maman Bi,u ba taji dadin yadda taga yanayina ba,
Don kallo guda mutun zai mun ya iya fahintar cewa ina cikin yanayin damuw daga fuska na,
Ina shiga dakina na fada wanka don bazan iya kwanciya haka na ba,
Ina fitowa sai naji wani irin yunwa ya ziyar ce bama zan iya kwantawa batare da naci wani abu ba,
Ina shiga kitchen na samu inda na aje abinci an kwashe ko ban tambaya ba nasan cewa Salawatu ce,
Raina yai matukar baci na fita zuwa part din ta inda na samu tana shafa man shafi jikin ta ma , saboda duk ashe wani dabbara dabbara jikin ta ya ke dashi ,
Nace Salawa ke dan Allah kika juye abincin kula dukka ?
Sai cewa tayi cikin wani irin kashe ido wani ya aiko ki ki tambayeni,?
Na ce eh to kaman hakane don bake, ce kika dafa ba ko ?
Ok to shine akace don ban dafa ba kada inci ko ?
Na murmusa kai nace Salawa ke nan ashe kina son ci kika ki tsayawa ki dafawa muna,
Bayan kin san cewa kece da alhakin bamu abinci yau agidan kika fita batare da kin sauke hakkin ki akan mu ba,
Mikewa tayi tare da cewa ke Meenat wallahi rashin kunyar ki ya isheni don bazan daukar maki raini ba,
Wani irin harara na watsa mata na ke baki isa ba wallahi,
Na juya zan bar dakin ina cewa kindai ji kunya wallahi mace bazata iya tsayawa tayi girki ba sai an girka tazo ta cinyewa mutane, don rashin kunya,
Nafito daga dakin fuuu muka hade da Yaya Abubakar wanda yafito kai Baba Wadda masauki,
Da mamaki yake kallon na ya na cewa a zuciyar shi may yakawo ni dakin Salawa a wanan lokacin haka ?
Itace tafito bayana tana cewa wallahi ni sai in maki dukan tsiya,
Ganin Ya Abubakar a tsaye tai saurin cewa yauwa Sweet Oga dama ina son in fada maka cewa Wallahi kajawa yarinyar nan kune,
Don muna auren ka a tare, does not means raini da rashin mutunci zai shiga tsakanin mu,
Yace cikin daga murya wai may ke faruwa ne haka duk kun kasa yi min bayani,
Salawatu tace, wai kawai sai gata tafado min daki tana tambayana cewa ina abincin da ta aje a cooler,
Ni ce har don samun guri zata zo har daki takawo min, rashin mutunci wai naci abinci,
Ya Abubakar yace to ke kinci ne ?
Tace na ci mana tunda angirkane don aci,
Kece jika girka da zakici au dear don bani na girka ba kenan bazanci ba,
Na fito daga kitchen ina cewa kawai na girka abinci sai ki zo min kamar shonike ki kwashe abincin, gaba daya batare da ma kin raga mun ko da kadan ne,,
Wani tsawa Yaya Abubakar ya daka min yana cewa ke Meenat ban son hayaniya fani a gidan nan,
Don kin dafa abinci taci shi har zai kawo fitina haka ?
Nace to ai yaya itace ya kamata ta girka muna muci amma tasa kai tafita tabar gidan,
Nima don zuwan Baba wadda yasani girkawa kada yazo aji kunya,
Ya Abubakar yace OK shine, kuma akace bayan shi kada wani yaci abinci ko ?
Nace yaya abinci na ne fa da nake son ci insha magani
Look Meenat bana son fitina for god sake kubarni in huta please ban so banso
Ban iya çewa komai ba sai idona da yakawo hawaye a lokaci guda, nake jin wani irin baci rai da mamaki suna cimin zuciya,
Na juta kitchen ina hawaye tare da dan sharewa a hankalo da bayan hannuwana,
Gashi bazan iya kwantawa ba banci ko mai ba saboda irin yadda nakejin cikina yana min,
Na dafa tare da kwashewa na nufi dakina dasu,
Sai da naci nasha sanan na kwashen kayan zua kitchen inda na samu ankashe wutan falon gaba daya ,
Haka ya tabbatar min da cewa maigidan ya kwanta ke nan a lokacin,
Wani irin tsoro naji don duhun da ya mamaye falon gaba daya a lokacin,
Da saurina aje kayan na juya zuwa dakina don sai ina ganin kamar wanan abin zai iya fito min a lokacin,



ZEEE MAKAWA YELWA
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
6⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- ASH -SHAHEED


Daga kwance nake rigingine fuskana yana kallon Ac din dakin da ke sako min ni ima wanda ke sani cikin wani yanayi mai dadi, ga kamshi dake tashi na turaren humra, daki,
Duk da Motsin da naji na shigowa dakina a lokacin, bai,sani juyawa don ganin kowaye ba,
Ya iso gab da gurin da na ke, zaune a bakin gado,,, yana min wani kallo acikin mamaki,
Muryan shi naji yana cewa lafiya kike kuwa yau, ?
Batare da na kalle shi ba nake cewa, lafiy kalau nake,
Hmmm naji yace,
Kamar zai juya amma sai naji muryan shi yana cewa,
Breakfast din Baba Wadda fa,?
Banyi ba na bashi ansa a takaice,
Saboda may ? ya tambaya cikin mamaki
Nace don banice da alhakin badawa ba nagani , yau din,
May kike nufi da hakan ne,?
Ai bani kadai bace da alhakin wanan laluran ko
Wani irin tsawa ya daka min tare da cewa
Ke ni zaki gaya wa magana haka kai tsaye kina rainawa hankali ina fadi ki na fadi ke ma,
Ban yi magana ba sai hawayen da idona ke fitar wa shar a lokaci guda,
Ki tashi ki fita ki girka mai abinda zai karya idan ya dawo,
Daga haka yasakai ya fita dakin a fusace cikin bacin rai,
Ban ce komai ba sai kokarin mikewa da na keyi don zuwa kitchen din,
Na jawo dan karamin gyale na na rufawa kaina tare da gyara daura zani na,
Abinci lafiyayye na hada mashi tare da ni da su Anty sadiya,
Nasa saura a kula don nasan cewa zuwa anjima kadan yunwa zai iya zo min,
Nakai abina daki na gyara gurin da nai aikin a lokacin na juya daki na shiga wanka,
Bayan na fito ina zaune a bakin mirror ina shafa mai don yanzu ba zama yin kwaliya na keyi ba,
Ina kokarin zura wani dogon rigan pepper lace da akaiwa combination,da shi,
Yaya Abubakar ne ya shigo dakin yana min wani kallo amma fuskan shi acikin daurewa yake,
Tambaya na abincin sa saboda yana son fita, ban kai ga bashi ansa ba idon shi ya kai, ga abincin da na zuba a plate saman mirror don yasha min isaka kafin in zauna ci,,
A tsatsaye yafara kai spoon abakin sa,yakai kusan sau biyar da yaci a tsatsaye don da alama sauri yakeyi a lokacin,
Bayan ya aje spoon din,Ya dan juyo gurin da nake tsaye ina gyara dankwalina yana cewa,
Shi zai fita amma da Baba Wadda zasu fita don akwai inda zasu tare,
Murya ciki, ciki nace Yaya lokacin komawa na sokoto fa yayi,
Wani kallo naga yai min na yarinyarga fa kin rainani naci gaba da cewa,
Don da mun koma zamu tafi final teaching practices din mu, inha Allah,
Tankar baiji may nace ba don bai ma nuna yaji din ba sai sa kai yayi yabar dakin,, abin shi
Ganin uana fita baice min komai ba nabi bayan shi da kallo,
Yana fita daga dakin gaba daya nasa wani irin kuka mai tsuma zuciyan mai sauraro ta,
Ina cikin kukan da babu mai rarashi na sai Allah naji anshigo dakin,
Yaya Abubakar ne ya dawo dakin yana cewa inzo mu gaisa da Baba wadda kafin su fita,
Ganin da yai min na kifa ciki ina kuka cikin filo ya sashi tsayawa yana kallo na acikin mamaki yana cewa,
May ke faruwa ne wai Meenatu ?
Banyi magana ba ya kara jefo min tambaya da cewa,
An maki wani abune wai don tun jiya nake ganin damuwa a fuskan ki,
Nadan tsakaita kukana ina cewa ni gida kawai nake son komawa yanzu,
Murmushin takaici yayi tare da cewa bazaki ba idan kuma kika matsa min karatun ma gaba daya sai ince a fasa yin sa,
Don dama banga amfanin shi ba don ba dai aiki zakiyi ba balle, jin haka yasa na,
Kara gumzan kukana nayi yadda zai tayar mai da hankali,
Da sauri ya juya ya bar dakin hankalin shi a tashe bai iya cewa Baba Wadda komai ba sai kawai ya nufi hanyar fita waje,
Shima Baba Wadda yana ganin haka ya tashi ya mara mai baya suka fita tare,,,

****** ********** ******
Labarin ciwon Anty Sadiya ya iso Birnin Kebbi ko
A, take zance ya fara yawo cikin gari kala,kala, don kowa da abinda yake fadi,
Wasu suce ai kishiyoyine sukai mata su suce ai sherin uwar ta ce,
Ranan da mama Ladi ta samu labari hankalin ta ya tashi sosai, don kada iyayyen Sadiya suji suce ba,a dauki mataki akan ta ba,
Don haka bata tsaya bata lokaci ko ina ba sai gidan Aminiyar ta Hajja,
Don kada taji labarin ga mutane tace ai ba,a fada mata ba,
Amma bayan zuwan ta sai tai mamaki da taji Hajja na cewa ai mai sunan malam ya bugo mata waya
Amma ta fada, ma shi cewa, ai basai ta tura,kowa daga nan ba,
Don a can ai,basu rasa mutane ko amma haka dai zai sa in tura mashi mutun daga nan,
Wama yasan ko may ke damun ta balle adawo nan ana yadda zance kan karya,
Abinda mutum baiji ba bai gani ba ya taho yace shi ya gano acan,
Don haka ni banga abinda za,a ce sai an tura wata ko wani daga nan ba,
Hakane inji Mama Ladi tace amma dai duk da haka da daga cikin yan uwan ta a samu wata a turata, mata can ina ga haka zai fi,
Don fa ranan wuya sai naka ,
Hajja ta tabe baki tana cewa, haka ne amma gaskiya ni babu wanda zan tura daga nan don
Ai fanin, ku, da kuma mijin ta baku rage ta da komai don haka abar zancen tura wani, saboda tana samun kula daga mijin ta ai,
Tun da Mama Ladi ta gane cewa Hajja bata kaunar zancen kwata kwata yasa ta kyale wa,,
Sai suka fara hiran wani abu can daba don sam bata kaunar wanan zancen,
Don zancen yana tayar mata da hankali saboda bata san may zatayi ba i yanzu akai,,
Haka mama ladi tai sallama da ita batare da ta gane komai ba gare ta,
Ga warin hamman Dodo da ya isheta tun zaman ta,


Amma anan cikin gidan mu gidan malam tsoho sai zance ya canza da cewa,
Ai sherin Hajja ce duk yadda akayi ke bibiyan don tunda har malam ya saka bakin shi ciki, zance,
Zance yazowa Mama Ladi cewa ai nayi barin ciki, a kwanakin nan,,
Anan Mama ta fara fitina tana zage,zage tana masifa,
Ita Allah ya tsare ta, da ta hada zuri,a da zuri,an irin Baba samaila,
Da kuma mahaifiyana ita dole Maisunan malam ya sako Meenatu, tun bata kara yin wani ciki ba,
Yanzu shi mai suban malam har may yagani ajikin Meenatu da ya,rude shi har ya afka mata wai harda samun ciki,
Aiko amanan ta ya ishi cikin ya zube don dai Allah yagani ita bazata hada da irin mu ba,
Kuma wanan sherin na malan tsohone shi da yai uwa yai makarbiya harda hada aure tsakanin jikokin shi,
Yakuma rasa wanda zai hada

53 / 61