Author : Dana sani Amarya Category : Complete Novels
is a blessing in our lives, we all love her, ba zamu so
wani abu mara kyau ya same ta ba, please Ikimat ki ƙara samun waje a zuciyarki ki yafe min, honestly
our Liyana ta na fuskantar wani hali a wajen mijinta, please Ikimat.''
Muryarta na breaking kaɗan ta ce ''Yaya......, ka daina dawo da hannun agogo baya, komai mai wucewa
ne, yanzu ƙuruciyyar mu ta wuce, tun da ba ta yi mana kyau ba, sai muyi ƙoƙarin sanya tsufar mu ta yi
kyau, ana kawo ƙarshen komai domin fara sabon abu, and I can see changes right now, tun da daman
Allah ba ya bacci Yaya, please ka bar komai ya wuce.'' Ammi ta ƙarashe maganar tare da kwantar da
kanta a kafaɗunsa.
Wayarsa ce ta fara ringing hakan ya sa shi yin tsaki kaɗan tare da ɗaukan wayar, ganin sunan Jiddah da
yake yawo ne ya sanya shi ɗaga wayar da ɗan hanzari.
''Assalamu alaikum, Sabahul khair ya Abbhi.'' Nabil ya faɗa a ladabce.
Cikin sassanyar murya Jiddah ya mayar ma sa martani da faɗin ''Wassalamu alaykum, Nabil duk inda
kuke ku ƙaraso hospital ɗin Aminu Kano yanzun nan.'' ya na faɗan haka bai jira cewar Abbhi ba ya kashe
wayar.
Tun da ya ɗaga wayar zuciyarta ke wani kalar bugu da sauri da sauri, hijab ɗinta kawai ta mayar sannan
ta sanya Ilham kiran Rufaidhat.
Ba ta bi ta kan Ilham ɗin ba ta ja ƙofarta ta kulle ta cigaba da baccinta.
Ilham ita ma tsaki taja tare da wucewa wajen su Ammin sannan suka wuce zuwa hospital ɗin.
Isar su ke da wuya cikin ward ɗin da aka yi musu kwatance suka tarar da su Mami da Sultan da Abbhu,
Amir da mahaifansa shi ma, sai kuma Neneh da Jiddah dake zaune a waje ɗaya, sai su kuma da suka
ƙaraso yanzun.
Ko ina shiru, su sun rasa gabaɗaya wa za su tambaya, dubansu suka ƙara kaiwa wajen ƙofar wani ɗakin
emergency wanda Hydar ke zaune idanunsa sun ɗan kumburo sun yi jaa.
Buɗe ƙofar room ɗin aka yi wasu doctor's suka fito su uku, cire facemask ɗinsa na farkon ya yi tare da
faɗin ''We are sorry to say......'' bai kai ga ƙarasawa ba Hydar ya yi saurin tashi tare da faɗin ''Ko da wasa
kar ka kuskura ka faɗi kalmar da ba ta yi min ba anan.''
Ɗayan doctor ɗin ne ya ce ''Calm down Sir, give him a listening ears.''
''Okay continue.'' Hydar ya yi maganar tare da ƙafe doctor ɗin da ido.
''Gaskiya aikin yarinyar nan yafi ƙarfinmu, because jinin da aka saka ma ta ya ƙara ƙonewa, her condition
is very very critical and cutar na nunawa ma ya daɗe a jikinta a yadda x ray ya nuna.'' ya na faɗan hakan
shi da sauran colleagues ɗinsa suka bar su a corridor ɗin.
Tun da Ilham ta fuskanci da Liyana ake critical condition, ta zube a wajen sumammiyya.
A rikice aka yo kanta Neneh da abin ya ishe ta ta sanar a platform ɗin family house na su gabaɗaya ana
buƙatar taron family duk nisan ka babu uzuri, a gobe ake buƙatar kowa.
Mami is Totally confused a yadda ake ta ambatar sunan Cancer tun shigowarta hospital ɗin, a hankali ta
kama hannun Neneh tare da wucewa office ɗin Doctor Farouk.
Bayan sun shigo nuna musu sit ya yi da alamar su zauna.
A hankali Mami ta ce ''Doctor since nake ta jin kuna ambatar cancer tattare da daughter na, I hope this
is a prank right?, because my daughter is pregnant, and you people are not even talking about the
unborn child.''
Murmushi ya yi sosai sannan a hankali ya ce '' Maama, nothing like pregnancy a jikin yarinyar ki, akwai
Mass ɗin da lulluɓe ma ta mahaifa, a yadda ruwayar wancan result ɗin ya bayar, kuma yanzu ya yi
explode ya zama Cancer and every minutes jininta ƙara ƙonewa yake.'' Doctor Farouk ya gama musu
bayanin tare da miƙa musu sauran test ɗin.
Da sauri Neneh ta amsa tare da faɗin ''Mass ka ce ko masa, meye haɗin shi da jikata da zai shiga jikinta
idan ban da zalunci fisabilillahi.'' ta yi maganar ta na jan majina.......
Manage please 💎🥀
Mutuwa kan kawo canji
''Ya Ubangijina ka basu daman share."
Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟
Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 😂😂
*THE REGRET*
PENDING AMARYA CE ✍️
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
The Noble Writers Team.
**Pending Amarya 51**
What goes around comes around ⏮️⏩
Every ending is a new beginning 🌕
even if the heart disagrees.✅🌕 🤝🦋
🤍🫧🤧
Not edited 🌟💔🥹
****
Da sauri Neneh ta amsa tare da faɗin ''Mass ka ce ko masa, meye haɗin shi da jikata da zai shiga jikinta
idan ban da zalunci fisabilillahi.'' ta yi maganar ta na jan majina.......
Murmushi ya yi sosai sannan a hankali ya ce '' Maama, nothing like pregnancy a jikin yarinyar ki, akwai
Mass ɗin da lulluɓe ma ta mahaifa, a yadda ruwayar wancan result ɗin ya bayar, kuma yanzu ya yi
explode ya zama Cancer and every minutes jininta ƙara ƙonewa yake.'' Doctor Farouk ya gama musu
bayanin tare da miƙa musu sauran test ɗin.
Da sauri Neneh ta amsa tare da faɗin ''Mass ka ce ko masa, mai haɗin shi da jikata da zai shiga jikinta
idan banda zalunci fisabilillahi.'' ta yi maganar ta na jan majina.
Kauda zancen Nenehn Mami ta yi tare da amsan result ɗin ta na ɗan dubawa a hankali, sannan ta kama
hannun Neneh suka fice daga office ɗin.
Ko da suka fito suna tsaitsaye cirko- cirko, Ilham ta farfaɗo, wucewa Mamin ta yi ta sami Abbhu akan
maganar a fitar da Liyana ƙasar waje tun da likitocin duk sun nuna aikin ya yi ƙarfi da yawa.
Bai ƙi tata ba ya sami Jiddah da Abbhi ya wassafa musu komai.
A take suka yi na'am da zancen, anan take aka fara preparations ɗin tafiyar, duk wasu takardu na rashin
lafiyar na ta sai da aka haɗa su as one documents.
Sannan Abbhi ya bada jininsa har leda biyu aka sa ma ta saboda ta samu wanda zai ɗan riƙe ta kafin a ta
fi a goben.
Fashewa Ilham ta yi da kuka akan ita ma sai ta bi Liyanar, jiki ba ƙwari ta koma gida ita ma ta fara shirye-
shiryen da ya dace.
Su Rashanda jikinsu duk a ruɗe bayan sun dawo daga lectures, kamar su yi kuka haka suka ɗinga ji,
Unaisah kam sai da ta zo da yamma duba Liyanar da ba ta iya shaida duk wanda yake kanta.
><><>><><><>>
Hydar kam gwanin ban tausayi, ya rasa mai zai yi ya samu sauƙi musamman idan ya tuno ranar da ya
sanyata wanke wanke kalar shirmen da ta ɗinga yi, wani kalar muryarta ya ji a cikin kunnenta ta na faɗin
''Yaya Alih please.'' wani kalar jaa idanunsa ya yi ya na ƙara hango yadda ta ɗinga rayuwa a gidan time
ɗin da yake China.
''Aliyu.'' Mami ta kira sunansa a hankali tare da dafa gwiwar ƙafarsa, daman already sun riga sun shigo
ɗakin da aka kwantar da Liyanar saboda sauran sun koma gida sanadiyyar dare yayi.
Ɗago kansa ya yi a hankali ya na ƙafe Mamin da jajayen idanuwansa, sannan a hankali ya furta ''Maa.''
tare da sauke idanunsa ƙasa.
''Aliyu are you not a Muslim?, ba ka yarda da ƙaddara ba?, ina ilimin ka yake?, tun jiya yaushe rabon da
kayi wanka ko ka ci abinci na tabbatar tun jiya, please ka cire damuwar nan a ranka, addu'a ya kamata ka
yi ma ta, have you prayed.?"
Bakinsa na ma sa nauyi ya ce ''Noo Maa.''
''And you genuinely wants her to be fine?, za ka tashi ka wuce gida ka yi abin da zai fishe ka ko dai na
mareka a wajen nan.'' Mami ta yi maganar idanunta a kansa.
Jiki a sanyaye ya wuce parking space tare da wucewa gidansa ya na sassanar ƙamshin turarenta da bai
bar motar ba.
Horn ya yi wanda Salimah dake bakin gate da hankalinta yake a tashe ta yi saurin buɗe gate ɗin da wani
mugun gudu ya yi parking motar ta sa tare da wucewa cikin gidan.
Direct ɗakinta ta nufa inda ya tarar da shi komai tsaff, banɗakinta ya shige tare ɗaukan brush ɗin da ya
tabbatar da cewa na ta ne ya yi brush da shi, tare da yin wanka da duk wani abu da take amfani da su,
sannan ya ɗauro alwala ya fito daga cikin banɗakin.
Manta na shafawa ya shafa ajikinsa tare da shafa roll on ɗinta har ma da turarenta sannan ya wuce
ɗakinsa ya sanya jallabiyarsa maroon color haɗe da haɗa wasu kaya a cikin trolly.
Sallolin da ake binsa ya gabatar tare da ƙara komawa hospital ɗin da har yanzu ta na yadda take babu
wani canji.
Pepe soup mai zafi Mami ta zuba ma sa, shima sai da ta masa jan ido sannan ya ci, kamar zai yi kuka.
Har yanzu mamakin yadda cutar ta zo ma ta yake, daga intercourse kuma sai Cancer, anya ba sa hannu a
lamarin nan kuwa.
Washegari kuwa da sassafe suka wuce ta private jet ɗin Abbhu wanda direct a Germany za su sauka
saboda suna da high quality cancer treatment and care.
Yanayin ginin hospital ɗin kaɗai zai tabbatar ma ka da cewa ba ƙaramin hospital bane, dake Abbhu ya
sanar da zuwan su hakan ya sanya suna zuwa doctor Marcus ya sa aka shigar da ita wasu machines na
gwaje gwajen da ya dace ace an yi ma ta dan duk wani takardun Nigeria watsar da su suka yi a gefe aka
fara sabon bincike akan Liyana.
After the test results ✨😪🥹💔
Gabaɗaya test ɗin Abu ɗaya yake nunawa, amma wannan ya banbanta da sauran,dan wannan na
tabbatar da cewa ba lallai ta ƙara jimawa ba a duniya duk da basu san yadda ta Allah za ta kasance ba.
Ilham, Hydar, Mami, gabaɗayansu sun shiga tashin hankali mara misaltuwa, barimma Hydar da
gabaɗaya ya kusa fin Liyanar shiga wani hali, shi idan ma mutuwan za ta yi ta taimaka ta yafe mi shi , da
abin zai fi ma sa sauƙi a rayuwar shi.
Haka rayuwar Liyana ta ci gaba a DKFZ dake a ƙasar Germany gwanin ban tausayi, sam rayuwarta a
kwance take yin sa sannan Oxygen a hancinta, sai wani abu da aka sanya mata shi a hannunta wanda
kamar supporting numfashinta shi ma yake.
Zaune suke a cikin VIP room ɗin da yake su kaɗai, sai Liyana dake kwance samɓal a kan gadon ɗakin
tamkar ba za ta yi motsi ba.
Ilham na zaune kusa da Mami kanta a kan cinyar Mamin da take shafa ma ta kai haɗe da daɗaɗan
kalamai wanda ke ƙara sanya zuciyarta cikin positive taughts game da rashin lafiyar yayarta.
Hydar shi kam ya na zaune wajen gefen Liyana kansa a ƙasa ya na kallon wayarsa wanda dukkanin alamu
sun nuna kamar hoton Liyana ne, time ɗin da take ji da kanta.
Ɗago kansa ya yi daga kallon videon da ta yi shi ita da Ily a wani babban restaurant jikinta sanye da
palazzo trousers fari sai wani top shi ma fari, sai wani faux fur v neck jacket shi ma fari, sai wani heels da
ta saka black da jersey veil black color ya yi ma ta mugun kyau, sai wani sun shade da ta ɗaura akan
black veil ɗin.
Hannunta riƙe da wani ice cream a wani ice cream disposal container mai kyau.
Ɗayan videon kuma a lokacin suna yara da ita da Ily da Ammi har Abbhin a Saudi Arabi, fuskarta sanye
da glasses masu kyau, a ƙasan picture ɗin ta rubuta ''Family over everything ✅ 💎.''
Wasu kalar hawaye ne suka zuba a idanunsa, ya yi sauri ya share su tare da ajiye wayar ya ɗan jinginar
da kansa kaɗan.
Ƙarar heart monitor dake control numfashinta ne ya fara karaɗe ɗakin irin na cewa mutum na gargarar
mutuwa, a firgice ya taso inda har su Mami sun danna bell ɗin kiran doctor, wani kalar ƙara ya ɗinga yi
mai mugun ƙarfi, wanda hakan ya sanya doctor's mayar da su waje suka duƙufa wajen ceto rayuwarta.
Ɗiff gaba ɗaya na'urar ta kawo flat line without any zigzag, ma'ana zuciyarta ya daina bugawa, wani kalar
hawaye mai zafi ya zubo a kuncin Liyanar.
Sannan ta ja wani dogon numfashi haɗe da wani kalar zabura daga gadon sannan ta koma da ƙarfi, da
hanzari doctors ɗin suka fara danna ma ta ƙirji amma kuma Liyana is unresponsive,, Sam ba ta ba da
wani alamar ta na da sauran numfashi.
Doctor Samson ne ya naushi bango da hannunsa tare da furzar da wani iska daga cikin bakinsa sannan a
hankali ya ce ''Guys we have lost her.........''
Manage please 💎🥀
Mutuwa kan kawo canji
''Ya Ubangijina ka basu daman share."
Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟
Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 😂😂
*THE REGRET*
PENDING AMARYA CE ✍️
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
The Noble Writers Team.
**Pending Amarya 52**
What goes around comes around ⏮️⏩
Every ending is a new beginning 🌕
even if the heart disagrees.✅🌕 🤝🦋
🤍🫧🤧
Not edited 🌟💔🥹
****
Doctor Samson ne ya naushi bango da hannunsa tare da furzar da wani iska daga cikin bakinsa sannan a
hankali ya ce ''Guys we have lost her.........''
Ƙara kallon gawar Liyanar dake kwance samɓal suka ƙara yi, wanda hakan ya ƙara tabbatar musu da
cewa mutuwa ta yi.
A hankali Marcus ya zame daga cikin room ɗin tare da nufar ƙofar wajen da su Hydar ke tsaitsaye cirko-
cirko, Ilham na jikin Mami yayin da shi ke tsaye a bakin ƙofar kamar wanda ke jiran sallahu.
Jin ƙarar buɗe ƙofar ya sanya shi saurin shan gaban Marcus tare da tsastsare shi da manyan idanunsa,
face mask ɗinsa Marcus ya cire tare da sauke wani ajiyar zuciya sannan a hankali ya ƙara kai dubansa
wajen Hydar ɗin tare da faɗin ''Sorry to say, I know how you feel bro, buh we have lost your wife.'' ya na
maganar ya wuce Hydar ɗin.
Saurin dawo da shi baya Hydar ɗin ya yi muryarsa na breaking ya ce ''I...... Don't gerr you well, ban gane
abin da kake nufi ba.'' ya yi maganar idanunsa na kawo ruwa.
Shi kansa Doctor Aliyu tausayi ya ba sa, bai iya yiwa Aliyun magana ba ya zare hannunsa tare da kallon
Mami da ita ma wasu kalar hawaye sun fara kawo ziyara idanunta.
Ilham kuwa shock ne ya sameta ta nemi hawayenta ta rasa ga wani zafi da zuciyarta yake ma ta.
Zubewa ya yi a wajen ya na girgiza kansa ya na wani kalar kuka kamar mace, tare da faɗin ''Noo, Fatimah
not now, ba yanzu da zuciyata ta aminta da ke ba.''
Ya yi maganar a zauce tare da fito da wayarsa ya na dailing number Amir.
Ring ɗaya kamar Amir jiransa yake ya ɗaga tare da faɗin ''Aliyu ta tashi?,'' bai kai ga yin wata magana ba
Ammi ta amshi wayar daga hannunsa tare da faɗin ''Aliyu ka bawa Liyana wayar na yi ma ta magana.'' ta
yi maganar itama hawaye na fita a idanunta, dake gaba ɗaya family ɗin kowa ya hallara.
Kukan Ammi da na Mami da yake ji ke ƙara sanya zuciyarsa zafi, da wani kalar murya mai ɗan kauri ya ce
''Liyana is gone Ammi Matana ta mutu.'' ya na faɗin hakan ya saki wayar a wajen tare da jinginar da
kanshi a bango ya ci gaba da kukansa.
><><><>><><>><
Can Nigeria kam tun bayan tafiyarsu Hydar ɗin kullum cikin sadaka ake, ba ka taɓa ganin gidan Neneh
babu jama'a.
Kamar yadda gidan ya saba gaba ɗaya family ɗin shuwa arabi ne a gidan,wasu na addu'a wasu na hira,
har da su Abbuh da Sultan da Amir da iyayensa dukkanin su suna gidan Neneh.
Ganin wayar Amir na Ring ne ya sanya shi saurin ɗagawa saboda ganin sunan Hydar ɗin.
Ya na fara magana Ammi ta amshe wayar wanda daga ƙarshe sai sumanta suka gani a ƙasa, da sauri aka
ɗagata saboda su Abbhun da manyan duk sun fita kai sadaka gidan marayu.
Already daman wayar a handsfree yake, hakan ya sanya su jin muryar Hydar ɗin ya na faɗin ''Ammi
matana ta mutu.''
Gaba ɗaya falon aka saki salati da salallami banda Mama Fatuh da jikinta ya yi sanyi har ya fara
kakkarwa.
Take bowl ɗin wata melon dake hannunta ya faɗi a ƙasa tare da tarwatsewa ta na mai faɗin ''Innalillahi
wa inna ilaihir rajiun, Ni Fatuh, Liyana ce ta mutu.'' ta yi maganar muryarta na dashewa a lokaci ɗaya
tare da yin wajen gidan ta fice daga gidan gabaɗaya.
Kowa na wajen ya sha jinin jikinsa barin ma yadda Ammin ke zubda hawayenta, Umma Mansura ita
kanta ta rasa ya zata yi.
><><>><><>><>
Kamar wani abu ya mintsine shi ya yi saurin buɗe ɗakin dai-dai time ɗin da ake haɗa mortuary injection,
domin kar gawar ta lalace.
Cikin muryarsa mai amo ya ce ''Don't you dare lay your hands on my wife, she's not dead.'' ya na faɗin
hakan ya ƙaraso wajen Gawar Liyana tare da ɗaukan ta a hannu kamar baby, ta yi masa nauyi sannan
kuma ta ɗan sake.
Fitowa ya yi da ita daga ɗakin inda ya tarar da Mamin a corridor jikinta riƙe da Ilham, Ilham da ta kasa
kuka ta na ganin Liyanar kawai ta wani irin fashewa tayi da kuka ta na ƙara ƙanƙame Mamin a jikinta.
Authority ɗin hospital ɗin suka hana shi fita da gawar akan sai sun ƙara tests da wasu binciken, amma
sam Hydar yaƙi yarda akan shi a basa matarsa ya fasa maganin, sai da Mami ta kusan kai masa duka
sannan ya ajiye Liya a kan gadon patients aka nufi X-ray da ita.
After 2 hours.
Result ya fitar da komai na ta lafiya, cikin jikinta shi ma ya na nan cikin ƙoshin lafiya amma babu
numfashi a tattare da ita.
Abin ya mugun ɗaurewa doctors ɗin kai, amma ba su iya nunawa su Mamin result ɗin ba suka basu
gawar Liyanar domin tafiya da ita gida Nigeria.
A cikin jet ɗin ma hannunsa na riƙe da na ta idanunsa na fidda hawaye.
After 7 hours.
Direct airport jet ɗin ya sauka, wanda har su Amir da Sultan sun zo ɗaukarsu dan har ƙarfe tara na dare
ya yi, hannunsa riƙe da ita aka gangaro da gadon patients zuwa wajen da yake dan har da ambulance a
masu ɗaukan su.
Bayan an sanyata a motar sai da yabi ganyen dake jikin motar gabaɗaya ya ciccizge sannan ya shiga
bayan ambulance ɗin shi ma ya na riƙe da hannunta tare da ɗora kansa akan kan Liyanar.
Hawaye na ɗiga a idanunsa zuwa kumatunta.
Har suka ƙaraso cikin gidan bai san an ƙaraso ba sai da aka buɗe ambulance ɗin.
Abbhi ne tsaye da