Advertisements
Chapter 23 Reading The REGRET by Dana sani Amarya BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

The REGRET by Dana sani Amarya

Author :  Dana sani Amarya Category :  Complete Novels

Chapter   23 / 39

66K to 69K   out of 116.5K words

yi daga nan sai ku ɗaura girkin dare, ma za Sultanah kuje ku yi sallah ku mana
girkin dare kafin Abbhu ya dawo.''



Ta ƙarashe maganar ta na kallon Sultan da ya zuba mu su idanu, wani harara Mami ta maka ma sa tare
da faɗin ''ka wani tsare mu da ido ba zaka wuce ka fita wurin da ya aike ka ba sai ya dawo.''



''Mami fa har yanzu am heart broken à ɗinga lallaɓa ni.''

''ƙanin ubanka Wanda Qassim da zuwaira ba su haifa ba suka mutu, leave my presence, oloshi.'' ( Ashe
yaya Alih anan aka samo leave my presence 😂😂😂).




''Sorry Maa.'' daga haka ya ɗauki laptop ɗinsa da car key sannan ya fi ce daga falon, ita dai Liyana ko
kallonsa ba ta yi ba, dan ta na kiyaye eye contact da shi a yanzu.




Hannunta Sultanah ta ja suka nufi kitchen ɗin tare, in less than 30 mins suka dafa lafiyayyan cous cous
jollof da ya ci hanta da kaza, sai pepe soup da fruit salad da suka yi, duk da Sultana ce jagaba wajen
ayyukan.



Sosai gidan ya ɗau ƙamshi y'an aikin har sun gama gyaran gidan sosai.
Mami ce ta fito sanye cikin wani Adire gown maroon color ta yi kyau sosai, a time ɗin har sun kammala
komai akan dinning table ɗin.



A daidai lokacin kuma suka ji parking motoci a cikin compound ɗin, cikin minutes suka shigo shi da
Abbhu hannunsa riƙe da award ɗin mai form of takalmin wanda aka kera shi da glass, amma kallo ɗaya
zaka ma sa ka san cewa da diamond aka yi shi.



Bayan sun yiwa Abbhu sannu da zuwa, basu zauna ba suka wuce masallaci da Abbuhn da kuma Hydar,
after 20 mins suka dawo gidan, suka ci abincin gaba ɗayan su amma ban da Sultan da har time ɗin bai
dawo ba.



Sosai ta buɗe cikinta ta ci abincin, ƙarfe tara na dare ya ce da ita ta shirya su koma gida.

Lokaci ɗaya wani kalar baƙin ciki ya ziyarce ta mara misaltuwa, dan har Mami sai da ta yi noticing ɗin
halin da take ciki.



''Fatima ba kya son komawa gidan na ki ne ko ƙaƙa?."

''A'a Mami, ban leƙa gidan Neneh ba ne kuma gashi har zamu tafi.'' taƙarashe maganar hawaye na zuba
a idanunta.



Ga mamakin Mami sai kawai ta ga hawaye a fuskarta ta na gogewa.

Ita tun shigowar su daman yadda ta ga yarinyar wani iri duk a rikice ta san ba lafiya ba, kamar yarinyar
ba ta jin daɗin gidan Aliyun.



''Is Okay daughter, Aliyu maza ka kaita wurin Neneh sai ku wuce.''

Da toh ya amsa tare da kama hannunta suka fice daga gidan gaba ɗaya.



***_____________***
Ɓangaren Neneh kam kullum sai sun yi hirar Liyana da Salimah, ta na ba ta labarin yadda Hydar ke kula
da ita.



Cikin muryarsa mai amo yayo sallamar hannunsa sarƙafe da na Liyanar suka ƙaraso cikin falon.

''Ɗan halak ya ƙi ambato, ku ce shegun kuna kusa, toh Allah yaso ni alherin ku nake faɗa ba sharrin ku ba
balle ku ɗebe min albarka." Nenehn ta faɗa ta na gyara zaman glasses ɗinta.



Har ƙasa ta durƙusa cikin sassanyar muryarta ta ce "Nda Dubdo Neneh."



Amsa gaisuwarta Neneh ta yi tare da faɗin.

''Yau kuma da wannan salon aka zo kenan.''

A fakaice Liyana ta dallah ma ta harara wanda hakan ya haɗa idanunta da Nenehn.




" A uzubillah, Fatima mai ya sami fuskarki ta yi baƙi haka kamar lantarki?, Aliyu a haka na baka jiƙata ko
zallar baƙin halinka ne haka?."



" Malama za ki tashi mu tafi tun da kin ganta, ko jiƙata za ki yi ki shanye?." Ya yi maganar tare da ɗago
kansa daga wayarsa da yake dannawa.



Kamar za ta yi kuka ta ce " Neneh sai da safe."




" Allah ya tashe mu lafiya, kai dai Aliyu ko a aljanna na ganka sai na tambayi sababi, dan har ga Allah
kallo ɗaya za'a yiwa jiƙata aga wani kalar baƙi da tayi kamar hadari, toh daman dai wajen ƙiba bana ce ka
ramar da ita ba saboda daman can ko skeleton ya fi ta ƙiba."
Cikin muryarsa mai amo ya ce" nifa Neneh kar ki jefa ni à bakin duniya, ciki ne da ita, laulayi take, sai ki
barni na huta ai ko?, ke kuma taso mu tafi.''



Daga haka ya finciki hannunta suka koma can gidan nasu, ko ledar da Sultana ke bata, ba ta bi ta kansa
ba ya wulla ta cikin motar tare da mata key suka bar gidan.



''Ke dan ubanki ba nace dake you should feel free ba, kiyi rayuwarki yadda kika saba ba?." Ya tambaye ta
ya na wani kalar zaro idanunsa waje, wani kalar karkarwa jikinta ya soma yi, sannan a hankali ta ce
''Please, ka bar ni ko fuskar iyayena na gani i don't think idan na cigaba da rayuwa da kai zan kai labari,
ban san tsoro ba, kai ka fara sanar da ni, ban san menene zubar hawaye ba a silar ka na san hakan,
please and please, for once ka barni na shaƙi iskar farin ciki arayuwata, honestly na gaji am tired please.''

''Okay ni da ke mun zama sa'anni da har za ki kalli idanuna ki gaya min magana san ranki ko, ko dan na
riƙe hannayenki yau a tunaninki shinfiɗa na haɗa dake?, is alright, za ki wuce ki buɗe gate na shigar da
mota ko sai na ɓaɓɓalla ki?."




Ba ta tanka ma sa ba ta ɗauki key ɗin tare buɗe ma sa haɗe da buɗe gate ɗin gidan, da gudu ya shigo
cikin gidan haɗe da parking motar a wajen da aka tanada.




Hannunsa riƙe da award ɗin da Abbuhn ya bashi ya ajiye a wurinsa ya fito daga motar, ya na kallon
yadda take kiciniyar kulle ƙofar.



Da ƙyar ta gama sannan ta wuce backyard ta kunna solar, haɗe da watering flowers ɗin gidan gaba ɗaya.

Sai wajen 12 na dare ta kwanta, kasa bacci ta yi saboda tunawa da Birthday ɗin Abbhi da ta yi, wanda
al'adarta ce ita ke fara yi masa wishes da gifts.
Wani kalar fashewa da kuka ta yi ta na mai ƙanƙame jikinta, murɗa handle ɗin ƙofar aka yi tare da
shigowa cikin ɗakin, wanda daman ba ta kulle ƙofar ba, dan ya sha mata warning akan kulle ƙofa, akan
hakan ma ya sha mata duka, jikinsa sanye da pyjamas white color ta janye sleep mask ɗinsa zuwa kan
gashinsa, hannunsa sanye cikin aljihunsa.

Kallonta ya yi cikin shigar kayan baccinta pyjamas purple color, buh wandon is short, kanta sanye da
hula, santala santalan cinyoyinta ya bi da kallo da sai wani kalar sheƙi suke, dan yanzu ba ta kwana babu
haske tun da ta na rashin waya.



''Am even regretting why ƙanwar ki ta ɗauki number na ta bawa mahaifinki, kusan kullum sai ya min 10
miss call I donno ko ba shida aikin yi ne.''



Ba zato babu tsammani ta ji kawai ta yi wani mugun fashewa da wani kalar kuka mai cin rai, ita
arayuwarta da a zagi Abbhi gwara a zagi Ammi, dubi filthy words da yake faɗawa mahaifinta fi sabilillahi.



Dailing number Abbhinata ya yi tare da miƙa ma ta wayar, ring ɗaya kamar jira ake ya katse kiran haɗe
da biyo kiran, ''Hello dear, kin wuni lafiya?."

Sai da ta kalli fuskarsa sannan ta ce ''Ina wuni Abbhi, ya gida, ya su Ammi da Ilham?."

Sai da Abbhi ya yi ƴan sakanni, because all his life Liyana ba ta taɓa gaida shi cikin ladabi haka ba, sannan
a hankali ya ce ''Lafiya lau, kowa lafiya, mai sa muryar ki ya yi sanyi haka rashin lafiyar ne har yanzu?, ga
shi kusan last 3 weeks kika ce za ki zo, ba ki zo ba?."



Ita ta manta da wani Hydar ma a kusa da ita cikin wani ɗan murya mai nuna zumuɗi ta ce ''Kaji Abbhi da
wani zance, Allah na tuba sai ka ce baka san gidana ba, kai ba zaka zo ba ni zan ta zuwa?.'' ta yi maganar
ta na wani kalar dariya haɗe da rufe bakinta da hannunta.



A ta can ɓangaren Abbhi ya ce ''Daughter kin manta birthdayn Abbhinki kenan?."

''Allah sarki Abbhin Liyana kar kayi fushi kana can cikin raina, wallahi riga ni faɗa kawai ka yi, toh Happy
Birthday,my rock, Allah ya kawo shekaru masu Albarka.''

''Yeah Daddy's girl.''

''Abbhi am a lady not a girl manaa.''

Ta yi maganar ta na turo baki.
''I will come tomorrow in shaa Allah, let's goo for our annual shopping.'' Abbhin ya faɗa ma ta tare da yi
mata sai da safe.



Wani banzan kallo ya watsa mata sannan ya ce ''Sai in ga uban da zai fita gate balle yaje shakatawan.''
daga haka ya fice daga ɗakin.......




Manage please b yawa🤗

*THE REGRET*

PENDING AMARYA CE ✍️

JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

The Noble Writers team.




**Pending Amarya 41**
What goes around comes around ⏮️⏩



Try to be a good father to your children not a cowed 🤍 🫧 🤧



Not edited 🌟💔🥹



****




Wani banzan kallo ya watsa mata sannan ya ce ''Sai in ga uban da zai fita gate balle yaje shakatawan.''
daga haka ya fice daga ɗakin.



Da ido ta bi shi har ya fice daga cikin ɗakin, sannan a hankali tayi kwanciyarta haɗe da rungume jikinta,
bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita.



*******



Washegarin ranar da sassafe ta tashi domin shirya abubuwan da za tayi ta koma bacci tun da har yanzu
bai barta ta koma makaranta ba, hakan ya sa lokacin ta a barci da aiki take ɓata shi.



Sai da ta gyara gidan tsaf sannan ta ɗaura chips da plantain da yanzu hannunta ya faɗa sosai a sarrafa su
a yanzu.



Bayan ta gama jera abincin a dinning table kitchen ɗin ta koma domin haɗa masa coffee kafin ya dawo
daga gym, ƙarar buɗe ƙofar da ta ji ne ya sanya ta rikicewa.

Direct kitchen ɗin ya nufo tare da duba coffee maker ɗin domin haɗa coffee, ganin coffee akan kitchen
island ne ya sanya shi kallon kitchen ɗin dan ganin ta inda za ta ɓillo.
''Kina ina?, za ki fito daga bayan ƙofar nan ko sai na ba ki dirty slap wanda za ki ga kan ki a gidan ku.''



A hankali ta fito daga bayan ƙofar kanta a ƙasa ta na wasa da hannayenta, wani shegen kallo ya bita da
shi tare da faɗin ''Sau nawa ina faɗa miki ki daina haɗa min coffee a gidan nan?."

Fashewa ta yi da kuka haɗe da ɗaga hannayenta ta na ma sa alamar biyu.

''zan kwashe ki da mari idan ba ki min magana yadda na miki ba.''

Cikin shashsheƙar kuka ta ce ''Sau biyu yau ne na uku.''



''Alright, tun da ke naga ba kyau jin magana is like ba kya son rayuwar da babu punishment, ki zauna
kayan ki ba tare da kin shiga harkokina ba ke ba kya jin daɗi, ya'r tusai ba kwarjini, i command you ki
wuce ki gyara min ɗakina, ko da wasa kika min abin da ba shikenan ba yau ɗinnan na lahira sai ya fi ki jin
daɗi, oya!."



Ya yi maganar tare da yi mata pointing ƙofar.



Jikanta a sukwane ta nufi hanyar corridor ɗinsa idanunta na fidda hawaye, a hankali ta buɗe ƙofar ɗakin,
falo ne mai kyau sosai babu tarkace kallo ɗaya za ka masa ka ga luxury living room, it looks rich and
elegant, parlourn bai yi wani datti ba sai wani kalar zallar ƙamshin turarensa dake tashi kamar ya na cikin
ɗakin.



A hankali ta fara tattare falon duk da ba wani lalacewa ya yi ba, kawai tsabar tsafta ce irin na Hydar
amma ai babu abin da falon ya yi hakan ya sa ta kawai mopping ɗinsa ta yi sannan ta shiga master room
ɗinsa da ko ina yake tsaf tsaf, standing mirror ne kawai yake ɗan hargitse daga shi babu komai a ɗakin da
za'a gyara, dan alamu sun nuna kullum sai ya gyara ɗakinsa da kansa.



Mirror ɗin ta nufa tare da ɗaukan glass cleaner da towel ta fara goge mirror ɗin, mistakely jikinta ya gogi
turaren da aka ajiye shi ba dai-dai ba, hakan ya sa turaren faɗuwa a ƙasa tare da fashewa, wani kalar ihu
ta saki wanda a garin juyowa shima kansa madubin ya biyota ya tarwatse a ƙasa, kalar mirror ɗin nan ne
wanda ake jingina shi akan standing ɗinsa.

Wani kalar kakkarwa jikinta ya fara yi wanda hakan ya sanyata fashewa da kuka tare da tisa mirror da
turarukan agabanta ta na kallonsu.
Ta ma rasa wani kalar addu'a za ta yi, hakan nan ta tsinci kanta da faɗin ''La 'ila ha illa anta subahanaka
inni kuntu minal lil zali min.''

Haka tai ta nanatawa ta na kuka.




Ganin ta kai kusan hour ɗaya har yanzu ba ta fito ba ne ya sanya shi hawa saman a fusace tare da tura
ƙofar ɗakin, zaune ya ganta agaban mirror ɗin dake zube a ƙasa duk dakin ƙamshi ya baibaiye shi wanda
hakan ya bashi tabbacin cewa turarensa ne suka fashe.



Kallonta ya yi sosai tare da faɗin ''Gyara na ce ki yi ko ɓarna?."

Cikin shashsheƙar kuka ta ce ''Dan Allah dan Annabi ka yi haƙuri, wallahi ban san ya akayi ba sharrin
shaida'n ne.''

Ta ƙarashe maganar ta na kneeling da ƙafafuwanta hannunta ta na alamun pleading da shi.''

Kallonta ya ƙara yi da kyau tare da kaudar da kan sa gefe haɗe da faɗin ''Kina da zaɓi biyu, na ɗaya, za ki
bi ta kan glasses ɗinnan ki wuce ki fita, na biyu kuma za ki frog jump za ki zagaye compound ɗin gidan
nan sau goma.''



Ƙura mai idanunta ta yi na ya'n daƙiƙu, sannan a hankali ta fara tunanin gwanda ta jewa zaɓi na biyu,
akan ta yi jinya kuma dole ne ta yi aikin gidan.



" I choose the second punishment." Ta faɗa a sanyaye.

Press ɗinsa ya buɗe tare da ɗaukan wani bulalar fata mai baki biyu, wanda ya siye shi da daɗewa.

Zaro idanunta ta yi waje ba tare da ta yi magana ba ta bi bayansa ganin har ya fice daga ɗakin.



A lokacin har sha biyu ta gota wani kalar rana ake yi mai zafin gaske.
*****



Ɓangaren Abbhi kam tun bayan da suka yi waya da Liyanar sa yake jin wani kalar farinciki, dan Rufy ji
take kamar ta mauje shi, dan sam - sam ba ya barin su su wataya a gidan sanadiyyar shaiɗaniyyar
yarinyar da yake kira favorite, ita matsalar ta ɗaya yadda doctor ya ce mahaifarta ba zai iya ɗaukan ciki
ba, shi ne babban damuwarta a yanzu.



Da sassafe ya fara shirye-shiryen zuwa gidan Liyanar saboda suje shopping ɗin da suke yi duk shekara
idan birthday ɗin waninsu ya zagayo a gidan, wani black color tissue yard ya saka wanda suka masa
mugun kyau na fitar hankali.

Cikin shigarta na Abaya Ammi ta shigo ɗakin na sa tare da ajiye ma sa break fast cikin sanyin muryarta ta
ce " Abbhinsu Happy Birthday, Allah ya ƙaro shekaru masu albarka unlimited money in your account."

Sai da ya ɗan kalleta sannan ya yi ɗan murmushi da suka tsaya a iya lips ɗinsa tare da faɗin ''Amin Iki
dear, Finally yanzu kin girma, da wannan breakfast ɗin da kika kawo da kin sha ranƙwashi, kin taɓa ganin
na sha hollandia yourghurt ba strawberry hollandia ba?." Ya yi maganar ya na kallonta sosai.



A hankali ta ce ''Ayi haƙuri Yallabai strawberry ɗin ne ya ƙare shiyasa, amma bari a mayar.''

Ta yi maganar tare da kai hannunta kan tray ɗin.

A hankali ya ce ''Just leave it I will manage.''

Murmushi ta sakar ma sa mai kyau tare da faɗin ''Your wish is my command sir, thank you Sir.''

Daga haka ta baro ɗakin.



Till date ta na matuƙar son Nabil ba ta son wani abu da zai ɓata mata ransa.



Bayan ya gama breakfast ɗin ma sai arround 12 ya fito domin zuwa gidan Liyanar, Ammin na ma sa a
dawo lafiya.



A hanyarsa na zuwa gidan Liyanar ma sai da ya biya ta Boutique ya mata siyayya sosai, daga kan palazzo
trousers da jeens skirts, da boots, da shirts babu abin da ya manta, sosai ya mata shopping, dan so yake
ya ga murmushi a fuskar mafi soyiwa a wajensa.
Ya ɗan sha wahala wajen gane gidan Liyanar saboda ko ranar da yazo shi da Ilham, da daddare suka zo
gidan, kuma Ilham ce ta yi driving ɗin motar dan zuwan bazata ya mata, kuma a time ɗin da ita yake
waya, shiyasa da ƙyar ya gane gidan.



A hankali ya fara horn a daidai luxury gate ɗin, ganin ya ɓata kusan mintuna biyar ba'a buɗe ma sa gate
ɗin ba, ganin small gate ɗin a buɗe ne ya sanya shi canza shawara haɗe da yin parking ɗin motar ta sa a
wajen gidan.



Fuskarsa ɗauke da ɗokin ganin ɗiyar ta sa ya buɗe motar haɗe da fitowa daga cikin motar hannunsa riƙe
da ledoji wanda ke cike da kayayyaki na alfarma.



Unguwar shiru take babu wani hayaniyya abin ka da unguwar masu hannu da shuni, a hankali ya ƙarasa
bakin gate ɗin tare da buɗe ƙofar a hankali.



A tsugunne take idanunta na fiddar da zallar hawaye, fararen ƙafafunta babu slippers, hannuwanta na
kame da kunnuwanta, wanda dukkan alamu sun nuna frog jump take.

Tsayawa ta yi da niyyar hutawa, hakan ya sanya shi ɗaga bulalar hannunsa, haɗe da zula ma ta shi a
gadon baya, wanda hakan ya sanyata sakin wani ƙara haɗe da wani kalar nishin wahala, ka na ta saki
kuka mai mugun cin rai.



A hankali aka turo ƙofar haɗe da shigowa cikin compound ɗin gidan, idanunsa suka ma sa mummunar
gani, ganin Liyana acikin rana, shi kuma Hydar ya na zula ma ta bulala kamar an jefo shi.



Take Abbhi ya saki ledar hannunsa wanda hakan ya jawo hankalin Liyanar da Hydar ɗin suna mai kai
duban su wajen gate ɗin.



Cikin muryarsa mai amo ya ce ''Abbhi ina wuni.''

Cikin wani kalar murya wadda ba ta fita sosai Abbhin ya ce ''Riƙe gaisuwarka ba na buƙatar ta, Liyana
kwaso kayan ki mu tafi.''
Cikin wani kalar murya wadda ba ta fita sosai ga wani kalar kuka da take ta ce ''Abbi kayi haƙuri bazan iya
rabuwa da mijina ba ko da ka d'auke ni gangar jikina ka d'auka sabida my heart and soul will be left in
this house, Just pray for me Abbhi ka faɗawa Amminah I really need her prayers.'' ta yi maganar haɗe da
goge hawayenta, ta na mai kallon Abbhin da ya matso dabb da ita.



''Are you out of your mind?, ta ya kike tunanin zan barki acikin wannan gidan a kuma halin da kike ciki,
anya ba ki fara zarewa ba?.''



Cikin murya mai sanyi ta ce ''Abbhina ni ina son mijina, ba zan iya barinsa ba, and I know what I'm doing,
Abbhi just go and seek Ammi's forgiveness, na san duk abin da ta fuskanta acikin gidanka, akwai wani da
ga danginta da suka zo suka ɗauketa?, ka tafi kawai na girbi abin da ka shuka, my hope and prayers shi
ne punishment ɗin ya tsaya a kaina kar ya taɓa min Ily, just goo and

23 / 39