Author : Dana sani Amarya Category : Complete Novels
riķo, duk da fita kayi ka barmu, kai Romeo you can’t watch her in pain right?.” Doctor Zhu ta
ķarasa maganar tare da zare hand gloves ďinta daga hannunta ta na mai ijiye su akan wani tray da
cleaner ta zo wucewa da shi.
“Alhamdulillah, Alhamdulillah ala kulli hal, Mrs Zhulaihat, kina da 5% share a H&K, thanks for saving
her.” Ya ķarashe maganar kamar Wanda zai rungumeta.
“Thanks I really appreciate, and then wa
ni hanzari ba gudu ba, her womb is very weak kafin ta ďauki wani cikin za a dan ďau lokaci.” Ta yi
maganar ta na mai ďan mayar da murmushin fuskarta.
“Babu komai a hakan ma mun gode ma Allah.” Ya ķarashe maganar still murmushi a kan fuskarsa.
“ Yeah, yanzu Ana gyarata da Babies ďinta, in the next hour za ka iya shiga, amma please a samo mata
abin ci wanda za ta iya ci sosai, ba lallai ta iya cin Chinese food da ake badawa a hospital ďin nan ba.”
Doctor Zhu ta faďa tare da barin wajen nasa.
Da sauri ya fice daga hospital ďin tare da nufar hanyar gida.
Ko da ya isa gidan ma direct kitchen ya nufa tare da ďaura ruwa a cikin wani electric flask, tare da kwaso
madara da cocoa powder da wasu abubuwan da suka dace.
Tare da ķara tilan kayan babies ďinsa, dan ya ķudiri cewa babu Wanda zasu gayawa ta haihu sai dai
saukarsu jibi a Nigeria.
※※※※※※※※※
Gida Nigeria kam tun safiyar ranar da Liyanar za ta haihu Ammi gabanta ke ta faďuwa, ta kira numbersu
ya fi sau dubu amma sam ba ta ďagawa daga ita har Aliyun.
Amma Abbhi sai ya ce da ita kar ta damu dan jiya sun yi waya kuma ya ji ta garau.
Haka dai ta ajiye maganar ta ci gaba da sabgoginta ba tare da ranta ya so ba.
Shi ma kansa Abbhi ji yake kamar ba lafiya take ba, ji yake tamkar ya yi booking flight zuwa China ďin ko
ya ji sanyin rashinta.
Ga bikin Ilham da ya rage saura one month da two weeks, ya kamata ace ta na nan ďin.
AFTER FIVE HOURS ❤️
Liyana ta samu kanta har ta fara breastfeeding yaran duk da ciwo da kirjinta suke mata.
A hankali ya buďe ķofar ďakin tare da shigowa ya na mai zama a kusa da ita.
D’aya ce a hannunta take bama nono sauran kuma suna kwance a baby cot.
Kallon su ya yi sosai tare da faďin “ Wacce na bawa Fatima a cikinsu ma?, I’m confused kin san kamar su
ďaya.” Ya ķarashe maganar ya na mai ďaukan wacce ke ďan motsi da bakinta.
“Gata nan a hannu na, ko baccin da sauran ke yi ba ta yi ba, sai cin abinci kawai take.” Ta ķarashe
maganar ķwalla na ďiga a idanunta dan ta gaji yau kaďai wallahi.
“Keep her lemme thank you well , because ďazu bacci na idonki ba sosai kika ji ba.” Ya yi maganar tare
da ďauke ta daga kan cinyarta ya na mai maida ta a cikin yan uwanta.
“Haihuwa ba Abu bane mai sauķi ba Liyana, kin sadaukar da jikin ki lafiyar ki rayuwarki, just for me naga
ya’ya’na a duniya, Allah ya miki albarka, Nagode miki sosai bisa haķuri da juriyar da kika yi da ni tun daga
ranar da muka fara haďuwa dake, you were sturbborn back then, Buh honestly your sturbborness is one
of a kind, and I always love it that way ko a lokacin, Allah ya yarda dake ya taya mu riķo, don’t worry
about what Marwa is saying earlier, let’s focus on our daughters, shower them with the love they
deserved, wallahi Fatima babu wadda nake so a duniya sama dake idan kika cire Mami, may we always
be happy with the zab’in da iyayenmu suka mana, no devil shall come against our happiness, I can’t
thank you enough Liya bae.” Ya ķarashe maganar ķwalla na zubo masa.
Tallab’o fuskarsa ta yi tare da share hawayen da ya zubo masa, sannan suka shiga kallon juna.
Ķurawa juna lips suka yi sannan suka shiga bawa juna Wani kalar French kiss mai tsayawa a rai.
Buďe ķofar da a ka yi ne ya sanya su ture junan su da sauri dan har sun manta inda suke.
Nurses biyu ne suka shigo sakamakon kukan da jarirai ke yi.
Da sauri liyana ta ďauki ďaya ba tare da ta kalli nurses ďin ba ta cigaba da basu ďaya bayan ďaya.
Washe garin ranar da sassafe aka sallame su, ko da ya mayar dasu gida kiran maids ďin gidan ya yi
sannan ya fita daga gidan ya nufi office, hours dinsa biyu ya gama abin da zai yi a office din, daga nan ya
wuce shopping mall ya yi wa yaransa siyayya masu mugun yawa da tsada dan tun yau zai bawa pilot ďin
jet ďin Abbhu…..
TTHE REGRET🦋🥰
PENDING AMARYA CE📓🦋
J🦋 A🦋 W🦋👊🏿
THE NOBLE WRITERS TEAM
✍🏻
PENDING AMARYA 60
Nayi adding pages 😊
enjoy 😊
Washe garin ranar da sassafe aka sallame su, ko da ya mayar dasu gida kiran maids ďin gidan ya yi
sannan ya fita daga gidan ya nufi office, hours dinsa biyu ya gama abin da zai yi a office din, daga nan ya
wuce shopping mall ya yi wa yaransa siyayya masu mugun yawa da tsada dan tun yau zai bawa pilot ďin
jet ďin Abbhu.
Zaune take kan kujerar dake ďakinta ta ķurawa yaran dake bacci cikin cot ďinsu hankalinsu kwance ido,
sanye take cikin wani body hug da ta ďora masa summer abaya Wanda ya dace da shigar jikin nata.
Wayarta dake ring din video call ta ďauka domin ďagawa amma gannin Wanda Ke kiran nata ne ya
sanyata ajiye wayar tare da lumshe idanunta ganin Mami ce mai kiran nata.
Turo ķofar ďakin nata a ka yi a hankali Wanda Jin an bude ķofar ya sanyata ďago kanta dan a tunaninta
Hydar ne, amma sai ta ga sab’anin hakan domin Marwa ce cikin shigar wani abaya mara nauyi, hannunta
ďauke da tray wanda ke nuna cewa abinci ne a ciki.
D’aure fuskarta Liyana ta yi kamar ta ga maķiyarta, ķarasa shigowa Marwan ta yi ba tare da ta tankawa
mugun kallon da Liya ke bin ta da shi ba, ta ķarasa shigowa tare da ajiye abincin a kan center table ďin
dake falon.
“Liya ga abincin nan za ki iya fara ci kafin ya yi sanyi, sannan dan Allah idan babu damuwa ina son yin
magana dake.” Marwa ta faďa ta na mai tsare Liya da idanunta.
“Za ki iya faďan abin da ke ranki tun da abincin ba dole bane sai na ci.” Ta yi maganar tare da ďaukan
wayarta.
Zama Marwa ta yi a kan kujerar kusa da Liyanar a hankali tare da dafa gwiwar Liyanar da ta yi crossing
ķafarta da shi.
Wani banzan kallo da Liya ta bita da shi ba ta san lokacin da ta cire hannunta a jikinta ba tare da fara
magana a hankali.
“Ki yi hakuri da duk wasu abubuwan dake faruwa a tsakanina da Aliyu like kalar maganan dana faffaďa
har ya zama sanadin haihuwar ki, na san ba sona kike ba tun kafin mijinki ya sanar dake duk wasu
abubuwan da suka faru a baya a tsakanina da shi, amma ina so ki sani komai muķaddari ne daga
Ubangiji, ba wai kuma zan faďa miki hakan bane dan ina Jin tsoranki, sai dan kawai na fayyace miki da
cewa a zamanin da suka wuce ne Aliyu ke gaba na ba yanzu ba, duk da ina son shi.” Marwa ta faďa tare
da gyara zamanta.
“ Ki yi sauri kiyi maganarki dan Allah kafin mijina ya shigo.” Liyana ta faďa a ďan faďace.
“Okay lemme go straight to the point, Na san ya riga da ya faďa miki da cewa mun yi soyayya a baya
da……”
Ba ta ķarasa ba Liyana ta ce “har haihuwa kun yi.”
Murmushin yaķe Marwa ta yi sannan ta ďago da fuskarta tare da faďin “Yeah mun haihu tare, and the
funniest part is that har yanzu ina kan rufa masa asirin da shi ya zama sanadiyyar tarwatsewar
rayuwata.” Marwa ta faďa tare da goge ďan guntun ķwallan da ya zo mata.
Sosai jikin Liya ya yi sanyi sannan ta ďago a hankali tare da faďin “Mai ya tarwatsa rayuwar naki?.”
“Yarda!, Yarda Liyana, na san kin ji last call da muka yi da Aliyu a kan wani birthday da naje, she’s my
close friend a kaff China ko Aliyu shaida ne, da akwai ranar da ni da su muka je wani hotel dan kawai mu
huta dan Aliyu ya Saba min da idan a ka ďan yi tafiya a hotel muke zuwa mu huta ba a gida ba, toh a
ranar mun je wani presentation wanda har Aliyu ya kama mana ďaki, bayan mun fito ma ni ya bawa key,
then sai na kawo Qawayena cikin ďakin domin mu ďan huta.
Ko da muka huta ma ashe a cikinsu wata ta saka camera a ďakin.
kusan shekara 7 ana threatening ďina a kan porns video ďin ni da Aliyu, suka gayyato min wani guy ya
kwana da ni a can Nigeria shine ranar da Aliyu ya kama ni da shi.
Ko da na bi shi can North Korea ďin ma ashe duk setup ne Qawayena suka ďana min.
Wallahi Liyana a yanzu ina da wanda yake son aure na amma sun hanani, because since lokacin suka
nuna min bukatansu na joining lesbianism , sannan suka ce idan ban yi joining ba sai sun yaďa video ďin.
Ni na gaji da duniyar nan no body loves me.” Ta ķarashe maganar hawaye na fita a idanunta.
“Ai kin ga hotel, ke mai ya kai ki yarda da ķawance?, ni da nake nan sai da na shiga university sannan na
fara ķawance shi ma dan kawai Asha ruwan tsuntsaye ne tun da nayi aure ban cika kulata ba, dan wallahi
Aliyu nan gani nan bari, gwamma ki goge hawayenki mu san yadda zamu b’ullowa lamarin.” Liyana ta
iddashe maganar a tausashe.
“Na barwa Allah komai zai yaķe min duk wani azzalumi dake cikin rayuwata, sannan zan faďawa Aliyun
duk abin da ke faruwa domin fitar porn ďinnan dai dai yake da b’ata komai nasa, domin Aliyu babban
mutum nè a faďin duniyar nan ba ki ďaya.” Marwa ta faďa tare da fara ķoķarin tashi a wajen.
“Da ya fi muku.” in ji cewar Liyana tare da ďaukan wayarta.
Har dare gaba ďaya Marwa ke ta ďawainiyya da ita, amma duk da haka a wajen ta gani take Marwa babu
abin da ta mata na burgewa.
Yaranta kam Ma shaa Allah, kamanninsu ďaya farare tal- tal da su.
Sai dare sosai sannan ya samu dawowa.
A zaune ya tarar da ita cikin shigarta na kayan bacci ta na gyangyaďi hannunta na riķe da daya daga cikin
jariran da sai tsula kuka take.
“Sorry Wifey na bar ki da raino, kawo ta na riķeta kiyi baccin ki.” Aliyu da shigowarsa ďakin nasu kenan
ya yi maganar tare da ajiye key din motarsa a bed sides.
“Ya Alih mai sunan Mami tun tuni take ta kuka har yanzu bata daina ba, ka taimaka min dan Allah Kar ta
mutu.” Ta ķarashe maganar muryarta a karye.
“Daga kuka sai mutuwa?, normally yara na hakan ai, it’s a normal thing.” Ya ķarashe maganar tare da
amsar Khairat wadda suke kira da Alynerh daga hannunta……
Wayyo Allahna manage gobe zan kokarta nayi muyi mu gama a week dinnan sorry for the late post🦋
😭
🤌🏻
🥹
THE REGRET 🦋👊🏿
Pending Amarya ce😇
J🦋A🦋W🦋👊🏿
The Noble writers ✍🏻
Pending Amarya 61🦋🦋🦋🦋
“Daga kuka sai mutuwa?, normally yara na hakan ai, it’s a normal thing.” Ya ķarashe maganar tare da
amsar Khairat wadda suke kira da Alynerh daga hannunta.
Manna yarinyar ya yi a ķirjinsa sannan ya tashi a hankali tare da fara zagaye ďakin da ita yana mai ďan
jinjigata.
Tsagaita kukan Alynerh ta yi wanda hakan ke tabbatar masa da cewa bacci ta fara.
A hankali ya ajiye ta a cot ďinsu na ďakin, sannan ya sanya bargonsu ya lullub’eta da shi.
“Ahh Done with this young lady, saura kuma Mamansu, ban san da wani drama ta zo min da shi ba,
wannan da take cuno baki, anyways I’m ready for you.” Ya yi maganar ya na mai kwanciya a kan gadon
nasu.
“Babu wani drama, na gaji da rashin ďaga wayoyinsu Mami da ka sakani, yaushe zamu koma gida?.” Ta yi
maganar a shagwab’e.
“Tomorrow in shaa Allah, just be ready, bara na ďan watsa ruwa wallahi na gaji da yawa Liya.” Ya faďa
tare da fara shiga changing room din dakin.
“Idan ka fito please ina son maka magana if you didn’t mind?.” Ta faďa cikin tattausar murya.
“Sure, anything for you my dear.” Daga haka ya shige changing daga nan kuma ya shige bathroom.
Babu tunanin dake zuwar mata kai sai maganganun Marwa da tun rabuwarsu a ďazun yake mata yawo a
brain.
Cikin mintunan da basu haura 20 ba ya fito daga banďakin ķugunsa ďaure da towel.
Dressing room nasu ya shiga tare da ďauko kayan baccinsa daga clothset, sannan ya dawo ya feshe
jikinsa da turarukansa masu tsadar gaske, sannan ya ďaura da kayan baccinsa masu taushi tare da
ďaukan sleeping mask ďinsa ya nufi kan gadon da shi.
“Ife, gani na zo mai zamu tattauna.?”
Ya ķarashe maganar tare da ďaura sleeping mask ďinsa a goshinsa.
“Ya Alih is about Marwa.” Ta faďa a sanyaye.
“Mai ya faru da ita Marwan?.”
“Ya Alih wallahi yarinyar nan ta na ganin rayuwa, rayuwarta ya rushe da yawa a dalilinka, kuma Billah ta
rasa ta ya zata b’illowa lamarin har ya yi tsamari.” Ta yi maganar ta na ďan kallon reaction ďinsa.
“Mai ta faďa miki.” Ya faďa da ďan zafi.
Bata yi ķasa a gwiwa ba ta sanar da shi komai dake faruwa.
Sosai ya girgiza da Jin lamarin da ta kawo masa, amma still bai nuna damuwarsa ba ya sanya slippers
ďinsa tare da barin ďakin.
Bai zarce ko ina ba sai ďakin Marwa, a hankali ya buďe ķofar ďakin tare da shigowa a hankali.
Zaune ya tarar da ita ta bawa ķofar ďakin baya idanunta na kan laptop ta na kallon pictures ďinsu na da.
“Why Marwa!, mai sa ba ki faďa min ba why?.” Ya faďa a sanyaye,
“ ba ka fahimce ni ba a lokacin, ko da ka same ni da shurem you walk out on me ba ka bar ni na maka
bayani ba, I chatted you on Facebook, what’s app, Telegram, instagram, Imo, gaba ďaya block ďina kayi,
and now it’s too late, kai ma ka san da hakan.” Ta faďa tare da goge hawayenta.
“waye a cikinsu yake threatening ďinki?.”
“It’s Zola, my best friend.” Ta faďa a sanyaye da disassar murya.
“kina da pictures ďinta wanda faces d’inta suka fito sosai?.”
“Yeah ga su nan.” Ta faďa tare da nuna masa screen din wayar nata.
“Tura min shi a wayata, har da na ubanta idan kina da shi.”
Daga haka ya fice daga cikin ďakin.
Ko da ya fita a ďakin na ta ma bai zarce ko ina ba sai study room ďinsa, sai da ya ďau kusan awanni biyar
sannan ya gama haďa pictures ďin da ta tura masa tare da yi mata forward ďinsu.
Har an fara kiran sallar farko hakan ya sanya shi yin sallah sannan ya koma bacci.
Liyana kam maganar komawarsu Nigeria ba ķaramin farinciki ya sanya ta ba. Tun safe Chinese maid ďin
ta shigo tare da yiwa babies wanka, sannan ta haďawa Liyanar ruwan wanka da sauran kayan gargajia da
suke hadawa wankan masu jego da shi.
Sai a lokacin ya samu daman fitowa daga study room ďinsa, direct wanka ya yi shi ma tare da yin brush
sannan ya shirya cikin wasu black suits wanda suka mugun yi masa kyau.
Wani black Mecury chiffon yard ta saka wanda ďinkin ya zauna ďass ďass a jikinta suka mata kyau mara
misaltuwa, high heels ta saka black color, sannan ta naďe kanta da mayafinta, tisa yaranta a gaba ta yi
ta na kallon kyakkyawar fuskarsu.
wacca ta fara zuwa duniya ita ce Fatima suna kiranta da Alya, then wadda ta ci sunan Ammi suna kiranta
da Aida sai Alynerh wadda ta ci sunan Mami……
Gobe zamu cigaba besties 😂
😂 🦋🤌🏻
Allah ya huci zuciyar masu imani 😂😂
THE REGRET 🦋💖
Pending Amarya ce 🦋🎉
J🦋 A 🦋W🦋
THE NOBLE WRITERS TEAM
Pending Amarya 62💖
This page is Dedicated to me Pending Amarya 💖
wacca ta fara zuwa duniya ita ce Fatima suna kiranta da Alya, then wadda ta ci sunan Ammi suna kiranta
da Aida sai Alinerh wadda ta ci sunan Mami……
“Ta so mu tafi driver na jira around 3 na yamma zamu sauka a Kano.” Ya faďa tare da ķara feshe jikinsa
da turare.
murmushi ta sakar masa tare da ďaukan Baby backpack ta goya Alya shi Kuma ya ďauki Aida.
“Ita kuma Alynerh fa ya zamu yi da ita…..”
Ba ta kai ga ķarasawa ba Marwa da shigowarta ďakin kenan ta ce “Ni zan ďauketa.”
Babu yabo babu fallasa ta ďauki Alynerh tare da miķawa Marwar.
Goya ta tayi ita ma da abin goyon sannan suka fice daga