Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : Complete Novels
yi har da tulawa, a gurin malam
Sai a lokcin na dan sake fusakana kadan nace ai dole, ne in dai agidan malam ne,
Ya ai Babana yace min kai babban malami ne agidan mu don haka naji yana wa yaya Ibrahim fada
Sai naji ya saki yar dariya yace to ai, Baba samaila Baba na ne ba naki ba ke kadai,
Murmushi na danyi tare da gyada kai na ce shima Baban haka naji yana cewa, wai kai dan shine da yake ji da kai aduk gidan mu,
Da alaman zance yai wa yaya Abubakar dadi a irin yadda naga ya lumshe idon shi,
Can kuma ya bude idon shi a hankali ya kalli gurin da nake tsugune a takure,
Da hannun shi yai amfani gurin buga gefen katifan da yake zaune,
Ya mai kallo na kai tsaye yace zo nan ki zauna,
Idon shi ya na kokarin mu hada ido cikin ido dashi,
Daidai Gurin da ya dan buga da nufin wai in zo inzauna nake kallo a cikin mamaki,
Dago kai nayi don in kalle shi amma sai ya daga min gira alamar eh,da dan rausaya kan shi,
Yace ina malam yace ne kizo ki kula da yayan naki ne wai ?
Wani iri naji a take hankali na ya tashi, abinda ya faru jiya ya fado min a rai, irin yadda yayan namu ya jagwalgwalani a daren jiyan,
Kasa nayi da kaina yayin da wasu zafafun, hawaye suka ziyarci ido na,
Saboda tuno min da abinda ya faru a tsakanin mu a daren jiya,
No, No, bana son ganin wanan hawayen daga yau muddin kina gidan nan,
Ban aune ba sai ji nayi hannun shi a jikin nawa ya,namai jawo ni izuwa gare shi,
Saman ciyan shi, ya zaunar da ni, ya yin da ya ke kokarin daga fuskana,
Subbahanallah, Meenat kukan may kuma a haka zaki kuladain din kina wanan hawaye haka, ?
A hankali yasa hannayen shi yana share min hawayen,
Yana mai kallon fuskana, ya ce, kin ga dakata muyi magana, da ke,
Naga hankalin ki a tashe ya ke da ni Meena har yanzu,
Ko dai, ba kya son zama da mune wai ?
Idan har bakya son yanzu fada min in kira malam da su baba in fada masu sai su san yadda zasu yi da mu,,,
Da sauri na shiga goge hawayen fuskana ina cewa cikin murya mai kama da rada, dan Allah yaya kayi hakkuri kada ka fada masu,
Dariya na ba shi amma sai ya daure yana cewa cikin murmushi,
No ai kawai ki bari na fada ma malam tsoho din kawai don ya aiko a dauke ki,
Da Allah yaya kayi hakuri kada ka fada masu don naiwa Babana alkawari bazan kunya ta su ba, insha Allah,
Tausayi na ne ya kamashi a lokacin da yaji ko may na ce,
To daga yau idan kin gani ki daina tsorata ni ba dodo bane ko mugu, ni yanzu mijin ki ne mai bukatan kulawan ki da kuma neman taimakon ki gurin kula da al,amarin rayuwa na,
Kai na gyada mai alaman na yarda da zancen shi insha Allah zan kula,
Rigar barcin da ke a jikina mai baiyyana surar jiki a fili, don haka komai gashi nan free,
Shi na ga ya tsura wa ido, jikin nawa ido a lokaci guda,
Gurin da ya,ke kallo nai saurin kallo sai na gane cewa kirjina ya tsura wa ido, wanda kunya ne ya kamani,
Idon shi naga ya lumshe tare da sauke ajiyan zuciya
Babu zato sai jina nayi a tsakiyar kirjin yaya Abubakar ya matse ni gam yana wani sauke ajiyan zuciya,
Dadircewa nayi kasancewar hakan sabon abune a guri na,
Amma shi yaya Abubakar, tuni yai nisa da inda yake,
Bai taba samun irin wanan rayuwan ba da har ya gigice a lokaci guda saboda mace,
Sosai hankalina ya tashi amma babu yadda zan yi in kwaci kaina, a lokacin,,
Kawai sai na sakar mashi kuka kamar jiya amma abinda bambanci don yau bai sarara min ba sam,
Kuka sosai nake mai da magiya da kyat na samu yaya ya sarara min
Ya koma, saman gado yana sauke numfashi guda,guda,,
Ya kai minti goma sha a gurin yana sauke nufashi guda guda,
Kukan da na keyi ne ya ke cin zuciyar shi ya mika hannu da niyar ya lalashe ni amma kuma sai ya kasa kai hannun shi gareni,
Don bai san may zai ce indan ya tabani da niyar bada hakkuri ba
Jikin sa duk a dake kamar ya yini a gona, yana aiki,
Gefen da nake kwance ya kalla idon shi ga kitson kaina wanda ya hargitse,
Lalai Aminatu daban ce daban take da sauran mata komai na yarinyar burgeshi ya keyi sosai, komai nata tun tana yarinya special, ne,,,
Dole ne yanzu ya sawa kan shi zama da ita kamar yadda iyayyen su ke bukata,
Da kyat ya mike ya mai,da rigar shi da ke yashe a kasa,
Bargo ya jawo ya rufa min har kai yana mai jin kukan har a cikin ran shi,
Falo ya nufa don ya sha ruwa a fridge saboda zuciyar shi da ya ke jin yana mai kuna,
****** *********** ******
Direct gurin fridge ya nufa ya dauko goran ruwa mai sanyi ya balle marfi ya sawa bakin shi,
Sai da ya kusa shaye ruwan ne yaga kamar Innuwar mutum zaune a saman kujera,
Goran ruwan yai saurin cirewa ya kallon gurin cikin mamaki,
Inda ya taka har zuwa gurin, Sadiya ce zaune cikin wani farin nightgown har kasa,
A hankali yaya, Abubakar, ya ce Sadiya lafiya may kike yi anan cikin wanan lokacin, haka ?
Dago kai tayi fuskanta duk hawaye shabe shabe sai she,shekan kuka takeyi,
Sai wani kallo take masa mai cike da zargi ganin yanayin ta yasa shi daure fuskan shi tama,u,,
Kara maimaita tambayan shi yayi gare ta da cewa lafiya dai ko ?
Cikin wani irin murya tace yanzu Abubakar don ka auri yar uwar ka,shine har zaka fara wulakantani,
Subbahanallahi yace a hanzarce,
May nai maki Sadiya,
Cikin wani irin ya mutsar fuska tace,
Girkina ne yau fa ka barni ka tako zuwa dakin yar uwanka don ku nuna min bambanci,
Tsaki ya ja mai karfi yace ke wace irin mahaukaciya wai Sadiya ?
Sam baki da wayo baki da hankali baki san komai ba banda kwanciya kiyi kallo,
Baya ga rashi ilimin addini harda ma rashin sani ka,idar komai baki sani ba,?
Ita yarinyar da kike ikirarin yar uwa ta ce wace iri ce ita,
Budurwa ko bazawara?
Kwana nawa aka yankewa wa budurwa a yi da ita indan an aure ta,
Sannan Bazawara kwana nawa za,a yi a ta re da ita ?
Tabe baki tayi tare da gyara tsayuwar ta wani bakin kishi ke cin ta a lokacin,
Ta ce yanzu kana nufin cewa sai, ka yi sati a tare da ita ?
Ke dakata na fada maki sai wanan yarinyar ta cika sati guda sanan zan dawo gurin ki,
Zubur ta mike tsaye tana cewa, dama nasan abinda za kuyi min ke nan ,
Gashi ba a,kai ko ina ba har kun fara nuna min,
Rai a bace yaya Abubakar yace, look Sadiya ban son abin surutu na fada maki yadda akeyi kije ki tambaya fakat,
Ya daga goran ruwan shi ya shiga kwankwada kamar yadda ya fito yi,
Nan ya barta ya juya zuwa hanyar dakin na, Meenatu,
Wanda tun fara rikincin su na kargamay kofana don gudun kar ta,shigo tai mun masifan ni ma,
Jin na rufe kofa yasa shi saurin juyawa inda ya fito nan yabar Sadiya tana ta rusa kuka wai ya cuce ta,
Dakin shi ya fada ya wuce zuwa bathroom kai tsaye yai wanka,
****** ********** ******
Hajja ce a cikin damuwa saboda yau gaba daya Dodo ya hana ta shakat kamar zai halakata,
Saboda kwana biyu bai samu abin da tai mai alkawarin samu ba,
Gashi duk yadda yaso shiga gidan wanan bakuwar yarinyar ta hanashi duk ta kona shi da abinda ta keyi duk dare,
Allah Allah ta keyi Asuba yayi tabar gidan zuwa gidan mai,lassa,
Ta yi diban ruwa har ta gaji ta hakkura, takoma gefe tana mai nadama da wanan rayuwan da ta jefa kan ta, a ciki, saboda kwadayin duniya,
Don yanzu ta koma kamar mujiya a cikin mutanen gari,
Ko yaro ke abu yanzu za,ace akai shi wurin hajja manya,
Bata da dama ta shiga taron mata yan uwanta sai su watse su ce ai ita muguwa ce,
Ga dukiya kamar ya kashe ta amma bata iya ci don bata iya amfani dashi,
Gashi yar ta Sadiya dake a birnin taraiya Abuja tana aiko mta da sako jefi jefi,
Idan da tasan da hak gaskiya da bata sa anta acikin fitina ba,
Yanzu tana da buhuhunan shikafa sukai dari, biyu, taa da wake tana da gyada da diyan dorawa,
Amma bata iya kashe su ga harkokin ta idan ka ganta mutsu,mutsu da ita, kamar mahaukaciya don wahala,
Wani kugi da wanan abin boyen nata yayi don azaban da yake ji, shiya kara firgita ta,
Kusan duk mutanen dake a farke lokacin a unguwar nasu sai da su kaji wanan kugin,a dodon Hajja, mutane suka tsorace,,,,
Bai samu shakat ba sai zuwa sallah asuba yasu ya dan lafa acikin randan roban da yake ciki,,,,,,
****** ********** ******
Yau kan a cikin daurewa na, mike saboda karfin hali irin na fulani,
Ina jin jiki amma dole indaure in fita don hadawa yaya abin kari kafin ya fita,
Sai da na tabatar da na gama dafa komai na koma daki na watso ruwa,
Nafito daure da dan guntun towel sanin cewa ni ka dai ce a dakin nawa, ina kokarin daukan wani sabulu don wanda ke aciki ya fadi kasa,
Zaune yake saman sabon zanin gafon dana kara shimfidawa da safe, bayan nai sallah,
Wayana ne a hannun shi yana game din snake a ciki,
Gabanane ya fadi don ganin shi da nayi a daki lokacin,
Wani irin dip naji kamar in dauke wuta ko in shige kasa, don kunyan yadda ya ganni a haka,
Ido ya zuba min, duk sai na rude nakasa koda motsawa,
Da kyat na iya cira kafana zuwa bakin drower mirro, don in dauko sabulun,
Daidai zan taso naji an riko ni tabaya na ji na yi ya rungumay ni tsam a jikin shi,
Ido na a runtse ya zagayo dani muna fuskantar junar mu,
Cikin wata irin murya nake cewa don Allah yaya kayi hakkuri na saka hijabina pls,duk a cikin runtse ido na.
A daidai saitin kunnuwa na naji muryan shi ya na cewa a hannun shi a gashin kaina yana dan yamutsawa a hankali,
May yasa jiya don nafita shan ruwa kika rufe min kofan daki,?
Naji shi ya kara cewa Uhmmm?
Kai na a kasa ido a runtse na ce kayi hakkuri yaya nazata ka wuce ne,
Abinda naji a lokacin ya hanani ko da motsin da kafana,
Ina jin lokacin da ya cire dan guntun towel din dake a jikina,
Inda kyakyawan surar jikina ya baiyyana afili ta yadda zai iya ganin komai nawa,
Wani irin ajiyan zuciya naji ya sauke da karfi hankalisa kamar baya a jikin shi,
Duk abin da ya keyi idona yana a rufe don bazan iya budewa na kalleshi ba, saboda nauyi da kunya,
Hawaye naji suna biyu fuska na a hankali
Kuka again Meenat ?
Why pls?
Ko ba kya so na ne ?
Kai na girgiza mai cikin rufe ido ,
To ki daina kuka Meena ni mijin ki ne a yanzu ina da right din da zanyi duk yadda nake so dake,
Iya wahala na shashi ranan a gurin yayan nawa kuma miji na inji Allah,
Ina jin lokacin da ya gama abinda zai yi yafita dakin nawa,
Da kyat na samu na tashi zuwa bathroom, sosai na gasa jikin ina kiran mugu macuci kawai, jarababbe,
Malam tsoho da su baba sun cuce ni sun hada ni dan barikin mutum,
Wando ko kunya baiji a matsayi na yar uwar shi kuma kaunar shi yake bude min tsiraici haka agaban shi,
Sai naji wasu sabbin hawaye sun kara biyo fuska na masu zafi, nasa bayan hannu na na goge,
Kallo guda zakai min yau kasan na fada sosai don fuskana yai wani zurun,zurun, kamar nai ciwo,
Ina kokarin zura riga a wuya na, naji shigowar shi dakin
Tun daga nesa na fara kokarin mikewa inja baya don kaduwa da tsoron da nayi,
Haba Meenat sai kace kinga dodo ki saki jikin ki da ni please ba zan cuce ki ba fa, ko in zalunce ki,
Cikin wani irin murya nace don Allah yaya kayi hakkuri, ka kyaleni hakana please,
Murmushi ya yi mai nuna yarinya ai yanzu nake ni,
Sa kaya kizo mu karya ke muke jira, awaje,
Ina fitowa mukayi arba da Anty Sadiya wace idon ta yai ja don kuka,
Kau da kai nayi gefe tankar ban ga yanayin ta ba sai da nace ina kwana Anty Sadiya,
Ta ansa min ciki,ciki da cewa, Lafiya,
Ta wani kau da kai gefe da sauri,
Yaya da ke a gefe ya girgiza kai don takai ci
Kujera na jawo na dan zauna a hankali gefe guda,
Sam na kasa sakin jiki inci abincin sai wasa da spoon din hannuna nake yi,
Kur da ido yaya yai min bazaki daure ki kici koda kadan,ne ba ?
Anty Sadiya ce naji ta dangwaran da plate din da take cin irish ta mike zuwa part dinta,
Gaba dayan mu muka bita da ido har ta bace zuwa ciki,
Murya yaya naji ya na cewa, ko inzo in baki a baki ne?
Da sauri nakai spoon guda abaki na, badon naso ba,,,, ,,
ZEEE MAKAWA YELWA,,,
[7/28, 05:45] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
3⃣6⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA,,
ALLAH-AL-MU`IZ,,,
Zaune take a farfajiyan gidan su ita kadai tana tunane,
Duk da a lokacin duhun dare ya tsala ko ina bakikirin za ka ga guri amma ita duhun bai damay taba a lokacin,,
Yau idan zata iya lissafawa kwana kusan hudu ke nan rabon da ta ga Yallabai kamar yadda take kiran shi,
Don dai tun ranan da a,kace anbashi, rikon a counter din su gaba daya,
A yan kwanakin da su ka wuce bai tafiya gida sai tare da ita,
Amma yanzu sai kawai ta ga ya sa kai abin shi ya wuce before ta iso, gurin motan shi,
Mutumin da aka san shi da ko,karin over work a ma,aikantan baki daya, amma yanzu sam ya daina, wanan cikin kwanakin nan gaba daya,
Shi wai wace irin yarinyace ko kuma mata Yallabai din ya aura ne wai da har zata saurin jaye mai hankali haka,?
Dole ta bincika taji ko ya wanan matar take, shin yarinya ce, tsohuwa ce yar kauye ce, ko kuma wai ma yaya take, ne wai ?
Malam Audullahi masinja ne ya fado mata a,rai, gurin shine za ta dan samu wanan labarin amma fa sai ta hanyar, zolaya don taji komai a gurin shi,,,
Da wanan shawaran ne ta mike zuwa cikin dakn kwanan su don ta kwanta kamar yadda kowa ya natsu, don yanzu karfe daya da rabi ke nan na dare,
Washegari a gurin aiko kowa sai harkokin gaban shi ya keyi a lokacin,
Amma ita tunane takeyi yadda zata dan kebe da mudi ko malam Audullahi,
Don duk cikin ma,aikatan su da su biyu ne kawai yake hurda sosai ta gani,
Kamar kullun a zaune suke su biyu suna hira kamar yadda suka saba,
Salawatu ce ta zo cikin shigan irin nasu na yan gayu,
Buje ne na atamfa amai tsaga ta baya har zuwa sharaban ta,
Idan tai tako daya zaka iya ganin naman kafarta a fili,
Dinkin rigar mai umbrella ne har kusan gwaiwan ta mai dan tsawon hannu,
Tana rataye da handbag mai shige da launin kayan,
Daurin dan kwali har a gaban goshin ta, fuskanta ya sha makeup kamar kullun,
Takalman kafarta tsinin shi kamar marfin biro ya ke,,
Tun daga nesa malam mudi ya hade ran shi don dai shi sam baya kaunar wanan yarinyar da bawan Allah ga ,
Saboda ba irin tarbiyan su guda ba kai shi agurin shi basu ma dace ba sam gaskiya,
Da takon ta mai kama da karan kofato ta iso gare su,
Yau, ba, ta tsaya har su gaishe ta ba ,
Ita,ce ta dan sakata a gaban su tana cewa sannu ku fa,
Ya kuke ya kwanan iyali,?
Shikan malam Mudi ya sha toka bai son wani alaka da ita ta ko ina, amma shi malam Abudullahi cikin washe baki ta ke cewa,
Malam Abudullahi duk shan miyar amarya ne yasa yanzu