Author : Dana sani Amarya Category : Complete Novels
rayuwasa.'' so ya ke ya
tuno a ina ta faɗar mai da waya amma ya kasa, je must teach her a lesson, Allah ya ƙara haɗani da ke.''
Allah ne kaɗai ya kai Liyana gida, dan kawai tuƙi ta ke bata ko ganin gabanta, ranta ya ɓace sosai,ka
zageta da komai amma banda rashin tarbiyya tana cikin haka ta ji wayarta na ringing, ''Who's that
idiot?." tare da ɗaga wayar a ƙufule.
Lily cikin muryarta ta ce '' Liya it's time already kuma ba ki shigo ba har yanzu.'' ''I'm not coming.'' tana
faɗan hakan ta kashe wayar.
Wani kalar horn ta ja wanda ya sa mai gadi ta shi a guje ya buɗe gate ɗin a miliyan ta shigo gidan tare da
parker motar ta shigo cikin gidan Neneh na zaune ita da Salimah suna taɓa hira.
''ni dai wallahi a wurinmu da safe ake wannan, ya mutum zai shigo ba sallama kamar jiƙar bob Marley,
ayi mutum ba tsari Allah na tuba.''
''Neneh da na shigo gidannan ban miki magana ba ki bar ni da abin da na ke ji.''
''Ahaf ai sai haƙuri nima haka na yi ta fama da samari a zamanina wallahi, ai na ki mai sauƙi ne.''
Tsaki Liya ta ja tare da kulle ƙofar ɗakin da ƙarfin tsiya.
Cire kayanta ta yi tare da watsa ruwa ta shirya cikin kayan bacci mai tsantsi dan yau ana isha za ta
kwanta.
Salima ce ta shigo tare da kawo mata strawberry hollandia ɗinta ta ajiye mata a bedsides.
''Aunty Liyana Jiddah na kiranki wai a ɗakinsa.'' ''I heard you.''
Tana faɗan haka ta ɗauki wayarta tare da ficewa daga ɗakin.
Kallonta Neneh ta yi ta ce '' masu magana da yawun Queen Elizabeth, an fito kenan.''
''Wallahi Neneh darajar Abbhina da Jiddah ki ke ci a gidan nan, na bar Rufaidhat a gida na zo na huta
kuma ki tiso ni gaba, who does that huh.''
''Salimah maza ki je, can ƙarshen layi, gidan gonan Alhaji Kyari ki tsinko mata tsamagiyya ta mun duka
hankalinta ya kwanta.''
Kallon Nenehn ta yi sannan ta buga ƙafarta ta hau saman stairs.
''Ni na rasa mai Khairatu ta gani jikin wannan ta kamawa Hydar, dan wannan ta fi ƙanjamau illa.''
''Amma ai Neneh ke kika fara yin maganar kafin Mamin.'' Salimah ta faɗa ta na kallon Nenehn.
''yi aikin ki banason shirmen banza.''
Ƙarasawa ta yi ɗakin Jiddah da ke magana akan companyn sa da ake rulling na man gyaɗa a can Lagos.
Zama ta yi kusa da shi ta ce '' Jiddah da ma ina son maka magana da daɗewa.''
As usual he just smiled, sannan ya bata attention, '' Jiddah Please ka taimaka ka yafewa Abbhina abin da
ya maka, we are all humans, we make mistakes, we are not perfect, at times wallahi sharrin shaiɗan ne
ba komai ba, forgive and forget, you are a muslim, let bygones be bygones, please grandpa.'' ta ƙarasa
maganar da hawaye because ba ta ɗaukan abin mahaifinta da wasa.
'' Ya Zahra.'' a sanyaye ta ce ''Na'am.''
''ki ce mai ya zo ina neman sa gobe In shaa Allah, kuma kar ki ba ri Neneh taji am I clear.''
''Yeah grandpa, tomorrow is my birthday anything for me, kuma dama ya ce gobe zai kawo min birthday
gift soo no need na gaya masa ai.''
''Idan kika aminta da ni i promised you kujerar Hajji this year In sha Allah, Allah ya miki albarka za ki ji
saƙona ta wajen mahaifin na ki, and kina da manemi?.''
A rayuwar ta sai yau ta taɓa jin kunya '' Noo i only have friends.'' (Ashe Liya na da kunya ).
😂
''alright.'' daga haka ya cigaba da aikinsa da ya ke kafin shigowarta.
Murmushin ta mai kyau ta yi tare da ɗaukan wayarta ta masa sai da safe sannan ya wuce ta koma
ɗakinta.
Washegari da sassafe tasa Salimah ta haɗa ma ta snacks with cupcakes, da kuma wasu abubuwan
munch it.
Sai kuma juice because yau ne za ta cika 20 years 15 December. Kuma yau Sultan da yayan shi za su zo
gidan Neneh, kamar yadda ya tsara birthday gift ɗinta zai zama shigowan magabata cikin relationship
ɗinsu.
Zoo road tasa driver ya kai ta ta amso ɗinkinta na corset gown ta dawo gidan tare da haɗa komai a cikin
wani ɗan ƙaramin trolly because kwalliya zata je yau ɗin.
Wankan ta ta fesa arround 10 O'clock saboda partyn zai fara from magrib kuma Leena event center za su
yi ita da ƙawayen Lilian dan ita ba gwanar tara friends ba ce ba berekete.
Mint chewing gum ta cilla a baki tare da ɗaukan wayarta ta sa slippers ɗinta ta yi sama ɗakin Neneh ta
na waƙan Ayra star _Bloody Samaritan_ .
A hankali ta tsaya a bakin ƙofa tare da leƙo kanta ta ce '' Tsohuwar manya, na fita unguwa ki sa ka
Salimah ta dafa min fried rice dan Allah.'' ''Fridge za ta dafa ba fried rice ba.''
''Kya ji da shi.''
Daga haka ta fita daga ɗakin tare da kiran Ily dan tare da su je makeup ɗin.
Mukullin motar Jiddah ta amsa a hannun Adnan tare da barin unguwar ba ki ɗaya.
Sai da ta biya ta ɗauki Ily sannan suka ɗau hanyar France Road, wajen TMUAH, makeover.
Sun ɗauki lokaci sannan Abbhi ya zo ya ɗauke su.
Wani kalar sinadarin kyau Liya ke fitarwa, ta yi kyau sosai. Sam ba za ka ce Liya ba ce duk da is not heavy
make-up.
Sai videos ta ke ta na Posting a Instagram because she's not a fan of TikTok dan mahaukatai ne marasa
class, a cewarta.
''Abbhina yau Jiddah ya ce zai yi magana da kai i hope all is well.''
'' kar ki damu kan ki okay.''
ILY dai ba ta yi magana ba she's busy chatting with her friends da ta ke inviting zuwa birth day ɗin.
Sai arround 5 su ka isa gidan, wan da a ɗan kiɗime ya ke dan bai san mai zai tarar ba ya san waye Jiddah,
farin sani ya yi mai ba kaɗan ba.
A hankali ya yi parking motar, idanun Liyana na ta yawo akan wani mota ɗan ƙarami ƙirar Kia Picanto da
ke parke a compound ɗin ga rubutu a jiki _HAPPY BIRTHDAY DAY MAKER_ da sauri ta rungume Abbhin
da ke kusa da ita ta na mai addu'a sosai.
Sannan ta amshi wayarta a hannun Ily ta fara videos ''_I love my Dad, my rock, bla bla bla_.''
(Sai shegen iyayin tsiya).
😂
Shi ya fara shiga cikin gidan Neneh na zaune ana mata tausa.
Ko da ya shigo ya tarar da Neneh da ta ɗago kanta ta gan shi, cikin muryarta na manya ta ce '' Fita, fita,
fita, kar Mala'ikun rahama su ƙi shigo min gidan dallah.''
Ta na ganin Liyana cikin shigar purple material da white stones da ya bi shape ɗinta ya lafe ga nude
make-up da ya saje da fatar ta, ta ce '' wai Nabil ka haifo min skeleton a gida fi sabilillahi du be su kamar
zombies, ita kuma wannan wacece? Ko Rufaidhat ɗin ce wannan?."
Liyana ba ta kalleta ba haka ma Ily da ta ke ta kiciniyar tafiya da heels akan tiles (😅hegiya gayu 😂).
Jiddah ne ya sauko cikin shigarsa ta kullum da walking stick ɗinsa.
A hankali ya ƙaraso ya zauna tare da kiran sunan Abbhi ''Nabil." ''Naam Babana.''
Cikin muryarsa na manyantaka ya ce '' Liyana maza kije bidirin na ki zan sa Adnan ya ɗauko ki.''
'' Okay granny."
Daga haka su ka fita tare da kama hanyar zuwa Leena event center.
Kallon Nabil ya ƙara yi sannan ya ce '' Nayi wa Liyana miji.'' zunbur Abbhi ya miƙe..............
Sorry da bana update kwana biyu yau da zafi na na taho 🥹💎
THANK YOU FOR READING 💜
To everyone who took the time to read The Regret, you’ve just held a piece of my heart in your hands.
Kuna daga cikin dalilin da yasa zan ci gaba da rubutu.
See you in the next chapter of our journey.
With love,
Pending Amarya 🦋
> Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋
> Share for more pages in sharing ɗinku ya yi yawa zan ƙara typing da yawa.
Pending Amarya as usual 🦋 🫠
I really love you readers 💎
> Pending Amarya's book corner Extraordinary Everyday
> Mondays to Fridays from 8am to 12am follow for more 🎊🫂📚> PENDING AMARYA'S BOOK CORNER
EXTRAORDINARY EVERYDAY POSTING LINK 👇 🤫
https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
The Noble Writters ✊
Dedication is our strong
THE REGRET 🙆
when love meets temptation who survives?
The Regret Mallakar pending amarya ce ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani siga, idan hakan ko
ta faru kotu ne zai rabani da ke!!!!
Pending Amarya ni ce satellite ina haska su kamar ring light 😂😂
Mallakar Pending Amarya ce_
NDA DUBDO🦚
My Maiduguri ppl
THIS PAGE IS DEDICATED TO AUNTY KHAIRY AND MY LOVELY FANS, MY LOVE FOR YOU IS BIG, BIGGER,
BIGGEST 🫵🫂
Am in love with you 😂
I won't lie babies 🤗😂 🌚
🦚💎
LONG CHAPTER ✍️
_PENDING AMARYA _
Page 20
Daga haka su ka fita tare da kama hanyar zuwa Leena event center.
Shima Jiddah da Abbhi su ka hau parlourn sama domin tattaunawa.
Kallon Nabil ya ƙara yi sannan ya ce '' Nayi wa Liyana miji.'' zunbur Abbhi ya miƙe, sannan a hankali ya
koma tare da durƙusawa a gaban Jiddah ya na mai alamar roƙo da hannunsa, a hankali ya fara magana, ''
Baba ni nasan mai laifi ne, na amshi laifina, amma Dan Allah Dan Annabi kar laifina ya shafi Liyana, ba
yanzu na ke da burin aurar da ita ba na fi son idan ma auren zan mata ta kai irin 30-35 haka kafin nan ta
mallaki hankalinta, idan na mata aure yanzu, zai iya zama child abuse, kuma law zai iya kamani please
Ba........
Bai kai ga ƙarasawa ba Neneh da shigowar ta kenan ta ce " Da kai da law ɗin kun ci kaza - kazan
ubanku."
Jiddah da ya ke ta kallon Nabil tun da yafara magana ya ce " Umarni na baka ba shawarar ka na ke nema
ba, ta shi ka ɓace min a wuri na gama magana."
" Ai kai ka tsaya jin sa ka ɓata lokacin ka akansa, in dan ta ni ce ai sai dai ya ga invitation card and kawo
masa, kawai dan a fita haƙƙinsa ne a matsayin uba shi ne kawai, amma ai yarinya na hannun mu yanzu
sai yadda na yi da ita Nabil ɗin banza Allah na tuba.'' Neneh da shigowarta kenan ta faɗi hakan.
Shi dai Abbhi kansa na ƙasa ya na jin tausayin Liya na kamasa, yarinya ƙarama haka a kawo mata
maganar aure duk da ace mijin ta ɓangarenta ya fito zai yarda.
Nenehn ta ƙara faɗin ''in ka je ka sanarwa Salamatun, ita kuma uwar daɗin miji, kar ta tashi tsaye, kuma
ka aiko min ita nan gobe da sassafe, zan yi magana da ita, in kuma ka isa kaje ka hure mata kunne.''
''wacece Salamatu kuma?." Nabil ya tambayi Nenehn, ''Matarka mana, sallamamiyya, sannan zuwa sati
mai zuwa za'a sa ka rana.'' maza ta shi ka fice min.''
''sai da safe.'' ''mu kwana lafiya.''
Ɓangarensu Liyana waƙoƙin afrobeat ake ta saki a hall ɗin , ga komai is white and purple hatta color , ɗin
wutan..
her favorite artist aka saka wan da hakan ya sa ta fara bin waƙan _O. B. O. Baddest, it's Davido_ camera
man na mata video , komai na masu aji suke yi, ga shampaign, ga kayan ciye ciye, dan ita ta wani manta
da wani Sultan, shagalinta kawai take yi.
An ci an sha sannan an yi pictures, daga haka ita da Ily su ka hau mota su ka koma gidan Neneh, gidan
shiru ba kowa a ƙasa sai Tv da ke ta aiki.
Ɗakinta su ka nufa tasa Ily ta yi wanka sannan itama ta yi.
Ko da ta kwanta da niyyar bacci miss calls ɗin Sultan sun kai 100 , ga text messages berekete.
Ba ta bi ta kansa ba dan ta san ba ɗagawa zai yi ba.
Kasa bacci ta yi, saboda kalmar ''Mara tarbiyya da kamun kai da ke ringing a brain ɗinta, Dan sai da ta yi
shagalinta hankalinta ya kwanta.
''Allah Nagode maka dana mari wannan jar fuskar .''
Daga haka ta hau online ta ɗan yi chat kaɗan tare da sauka ta ja blanket ta na ƙara jin mauryarsa a
kunnenta.
Washegari da sassafe bayan an gama komai na gidan Liyana bacci ta koma , dan ta gaji sosai ga kanta da
ke mata ciwo.
Ɓangaren gidansu Hydar kam tun da ya dawo mamaki da al' ajabi sun hana sa ta ɓuka komai, is he
dreaming? Numfashi mai nauyi ya furzar tare da ɗaukan mack book ɗinsa ya gama abin da zai yi da
dealers, sannan ya cigaba da zaman shi ya na daddanna waya, amma still ya ma kasa concentrating,
saboda saukan marin da ya ke jin sa har yanzu a fuskarsa.
Washegarin ranar.
Sultana ce ta shigo tare da faɗin ''Yaya Hydar, Abuh na kiran ka.'' gyaɗa kai ya yi tare da saka slippers
ɗinsa ya nufi ɗakin Abuh.
Bayan ya shigo da sallama, kallonsa Abuh da ke tare da Mami ya yi sannan ya sakar masa murmushi, shi
ma murmushin ya yi tare da zama a ƙasan Turkish carpet ɗin parlourn.
Sai da ya kalli fuskan iyayen nasa, sannan a hankali ya buɗi bakinsa ya ce ''Good morning Maami, Good
morning Abuh.'' ''Mornig son.'' iyayen na sa su ka haɗa baki wurin faɗa.
Sai da suka mai kallon some seconds, sannan a hankali, Abbuh ya ce ''Aliyu.'' a hankali ya ɗago kansa ya
kalli Abbuhn dan ya san everything serious, directly name na shi ake kira, from that stage da aka kira
sunan sa ya san everything is serious, kuma babu maganar ma kar ya yarda, dan last last, ran shi ne zai
ɓaci.
''Tunanin mai ka ke haka Papa.'' Mami ta tambaye shi.
''Nothing much maami.''
''Okay Papa, daman is about your wedding preparations.''
''Buh Mami, ni ai ban fitar da kowa zan aura ba, kuma na ji kina wedding preparations.''
Ajiyar zuciya Abbuh ya sauke, sannan a hankali ya ce ''kar ka bani kunya mana zaki, mun zaɓa maka mata
ne dan mun yarda da tarbiyyarta da nasabarta, jiƙar Neneh ai abin so ce a wurinka, don't do that son.''
Kallon Mami ya yi sosai, sannan ya ce ''Mami am not ready, wallahi, ta ya ma za'a ce ni zan yi aure
imagine, it doesn't make sense at all."
" Son ba za ka iya share min hawayena ba kenan, we have already discussed this with her parents please
don't do this to us son."
" Son our last alfarma please."
" Ni Mami stop saying this please Dan Allah."
" Then ka aminta da zaɓinmu."
"Mom."
"Son."
"I can't do that."
"You can son, just try."
Ɗauke kansa ya yi ya cigaba da danna wayarsa.
Muryar Mami ya ƙara ji "please son."
"Mami ga Sultan ku basa ita mana, why me."
" It's because ka fi Sultan hankali, and you're the elder, by this time ya kamata ace kana da aure Papa."
" Am not ready Mami."
"It's alright an yi ta lallami ba ka yarda ba, yanzu kuma ko kana so ka ba ka so sai ka aure ta."
A hankali ya ɗago kansa ya kalleta tare da kallon Abbuh.
"Yeah ko ka na so ko baka so it's a most tun da ba za ka mai da mu ƙananan mutane ba, it's impossible,
get out of my site."
Abbuh ya faɗa ya na kai dubansa wurin Mami.
Sai da Aliyu ya furzar da wani numfashi mai zafi sannan ya ce " na yarda zan aureta, buh make sure that
a tabbatar duk wani shagali count me out ba na ciki."
"Better." Mami ta faɗa sannan Abbuh ya ce " sai ka shirya ka je ka ganta dan next week or next month,
za'a yi komai, leave my presence."
Wayarsa kawai ya ɗauka tare da shiga ɓangarensa. Wanka ya yi kawai tare da shiryawa cikin kaftan black
color, with cover shoe, sai hula da ya saka, tare da feshe jikinsa da turarensa na Armani Georgia, haɗe da
Valentino.
Car key ɗinsa ya zara daga wurin ajiyar mukulli da ke jikin wardrobe, sannan ya fice daga gidan ba tare
da ya yi wa kowa magana ba.
Ɓangaren Abbhi kuwa, ya rasa ta ya zai sami Liyana da zancan, dan sun ce idan aka yi auren Liya da zaɓin
su za su yafe masa. Amma ya rasa ta ya zai ma fara mata wannan bayanin, dan shi ya ma manta da ance
ya kira Ammi ta je can gidan, tunanin Liyana kawai ke kansa.
Liyana ba ta tashi ba sai arround 12 thirty shi ma da ke unguwar izala ce kiran Sallah ne ya tashe ta.
Wanka ta yi haɗe da wankan tsarki, sannan ta saka palazzo trousers ɗinta da wani polo shirt coffee color.
Ta maka slippers ɗinta, ta zauna a parlour ta na jiran a kawo mata ƴar everyday ɗinta.
Tun da Salimah ta ga ba ta tashi ba ta haɗa mata milky donut ɗinta da kuma, strawberry hollandia
yourghurt , ta sa mata a fridge, da ta ji sawun ƙafarta ta fito tare da ajiye mata komai yadda aka saba.''
Bayan Salimah ta kawo mata ta ke tambayar ta ina Ily, ''Ai Aunty Liyana da sassafe ta wuce.''
Gyaɗa kai kawai ta yi tare da cigaba da cin kayanta.
Ko da ta gama sama ta haye ɗakin Neneh, tare da kallon Nenehn da ke ta waya da Mansura.
''Ai idan ba haka aka yi masa ba ba zai gane akwai ragowan ƙafiya a kan Babanku ba, sai kinji yadda ya ke
magana wai sai Liyana ta cika shekara arba'in zai aurar da ita kiji fa rashin lissafi irin na shi.''
''Wace Liyanar za'a aurar a 40s Neneh ki daina min fata mara asali wallahi.''
''jai'ra uwar jin sirri, ki daina shigo min ɗaki babu sallama tun da ba gidan ubanki bane ba.''
'' ai ke na kakannin ki ne.''
Katse wayar ta yi tare da faɗin ''Wallahi na jima da sarewa a kanki, gwara na miki