Author : Dana sani Amarya Category : Complete Novels
jallabiyarsa shi da Jiddah da Abbhu.
Abbhi idanunsa ya yi jaa, he can't even talk sai hawayen da yake zubarwa, kama gadon ma aikatan
ambulance ɗin suka yi tare da yin entrance ɗin gidan Nenehn da ita.
Gidan cike yake maƙil da mutane har da bloggers, ''Ƴar gidan Abbhi is dead.'' ya'n school ɗinsu da exes
ɗinta gaba ɗaya duk suna jiran gawar da sai gobe da safe za'a kaita.
Classy Reeda da Sandy Rash da sauransu are all crying, sun rasa ma ya zasu yi kowa sai posting pictures
ɗinta yake Ya'r gidan Abbhi ta rasu, Liyana bae is dead.
Ko ina a yanzu ya amsa mutuwar Liyana.
A falo aka shinfiɗeta bayan kulle ƙofar ɗakin iya love ones ɗinta ne a falon, a hankali Abbhi ya rarrafo
idanunsa na zubda hawaye tare da faɗin ''Ya'r Abbhinta why?, mai sa za ki tafi ki bar Abbhinki,? Where
are the promises?, First fruit wake up na san you're pranking me.'' Abbhin ya yi maganar tare da riƙo
hannunta ya na karawa a hancinsa.
''Yaya dan Allah kayi haƙuri ka daina kukan nan.'' Umma Mansura ta faɗa hawaye na sauka daga
idanunta itama tare da ɗan jan Abbhin daga kusa da gawar Liyanar.
Neneh kam sai gwale ido take ta kasa kuka sannan ta kasa dariya, duk ilaihirn falon na cike da ya'n
uwanta amma banda Mama Fatuh da Rufaidhat, dan har Yusrah kuka take na rashin Liyanar.
Hydar na can gefe Amir na rungume da shi, yayin da Sultan ke shafa bayansa shi ma duk ransa babu
daɗi.
Ɗaki ɗaya aka ware ma Liyanar inda za'a ajiye gawan na ta a kwana da shi, da Neneh da Umma Mansura
sai Ilham da Unaisah su kaɗai aka ware da zasu kwana da ita.
Ganin duk mutanen falon na ta preparations na binne Liyar da safiyar ranar ya sanya shi barin wajen su
Amir tare da nufar ɗakin gawar na ta.
Auduga na toshe da hancinta da kunnenta ya iso wajen da take wanda Ilham ce ke kusa da ita, matsa ma
sa Ilham ɗin ta yi tare da komawa bayan su da kaɗan.
Mami ce ta fara yi ma sa alamar ya fita da hannu ganin kukan da yake amma ya yi mata biris tare da
ɗauke kansa.
''Hey sweet heart, duk ranar da na mutu, don't cry dan Allah,secondly idan ina da aure a lokacin after 40
days ki auri mijina, thirdly, kin san dai suratul mulk is my favorite surah, and Sheik ya ce ya na sanya
sassauci ga mamaci, try to read that surah for me, to cut it short I will miss you guys.'' Liyana ta ƙarashe
maganar tare da yin ƙwai da chewing gum ɗin bakinta.
''Yaya da wani talk, TOH yanzu mai ya kawo zancan mutuwa?, ko santin chewing gum ɗinne har haka.?"
Ilham ta faɗa ta na ƙarasa saka hular baccinta.
''Ke wasiya nake ba ki, sannan ki kula da yarana abeg.'' ta yi maganar ta na ɗaga video call ɗin Sultan.
''Toh ni ki daina min kalar wannan wasiyar ba na so.'' daga haka Ily ta yi kwanciyyarta akan gadonta
hawaye na zubo ma ta.
Firgigit ta dawo daga tunanin jin an dafa ta amma still muryar Liyanar take ji ta na faɗin ''Ily I'm stuck in
this pot, please hurry up, ILY save me, kar ki barsu su kai ni ƙasa lokacina ya kusa.''
A zabure Ily ta tashi tare da ɗauko Al- K'ur'ani mai girma cikin muryarta mai daɗi ta fara karanta Suratul
mulk.......
Manage please 💎🥀
Mutuwa kan kawo canji
''Ya Ubangijina ka basu daman share."
Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟
Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 😂😂
*THE REGRET*
PENDING AMARYA CE ✍️
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
The Noble Writers Team.
**Pending Amarya 52 countinuation.**
What goes around comes around ⏮️⏩
Every ending is a new beginning 🌕
even if the heart disagrees.✅🌕 🤝🦋
🤍🫧🤧
Not edited 🌟💔🥹
****
Firgigit ta dawo daga tunanin jin an dafa ta amma still muryar Liyanar take ji ta na faɗin ''Ily I'm stuck in
this pot, please hurry up, ILY save me, kar ki barsu su kai ni ƙasa lokacina ya kusa.''
A zabure Ily ta tashi tare da ɗauko Al- K'ur'ani mai girma cikin muryarta mai daɗi ta fara karanta Suratul
mulk.......
><><><><><>><<>
Tun fitar Mama Fatuh ba ta zame ko ina ba sai ɗan ɗishe, gidan Malam Barbushe, sosai ta firgita ainun
da abin da ke faruwa da Liyana, idanunta sun yi jaa kamar zasu firfito saboda firgici, number Rufaidhat
take ta dailing wanda MTN suke ta nuna ma ta network busy.
''Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Ni Fatuh mai na aikata hakan, Ni sam ban so a kashe ki ba Liyana, ban
taɓa tsammanin hakan za ta faru ba, duk tsubbu na ban taɓa kisa ba, sannan na rasa wa zan kashe sai
ya'r ƙanwata, Noooo ba zai yiwu ba.'' ta ƙarashe maganar tare da dukan stiring motar ta ƙirar 206
hawaye na zuba a idanunta a daidai lokacin da ta shawo kwanar gidan Malam Barbushe.
Parker motarta ta yi wanda tun a bakin ƙofar gidan ta fara cin karo da motar Rufaidhat, kutsa kanta ta yi
cikin shagon dake ƙofar wani gida, inda candles ke kunne berekete sai turarukan aljanu da babu adadi ke
jere reras a kan wani ɗan tebur, sai tulu ƙananu dake ɗaure da jan ƙellaye suma da ɗan yawan su, face
wani guda ɗaya dake ware akan wani abu mai kama da mangal amma babu wuta a ƙarƙashin sa.
Wani ɗanyan ƙwai ne a hannun Malam Barbushe jikin ƙwan sanye da wani ƙyalle sai wani ɗan rami dake
kusa da shi wanda alamu sun nuna kamar ƙwan yake ƙoƙarin sakawa aciki.
Cikin muryarsa mai amo ya ce ''Daga zarar na saka wannan ƙwan a cikin wannan ramin, Fatima ba zata
ƙara rayuwa ba sai dai na bayan mutuwa, kin tabbatar a aikata tun da na ɗauko ruhinta daga tulun nan.''
Malamin dake sanye da wani shegen kwalli ya yi maganar ya na kafa Rufaidhat da ido.
''Malam ni kayi abin da ya dace akan yarinyar nan, bayan komai ya lafa zan dawo a naɗe min ita ma
ƙanwarta, ita kuma mahaifiyyarta abin da aka saba za'a ci gaba, dan yanzu ita ce da gidan, amma ni a
yanzu idan akwai gaba da mutuwa toh a shirye nake ka aika min Liyana tun da ita ma wadda ta fara
kawo shawarar ita ma ta ce ko mai ya dace ayi ta bani wuƙa da nama, kai ma kuma bayan kuɗi akwai
ɗayan ihsanin.'' ta ƙarashe maganar tare da kanne ido da kuma lashe leɓenta duk a lokaci ɗaya.
''Ba ki isa ba shegiyya algunguma ya'ta za ki kashe, Malam kar ka saki ka kashe Fatima, saboda babu wani
laifi da ta yi, ni ban san kashe ta zata yi ba.'' ta yi maganar tare da fashewa da kuka tana mai durƙushewa
a wajen.
Kallon mamaki Malam Barbushe ya tsaya yiwa Mama Fatuhn sannan kuma a hankali ya ce ''Idan za ki iya
bawa aljanu kanki su kwana dake na sati ɗaya, a shirye nake da na fasa abin da nake shirin aikatawa.''
Malam Barbushe ya faɗa tare da ƙafe Mama Fatuh da ido.
Cikin sauri ta ce ita ta yarda ko da wata ɗaya zasu yi da ita, ita dai ba zata so a kashe wani ba, da ace
kurciyya ne ta saba yiwa ya'ya'n mijinta.
''Toh haka ake so, ku ci gaba da tsula tsiyarku mutuwa ba yanzu ba ya'ya'n sheɗan'' haka ya yi ta yiwa
mata kirari tare da kiran jinnuh kala kala sannan ya fara magana cikin wani kalar yare.
Bayan mintuna biyar ya fara warware ƙyallen dake jikin ƙwan, sannan ya rufe ramin da yake a buɗe,
bayan ƙyallen ma da akwai wani baƙin zare da jan zare dake tattare da jikin ƙwan, duk sai da yabi ya
warware tare da wanke ƙwan acikin wani ruwa saboda wasu rubutu da suke jiki, na kulle ruhin Liyanar
wani Ya'r tsana ya ƙara zarowa daga bayan sa tare da fara ciccizge allurorin dake jikinta sannan ya zare
pad lock ɗin da aka kulle ya'r tsanar da shi.
''Yawwa an gama abin da ya dace, amma wani hanzari ba gudu ba, idan fa kika kwanta da aljanu babu ke
babu haihuwa.'' ya na faɗin haka ya ci gaba da iza wutan sa akan wani allon ƙarfe ya na ɗiga wasu
turaruka, wanda ke nufin auran wasu yake shirin farraƙawa. (Allah ka mana tsari da tsarewarka ).
😭
" Malam ban gane babu haihuwa ga wanda ya kwanta da aljanu ba.?" Inji cewar Rufy ta na zaro
idanunta.
''Eh mana ko kin taɓa ganin kin yi ɓari tun lokacin da kika zo ɗaukar fansar ɗiyar ki da aka kashe, kin san
dai ba na son ja in ja, ku ɓace min a wuri ko na mayar muku da cututtukan da na ciro dan kutumar
ubanku, in banda ƙarfin Kur'ani da kuma tausayin yarinyar nan wa ya ce muku zan sake ta haka kawai,
yanzu ana can ana ƙona Aljani Gujungu, ma za ku tafi kar ɓacin rai ya shafe ku Dan uban Babanku, shegu
dangin iblis.'' Malam Barbushe ya yi maganar ya na wani kalar fari da idanunsa.
Da sauri suka fita daga shagon Rufaidhat na zagin Mama Fatuh ta na faɗin ''Wallahi Fatuh nima kin san
wacece ni tun lokacin da nake soyayya da Nabil, kin san banda hali, kuma a juri zuwa rafi watarana sai na
fasa komai wallahi.'' Rufaidhat ta faɗa ta na dallawa Mama Fatuh harara haɗe da dungure ma ta kai.
''Wallahi Rufaidhat kema kin san duk kilakancin ki sai dai ki biyo Fatuh, babu record ɗinmu da ban da su,
dan haka ki bi ni à hankali, ko an gaya miki ban san ke kika kashe iyayenki ba, ko an gaya miki ban san
wace uwarki ba Asabe Karuwar ya'n garuwa.'' Mama Fatuhn ta faɗa tare da shigewa cikin motar ta ita
ma.
Wani hawaye ne ya silale ma Rufy, sannan a hankali ta shige cikin motar ta ita ma ta bar wajen jiki a
saɓule.
><><><><>><><><
Tun da aka fara karatun take jin wani kalar Abu na sakin jikinta ji take kamar inda ta maƙale an sakar ma
ta ƙofa ta fice daga wajen.
Motsa hannunta ta yi kaɗan tare da ɗan damƙe hannunsa jin kamar ana zare wasu abubuwan da aka
daɗe da ajiyar su ajikinta.
Jin kamar an damƙe hannunsa ya sanya shi ɗago kansa a firgice tare da amsar Alkur'anin hannun Ilham
ya fara karanta Suratul Baƙara da daddaɗan muryarsa mai sanya zuciya sanyi.
Ya yi kusan minti talatin ya na karatun sannan yaji ta yi wani kalar attishawa tare da buɗe idanunta, a
firgice ya ɗago kansa sannan kuma a hankali ya ci gaba da karatun hawaye na sauka daga idanunsa.
Hannunta ta sanya a hancinta tare da zaro duk wani auduga cikin hancinta, banda Aliyu dake ɗakin
kowannensu a tsure yake barimma Neneh da take ƙoƙarin jike jikinta da fitsarin da ya taho ma ta .
Sai da tayi attishawa sau uku sannan ta fara miƙewa a hankali, tsabar murna Aliyu bai san lokacin da ya
ajiye Alkur'anin hannunsa ba ya rungume Ilham da har ta kusa suma tsabar firgici ba.
Da sauri ya saki Ilham tare da rungume Liyanar da kanta ke wani kalar sara ma ta.
Ita ma ƙanƙame shi ta yi jikinta na wani kalar rawa, sannan a hankali ta ce ''Yaya mai yake faruwa?,
Neneh yaushe kika z.......'' ai ba ta ƙarasa maganar ba Nenehn ta arce da wani gudu kamar ba tsohuwa
ba, ita ma Ily ta mara ma ta baya.
Mutanen falon na zazzaune suna ɗan hawaye da jimami suka ga afkowar Neneh da Ilham cikin falon.
Tambayar su ake mai ya faru amma sam ko wannensu ya kasa faɗar komai, da wani kalar acceleration
Mami da Reedah suka fito daga ɗakin.
Hakan ya sanya sauran mutanen falon tsorata, Ammi da Abbhi ne suka fito daga cikin ɗakin Liyana jin
ana ihu a cikin falon.
Hydar ne riƙe da Liyana suka fito har cikin falon, jikin Ammi na ɓari ta nufo wajen da Liyanar da ke tsaye
fuskarta ya yi wani kalar fayau.
''Iki nah ina za ki je?." Nabil ya yi maganar tare da janyota jikinsa.
''Yaya Liyana nake gani ga ta can, dan Allah ka bar ni na ji ɗimin ya'ta.''
Shi sai a lokacin ya lura da Liyanar dake tsaye jikin Hydar ta na bin mutanen falon da ido.
Jiddah da Abbhu da Abbahn Amir da shi Amir da Sultan ne suka shigo cikin gidan daga amso makara da
kuma linkafani, jin ihu, hakan ya sanya su hanzartawa kar a zo matan ne ke kururuwa akan gawar
Liyanar.
Da sassarfa suka shigo cikin falon a daidai lokacin da Mami ta taɓa kafaɗar Liyanar tare da rungumeta
tsam ajikinta, cikin shashsheƙar kuka Mamin ta ce ''Welcome back to life daughter.''
Ita dai Liyana bin kowa take da kallo kamar wawiya, haɗa idanunta da Sultan da Amir shi ya ƙara razana
gidan, dan sosai Sultan mugun matsoraci ne.
Dan bai san lokacin da ya ɗane Amir ba shi ma kuma Amir ya na neman ta yadda zai cillar da Sultan ya yi
waje.......😂😂😂
Mu haɗe on Monday
Manage please 💎🥀
Mutuwa kan kawo canji
''Ya Ubangijina ka basu daman share."
Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟
Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 😂😂
*THE REGRET*
PENDING AMARYA CE ✍️
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
The Noble Writers Team.
**Pending Amarya 53.**
What goes around comes around ⏮️⏩
Every ending is a new beginning 🌕
even if the heart disagrees.✅🌕 🤝🦋
🤍🫧🤧
Not edited 🌟💔🥹
****
Da sassarfa suka shigo cikin falon a daidai lokacin da Mami ta taɓa kafaɗar Liyanar tare da rungumeta
tsam ajikinta, cikin shashsheƙar kuka Mamin ta ce ''Welcome back to life daughter.''
Ita dai Liyana bin kowa take da kallo kamar wawiya, haɗa idanunta da Sultan da Amir shi ya ƙara razana
gidan, dan sosai Sultan mugun matsoraci ne.
Dan bai san lokacin da ya ɗane Amir ba shi ma kuma Amir ya na neman ta yadda zai cillar da Sultan ya yi
waje.......😂😂😂
Ita kanta Liyanar tsoron kanta take, a hankali Jiddah ya ƙaraso wajen da take tare da faɗin ''Ya Zahra,
kina raye, Alhamdulillah.'' sannan ya kamo hannunta daga cikin na Mamin ya zaunar da ita a kan cushion
ɗin dake falon.
Har su Sultan na niyyar ficewa daga cikin falon Jiddah ya ce da su su dawo.
Duk sanyin Acn falon sai da gumi ya keto ma Sultan da Amir, sannan suka zauna a hankali nesa da
Liyanar da kuma shi kansa Hydar ɗin.
Neneh kam sam ta kasa zaune ta kasa tsaye kawai jira take taji tak ta fara ta kanta.
Ily da Reedah da sauran ya'mmatan na zazzaune amma ba kusa da su Jiddahn ba, a hankali Jiddah ya
fara magana tare da faɗin ''Ba abin gudu bane dan min kalleta ta tashi, ina ilmin ku yake?, da za kuyi ta
yin ihu a cikin dare kamar wasu ya'n karkara, wannan sam ba dacewa ba ce, ai abin farinciki ne ace
wadda muke kukan kewarta ta dawo cikin ƙoshin lafiya, kuma duk wanda ya yiwa Zahra Mummunan abu
zai koma kansa da yardar Allah, kowa ya nemi waje ya kwanta.'' Jiddahn ya idasa maganar tare da
ɗaukan walking stick ɗinsa.
''Ni dai a wurin mu da safe ake wannan, wa zai nemi wuri ya kwanta a gidan nan, salon na ga wannan
al'amarin a kaina ta na ƙoƙarin ja na mu tafi, nifa daman ta sha faɗa min ko ta mutu sai ta dawo ta
ɗaukeni mun tafi tare, TOH maganar gaskiya ba da ni za'a yi kwanan gidan nan ba Rafiƙ, yawwa.'' Neneh
ta ƙarashe maganar ta na satan kallon Liyana da ta ma ta ƙuriii da ido.
''Ajiddeh ba na magana biyu maza ku nemi waje ku kwanta wa'yanda zasu koma gidajensu kuma suyi
saurin tafiya kafin ƙarfe 12 ta yi.'' daga haka ya wuce stairs.
Hydar ne ya ƙaraso wajen da Liyanar take tare da miƙa ma ta hannu, ganin yadda mutanen wajen ke
ɗan tsoranta sai shi kaɗai da Maminsa hakan ya sanyata miƙa ma sa hannunta tare da manne ma sa ajiki.
Har wajen Ammi ya ƙarasa da ita, wanda a take Ammin ta rungumeta ta na wani kalar kuka mai tsuma
zuciyar mai sauraro.
Da ƙyar ta saketa, ita dai Liyana sai ganin yadda Hydar ke fasin fasina da ita kawai yake, har wajen su
Abbuh da Abbha duk sai da taje sannan suka nufo wajen Neneh, wanda in less than two seconds ta fara
ƙoƙarin hayewa sama.
Reedah kam a daren nan sai da ta saki reel a Instagram da Video ɗin Liya da Hydar ɗin ta rubuta
''Alhamdulillah, she's still alive.''
Daman mutane jiran updates suke, haka Fans ɗin Liya da na Reedahn sukai ta hamdala, kowa na
farincikin ganin Liyanar na hugging mutane.
After 2 days.
Da sassafe Hydar ya tashi dake a gidansu ya kwana Amir dake nace ma ɗakinsa idan zai kwana a gidansu
yau kam a ɗakin Sultan ya kwana.
Duk wannan badaƙalar da aka yi sai jiya Assultanah ta ga news ɗin mutuwar Liyana na yawo a social
media ba ta wani jira ba ta kama hanyar jirgi ta dawo gida ta na wani kalan kuka, ita ma Lily sai a lokacin
ta ga news ɗin a Instagram wanda hankali a tashe ta tashi ta yi hanyar gidan Nenehn tun da compound
ɗin ake nunawa a cikin video ɗin.
Salimah kam tun ranar da Hydar ya zo gidan gaba ɗaya ta rasa yadda za ta yi da rayuwarta, dan ta ji
cewa Liyanar babu lafiya, sai ita ma a ɗazun ta ga cewa news na yawo ya'r Nabil is dead, hakan ya
sanyata kulle ƙofar gidan ta nufo hanyar zuwa gidan Nenehn.
Kusa da Ammi Liya ta kwana ta na baccin ne kawai amma sam ba ta jin daɗinsa dan jinta take kamar a
wajen da ta yi kusan sati a takure, dan sai anyi sadakan uku yadda Jiddah ya faɗa sannan kowa zai koma
gidansa, tun da Liyanar ma lafiyarta ƙalau.
Bayan Ammi ta tasheta da Asuba sallarta ta yi tare da ƙoƙarin komawa