Author : Dana sani Amarya Category : Complete Novels
auren nan na huta, ke
ba aikin fari bare na baƙi, kullum rawa a yanar gizo, wallahi duk rashin ɗan idon fir'auna Asiya ya aura
nutsatsiyya da ita wallahi.''
''Kin taɓa ganinta ai.''
''Fita, fita kar ki min saɓo anan.''
''kin ga ba wannan ne ya kawo ni ba, amma dole na tambaya, wace Liyanar za'a yi wa aure? Bayan ni ban
kawo wa kowa saurayi da sunan xan auresa ba?."
''Jiddahnku ne ya ce ya miki miji, ɗan gidan Alhaji Kyari.''
''Hankalinki ya kwanta ai ko?.'' toh wallahi Neneh in na mutu ke zan kama, Abbhina ba zai taɓa bari a
min haka ba ma nasani.'' ta faɗa tare da murkuɗa baki.
''Shi ya ce a sa sati biyu ai, yau ɗinnan za'a yi komai.''
''Hala nasan rikicin tsohon saurayinki ne ya tashi kike ta imagination yau ɗinnan, bara na yi abin da zai
fishe ni daga haka ta fita daga ɗakin Neneh.
Ko da Hydar ya fita gidansu abokinsa Amir ya nufa can Lamiɗo crescent.
Ko da ya zo unguwar a ƙofar gidansu Amir ya parker motarsa, dan ba daɗewa zai yi ba.
A farfajiyar gidan ya tarar da Amir da ke ta zaune ya na jiransa, shi ma ɗan saurayi da shi kyakkyawa ne
ba laifi.
Bayan sun gaisa ya zauna ya na shan ɗan fresh milk da ya ke glass cup ɗin a hankali.
''Wallahi Hydar da ma ni na samu damar nan ace an samar min mata, da na fi kowa murna wallahi, ka
daina wannan shirmen kawai just focus, babu wani China da zaka koma bayan handling business da ka
barwa managers, kuma komai da ake yi kana gani anan since camera ɗin is connected da laptop ɗinka,
wallahi kawai ka yi sha'ani.''
''You're mad, kawai ka yarda you're mad Amir, ni fa bana sonta, ban ganta ba amma ba na sonta, ni
wallahi har su gama bikin na su baza su ganni ba.''
''Thats your own good oo.''
Tsaki ya ja ya cigaba da kallon Camera ɗin da akai connecting da laptop ɗin na sa.
Ɓangaren Ammi kuwa business ɗinta ta ke yi sosai, babu kama hannun yaro, dan yau akwai kusan gidaje
uku da ke son, Classic Abayas, da hijabies a Lamiɗo crescent, tun safe ta ke kiran delivery guy ɗinta
amma ba ya picking hakan ya sa ta ɗauki mukullin motar ta tare da fita daga gidan gaba ɗaya.
Gidaje biyu ta kai wa Abayas da hijab ɗin, ta na tuƙinta hankali kwance motar ta kashe kanta ba tare da
tasan dalili ba.
Sakkowa ta yi ga ranar da ake tsalawa, mai mugun zafi, duk ya yi mata yawa.
Wayarta ce ta fara ringing, dubawa ta yi ta ga Abbih ke kiranta cikin muryarta mai sanyi da kamala, ta ce
'' tohh lafiya? , yau kuma.''
Cikin muryarsa mai amo ya ce ''Hello, kina ina?. ''Na ɗan ta fi delivering kayane.'' ''Where?."
''Lamido crescent.'' ''in kin kai kije rijiyar zaki ana neman ki.'' '' da fatan dai lafiya.'' ''in kin je kya gani.'' ƙit
ya katse wayar.
'' murmushi kawai ta yi ta na ƙara jinjina al' amarin Nabil ɗin.
Titin tsit ya ke babu napep ɗin da ke gilmawa, ko ina shiru.
Hydar da ke tsaye tare da Amir da ya fito raka sa ya ga wata mata ta ɗan yi backing na su duk da abaya
ce a jikinta.
''Amir ne ya ce is like that lady overthere is searching for help.'' ''ni fa na fita harkar mata a yanzu, za ka
iya zuwa ka gane ma kan ka idan hakan ne.''
''Dude Dan Allah zo muje we won't be local a sanadin haka please, kalli bayan ta da kyau wallahi uwa ce
ta haife mu.''
''OKAY.''
Daga haka su ka nufi Ammi dake tsaye ta na duba ko Allah zai sa ta samu number mechanic a wayarta.
''Assalamualaikum, good noon Maa.'' Amir ya faɗa, Juyowa ta yi tare da faɗin'' Noon My dear.''
Ɗago kansa ya yi shi ma ya gaidata.
Sannan su ka tambaye ta mai ya sami motar.
''Wallahi Son I don't Actually know, kawai motar ta tsaya, ban ma san ya zan yi da shi ba .''
''Hydar ɗan zo ka duba tun da kai ne ke hawa lexus.''
A hankali ya ta ko tare da buɗe gaban motar ya ɗan yi taɓe-taɓensa sannan ya ce ta shi ga ta kunna, a ta
ke motar ta kunnu.
Murmushi ta yi tare da faɗin ''Thank you Son, What's your name?.'' ta faɗa tare da nuna Hydar, '' Am
Aliyu buh ana kirana da Hydar.'' ya yi maganar ba tare da ya kalli fuskarta ba, dan haka kawai nauyinta ya
ke ji.
'And you?." Ta nuna Amir. ''Am Umar Maa.'' '' Ku duka babana ne kenan motar ta ta buɗe tare da
ɗaukan dubu goma, ta bawa Aliyu dubu biyar, shima Amir ɗin dubu biyar.
''toh ga shi ku sa yi chewing gum.'' ''murmushi Aliyu ya yi ban da Umar da ya fara dariya ya ce Maami no
need, we are very grateful.'' ''chicken change right?, lemme add more.''
''Noo Mom wallahi, Alhamdulillah, kawai dai we are now men not boys, that's why.''
Da ƙyar ta samu su ka amshi kuɗin, sannan ta shige motarta ta ɗauki hanyar delivery ɗinta.
Shima Aliyu ya ɗauki hanyar gidansu five kee ɗinsa a hannunsa (za ta yi maka rana ).
😂
Bayan ta yi delivery ɗin gidan Neneh ta kama hanya amma, yanayin unguwar ya canza.
Ko da Aliyu ya koma bai fi minti talatin ba Mami ta aike sa siyan fruits, Dan sun ƙare a fridge.
A hanyarsa na fita da ga unguwar su ka yi clashing da wata mota zuge glass ɗin ya yi ahankali itama ta
zuge nata. ''Murmushi Ammi ta yi tare da faɗin "You again son?, you live arround here?." ''Yes Maa, ina
wuni." "An wuni lafiya." Su ka ɗan gaisa sannan kowa ya yi hanyar sa, dan shi rumfar Shehu zai je siyan
fruits.
A hankali ta ke gangara motar na ta akan titin da ke malale da kwalta, saboda gidan Nenehn ya ɗan shige
mata duhu.
A side ɗin right hand ɗinta ta ga Aliyu shuwa Arabi's mansion, hakan ya ba ta dama da dalilin karkatar da
hancin motar ta ta danna horn a cikin gidan.
Mai gadi ne ya buɗe, tare da tambayarta wa ta zo gani, sai da ta ba shi amsa, sannan ya barta ta shiga
cikin gidan.
A hankali ta yi parking tare da futowa cikin shigarta na Abaya, ta nufi in da ta fi tunanin entrance ne,
shigarta kam ya yi dai-dai, da fitowar hajja daga kitchen dan yau Salimah ba lafiya,.kuma slay queen na
bacci.
" Duniya kenan, ƴar ɗakina ta yadda ni, toh yanzu ke miye riba, wallahi kin bani kunya har wannan mai
fuska kamar jan ƙosai ya samu raba ni da ke wallahi kin ji kunya, ki tsaya anan na kawo miki ruwa, ƴar
daɗi miji, maganar da zan miki second ɗaya ma wallahi ta yi yawa, Allah na tuba an gaya mana miji, har
ya gama dai ƙuruciyyar sa bai min kishiyya ba." Neneh ta faɗa ta na kama kujerar falon, ta zauna akansa.
Durƙusawa Ikimat ta yi har ƙasa ta gaida Nenehn, sai da ta amsa sannan ta shigo ta zauna a ƙasa.
"Bara na kawo miki ruwa ƴar albarka, mai shiga tsakaninmu sai Allah, ko Maimu ba ta iya ba."
" Neneh da kanki za ki kawo min ruwa? Ina Liya, ina ƴan aikin?."
Har ta tafi ta dawo ta zauna.
"Liyana ko masifa da kata'i, ai ƙarar ta zan ba ku daman, bata gaida ni, in ban da zagi, da cin mutuncina a
gidan nan da ta iya.
Akwai ranar da ta sa aka tsinko mata tsamagiyya wai za ta zane ni fa in gayamiki, nikam nace,hoho hoho
idan ƴaƴan Ikimat ba su ji kaina ba wa zai ji kaina."
"Ita Liyanar?."
"Zan miki ƙaryane?."
"A'a Neneh."
" Ta shi kije kiyi girkin ma na fasa."
Ta shi ta yi ta shiga, kitchen ɗin da ya ke a goge sai sanyin tiles ya ke fitar da ƙamshin kayan ƙamshi, dan
Neneh na son su sosai.
Cikin minti talatin ta gama haɗa cous-cous da ya sha goat meat, sai ƙamshi ya ke.
Ba su jima da cin abincin ba, Neneh ta fara sanar da ita an yiwa Liyanar miji, da kuma abin da Abbhi ya
ce.
"Toh Neneh Allah ya tabbatar da Alkhairi."
"Amin."
Har Ammi ta tafi Liyana ba ta ta shi ba itama kuma ba ta tambaye ta ɗin ba.
Sai da aka kusan kiran magriba sannan ta tashi ta nufi bathroom ta yi wanka tare da saka kayan bacci, sai
da ta sha maganin mura sannan ta koma baccin ya ƙara ɗaukanta.
Washegari da safe ma ba ta wani kula Neneh ba dan ba ta jin daɗin jikin na ta tun jiya, ga shi Abbin ya na
ta magana akan ta yi haƙuri ta rasa ma da uwar mai za ta haƙura.
A kwana a tashi asarar mai rai hausawa kan faɗa, yau aka sa ranar Liyana da Hydar wan da gaba ɗaya a
gidan Nenehn aka saka nan da sati huɗu biki.
Kuma har yanzu ba'a sanar da Liyana bikin ba, kuma har yau sai dai su haɗu da Sultan a gidan Lily ko
kuma joint tun da ba school.
Yau dai kam kamar kullum shigarta na palazzo trousers da long sleeve shirt ne a jikinta sai hula black
color da slippers ɗinta baƙi, car key ɗin motarta ƙirar Kia Picanto ta ɗauka tare da ɗaukan Atm card
ɗinta, ta cilla mint chewing gum ɗinta a baki, ko da ta fito ba ta tarar da Neneh ba, dan haka wucewa ta
yi kitchen ta ɗan ɗauki bottle water ta sha rabi sannan ta nufi hanyar motarta, ta ajiye tare da tada
motar, mai gadi ya buɗe mata ta cilla motar titi, tare da sakin waƙan _Asake, terminator._
Ta na bin waƙar ta na gyaɗa kai har ta ƙaraso kasuwar kwari, dai-dai wani ƙaton shopping plaza na
atamfofi da abayoyi , mai suna _LIYANA PASSION CO._ ta tsayar da motar ta, tare da futowa ta nufi cikin
wurin da zamu iya kiransa da kasuwa, dan babu abinda babu a ciki na kayan da mata ke sawa ajikinsu.
A hankali ta sauko tare da shiga cikin babban boutique ɗin, Abbhi da ke tsaye ya na magana da
receptionist akan duk wanda ya zo nemansa in dai ba Liyana ba ce ace baya nan ya na companyn
atamfarsa.
A hankali ta tako tare da rufe masa idanu.
Murmushi ya yi sosai sannan ya ce "Day maker."
A hankali ta sake masa ido sannan su ka ƙarasa office ɗin sa.
Zama ya yi a CEO chair ɗinsa mai juya mutane, tare da faɗin " Sweet heart, The reason why I called you
here is that......"
Kasa ƙarasawa ya yi dan bai ma san ya ya zai fara ma ta bayani ba , kuma this is the only way out for him,
Dan Jiddah ya rantse idan ba'a yi auren ba babu su babu shi, ita kuma Neneh ya biya ta nonon ta da ya
sha.
He has no choice than ya yi hakan, shi ya rasa mai ya musu da suka ɗauki zafi hakan.
"Abbhi just say it, kar ka ji komai okay, you're my own father, na san ba ka son ɓacin raina buh just say
it."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin " Liya Jiddah ya zaɓa miki miji." Ya ƙarasa maganar tare da runtse
idanunsa, wani kalar bugawa zuciyarta ya yi, arazane ta ce " Sultan fa...........
Sorry da bana update kwana biyu yau da zafi na na taho 🥹💎
Rashin data ne ke sa ni rashin update, ga ciwon wuya amma kuna raina habibties 😌
THANK YOU FOR READING 💜
To everyone who took the time to read The Regret, you’ve just held a piece of my heart in your hands.
Kuna daga cikin dalilin da yasa zan ci gaba da rubutu.
See you in the next chapter of our journey.
With love,
Pending Amarya 🦋
> Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋
> Share for more pages in sharing ɗinku ya yi yawa zan ƙara typing da yawa.
Pending Amarya as usual 🦋 🫠
I really love you readers 💎
> Pending Amarya's book corner Extraordinary Everyday
> Mondays to Fridays from 8am to 12am follow for more 🎊🫂📚> PENDING AMARYA'S BOOK CORNER
EXTRAORDINARY EVERYDAY POSTING LINK 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
The Noble Writters ✊
Dedication is our strong
THE REGRET 🙆
when love meets temptation who survives?
The Regret Mallakar pending amarya ce ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani siga, idan hakan ko
ta faru kotu ne zai rabani da ke!!!!
Pending Amarya ni ce satellite ina haska su kamar ring light 😂😂
Mallakar Pending Amarya ce_
NDA DUBDO🦚
My Maiduguri ppl
THIS PAGE IS DEDICATED TO PRETTY SK ✅🎊
THANKS YOU DEAR ✅
Zan so kije da ni🫂 Babyn bae ai kinsan dani🤗
Baby na you promise say that you no go leave me kar ki yada ni 🤌🙌
Baby zuciyata zo gata 😩 zan kula da ke likeee ƴar auta, so nake kin zamto min mata zo masoyiya 🤧 Soo
tell her ta ko taka a hankali 🥴💔🦧🥀🫵
🦚💎
LONG CHAPTER ✍️
_PENDING AMARYA _
Page 21
Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin " Liya Jiddah ya zaɓa miki miji." Ya ƙarasa maganar tare da runtse
idanunsa, wani kalar bugawa zuciyarta ya yi, arazane ta ce " Sultan fa...........
''Sultan kuma?, which Sultan Liya?."
'' Saurayina mana wanda na ke baka waya sometimes ku gaisa, that fair guy da kake gani a status ɗina,
ka ke tambayata akansa.'' ta ƙarasa maganar ta na gunjin kuka.
Kenan abin da Nenehn ke faɗa gaskiya ne da ɗan gidan Alhaji Kyari ta haɗa ta. Ashe yau ita da Neneh sai
kotun ƙoli ta ji su.
'' Sorry princess, ni ban taɓa kawowa is your boyfriend ba, ni à tunanina is just a normal friend ,
Buh I'm really sorry. Find a place in your heart ki yafe min, please.''
Ta fi minti biyar ta na kukan ba ta daina ba, ta na kukan kuma still ta na taunar chewing gum ɗinta.
A hankali ya ce ''tashi muje ki sha ice cream, Allah ya huci zuciya mai muhimmanci.''
A hankali ya ke jan hannunta har suka fito wajen, motarsa ƙirar Benz, wacca ya saba hawa, ya buɗe
mata gaban motar sannan ya ja hannunta ya zaunar da ita.
Shima motar ya shiga tare da bawa motar wuta ya bar boutique ɗin gaba ɗaya.
A hanya ma ba ta fasa kukan ba, dan kuka ta ke har da majina.
A hankali Abbihn ke satar kallonta, sannan ya cigaba da tuƙi har suka ƙarasa babban eatry.
Sauka ya yi daga cikin motar wanda sai da ya yi da ƙyar sannan itama ta sauko.
Ya riƙe mata hannu, su ka shigo eatry ɗin.
Zama suka yi a wani ɗan ƙaramin parlour da nan ko wani VIP ke zama sannan ya yiwa waitress alamar ta
kawo musu menu.
Sai da ya zaɓa sannan ya zaɓarwa Liya dan ita, kan ta na ƙasa ta na aikin kuka.
Ɓangaren Hydar kam tun ranar da aka mai magana, ya daina shiga sabgar kowa a gidan, ko Sultana ya
daina sakarwa fuska rayuwarsa kaɗai ya ke yi.
Ko last week da aka sa rana, babu wanda ya yi wa magana ballantana a kai sa gaba.
Yau dai kam ba ya wani jin daɗin jikinsa, ɗan wani kalar kasala ya ke ji.
Mami ce ta shigo ɗakin na shi a hankali, ta shiga tashin sa daga barcin, da ya ke faking ya na yi.
''Shirya za ka kaini unguwa.'' Mami ta faɗa tare da tsare shi da manyan idanunta.
''Buh Mami bacci na ke yi, kuma akwai drivers a gidan.''
''Ni kuma na ce kai za ka kaini, ko da magana.''
Bai ƙara cewa komai ba ya tashi tare da zira slippers ɗinsa ya yi hanyar dressing room.
Cire kayansa ya yi ya saka bathrobe, ko da ya fito bai tarar da Mami ba.
Sai da ya tara warm water a jacuzzi, ya yi wankansa sosai, sannan ya fito haɗe da shiryawa cikin kaftan
white color, da black cover shoe, sai Rolex Explorer ll da ya manna a tsintsiyar hannunsa, tare da manna
hularsa a gashinsa da ya ke a gyare.
Sannan ya feshe jikinsa da turarensa na Armani Georgia haɗe da Valentino.
Wanda ko bai fesa ba ƙamshinsa na nan.
A hankali ya ɗauki wayoyinsa tare da fita daga ɗakin gaba ɗaya.
Ko da ya fito daga ɓangaren sa, ɓangaren Mamin sa ya nufa, haɗe da yin sallama.
Babu kowa a parlourn sai TV da ke ta aiki, a hankali ya zauna a ɗaya daga cikin tsadaddun royal cushions
ɗin, sannan ya fara danne -dannensa a waya.
Saukowa ya ji ana yi daga stairs bai duba wanda ke saukowa ba ya cigaba da chatting ɗinsa da ya ke yi.
''Aliyu tun da aka maka maganar na yi maka mata ka ƙullaci kowa a zuciya?, C'mon amshi jakar nan daga
hannuna.''
Mami da saukowa ta kenan ta faɗi hakan.
Beyi magana ba ya amshi jakar na ta da kuma mukullin motar ta, ya fita daga gidan zuwa cikin mota.
Mami da ta ci ado cikin wani dakakken less ɗinkin bubu gown, ziconic chain ko kuma nace set ɗin ziconic
na wuyanta da kunnanta da kuma hannyenta which means earrings da bangles.
Ta nufi motar ta ƙirar Prado black color, ta shige bayan motar ta zauna.
Motar ya cilla titi sannan a hankali ya ce ''Mami ina za'a je.?."
''Kwari market.'' ta ba shi amsa a taƙaice
Ta hanya mai nisa ya bi saboda kawai ya yi shatale -tale da ita.
A wani babban eatry ya tsaya tare da parker motar sannan ya ɗan kalli Mami ya ce ''Lemme get some
water.''
''Be fast.''
''Okay Maa.''
Daga haka ya fito daga cikin motar ya ƙarasa cikin eatry ɗin.
Ko da ya shiga ciki receptionist da ta ke kuma a matsayin cashier ya sama.
Ya ba da ordern ruwa wanda a take a ka kawo masa ruwan ya bada Atm card ɗinsa a ka zari kuɗin.
Juyowan da zai yi, ya yi ido huɗu da ita, wani babban mutum na mata kiss a gaban goshi amma bayan
mutumin kaɗai yake gani.
Ɗauke kansa ya yi daga dubansa agaresa, dan tabbas wannan bad luck ce a wurinsa, haɗuwa da ita
tashin hankali ne.
Liyana kam kallo ɗaya ta masa tare da kama hannun Abbhi ta na wasa da shi.
Fita ya yi daga eatry ɗin da ya ke dana sanin shigowansa.
Sannan ya yi hanyar wajen da yayi parking