Advertisements
Chapter 48 Reading TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

TARKO Makircin Hassada by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  Complete Novels

Chapter   48 / 61

141K to 144K   out of 180.5K words

dauka na yayi cak muka,sauko zuwa,bai tsaya tada kowa ba daga cikin matan shi muka fita,
Ja mota a guje bayan ya,wagale get muka,fita zuwa,, asibiti,
Ban san shawaran da yayi ba sai gani nayi ya tsaya kofan gidan su Fattu yana kiran layin wayan Hamza,
Ba,a bata lokacin Hamza ya dauki waya nan yake sheda mai famu waje zamu tafi, asibiti banda lafiya,
Cikin yan mintuna duk suna waje gaba dayan su tare da Maman Bi,u muka tafi, asibitin,
Sai dai tun bamu karasa ba Jini ya balle min faaaaa,
Hankalin Yaya Abubakar yai mugun tashi da Mama ke cewa Jini ya zo min,
Tafurta da harshen yare su tana cewa Hamza bari ciki nayi,
Ya fadi da hausa yace barin ciki subbahanallahi, cikin damuwa da nuna tausayi,
Da sauri Yaya Abubakar ya juyo yana cewa barin ciki Meenatu din,?
Tana da cikine dama ?
Innalillahi ya fara maimaitawa, cikin wani irin tashin hankali,
Shigan mu asibiti ba bata lokaci aka karbe mu inda su ma suke sheda mai miscarriage ne na samu,
Sai da sunyi min allurai tare da bani gado barcin wahala ya dauke ni ban san yadda akayi ba,

Cikin wani irin tashin hankali yaya Abubakar yake don tun zuwan mu asibiti bai zauna ba
Sai huci ya keyi yana wani furzar da iska cikin tashin hankali,
Maman Bi,u taga yadda yake don haka ta nufi gurin shi cikin irin hausan ta tana cewa yayi hakkuri yazo ya zauna haka Allah ya nufa,
Hamza ya karaso gurin yana cewa, maigida kayi hakkuri, tunda ta samu lafiya zuwa yanzu,
Yana tsaye ya tokare hannaye shi a saman ginan asibitin kafan shi guda harde cikin guda,
Idon shi duk su canza kala zuwa wani irin ja kamar garwa shin wuta,
Ya najin kamar an rura mashi wuta a cikin jikin shi saboda zafin da ke fita mai,
Ya nisa da karfi yace tare da furtawa kun cuce ni wallahi kun cuce ni,
Gari yadan fara haske saiga Fattu da mijin ta sunzo muna da zannuwa da kuma abin karya wa,
Yaya Abubakar a lokacin yana zaune wajen asibiti zaune saman dogon bencin da aka tanadarwa mutane,
Ya dukar da kan shi sai faman tunane yakeyi cewa abinda ya dade yana nema aduniya ko da yaushe yake kai kukan shi ga Allah ,
Yau shine Allah ya karba masa,addu,an shi amma saboda mugun hali irin namu nai masa sakaci da shi har ya bare,
Mijin Fattu wanda yaya baya gama wayewa dashi bane tsaye gurin shi yana cewa maigida ashe abinda ya faru ke nan kuma,
To Allah ya sauwaka Allah ya kawo wani rabon mai albarka, na moriya,
A hankali can cikin makogwaro Yaya Abubakar ya ce Ameen, daga haka bai kara magana ba,
Sai duk wanda ya kalle shi yasan yana cikin tashin a lokacin don yadda yanayin sa ya nuna, kawai,

Sai musalin tara na safe Anty Sadiya ta ji shiru bai shigo sallaman ta tafito daga dakin ta,
Part dina ta fara dubawa shiru babu alamana a ciki,
Ta dawo, kofan yaya Abubakar dakin a bude yake sai dai babu kowa har bathroom ta bude amma sai bataga alaman anyi amfani a ciki ba,
Take wani irin kishi ya kamata sai tana ganin akwai inda muka tafi da yaya don jin dadi,
Tafito kofan falo tagani a bude alaman asake ya kwana,
Mamaki karara a fuskan ta don haka ta dauki waya takira nimban shi don taji yana inane,
Dafarko kamar ta share kada ta kira sai dai tace bari taji su inane,?
Itama Sallawatu wace ke saukowa daga stairs a lokacin sai ta ja ta tsaya don sauraro,
Bayan ya dauki wayan babu sallama babu komai Anty Sadiya tace cikin gadara kuna inane haka,?
Asibiti yabata ansa atakaice,
Asibiti ta kara maimaita zancen yace eh Meenatu ce ta samu miscarriage,
Subbahanallahi tace da sauki dai ko yace eh da sauki don jinin yanzu ya tsaya,
Allah ya sauwaka tace wani asibiti ne kuke kuma baku da bukatan komai ko ?
No ki barshi don muna tare da mutanen gidan su Hamza a nan,,
Ok ta ce cikin mamaki da jin abinda ya ce don ita dai wa yan nan mutane sai take masu daukan munafukai, kawai,
Sallawatu dake tsaye a bayan ta bata sani ba sai maganan ta taji har ta firgita, tana cewa,
Su ina yake cewa ?
A cikin hassala Sadiyaya tace mata asibiti a takaice Meenatu ce ta samu miscarriage,
Cikin wani irin murya tace what miscarriage dama tana da cikine ?


ZEEE MAKAWA YELWA,,,,
[8/20, 09:10] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
5⃣8⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL-HAKEEM,,,


Nafarka daga barcin dolen da nayi inadan kokarin bude idon a hankali,
Indon yai min nauyi don haka a hankali nake bude idon don sun min nauyi,
Kallon mamaki nakewa gurin don naga ba dakina bane ai,
Muryan Maman Bi,u da Fattu yasani karasa washe idon nawa
Maman Bi,u wace ke cewa Meenatu kin tashi yaya jikin,
Bakyajin komai yanzu ko ?
Ai anyi arziki don abin yazo da sauki in ba haka ba ai bari wahala gare shi yafi haihuwa wasu suka ce, zafi,
Ban fahknci may suke cewa ba sai ido kawai na zura wa Maman Bi,u din don ban fahince ta ba sam,
Ganin irin yadda nake kallon mamaki yasa Fattu dan dukowa daidai saitin kaina tana cewa,
Meenatu Mama na son fada maki cewa, kin yi barin ciki ne jiya cikin dare ya zube,
Cikin mamaki na kai, hannu na saman mara na ina kallon Fattu, nace ,
Ciki, ?
Ciki fa Fattu ni ce keda ciki ta gyada kai tace kwarai amma kuma ai ya zube, ko,
Innalillahi, wa ina alaihim raj,um, Allahuma ajirni fi musibati wa,akkali,lif,li hairain min ha,,,
Wasu hawaye masu dumi naji sun ziyarci ido duk yadda naso in controlling din su na kasa sai da suka tsiyayo min daga idona,
Daidai lokacin da Yaya Abubakar ya shigo dakin ke nan yana saye da jallabiyan shi tun na dare a jikin shi,
Kallo daya zakai mai kasan cewa yana cikin wani irin tashin hankali sosai,
Yana ganin idona da hawaye yai saurin kau da kai tankar bai gan ni ba,
Sai cewa yayi wa Maman Biu bata complaine, din komai ko da ta farka Mama tace mashi a,a ba komai, banji tace wani abu ba har yanzu,
Yace Doctor ya ce idan babu matsalan komai zuwa anjima zai sallamay mu sai taje gida ta ci gaba da shan maganin, ta,
So ni zan tafi gida inyi wanka in dan karya don banci komai ba,
Tausayi Yaya Abubakar ya bani irin yadda naga ya canza min a lokaci guda,
Don daga yanayin maganan shi zaka gane cewa ya cikin bacin rai sosai,
Fattu ce tafara fita tanawa Mama yaren su sai naga Mama ita ma tafita yarage dagani sai Yaya Abubakar a dakin,
A hankali na juya da niyar in da tashi in zauna sai naji jikin nawa still ba karfi,
Don haka na koma na kwanta tare da lumshe ido na a hankali,
Ya Abubakar ya kula da abinda nake son yi don haka na tsinkayo muryan shi yana ce min,
Kibi jikin a hankali fa don ba karamin jini kika zubar ba,
Idona na kara rintsewa nace Yaya wai da gaske Fattu ke yi bari nayi,
Banji ya bani ansa ba abinda ya sani bude idona ke nan,
Zaune yake a bakin gadon da nake sai hawaye kawai,nake gani yana tsiyayo mashi a fuska,
Why Meenatu why kinsan kina da ciki kika ,,,,
Sai ya kasa karasa zancen shi saboda hawayen da yazo mashi,,,
Mikewa yayi yabar dakin cikin wani irin bacin rai don jin kan shi ya keyi tankar zai suke,,
Yana fita nasa wani irin kuka mai tsuma rai tare da cin zuciya na saka alokaci guda,
Na daina tausayin kaina sai na Yaya Abubakar don mutum babba kamar Yaya yana kuka aikasan abu yai nisa, ke nan,
Mama Bi,u ce ta turo kofan dakin tana cewa haba, haba Meena kada kiyi kuka don, Allah ki yi hakkuri ki daina kuka,
Ai munyi arziki tunda ya tafi ya barki lafiya don naga shima maigidan naki ya tafi rai bace,,
A lokacin itama Fattu ta sako kai dakin tana cewa haba Meenat, ai ki godewa Allah da abin yazo maki da sauki kawai,
Nace cikin muryan kuka Fattu ni ban ma san cewa ina da ciki ba wallahi,
Da ban yarda na biyewa Salawatu mukai fada ba don ina ga shine sanadin wanan barin nawa,
Gaba dayan su sukace cikin mamaki fada kukayi da ita?
Nan na kwashe abinda ya faru na gaya masu yadda tayo cikina da nufin duka na nikuma na biye mata, mukai ta jidali da junan, mu,
Allahu, Akbar inji Maman Bi,u tace ai Meenatu irin wanan fadan na kishiyo yi tsiya yake haddasawa a gida,
Yanzu ma wanan abin kawai ya isheki ishara, don ke ta cuta,
Nashare hawaye na, nace mama bansan cewa, ina dauke da ciki ba,
Mama Bi,u tace, ciki har na wata daya da kwanaki shiyasa ma ki kai wanan jinin kadan,
Ai wanan matar wallahi ta cuce mu don dai, kawai fadan kishine da naci mata mutunci,
Fattu cikin dariya tace Mama ke ma ai yarki nada laifi da ta yatda har suka hada jiki da ita,,
Nan dai akai,ta zance wanda nake jin shi kamar zuban ruwan zafi a zuciya na,

****** ********** ******
Falon gidan babu kowa sai na,urorin da ke aiki, a cikin sa,
Ya fara hawa sama ya ji dan motsi a bayan shi abin da ya sa shi juyowa ke nan,
Sallawatu ce saye cikin wasu yan, kanan kaya duk sun fitar mata da suran jikin ta, fili, kirjin ta ba komai ya shafe plat,
Wani mugun kallo ya watso mata tare da saurin kauda kan shi gare ta,
Sallawatu ta ganshi ta kuma fa irin kallon da yai mata,
Take tasha jinin jikin ta don tasan cewa tun jiya a hake yake da ita ga kuma wani babban zance da ya ahigo ciki,
Yaya Abubakar yana shiga daki ya fada bathroom din shi don ya watsa ruwa,
Ya dauki lokaci sosai yana wanke jikin shi yana tuna irin jinin da yaga yana zuba min ajiki,,
Sosai hankalin shi yakara tashi take yaji wani irin tausayi na ya kama shi,
Don yasan kamar yadda na fadi cewa ban san ina da ciki ba gaskiyan zancen ke na,
Shima da ya girmay ni bai sani ba tayaya ni zan san cewa ina dashi,
Bakowa yaja mashi wanan hasaran ba sai Sallawatu, wace yanzu aure ta ya zama mashi da ya sani,
Sai yanzu zancen malam tsoho kakan shi yake fado mashi a rai,
Yadda malam yadage yana fada mashi cewa bai hanashi aure ba amma ya auri yar asali,
Lalai malam yayi gaskiya auren yar asali shine aure don tarbiya da addini ,
Shi yanzu ba ma zai ce Sallawatu tana cika ibadan ta ba, don baya ganin tanayi,
Amma abaki tana cewa ita musulmace, sai dai bata cika ibadun ta,
Yana, fitowa daure da alwala, ya sa wata rigan ya fara sallah,,
Ya dade zaune a gurin ya na kai kukan shi ga Allah,,
Yunwa yake ji zuwa lokacin ya fito don ya samu abinda yaci,
Nice da girkin a ranan don haka ban gida sai ba wanda yai breakfast daga cikin su,
Har kitchen ya leka ko zai samu wani simple din abinci ya dan ci ba ko mai da zai iya ci gurin,
Zai fito ne suka hade da Sadiya, itama kitchen din zata shiga alokacin,
Au ka dawo a she ?
Ya bata ansa a takaice da cewa Eh,
Ya mai jikin da sauki ko ?
Alhamdullahi ta samu sauki sosai,
Bakuyi abinci ba, ke nan a gidan nan ?
Gaskiya bamu yi ba don banzaci cewa zaku dade haka ba ?
Mamaki kwarai tambayan ya bashi, don baima san ansan da zai bata ba a lokacin,
Har ya kai tsakiya sai ya juto yana cewa kina nufin cewa baku dafa komai da za,a kai masu asibitin ba, ?
Bata bashi amsa ba sai tai shiru don tasan cewa bata kyauta ba sam,
Keys din shi ya kwasa ya bar gidan cikin bacin rai rayuwan shi na mai daci,
Restaurant ya tsaya yasai abinci ya ci sai kuma yai muna takes ways din su,

Ba laifi da ya dawo yasamu idona biyu sai dai ina cikin damuwa a lokacin don haka,
Ya umarce ni da in tashi in ci abinci ba musu nadan mike tsaye duk da ina jinnjiri a lokacin,
Dai taimakon Fattu na, shiga banda ki na gyara jikina,,saidai jinin zuwa yanzu ya tsane min bai zuwa sosai kuma
Jikina dai ne ban jin kwarin shi sosai saboda jiri nake gani da na mike tsayen,
Nadan fara cin abincin amma sai naji ban iyawa saboda yadda nake jin badadi a bakina ga zuciya na yai min baki badadi saboda bacin rai,
Hawaye ne ya,silalo min daga idona duk yadda naso su tsaya min abin baiyi ba,
Fattu ce ta matso kusa dani tana fadi a hankali Meenat kibar wanan hawayen haka please,
Nace cikin dan daurewa Fattu abin da ke sani kuka,shine, idan na tuna da duk yawan hakkurin danayi amma wai saida Salawatu ta kaini ga kasa hakkuri ga al,amarin ta,
Maman Bi,u tace babu komai haka Allah ya nufa wanan ba rabo bane,
Duk yadda suka so inci abinci nakasa ci don haka nakai kwance ina mai rintse idona,
A haka barci ya kara kwasa na yai gaba dani ban san inda nake ba,
Sai zuwa yamma lis Allah ya bano ikon farkawa saidai wanan karon da wani itin matsakaicin yunwa na farka daga barcin,,
Anyi daidai mijin Fattu ya kawo muna pepper soup din kasan rago yaji kayan yaji sosai a cikin sa,
Sosai Maman Bi,u tazuba min kuma nasha da yawa,,
Saura kadan in karasa Yaya Abubakar ya shigo dakin hannu shi daukw da ledoji,
Fuskan shi na gare ni yaje cewa, kin tashi nace masa eh a hankali,
Sai kuma yakai kallon shi ga plate din dake hannu na ina sha,
Gab da gadona ya karaso yana tambayana may ke damuna yanzu nace masa babu komai,
Nan yake cewa yaso a sallamay yau amma yace wa likita yabar ni har zuwa gobe idan na kara jin karfin jiki na, a lokacin,
Maman Bi u tace gaskiyane hakan yana da kyau sosai,

Tare suka fita da, mijin Fattu wanda yau ne haduwan su na farko
Mijin Fattu bayan sun dan fita can kasan wani bishiyan mangoro da ke cikin asibitin,
Yake cewa Yaya Abubakar gaskiya abin ma yazo da sauki don ba karamin tashin hankali bane zuban ciki,
Saboda halin damuwa da Yaya Abubakar ke ciki yau shi da kan shi ke cewa mijin Fattu a cikin yar damuwa,
Kunsan ance idan magana taima yawa kasamu wani yardadde ka fada mashi don samun shawara, ko dan warware damu saboda kunci,
Abinda ya faru tsakanin mu da Sallawatu ya fada wa mijin Fattu din, inda ya kare da cewa shi yanzu ya rasa hukuncin da zai dauka akan mu,
Mijin Fattu cikin kwantar da murya yace mashi,
Hakkuri zakayi maigida don ka ga ita wanan dai itace aka zalunta,
Saboda kaida bakin kace tasamay ta tana aiyukan gida ita kuma bata gidan ma tun safe,
Kadai a takaice ita aka zalunta sosai don wanan barin çikin da tayi ba karamin rashi bane ai,
Amma ita wacen matar, ya kama ka dan hukun tata don tasan batayi daidai ba,
Yaya Abubakar ya kada kai, alaman ya gamsu da zancen mijin Fattu,
Don haka ya mike yana cewa, yagode kwarai da wanan shawaran don shi da farko, so yayi ya sake ta gaba daya, ya huta da tashin hankali,
Mijin Fattu yace a,a ba,a hakana ya dinga hakkuri da mata don su haka su ke, kamar tunkiyoyi,
Daga haka ya ci gaba da bashi shawara akan abinda ya dace da kowacen, mu,
A take Yaya Abubakar yaji dadin zama da mijin Fattu wanda a kullun sukan hadu massalaci amma ba wani, alaka a tsakanin su,
Sai yau da dalili ya hada su har suka danfahinci junan su,
Har zuwa dare suna tare don a tare su ka tafi gida ranan,
Daga gurin da nake a kwance wayana ya fado min a rai sai na tunacewa Fattu ta bani, wayan da safe da ta zo,
Don haka sai na lalaba wayan na a karkashin filon da nake kwance ,
Wayan baida wani enough caji sosai, amma dai zan iya kira dashi hakanan,
Anty Amarya ce nakira ta dauki wayan tana magana acikin fada tana cewa ,
Meenatu wai yau ina kin ka shiga haka tun safe na ke kiran wayan ki amma bai zuwa,,?
Nace cikin murya irin ta yanayin mara lafiya,
Anty Walleh banda lafiya na yau,

48 / 61