Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : Complete Novels
YAURI
Tun safe yau idan ta shiga dakin ta sai ta dinga jin kamar kukan kaza, wace ta haihu,
Amma ita ga tunanen ta kila kazace a bayan dakin ta ke kiwo har take ji a cikin dakin,
Bayan shigar da fitan da takeyi a dakin sai ji take abin ya tsanan ta,
Mamaki sosai takeyi ya akayi har kaza ta shigo mata daki batare da ta sani ba,,
Neman gurin da kazar ke kuka mama Ladi ta fara yi, saboda kukan kara tsanan tawa yakeyi,
Yar ta Samira ce ke taya ta duban kazan, dukawa tayi karkashin gado don taga ni ko da akwai kazar aciki,
Sak kukan a karkashin gadon yake fitowa nan Samira, tadago kai tace wa mama ladi
Mama inaga a nan na tta,boye, don kukan nan, na yaka fitowa,
Shin wai minana a cikin wagga kwallan da nig gani ,
Gaban mama Ladi ne yaba da wani irin dam, a lokaci guda,
Ba abinda yazo mata a rayuwa alokacin sai zancen kwallah da malamin su ya ce kwana arba,in cif ta bude,
In ko ba demuwa ne ya kamata ba tana ganin yau kwana arbain ke nan cif ga lissafin da takeyi na kirga dutse,
Da sauri ta ce wa yar ta ke maza kibar gurin ka ke jiya ko ?
Sai yanzu nat tuna bakazata ba wallah daga waje na sautin ka hitowa ai,
Da mamakin mahaifiyar ta, samira ta dago daga duken da take a karkashin gado,
Kallon uwar takeyi ta ce cikin dan tsoro, mama walle cikin dakin ga na,
Don kega wagga kwallah da nig gani kamar daga ciki naka jin motsi da kukan kazan,
Kai yau Allah ya gwada min yarinya da dumin bazan ,
Shin bana hwada maki cewa ba kazata ba kuma aini hi ma ba anan kukan ka hitowa ba,
Samira dai mikewa tare da nufar kofar fita wajen dakin, zuciyar ta fam da dan zargi da tsoro,,,,
Ita ko mama Ladi, a lokacin tankar ta tsula fitsari a tsaye don tsoro,
A hankali ta dan leka taga ni idan yar nata tabar gurin,
Hanyar fita daga sashen na su ta hango Samiran,
Kira ta sa wa yar nata da sauri Samira ta juyu zuwa kiran maman nata sai dai a zaton ta mama taga kazan da ke kukan ne.
Don dai ita fa tabbas ta ji kukan kaza a gurin, da ta leka kasan gadon mahaifiyar su,,
Mama tace in ni,ji ke hwada ma wani cewa ga abinda mun ka jiya,
Walle yau sai na bata maki rayuwa yau don nasan ki da yawan bakin dumi,
Baki samira ta turo gaba tana cewa kasa, kasa,
Mi ruwa na da wagga maganan shin minzan tai zuwa hwadi ?
Daga haka ta juya abinta tabar gurin zuciyar ta, na mai jin haushin cewan da mama tayi tana da bakin surutu,,,
Da sauri mama taja kofan shigowa dakin ta ta rufe bakin ta dauke da kalman bissimillah ta mika, hannu ahankali ta jawo kwallah,,,
Cikin dan tsoro ta bude bakin kwallah don ganin ko may ye a cikin yake wanan kukan,,,
Zaune yake a office din shi aiki yai mai yawa, don a tsakiyan wata ake,
Irin wanan time din ai,yuka kan yi wa ma,aikata yawa ne, sosai,
Kan shi a duke yake yana fama da rubutu da ke gaban shi,
Massagen su ne ya shigo office din da sallaman shi ,
Mutumin, ya na da kokarin girmama na,gaban shi sosai,,
Duk da yasan cewa ya girmay masu so,sai ba kusa,
Amma hakan bai sa yai masu girman kan kai ba akan aiki,
Hakan ne ya jawo mai,samun alheri ga ma,aikantan da yake aiki tare da su,
Abubakar yadan dago kai don jin anyi sallama an shigo mai office a wanan lokacin da kowa ya natsu ya na aiki,
Duk da yawan daure fuska irin na Abubakar idan yaga baba masinja yakan sake fuska,
A,a baba kai ne tafe shigo ma,na karaso, in ce dai lafiya ko ?
Abubakar din ke tambayar shi ba tare da ya,daga,kan shi daga aikin da yakeyi ba,
Lafiya lau malam sai alheri, dama wani bako ne ke tambayan ka, daga waje,
Shine na ce, barin masa iso ko kasan da zuwan shi ?
Mamaki ne sosai a fuskan Abubakar din don dai shi yasan cewa baida wani wanda zaizo ya samay shi,
Asalima shi tun zuwan shi garin Lagos bai yi aboki da kowa ba,
Iyakar shi daga gurin aiki sai gida sai kuma makwabtan shi da,suke dan gaisawa sama sama da shi,
Cikin mamaki Abubakar din ya kara tambayar baba masinjan shin bakon shine kuwa,
Baba ya dan gyara tsayuwar shi da kyau yace, kwarai kuwa don ma harda sunan ka,da kuma addreshin ka yazo,
Dan shiru ya yi can kuma sai ya ce , ashigo dashi kawai malam mudi,,
Da sauri malam mudi ya juya zuwa, inda ya fito don yai wa bako iso,
Turo, kofan da akayi yasa Abubakar saurin daga kai, don ganin bakon,
Cikin sauri da dago kai, ya mike tsaye,, tare da fadin Baba Wada, da karfi,,
Shima dai Baba Wadan cikin jin dadin rashin shan wahalan da bai yi ba,sosai gurin neman gidan dan yayan nashi yasa shi saurin washe bakin shi,,,
Cikin jin dadi da nuna kulawa sukayi ban hannu da junan su tankar wasu abokai,
Baba daga ina haka, ?
Abubakar ya tambaya cikin mamaki, ?
Ganin bakon nasu ne yasa malam Mudi, masinja ya juya da sauri zuwa, waje,
Ba ai wani dadewa ba sai gashi dauke da kwalban Martina da, take,away a hannun shi,
Wanan Abin yasa Abubakar kara jin dadin malam mudi masinja,
Malam mudi ya kawo wani dan tebur ya aje mai a gaban shi,
Tare da aje abincin a saman tebur din yai wa baba wada wanda ke ta faman raba ido ga office din dan yayan nashi,,,,,,
A tare suka juyo zuwa gida inda Abubakar ke nuna jin dadin shi,
Sai tambayan Wada yake yi labarin kowa a gida, yana bashi ansa,,
Sun iso gida inda suka samu matar gidan kamar kullum a falo zaune, tana kallon TV, ga kuma littafi da cup wanda ke nuna cewa wani abu ta sha acikin shi, amma bata kawar ba ko ta wanke,
Ganin Baba wada bai wani sa Sadiya farin ciki ba sam duk da tagane shi tasan cewa zata iya jin labarin iyayyen ta agurin shi,
Sun dai gaisa sama sama da shi inda hakan bai wa baba wada, dadi ba, sam,
Amma sai dai ya dake saboda ya san cewa ba gurin ta yazo ba ai,
Abinda baba Wada ya fara lura dashi shine, ganin da yayi Abubakar ke ta kokarin, yin hidima da shi,,,
Da mamakin haka ya kwana a dakin da Abubakar ya gyara mai ya kuma kai mai yan abin bukata, na rayuwa,,,,,
A gida hankalin ma haifiyar Wada duk ya tashi don rashin ganin shi da batayi ba tun daren jiya,
Hakan yasa ta duk shiga cikin wani ya na yi don Wada bai taba yin hakan, ba,
Bayan majalissan malam ya tashi ya dan dogaro sanda shi irin wanda malamai tsofaffin hausawa sukan yawan rikawa, zuwa cikin gida,
Wanda sashin malam din kusan shine na farkon shiga gidan,
Shimfidar shi dama a gyare ya ke tun kafin ya shigo,
Da zaran ya shigo ya zauna matan gidan sarakan shi zasu dinga kawo mai gasuwa,
Daga sashe, sashe na gidan suna cewa Baba ho, shiko yana cewa ingwaiyya,
Idan kuma jikoki ne sai su ce A ho, Baba, sai yace shin wata, ta,
Mai shi zai fadi sunan shi sai tsufon ya ce a,a to ke ta,
Ko kuma ya ce kai na , ho dan nema, bakai barci ba, shin,?
Sai bayan duk kusan yan gai da baba malam sun gama sintirin su,
Sanan matan malam suka iso gurin shi,
A lokacin yana kokarin gyara zama da kyau don Abinci da ta gabatar mai da ruwan sha,
Sai bayan ya gama ci ne san,nan maman Wada ta kawo zancen rashin ganin dan ta tun daren jiya,,
Shiru malam yayi don shi ya ma riga ta gane cewa Wada bai gida tun dare, don ba da shi suka yi sallah asuba ba yau,
Maman tace walle tun dazun jiran ka dai ni kai ka, taho malam in hwada maka,
Shin saratu inba abinki ba yanzu da dare na ki hwada min Wada bashi gida ko, ko ya bata,
Da ina ki,ka son in, hwaro?
Da sauri tace
"Ko, ni an malam gani niyyi kana cikin jama,a shinas,sa ban hwada maka ba, malam an,,
Nan malam ya fara fada sosai akan rashin fada mai da mama saratu taki yi da,wuri,
Baba Buhari aka fara kira sai sauran yan uwa, inda atake hankalin mutane duk ya tashi a lokaci guda,,,,,
Kusan a tsaye ranan yan gidan suka kwana don dai su a sanin su Wada bai san ko ina iyakar shi cikin gari,
Baba Samaila wanda sai da safe yadawo daga kauyen da ya tafi lodin shanu don kawo wa kasuwan Kalgo da zata ci washegari,
Shine ya fara cewa cewa shin ko dai
Logos na Wada ya tai,
Inda Abubakar,?
Wa, gwada mai hanyan kurmi inji baba Shaibu,
Baba Buhari ne yace,
"Wane, ?
Rabu da dan yau kaji, ai tunda kaji Samaila ya ce haka to a kawai dai,
Malam dake jin muhawaran diyan nashi yace,,
Missa ka ce haka ?
Baba kwanakin baya da ni,ddawo yaka tambayana
Wai nawa na,ka kai mutum Lagos da nan kebbi, ?
Ni tambayai ko wa kazuwa Lagos din shina yace min wai wani abokinai kason zuwa,,,,
Don Allah kuyi hakkuri da,wanan pls ban da caji ne yan uwa,,,
ZEEE MAKAWA YELWA
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
5⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
ARRAHAMANIN RAHEEM
A hankali take kokarin mika hannun ta don ta bude kwallah da aka bata,
Sai duk a cikin tsoro take yin hakan, amma zuciyar ta ya kagu da ta bude saboda tana tsan manin KUDI,NE, ma su din bin yawa acikin, kwallah akai mata , na sihiri, kamar yadda take zato,
Amma tunanen ta, ya fara harbawa ganin ta a cikin dukiya tana yadda take so da KUDI,,,,,,,
Jawo kwallah tayi zuwa tsakiyan dakin ta a hankali, gurin da haske yake,,
Daga tsugunen da take ta mika hannun ta ta bude kwallah a hankali,
Cikin wani, irin gigicewa ta jefar da marfin kwallah a gefe guda tana mai, fadin
INNA,LILLAHI, WA,INNA,ALAIHIM RAJ,UN,,,
Yau naga shiga uku ne Ladidi may na daukowa kaina a gidan duniyar nan,
Kara kai idon ta tayi a karo na biyu don ta dubi kwallah ta kara ganin abin da ke a cikki karo na biyu,,
Amma ina sam bazata iya jure kallon wanan mugun halittan dake a cikin kwallah ba,
Wani irin halittane tankar fuskan mutum dan Adam aciki,
Amma da wasu irin abu bakikirin kamar gashin dabba ko kiya shi suna bin shi,
Ga abin wani jalo,jalo da shi kamar jani in,jaka, yana wani irin yawau,yawau a cikin kwallah,
Da farko taso ta nufi waje da gudu don neman agaji,
Amma kuma sai dan natsuwa ya shigo take tunane yazo mata may zatace wa mutane, akan abin,
Bayan an san cewa wanan kwallah ba nata bane,
Motsi taji kamar za,a shigo sashen nata cikin wani iri dakiya ta jawo marfin kwallan ta rufeshi da sauri ta tura karkashin gado,
Sai wani irin zufan tashin hankali ke tartso mata daga cikin jikin ta,
Waje tayo don ko dakin yanzu bata bukatan wani ya,shiga ciki,
Samira ce yar ta ta dawo daga sashen kanin mahaifin ta inda akwai yan mata har kusan mutum biyu sa,in ta,
Duk da Samira yarinya ce to amma ta dan kula da rashin natsuwan hankalin mahaifiyarta a,wanan lokacin,
Mama halan minana, shin,?
Ko kukan kazan na ka damun ki ?
Mi, kin,ka gani halan ?,,,
A,gani kawai nayi awa hankalinki a tashe, shike,
Ke Samira, walleh bani son diban albarka ke ji,,,
Haka dai ki ka lakako sheri ki azamin,,,
Ko ni mama Allah ya baki hakkuri walle gani niyyi awa, a hargitse ki ke,
Yau Allah ya gwadamin mara,kumyah, yariny,,,,,
Bata kai ga cewa yarinya ba,sai suka ji kukan kazan tankar a tsakiyan su,
Mama Ladi ce ta riga Samira ja da baya a,cikin tsoro,
Samira ma ta biyo bayan ta,a dan tsorace duk da dai ita bata ga abin tsoro a kaza ba,,,,,
Abubakar shi da baba Wada suka shiga kasuwa inda yai mai sayayyan tsaraba masu kyau da tsada,
Wada bai yi tsan,manin cewa Abubakar ya iya yi mai wanan irin tsaraban da yai mashi a yanzu,
Don dai, shi a zaton shi Abubakar iya albashin da zai ishe shi ciyar da iyalan shi ne kawai a hannun shi,
Amma sai yaga yayo mashi tsaraba kamar hauka,
Tun daga malam Manya har, zuwa iyayyen su maza sai kuma matan gidan,
Wada ya sa a,sayo mai yan kayayyaki da zai yi dan sana,a da,su irin wanda babu su anan arewa,
Mota guda Akai mai sheta, har zuwa birnin kebbi shi kadai,
Sai dai tun a mota Wada ke shawaran yadda zai bawa malam labarin irin yadda yaga zanan Abubakar da matan shi, a can Lagos,
Amma kuma yana ganin kamar in ya fadi abin da ya gani a can bai kyautawa Abubakar din ba irin yadda yai mai wanan alherin mai yawa,
Shi ko Abubakar ji yayi kamar kada, kanin mahaifin nashi ya tafi saboda yana son shi a ran shi,
Sai dai kuma tafiyan nashi yai mai dadi don gudun kada ya dade tare da su har ya fahinci irin rayuwan sadiya,
Hakan ne ma yasa baya, yarda, su ci abinci a gida gidan abincin da ke a unguwar su ya kai Wada ya ce duk sanda yake da bukatan abinci ko wqni abu na ci yaje gurin,
Inda yai jinga da mutanen masu shagon abincin kan yadda zasu kula mai dashi,,,,,
Sai da motan su Wada ta fara shigowa Arewa sai wani uban tsoro ya ziyarci zuciyar shi a lokaci guda,,
Take malam Manya ya fado mai a rai, da kuma yadda yabar gida batare da ya fada wa kowa ba,
Tsoro karara ya baiyyana a fuskan shi, jikin shi har dan rawa ya ke yi don bai san da wani fuska zai isa gida ba,
Wata zuciya tace mai ya dake kawai tun da har ya samu bukatar shi ya biya,
Kuma gashi ya samo jarin da zai dinga sana,a ya huta zaman banzan da suke a yar shiya shida abokan shi,,,,,
Ita kan Samira fita tayi abinta inda Mama Ladi ta koma ciki a hankali cikin tsoro ta jawo hijabin ta tare da rufe kofan dakin ta da kwado,
Gidan Hajja ta, sulale ta nufa hankali a tashe mata don duk ji takwyi tankar abin da tagani a kwallan ya na biye a bayan ta,
Mama Ladi hankali a tashe hajja ta gan ta don haka ta ja ta zuwa daki saboda kada mutanen da ke gidan ta masu sayen kaya su ji, zancen su,
Sai da ta gama koro wa Hajja yadda al,amarin nata yau ya wakana tas,
Sai Hajja ta washe, bakin ta wanda ya rine saboda cin gora,
Cikin jin dadi da farin ciki, tace ki ce min aiki yayi kyau ke nan Laduwa,
Wane, irin aiki yayi kyau, in hwada miki abinda niggani da injiyana cikin kwalla,
Aiki kan baci ya yi wallah,
Mama Ladi ce ke fadawa Hajja haka,,
Kamar wace zatai gulma ta matso kusa da, mama Ladi tace,
Yanzu komawa zakiyi, duk inda kaza wadda tai sabon haihuwa wadda kin kaji dodon ki na kuka shi zaki samuwa kitai a yanka maki ko dan jinin shi kadan kin ka samu ki,ka zuba cikin kwallan ya wadatar da ke,
Shi ke nan bukata tabiya Laduwa,
Ido waje mama laduwa, ke kallon, Hajja cikin sarkewan Murya tace, Hajja,
Shin mi, kki ce ?
"Ke san ko mi ki ka hwadi,
Shin, Ni Laduwa ta zan tai yin duk wagga abin da kin ka lissafo min,
Cikin nuna bacin rai Hajja tace ,
To wa kika son ya tai yai maki, ?
In kin ka samu kudin ki dawa za ki bushasha?
Babu ko sallama, mama Ladi ta mike duk da taji muryan Hajja tana magana amma bai sa ta tsayawa ba don sauraren ta,
Sai dai kunnuwan ta ya jiwo mata Hajha na cewa indai har baki bashi abin da yakaso ba walle yau kina rasa wani gidan ku,
Tafe take tana hadawaa da tun tube sai faman sababi takeyi a