Advertisements
Chapter 31 Reading The REGRET by Dana sani Amarya BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

The REGRET by Dana sani Amarya

Author :  Dana sani Amarya Category :  Complete Novels

Chapter   31 / 39

90K to 93K   out of 116.5K words

bacci wanda sam Ammi ta haneta
akan sai ta tsaya ta godema Allah da ya bata dama na biyu a rayuwa ta cike taskes ɗinta .



Da ƙyar ta yi addu'an sannan ta koma ta kwanta wanda sai a lokacin cikinta ya ɗan ɗago wanda da alamu
dai yanzu ya ta so daga kwancen da aka sanya shi yin.




Sai a lokacin idanun Ammi ya sauka akan cikin dake jikinta sannan a hankali Ammin ta ce ''Kina zuwa
awo or you're taking it un serious just like your life.'' Ammin ta ƙarashe maganar tare da ɗan taɓa cikin
Liyanar.




Marairaice face ɗinta ta yi tare da faɗin ''Ammi please later bacci nake ji.'' ta ƙarashe maganar tare da
ƙoƙarin kwantawa.

''za ki tashi ko sai kin gane rashin lafiyar da kika yi nafila ne.?" Ammi n ta faɗa rai a ɗan ɓace.

Fashewa ta yi da kuka tare da ɗan dire ƙafarta sannan ta ce ''Ammi please nah, ɗan ya na lafiya ko yanzu
sai da ya buge ni manaa.'' ta yi maganar tare da share ƙwallarta.




''Alright magana ta ce ba za ki ji ba kenan har yau, tashi ki fice min daga ɗaki kafin na ɓata miki rai.''



Ammin ta yi magana cikin fushi.

''Ammi atleast ki tausaya min mana, yaushe nayi rashin lafiya na tashi, ko 48 hours ba'a yi ba amma
gashi ana ƙoƙarin haɗa min wani.'' Liyana ta yi maganar haɗe da ɗan turo bakinta.
Yunƙurawa Ammin ta yi kamar za ta tashi dan ta ga sturbborness ɗinta ƙaruwa yake ba raguwa ba,
hakan ya sanyata saurin ficewa daga cikin ɗakin dan sam ba ta jin wani alamun rashin lafiya a tattare da
ita.



Bigewa ta yi da mutum a hanyar ta na ficewa daga corridor ɗin guest room ɗin sannan a hankali ta ja
baya ta na ƙoƙarin komawa ɗakin Ammin.

Saurin jawota ya yi jikinsa tare da buɗe ƙofar da yake tunanin empty room ne ya yi saurin kulle ƙofar
tare da jinginata da bayan ƙofar.

Ɓare baki ta yi kamar za ta yi ihu hakan ya sanya shi haɗe bakinsa da na ta ya fara sumbatar ta, zaro
idanunta ta yi dan ganin Abbhinta ya fito daga toilet hannunsa riƙe da wani towel ya na goge jikinsa da
shi.




Ƙara waro idanunta ta yi sanadiyar haɗa idanunta da ta yi eye ball to eye ball da Abbhinta da ya yi saurin
juyawa ya koma toilet ɗin ɗakin.



Da dukkanin ƙarfinta ta haɗa tare da turesa, ƙara jawota ya yi jikinsa da sassarfa ya na mai rungumeta
tsam jikinsa, buh he can't feel that comfort of hug, saboda tumbin da ya ɗan tokaresa.

Saurin waro idanunsa ya yi tare da yi ma ta pointing cikinta da ya turo gaba sosai.

Ita dai ba ta biye ma sa ba ta sanya kanta ta fice daga cikin ɗakin, dan har ga Allah ba ta son Abbhin ya
ƙara tadda ta a wajensa.




Ya yi kusan minti biyar a wajen da ta bar shi sannan ya saki wani kalar murmushi wanda ya tsaya ma sa
iya laɓɓansa tare da shafa gemunsa zuwa bayan wuyansa sannan ya bar cikin ɗakin shima.




Dan shi kansa bai san mai ya kawo shi gidan ba, he just feel like ba zai samu nutsuwa ba har sai ya ganta,
ya ji ɗuminta.
Fitowarsa daga ɗakin ke da wuya ya kusa cin karo da Neneh da ke cikin shigarta na Lifaya , sai da ta
firgita ganin Hydar ɗin a gabanta, sannan a hankali ta dalla ma sa harara ta bi ta gefensa ta shige
backyard zuwa traditional kitchen saboda ganin abin da mutanen gidan ke dafawa na sadaka.

Shima Hydar wani kalar harara ya banka ma ta tare da raɓewa ya bi ta kusa da ita ya fice daga cikin
gidan, dan shi ya na mugun son ya ga ana jin tsoro a rayuwar sa.




Ko da ya isa gidan Mamin ko ina na gidan tsit, suma ya'n aiki na can backyard ana ta dafa abincin sadaka,
ya na zaune a falo ya ji ana wani kalar ƙwanƙwasa ƙofa kamar za'a ɓalla sa, sannan daga bisani ya fara jin
muryar Assultanah dake time ɗin har 10 O'clock na safiya ta yi.



Kuka take mai tsuma zuciya ta nufo falon, ganin Hydar a falon, shi ya sanya ta ƙara sakin wani kuka tare
da faɗawa jikinsa ta na sakin wani kalar kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, sannan a hankali ta fara
magana ''Yaya mai sa a ka binne ta ba tare da an jira ni ba.'' ta ƙarashe maganar cikin shashsheƙar kuka.



Sai da Hydar ya ɗan kalleta sannan ya ɗauke kansa tare da cire kanta daga jikinsa sannan a hankali ya ce
''Gidansu za ki je, sai ki shigar da ƙara.'' daga haka ya ɗauki wani Apple da ke cikin wani fancy basket
dake kan center table ya nufi part ɗinsa dake nan tsaf.



Tashi ta yi ta nufi hanyar gidan Nenehn, duk ya'mmatan na zazzaune suna hira har da Liya da suka sa ki
jikinsu da ita ana ta hira har Yusrah dake ta shishige musu.




Ko sallama ba ta yi ba ta shigo cikin falon ta na wani kalar kuka, ganin Liyana zaune ta na dariya
hannunta riƙe da wasu guava da Hydar ya sa aka kawo ma ta ɗazun ne ya sanyata suman tsaye tare da
kallon mutanen falon.
Wani kalar ihu ta saki wanda hakan ya ƙara janyo attention ɗinsu gabaɗaya tare da ƙafe Sultana da
idanu.



Ta mugun tsorata da ganin Liyanar a cikin gidan, dan sai da tayi suman tsaye na ya'n daƙiƙu sannan ta
dawo hayyacinta.



A na tsaka da shawo kan lamarin Assultanah Lily ta danno kai cikin gidan, a kiɗime ta fara addu'ar ta cikin
Greek Words dan a tunaninta Ghost ce, sannan a hankali a ka fahimtar da su.




Har a ka yi sadakan uku da Jiddahn ya faɗa ko ƙeyar Rufaidhat ba'a gani ba a cikin gidan, wanda Abbhin
ke sane da ita da hakan da ta yi, ita ma Mama Fatuh tun bayan zuwan su Sultanah da ta zo suka tafi da
Yusrah a ranar suka wuce Niger.




Aranar sadakan ukun kan duk yadda aka yi da Neneh akan Liya ta yi bakwai a gidanta ƙi ta yi ta na faɗin
cewa ''Kyan ya' mace gidan mijinta.'' a haka aka bar zancen Liyanar ta koma gidan Hydar ɗin da har ya
dawo da workers ɗin gidan.




Bayan one week ta koma school dake duk ya'n school ɗin sun san da tashin na ta hakan ya sanya ta ci
gaba da harkar gabanta kamar yadda ta saba.
HYDAR kam har wani kalar tsoron kusantarta yake kar ya zamana cewa sihirin dake tattare da kwanciyar
ta su ba ta karye ba.



Ammi kullum cikin addu'a take inda soyyayar ta da Abbhi sai daɗa linƙaya take, amma dake ance zaman
aure sai haƙuri ba za'a rasa abin da ke damun zuƙatan masoyan guda biyu ba.

Ɓangaren Neneh kuwa har yau cikin shige da fice take dan wajen gano waya'nda suka aikata wannan
lamarin ga jikarta, duk inda taje siffofin mutane biyu kawai ake ba ta amma ta kasa gane su waye su.




Zaune take cikin shigarta na wani simple abaya mara nauyi, sai laɓɓanta dake sanye da wani lipstick mai
ƙyallin gaske, kanta sanye yake da hula, hannunta riƙe da wani bowl mai ɗan girma da yake cike da
kayan cikin naman saa da ya ci uwar garlic.



Ta na ci ta na kallo a TV ɗin falon dan yanzu sam wayar hannunta ba ya damunta tun da cikinta ya kai 5
months and 2 weeks, har yanzu da ta kusa sati biyu da dawowa gidan bai cika wani kulata ba illa ya
tambayeta mai za ta ci a siyo ma ta ko a dafa mata.




Sanye yake cikin wani combat black color sai wani white designer plane shirt da ya ɗan kama jikinsa,
fuskarsa idan banda ƙyalli babu abin da yake fitarwa banda zallar rich glowing skin.




Ƙarasa sukowa ya yi daga stairs ɗin tare da samun waje ya zauna kusa da ita, sidda kanta ta yi ƙasa dan
wani kalar nauyinsa take, ga soyyayarsa dake mamayar zuciyarta.




Waro idanunsa ya yi ganin ƙaton plastic bowl ɗin dake hannunta cike da kayan cikin da sai a iya amfani
da su na kwana uku zuwa huɗu.
Amsar bowl ɗin ya yi daga hannunta tare da tallaɓo kanta ya ɗaura akan kafaɗarsa, sannan a hankali ya
fara faɗin ''I know it will be a little bit difficult for us to live like a couple, duba da yadda haɗuwar mu ta
faro da kuma yadda muka yi treating junan mu a gidan nan, Liyana!." Ya ƙarashe maganar ya na mai
kiran sunanta tare da yin yawo da hannunsa akan gashinta.



Cikin sassanyar muryarta mai daɗin sauraro ta ce ''Na'am Yaa Alih.'' ta ƙarashe maganar ta na wasa da
hannun abayarta.



Sai da ya ɗan jinginar da kansa tare da shafa fuskarsa izuwa gemunsa sannan ya ce ''Ba zan iya cewa i
can't accept you a matsayin matata ba, duba da yadda kike ɗauke da cikin da nayi sanadinsa, and ni ba
zan ba ki haƙuri a kan wani laifin da yake a matsayin gyara na yi ba, soo can we friends, friends with
benefits........




Jiya banda data Wallahi kuyi haƙuri 😂




Manage please 💎🥀



Mutuwa kan kawo canji
''Ya Ubangijina ka basu daman share."



Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟

Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 😂😂



*THE REGRET*




PENDING AMARYA CE ✍️




JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION



The Noble Writers Team.




**Pending Amarya 54.**



What goes around comes around ⏮️⏩

Every ending is a new beginning 🌕
even if the heart disagrees.✅🌕 🤝🦋



🤍🫧🤧
Not edited 🌟💔🥹



****




Sai da ya ɗan jinginar da kansa tare da shafa fuskarsa izuwa gemunsa sannan ya ce ''Ba zan iya cewa i
can't accept you a matsayin matata ba, duba da yadda kike ɗauke da cikin da nayi sanadinsa, and ni ba
zan ba ki haƙuri a kan wani laifin da yake a matsayin gyara na yi ba, soo can we friends, friends with
benefits.'' ya ƙarashe maganar tare da ɗage girarsa guda ɗaya yana mai miƙa ma ta hannunsa alamun
shaking.
Sidda kanta ta yi daga kallonsa sannan a hankali ta ɗago manyan idanuwanta tare da faɗin ''Babu duka
babu zagi, only friends, and banda ranƙwashi.?" Ta ƙarashe maganar a ɗan shagwaɓe.



Matsowa ya ƙara yi sosai kusa da ita lips ɗinsa ya na brushing na ta, idanunsa a cikin na ta in a
whispering voice ya ce ''Yeah of course, amma in one condition.'' ya ƙarashe maganar ya na bata wani
light kiss a lips, sannan ya ɗora da faɗin ''Duk abin da na ce kiyi za ki yi shi, and when I want something,
dolen ki ki bani, are we good to go.?" Ya yi maganar ya na ƙara matsowa kusa da ita.

Gyaɗa kanta ta yi sosai kafin ta yi maganar da take da niyyar yi ya haɗe lips nasu trying to get what he
wants from her, sannan ya sunkucheta ya nufi ɗakinsa da ita, they made love.




Ita ta san ta na son Hydar, soyayyar da ko kwatan shi ba ta nunawa ƙaninsa ba, babu abin da zai ma ta a
duniya da za ta ji tsanar sa a duniya.




Da ƙyar ta tashi ta mayar da kayanta haɗe da ƙoƙarin barin dakin na sa amma ya hanata.



Kwance suke waje ɗaya kanta na kan kafaɗarsa jikinta gabaɗaya na mata wani kalar laushi, hannunsa
ɗaya na shafa yalwataccen gashin kanta, cikin wani kalar murya mai sanyi wanda ke ƙara jafa ta a cikin
wani yanayi ya fara magana ''Ina kike son muje honey moon?." Ta tsinci muryarsa a cikin kunnenta.



Gyara kwanciyarta ta yi a jikin na sa tare da ɗan ɗago kanta ta na mai duban kyakkyawar fuskarsa,
sannan a hankali ta ce '' Just suggest, abin da kake so nake so ni ai.'' ta yi maganar ta na wasa da
kwantaccen gashin dake ƙirjinsa.

Sosai ya ji daɗin kalmar ta sannan a hankali ya ce ''From Saudi Arabia, sai mu wuce China and
Switzerland are you okay with that.?"



Gyaɗa kanta kawai ta yi sannan ya ƙara gyara ma ta kwanciyya a jikinsa bacci mai daɗi ya yi awon gaba
da su.
Da sassafe ta tashi ta nufi ɗakinta ganin ba ya cikin ɗakin kuma bai tashe ta ba, bayan ta idar da sallarta
ma tilawarta ta cigaba haɗe da yin azkar sannan ta fito kitchen ta kamawa Salimah girki.




Cous cous ne sai pepe soup tare da bread suka dafa, sai coffee da ta haɗa ma sa a coffee mixer ta ajiye a
kan kitchen island ɗin.

Within 2 mins ya shigo cikin gym wears ɗinsa hannunsa riƙe da bottle water da kuma hanky.



Already daman bayan ta gama girkin ɗakinta ta shige tare da yin wanka ta shirya cikin wide leg trousers
ɗinta (palazzo) sannan ta ɗora da wani babban T shirt Wanda zai sa ka cikin jikinta balance sosai, sannan
ta ɗora simple hula a kanta tare da saka slippers ɗinta ta fito falon.



Ta na zaune ya shigo cikin falon, murmushi ya sakar mata mai kyau sannan ya zauna akan ɗaya daga
cikin kujerun dake falon.



''Girlfriend, you look beautiful today, irin wannan kyau haka kamar Zebra.''

Ya yi maganar tare da amsan coffee ɗin da Salimah take miƙo ma sa.

She just smiled at him, sannan ta ce ''Yaya ina kwana.'' ''Lafiya lau, ki shirya yau zamu fita siyayya.'' ya na
faɗin hakan ya haura sama domin shiryawa.



Tun da ya shige ɗakinsa ta na cikin falon babu inda ta motsa sai ma Tvn da ta ƙurawa ido.



Sanye yake cikin wani plane designer t shirt black color, sai wani _Saint Laurent_ jeans black color,
ƙafafunsa sanye cikin wasu Fendi slippers, sai car key ɗinsa a hannunsa.



Har ya ƙaraso wajen da take ba ta san da isowansa ba , ita dai kawai ba ta ma san mai yake damunta ba.
Saitin fuskarta ya saita tare da kaɗa ma ta car key ɗin hannunsa, a firgice ta dawo hayyacinta tare da
sakar ma sa murmushinta mai kyau.



''Je ki shirya, and don't keep me waiting.'' ya yi maganar a taƙaice tare da ficewa daga cikin falon.




A hankali ta tashi tare da nufar saman stairs.




Direct ɗakinta ta shige tare da sanya kimono akan shigarta, sannan ta ɗaura da wani babban mayafi
wanda hakan ya bawa shigarta wani kalar kyau na wuce misali.



Slippers ɗin ƙafarta ta bari ba ta canza ba sannan ta fito daga gidan ta na mai yiwa Salimah sallamah.




A hankali take takowa har ta ƙaraso cikin motar na sa.



Tayar da motar ya yi tare da barin cikin unguwar gaba ɗaya, shiru ne ya ratsa cikin motar, kowa na ta
saƙe -saƙe a cikin zuciyarsa.



A hankali ya kamo zara-zaran fingers ɗinta ya na kallon yadda suke a cike, farare tal dasu gwanin ban
sha'awa.



Jin lallausan palms ɗinsa a kan hannunta ne ya sanyata ɗagowa da sauri ta na mai kai dubanta kan sit ɗin
nasa.
''Dubi fingers ɗinki kamar na horror movies, Sam ke a rayuwarki idan ba kiyi ƙazanta ba ma ba kya jin
daɗi ne.?" Ya yi maganar da ɗan sauri tare da danna horn a dai-dai wani kantamemen building.




Bayan mai gadi ya buɗe gate ɗin, wajen parking space ya nufa tare da yin parking ɗin motar, a babban
parking space ɗin gidan dake jere reras da luxury rides.




A hankali ya fito daga cikin motar, ita ma jiki duk ba ƙwari ta sauko tare da zagayowa wajen da yake
tsaye.



''Kin san Allah kar ki min ƙauyanci dan naga ku mata da kun yi aure duk wayewarku ƙauyawa kuke
komawa, You better behave yourself.'' Ya yi maganar tare da fara tafiya towards the building.




Walking slowly ita ma ta bi bayansa trying to engage with her late courage.

A hankali ta ƙaraso har ƙofar entrance ɗin da yake tsaye yake danna door bell.

Bayan an buɗe musu ƙofar a hankali suka shiga cikin parlourn da sai tashin ƙamshi yake, wata ya'r
budurwa ce zaune kan cushion ɗin falon cikin wasu pyjamas white color ƙafarta sanye da wani soft
slippers na bacci, wanda da dukkan alamu daga bacci ta tashi.



Ɗago idanunta ta yi da kyau ta kalli yarinyar dake zaune wanda ita ma a dai-dai lokacin ta ɗago ta kai
dubanta wurin da suke tafe.



Waro idanunta ta yi ganin Papi a gabanta wanda hakan ya sanyata cilli da wayar hannunta da gudu ta na
mai rungume shi.



Unexpectedly ya ji saukar mutum a jikinsa wadda sam bai lura da wanzuwar ta ba a falon.
Shi ma Waro idanunsa ya yi da kyau tare da faɗin ''Ahh Marwa, kar ki karya ni mana.'' ya ƙarashe
maganar tare da janyeta daga jikinsa.



Murmushi wadda aka kira da Marwa ta yi tare da faɗin ''Papi na yi missing na ka sosai, for almost six
years we didn't see each other, Kuma you're expecting me not to hug you.?'' ta ƙarashe maganar ta na
murmushi mai nuna alamar zallar zumuɗi, tare da jan hannunsa ta zaunar da shi kan kujerar.



Ita sam ba ta lura da Liyanar da take tsaye a kumbure kamar yeast ba, ta matsa daga wajensa tare da
nufar hanyar kitchen domin kawo masa abin sha.

Cikakken hips ɗinta ya bi da kallo tare da mayar da kansa gefe wanda hakan ya sanya idanunsa da na
Liyana haɗuwa ta na tsaye wajen da ya barta.



''Ke azumin zama kike ne da ba za ki zauna ba.?" Ya yi maganar ya na ƙurawa kyakkyawar fuskarta ido.



Ɗauke kanta ta yi tare da juyar da shi gefe wanda hakan ya yi dai-dai da isowar Amir cikin living ɗin,
jikinsa sanye da wasu native dress masu kyaun gaske.



Amir na mata magana hakan ya sanyata yin murmushi suka gaisa sannan ya yi mata insisting zama kusa
da Aliyun sannan ta zauna.




Tafe ta ke hannunta riƙe da wani serving tray mai kyaun gaske, ɗauke da kayan sha da na motsa baki.



Sannan a hankali ta ajiye tray ɗin tare da kallon Liyana dake kusa da Papi da idon mamaki.

''Who's she Aliyu.?" Marwa ta tambayi Hydar idanunta a kan na Liyana da jin tambayar da ta ke ma
Hydar ɗin ya sanyata ɗago da kanta ta kalli Marwa ɗin.
HYDAR dake ta daddanna wayarsa ne ya ɗago tare da kallon Marwa kafin ya yi magana har Amir ya riga
shi da faɗin ''Don't you dare create any problem, kina dai jina ko.?" Ya yi maganar tare da dailing wayar
Umminsu ya na mai sanar ma ta Aliyyu da matarsa sun iso.



Babu jimawa Ummi ta ƙaraso falon cikin wani simple Egyptian abaya.



Sosai Ummin ta yi farincikin ganin Liyanar da Hydar.

Ba su fi mintuna talatin ba Hydar ke sanar ma Ummi zasu tafi, sosai ta haɗa ma Liyana turaruka da wasu
kayan sha'anin mu na mata.

Marwa dai ta kasa magana dan ita a tunaninta wajenta ma Hydar ɗin ya zo.



Bai ƙara kallon

31 / 39