Author : Dana sani Amarya Category : Complete Novels
Mamin ta yi ta Telegram, ring biyu wayar ta yi aka ɗaga, in a calm voice Mami ta fara
magana dan ko sallamarsa da gaisuwarsa ba ta bi ba ta ce ''Aliyu ko akuya ka ajiye a gida, za ka tambayi
lafiyarta, balle ɗan Adam, haka ka ga mahaifinku na yi min?, mai sa duk cikin ya'n uwanka ka fi kowa
baƙin hali ne?, a ina ka gado halin ka ni ban sani ba.''
Sai da ya sauke wani ajiyar zuciya sannan ya ce ''Mami I'm sorry aikin ne ya yi min yawa, and besides I
watch all her moves no need a ce sai na kirata.''
''Aliyu ubanka.''
Shiru ya yi ta cigaba da sauraron Mamin kafin daga bisani ya ce da Mamin a bata wayar.
A hankali ta saka hannu ta amshi wayar, Mami na bata wayar ta fice daga ɗakin.
Murya a sanyaye ta ce ''Ina wuni.''
''Lafiya, uban mai kika je kika faɗawa Mamina?."
Kamar za ta yi kuka ta ce ''Babu.''
''Ya jikin ki?, wannan wajen ya daina ciwo?."
Firfito da idanunta ta yi tare da faɗin ''Wani waje?."
''Don't pretend hajiyata, kin san abin da nake nufi, did you miss me?."
Banbarankwai ta ji maganar na shi acikin kunnenta, take zuciyarta ta yi wani kalar mummunan
faɗuwa......
''Ya Ubangijina ka basu daman share."
Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟
Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 😂😂
*THE REGRET*
PENDING AMARYA CE ✍️
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
The Noble Writers Team.
**Pending Amarya 46**
What goes around comes around ⏮️⏩
Try to be a good father to your children not a cowed 🤍 🫧 🤧
Not edited 🌟💔🥹
****
A hankali ta saka hannu ta amshi wayar, Mami na bata wayar ta fice daga ɗakin.
Murya a sanyaye ta ce ''Ina wuni.''
''Lafiya, uban mai kika je kika faɗawa Mamina?."
Kamar za ta yi kuka ta ce ''Babu.''
''Ya jikin ki?, wannan wajen ya daina ciwo?."
Firfito da idanunta ta yi tare da faɗin ''Wani waje?."
''Don't pretend hajiyata, kin san abin da nake nufi, did you miss me?."
Banbarankwai ta ji maganar na shi acikin kunnenta, take zuciyarta ta yi wani kalar mummunan faɗuwa....
Shiru ta yi ma sa na y'an daƙiƙu tare da sauke wani kalar nannauyen ajiyar zuciya, cikin muryarsa mai
Amo ya ce ''Soo you are missing me right?.'' shiru ta ƙara ma sa, abin ya mugun ƙona ma sa rai, dan ko
ba komai ta nuna damuwa ga mahaifiyyarsa shi yasa ma yake son ya ɗan yi ma ta magana ba dan komai
ba.
Tsaki ya ja tare da ƙara faɗin ''A haka za ki ƙare ai, za ki bawa mai wayar, wayarta ko dai na ɓillo ta wayar
nan na sauke miki maruka.''
Wani ajiyar zuciya ta ƙara saukewa, kamar wadda ke yin bacci, sallama Mamin ta yi tare da shigowa, ta
ga Liyanar a yashe a ƙasa bacci ya kwasheta, wayar na hannunta kamar wani zai ƙwace ma ta shi.
Ƙarasowa wajen Mamin ta yi ta na mai ɗingisa ƙafarta, tare da zare wayar a hannunta.
Baƙin ciki kamar ya kashe Hydar saboda banzan da ta ma sa, ko kan Amin dake ma sa magana bai bi ba
ya katse wayarsa.
Kallon fuskarta Mamin ta yi na ya'n sakwanni tare da ɗaukan blanket ta lulluɓeta da shi, dake akan
Persian carpet ɗin ɗakin take a kwance.
Around 2 O clock ta tashi daga barcin da take a dalilin wayarta da yake aikin ringing, wani kalar sara ma
ta kanta ya yi, ta na mai ɗaure fuska ta nufi kan cushion ɗin ɗakin Mamin da jakarta ke ajiye a wajen.
Ɗaukar wayar ta yi tare da kallon sunan Lily da ke yawo akan fuskar wayar , wani kalar tsaki ta ja tare da
ɗaukan wayar haɗe da faɗin ''Hello.''
''Yes dear, ba za ki shigo school ba, yau lectures ɗin Sadauki ne wallahi, ya kamata ki shigo, ten marks zai
ba da.''
Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce ''Okay on my way.'' daga haka ta katse wayar.
Mami ce ta shigo cikin ɗakin hannunta riƙe da tray ɗin dake shaƙe da pepe soup, sai kuma wani ɗan
bread daga gefen plate ɗin dake cikin tray ɗin.
''Daughter you're awake, zauna ki ci abinci, kin ji.''
Sai da ta yi ƙasa da kanta, dan har ga Allah ta ji kunyar ganin Mamin da abinci, kuma wai ita aka kawowa,
ita ta rasa ta ya ma ɗan iskan baccin da ta rasa dalilin yin sa ya kwasheta, dan ba ta san lokacin da baccin
ya sureta ba.
''Mami na ƙoshi, yanzu wai lectures za'a yi a school, idan na dawo daga school ɗin zan biyo kafin na wuce
gida.''
''Noo ta ya za ki tafi da yunwa, zauna ki ci kayanki kin ji.''
Murmushi kawai ta yi tare da faɗin ''Tom Mami na gode.''
Daga haka ta zauna ta fara cin pepe soup ɗin.
Ba ta wani ci sosai ba ta wuce ta yiwa Mami sallama tare da wucewa school ɗin.
><><><><><><><>
Zaune yake akan office chair ɗinsa, jikinsa sanye da wasu suits masu tsadar gaske sky blue color,
gemunsa na gyare tsaff da kyau, tsintsiyar hannunsa na ɗaure da agogonsa na Rolex explorer ll wanda
ya saba sanyawa fararen hannun na sa.
Wa ta Chinese Lady ce ta shigo cikin office ɗin, kayan dake jikinta shi zai ba ka tabbacin cewa ita ɗin
clearner ce.
''Good day Sir.''
Chinese ɗin ta faɗa da muryarta da yake na zallar Chinese.
Gyad'a kansa kawai ya yi tare da fara duba wasu documents ɗin da ta kawo ma sa tun safiyar ranar. Cikin
muryarsa da ke da ɗan ɓacin rai ya ce ''Kira min Manager's.''
Da ga haka ya cigaba da scrolling ɗin cikin apple computer ɗin dake gabansa, agogon hannunta ta danna
tare da yi musu magana ta agogon, sannan ta fita daga cikin office ɗin Hydar ɗin.
Turo ƙofar office ɗin aka yi, dukkaninsu suka shigo atare jikinsu sanye da baƙaƙen suits dake ɗauke da
logo ɗin companyn.
Zama suka yi a wajen da suka saba tattaunawa a office ɗin nasa, sannan kuma a hankali ya fara magana.
''Mai ya faru da 500 billion ɗin da suka fita last upper month?."
Shiru suka yi na ya'n daƙiƙu sannan Manager ya fara cewa ''An siyi business jets ne saboda yiwa
mutanen wasu ƙasashe delivery.''
''Eh haka ne Sir.'' Assistant manager ya amsa da hakan, kallon wasu daƙiƙu ya yi musu tare da faɗin ''Ina
jets ɗin suke?."
Ajiyar zuciya Manager Yhu ya sauke haɗe da faɗin ''An yi banning compayn daga ƙere-ƙere.''
Wani kalar baƙin ciki ya haɗiya sannan a hankali ya ce ''10 million will be deducted daga cikin albashin
ku, har sai kun gama biyan 500 billion ɗin, and no more allowances, daga yau na yanke wannan, next
time kuyi abu ba tare da kun shawarce ni ba.'' daga haka ya tashi ya fice daga office ɗin, suma suka bi shi
jikinsu babu ƙwari.
Ko da ya fito direct basement ya nufa tare da ɗaukan motarsa ya bar compayn gaba ɗaya, ya nufi hanyar
gidan nasa.
<><><>><>><>>><><>
A school ɗin ma da ƙyar ta samu ta iya yin lectures saboda baccin da take ji, around 4pm suka fito daga
cikin school ɗin, duk da ba ta wani biyewa Lilyn ba ta dawo gidan Mamin.
Sosai ta hana idanunta bacci ta taya ya'n aikin gidan aikin bayan sun sanar da ita Mamin na kwance tun
bayan fitarta.
Sai ƙarfe tare ta dawo gidan nata, shima kamar jiya haka ta tarar da pizza da ice cream akan dining table
ɗin.
Murmushi ta yi mai kyau dan na jiya ma mantawa ta yi ba ta tambayi Salimah wanda ya kawo ba, amma
ta na gani ta san wannan aikin Abbinta ne.
Yanka ɗaya kawai taci ta ji gaba ɗaya ya gimsheta, hakan ya sanya ta tashi a hankali ta nufi hanyar
ɗakinta dan wani kalar bacci ne a idanunta.
Ko wanka ba ta iya yi ba balle cire kayan jikinta, tare da abayar ta kwanta bacci mai daɗi ya sureta.
Kwance yake yana kallon yadda take baccinta hankalinta kwance, he's missing her badly, ya na son ya
ƙara kasancewa da ita, ko wannan kukan na ta da take, missing komai na ta yake.
Wayarsa ce ta yi ringing hakan ya sa shi kallon wayar domin ganin wanda ke kiran na sa, ganin Amir ne
ya sanya shi ɗaukan kansa ya na mai maida hankali wajen kallon laptop ɗinsa.
Sai da Amir ɗin ya jera ma sa miss call kusan guda uku sannan ya ya bi kiran na sa.
Ring biyu wayar ta yi Amir ɗin ya ɗauka.
''Assalamu alaikum Man." Amir ya faɗa daga kwancen da yake shima
Sai da ya ɗan ja wa Amir ɗin aji kaɗan sannan ya ce ''Wassalamu alaykum Dude.'' Hydar ya faɗa ransa
aɗan ɓace.
''Mai na maka, da idan na kira ka ba ka ɗagawa?, ko ka fara shaye - shaye ne?.'' Amir ya iddashe
maganar tare sakin dariya kaɗan.
Wani kalar haushi abin ya ƙara bawa Hydar dan ya tsani a masa laifi kuma a ɗinga ma sa dariya.
Cikin Wani kalar murya ya ce ''You're mad Amir, how could you?, you spoiled all my plans on that girl
Amir, ka ɓata komai Amir, wallahi idona idon ka a Nigeria ba zamu kwasa da daɗi ba.''
Wani dariyan Amir ya ƙara kwashewa da shi tare da faɗin ''Ka yi, ko ba ka yi ba?."
Wani ɓakin cikin Hydar ya haɗiya tare da faɗin ''That's not your business."
Da ga haka ya kashe wayar na sa.......
''Ya Ubangijina ka basu daman share."
Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟
Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 😂😂
*THE REGRET*
PENDING AMARYA CE ✍️
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
The Noble Writers Team.
**Pending Amarya 47**
What goes around comes around ⏮️⏩
Try to be a good father to your children not a cowed 🤍 🫧 🤧
Not edited 🌟💔🥹
****
Wani dariyan Amir ya ƙara kwashewa da shi tare da faɗin ''Ka yi, ko ba ka yi ba?."
Wani ɓakin cikin Hydar ya haɗiya tare da faɗin ''That's not your business."
Da ga haka ya kashe wayar na sa.......
After 2 weeks.
Sosai ta maida hankalinta kan lafiyar Mamin, dan yanzu kam baccin da take yawan yi ya ɗan sake ta, ta
na ɗawainiyya da ita sosai.
Yau ɗin ma kamar kullum ta shirya cikin wani dark purple color hijab, sannan ta ɗaura da wani farin
classic booth white color, sai kuma wani white designer bag na companyn dior.
Wayarta na hannunta ta fito tare da zama akan kujerar dinning ɗin ta na mai ɗaga tafasasshen madarar
da ta saka Salimah ta dafa ma ta haɗe da kaninfari.
Ta ji daɗinsa sosai hakan ya sanyata shan kusan rabin mug ɗin, sannan ta fice daga gidan.
Sai da ta biya gidan Mami ta ga lafiyar jikinta wanda Alhamdulillah ta samu sauƙi sosai, sannan ta wuce
school.
Bayan an gama lectures ɗin ma Lily ce ta nemi rakiyar ta hakan ya sanyata tashi haɗe da bin bayanta
suka bar school ɗin acikin motar Lilyn.
Basu zarce ko ina ba sai gidan Lilyn, ba ta iya cin komai ba in banda wani milk shake da ta gani akan
bedsides kawai ta ɗauka ta sha tare da ɗan kishigiɗa.
''Ahhh, i just dey wonder your situation OOO, anya ba ciki ne dake ba?." Lilyn ta faɗa tare da kanne ma
ta ido ɗaya.
A zabure ta miƙe sannan kuma ta koma ta zauna tare da faɗin ''Ke kika yi min?, ni mai nayi ma da zan yi
ciki.'' Liyanar ta faɗa a rarrabe.
Wani kalar dariya Lily ta yi tare da faɗin ''Wallahi you're very funny, ko da ace Hydar dutse ne , ba zai
taɓa escaping hanyar da na sa ki ba.'' ta yi maganar tare da ɗaukan wani magani ta na mai watsawa a
bakinta.
Wani tsaki Liya ta ja tare da faɗin ''Your hanya wey lead me to hell, ni na ƙara ɗaukar shawararki over my
dead body.'' ta ƙarashe maganar tare da kunna datar ta.
''Jezz!, gist me wetin happen babe.?'' Lily ta faɗa tare da matsowa kusa da Liyanar.
A taƙaice ta faɗa ma ta duk abin da Hydar ɗin ya mata har da wani ɗan kukanta ta ce ''Lily if you see the
kind wahala wey that guy give me, ba za ki so na zauna a gidan ba wallahi.''
Wani kalar ajiyar zuciya Lily ta sauke tare da faɗin ''Then leave, kar ki saka kanki cikin rayuwar da ba za ki
iya ba.'' Lilyn ta ƙarashe maganar tare da shafa bayanta.
''Lily i can't leave him, kin san ina son shi, na tsani kaina idan na tuno rashin mutumcin da na yi masa, Lily
I'm dying wallahi, idan da gaske ne ina da ciki, da sai na fi ko wace ya' mace sa'a a duniya.'' ta ƙarashe
maganar tare da ɗaukan wayarta da jakarta ta na mai miƙewa.
''Where are you heading to.?" Lilyn ta faɗa tare da ta shi tsayen ita ma.
'' To the hospital.'' ta faɗa tare da zira slippers ɗinta.
''Let's confirm it first before taking any action babe, ƙila period ɗinki ne ya zo da hakan.''
''Noo Lily na fi tunanin cewa cikin ne, dan yau wata ɗaya da sati uku da ban ga period ɗina ba kenan.''
Ajiyar zuciya Lilyn ta sauke tare da nufar kan standing mirror ta ɗauki mukullin motar ta suka fi ce daga
cikin gidan.
After 5 hours 🦚🌟
Ko da aka yi test ɗin kuwa result ɗin ya fito da cewa ta na ɗauke da cikin wata ɗaya da sati uku da
kwanaki biyar, wanda hakan ya ɗirar ma ta da farinciki da kuma aka sin sa, duba da yadda course ɗin da
take karantawa ya shaida ma ta da zafin haihuwa.
Daga hospital ɗin ma makarantar ta koma tare da ɗaukan motarta ta koma gidanta.
><><><><><>><>>><><
Zaune yake a makeken falonsa, hannunsa riƙe da wani book mac ya na duba kayan da suke out of stock
domin a fara ƙera sabbi, da ma wasu colors ɗin.
Wayarsa dake gefensa ne ya yi ringing hakan ya sanya shi kai duba wajen da wayar ta sa ke ringing ɗin.
Sunan Abbhu ya gani akan screen ɗin wayar hakan ya sanya shi ɗaukan wayar tare da karawa a
kunnensa.
''Assalamu alaikum Abbhu, ina wuni.'' Hydar ɗin ya faɗa ya na jiran amsar da Abbhun zai ba sa.
''Wassalamu alaykum, Son ya aikin.?"
''Alhamdulillah, Abbhu.''
''Daman na kira ne na sanar da kai ba kai kaɗai bane ba yanzun, you should come back home saboda
matarka, ka ji ni.?" Abbhun ya faɗa ya na mai jiran amsar da ɗansa zai ba sa.
Wani ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin ''Eh Abbhu daman am planning na dawo next month in shaa
Allah, ya jikin Mami.?"
''Okay, Allah ya maka albarka, jiki da sauƙi matarka na kula da ita sosai yadda ya dace, ta samu ƙarfin
jiki, dan karaya ce ta samu a wajen ankles ɗinta.''
''Mami really try gaskiya, Allah ya bamu lafiya ba ki ɗaya.''
''Amin son.'' daga haka suka yi sallama.
><>><><>><><>><>><>
Gidan Ammi kam soyayya tsakaninta da Abbhi ba'a magana kafin ta faɗi abu har an yi ma ta shi,
Rufaidhat yanzu babu dare babu rana kullum ta na yawon neman maganin infection wanda zai yi curing
ɗinta.
Ko ta kan girls ɗinta ba ta bi, dan so take ta samu ta tara dukiya ita ma a gidan.
Zaune suke suna yin break fast a katafaran dinning table ɗin na su, Ammi na sanye cikin wani kalar abaya
mai tsadar gaske, Abbhi na kusa da ita cikin wasu ƙananan kaya farare da suka yi ma sa kyau sosai, ya na
shan wani fruit salad da Ammin ta haɗa ma sa.
Cikin muryarta mai sanyi ta ce ''Yaya yaushe ne family meeting ɗin.?" Ta tambaye sa tare da k'afesa da
idanun, ɗago kansa ya yi a hankali, hakan ya basu daman haɗa ido da Abbhin, kanne ma ta ido ɗaya ya yi
tare da faɗin ''I think is today, why are you asking.?"
Sauke kanta ta yi dan har yau ta na mugun jin nauyin sa.
Murmushinsa ya yi mai kyau tare da faɗin ''Ki daina jin wannan kunyar Iki, shekaru kusan 27 da
kasancewar mu tare ba fa wasa bane, atleast said it out ki na son ganin Liyana, amma wannan noƙe -
noƙen ki daina shi." Ya yi maganar ya na mai ƙafeta da idanunsa.
Gyaɗa kanta kawai ta yi tare da cigaba da shan water melon juice ɗinta.
Tsaki da suka ji a wajen ne ya basu damar juyawa suna mai kallon Rufyn da take ta doka wata uwar tsaki.
''Hajiyata ke ba za ki shirya ba ne, ko mu tafi ne.?" Abbhin ya faɗa ya na mai kallon Rufaidhat.
''Wllahi Nabil ka na ba ni mamaki, wannan abin da kake ka na nuna min banbanci, wanda hakan sam bai
dace da kalar rayuwar da muka tsara ba kafin ya'r ƙunar baƙin waken nan ta raba.'' Rufaidhat ta faɗa ta
na mai kauda kanta gefe daga kallonsu.
''Kar ya dace ɗin mana, damanta ne ki barta ta dama, kema da daman ki ya zo kin fi kowa zaƙewa ai.''
Abbhin ya faɗa tare da miƙewa dan a rayuwarsa ya na mugun son ya ga ya haɗa faɗa.
''Haka ka ce.?" Rufy ta faɗa tare da ƙafesa da manyan idanunta.
''Tsoronki nake ji ai, Mamma ta so mu tafi, ke kuma Ikimat zauna ta fasa miki kai kin ji.''
Daga haka ya sanya kansa haɗe da fita daga cikin falon.
''Shegiyya karuwa, wadda ba ta zo da budurcinta gidan mijinta ba, mai halin akuyoyi.'' in ji cewar
Rufaidhat da ta tashi ta yi hanyar fita daga falon.
''Ammi idan ba ranar da na ci uban matar nan ba, ba za ta saurara da kiran wannan sunayen ba.'' Ily ta
faɗa zuciyarta na ƙuna.
A zuciye Ilyn ta bi bayan Rufaidhat da ta nufi hanyar fita a falon domin zuwa wajen Abbhi, ita ma Ammi
da saurinta ta biyo ta ganin kamar yarinyar ta fita a hayyacinta.
Cimma Rufaidhat ɗin ta yi tare da wani kalar hankaɗeta, Rufaidhat har ta sadaƙar za ta faɗi Abbhi ya yi
saurin riƙe hannunta dan kaɗan ya rage maƙogwaronta ya caki wani ƙarfe da shi ya raba parking space
da garden ɗin gidan.
Tare da janyota jikinsa, ''Mammah mai ya faru haka?, da za ki kasheta.'' ya yi maganar ya na tsare Ily da
idanunsa, ''Abbhi just let me, ka barni na koya ma ta hankali.'' ta faɗa idanunta na zubar da ƙwalla.
''Shut up, shiga cikin mota, matar ta wa za ki koyawa hankali, kamar wa ta sa'ar ki?, get in.''
Fashewa ta yi da kuka tare da shigewa bayan motar, ita ma Rufaidhat bayan ta shiga, sannan Ammi da
fitowarta kenan ta shige gaba.
><><>><><>><><>>><>><>><>><>
Bayan ta tashi daga baccinta sallah ta yi tare da yin miraja'a haɗe da azkar da ta sabawa kanta da su
ayanzu, sannan ta wuce kitchen suka fara haɗa breakfast ɗin da zasu sama cikin su.
Bayan sun gama karyawan ɗakinsa ta shiga, tare da goge shi tass haɗe da sanya turaruka masu ƙamshin
gaske, ɗakinta ta koma tare da shiryawa cikin wani abaya mai kyaun gaske, tare da sanya wani face mask
haɗe da saka